← Book details Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 18

Sashe 5

Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakinta Abba yake
yagama karyawa ya shirya zai tafi aiki, ummi ta
kalle shi tana son tambayar zuwa gidan umma
tna jin tsoro.

Ya dubeta kamar kina son cewa
wani abu ko?

Ta ce am dama inaso inje gida in
gaida su umma, yajuyo yadubeta suka hada ido.

Gabanta yafadi, ta sunkuyar dakanta, yace a'a
tadaga ido takalle shi, wani kunci taji aranta, ga
matanshi nan yini take garari a layi bata ko
tambaya amma ita ta tambaya shine ma zai
hanata?

Ya dauki jakar shi, ta mike ta rakashi
har tsaka gida tare da yi masa addu'ar Allah
yatsare, yini tayi da takaici dama haka mata suke
ji in an hana su zuwa anguwa?

Daran ranar zai
koma ga bishira don haka bata san dawowarshi,
tana kwance kan doguwar kujera tana karanta
littafin hausa ( naleka muku kozanga sunan
littafin amma bangano mukuba) kamshin turaren
shi ne yasa tasan yashigo, don littafin yadauki
hankalinta.

Ta amsa sallamar daya sake yi tare
da mikewa zaune, yana sanye da kananan kaya
tamkar wani dan saurayi, yayi kyau a idonta
kamar ta rungumeshi.

Tace sannu dazuwa yace
yawwa, dauko mayafinki muje tazura takalma
bayan tagoge sannan ta ciro mayafi, yace a'a
dauko hijabin.

Ta maida ta dauko hijabi tafito
sannan yakulle kofar, saida suka fita waje sannan
yadubeta, hannu rabbana zakije musu?

Tace yaya
Abba toni bani da kudi ai.

Sukabi ta wani super
market suka sai sabulai da turare, akafa suke
takawa sannu ahankali suka jero duk da cewa
bawata hira suke ba, Abba ne yake amsa waya
jifa-jifa na jama'a masu sonshi.

Tun daga nesa
suka hangi mahaifansu suna cin abinci a inda
suka saba.

Alhaji babba dakarami.

Cikin zumudi
ummi ta ce, yauwa gasu alh.

Abba yaje haka
zakije musu da rawar kanki ko?

Cikin shagwaba
tace, wanne rawar kai nayi toni yaya Abba?

Yace,
na gani kinayi kamar zaki kwasa da gudu, kafin
tayi magana sun iso gurin dukkansu suka zube
akan tabarmar daga gefe.

Abba ne yasoma cewa,
sannunku alh.

Alh.

Yace, a'a kune?

Alh karami
yace, uwata harda ke?

Tace, eh ina yininku?

Sukace lpy lau.

Alh.

Karami yace, uwata kunanan
lpy ba wta matsala ko?

Ta ce, ba komai alh..

Yace to Allah yyi maku albarka, ya azurtaku da
'ya'ya ma su albarka wadanda kuma zasu biku.

Abba yace amin suka hada baki da Alhaji babba,
alh babba yaci gaba da cewa, Abba ya hakurin
shirmen ummi kuma?

Ince dai bawata matsala?

Abba yakalleta mun gode Allah alh, amma bwata
matsala, ummi tamike dazumudi bari a karasa.

Tun daga soro take kwala ma umma kira.

Umma
tce, A'a muryar wa nake ji haka?

Ummi tashigo
da gudu ta cakume umma, tsohuwa tafito tana
fadin lale.

Dakin tsohuwa tasoma shiga suka
gaisa sannan tadawo dakin umma, sun gaisa
umma tasake mata nasiha, ummi tace umma ni
matsalata daya matarsa.

Kullum saitayi min
habaici tana zagina wata rana r harda kawayentaRFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 9 ZURFIN CIKI book 4 part 9 Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:54 Ita ko bishira gidan su umman bashir ta tafi dakuka wiwi, tace Abba yamata duka takan sun taka hakkinta sun fita ranar girkinta.

Tayi magana ummi ta mata tsaki shi kuma yazo yazo yahauta da duka, umman bashir tace duka!

Duka akan ummi?

Tabdi, tashi muje gurin wadanda suka daure masu gindi.

Umma na kokarin shiga daukin alhaji taji sallamarsu sama-sama, gabanta yafadi ta amsa tare da dawowa baya.

Sahura tace to suwaiba, abinda kuka shiirya yasoma tasiri.

Abba yayi wa bishira shegen duka saboda 'yarku, umma tace haba sahura, yaya ki ke irin wannan maganar?

Mu ne zamu sa Abba ya cutar da iyalinsa?

Sahura kiyi nazari.

Alhaji yafito, me yafaru ne ni kejin hayaniya suwaiba?

Umma tace, oho.

Sahura tace, bishira fada musu.

Nan bishira ta shaida masu yanda ta tsara ma umman bashir, alhaji yadaga waya yakira Abba, Abba yana dagawa alhaji cikin zafi yace Abba maza kazo yanzun duk in da kake.

Abba yace to alhaji, ummi ta mike zan bika tsoro nake ji ni daya, cikin zafin rai yace abin daki ke tsoro ya cinye ki, ya fita fuuu.

Cirko-cirko ya same su a tsakar gida, sai muryar sahura kake ji tana rashin mutunci.

Alhaji karami yadawo gidan shi sai ya jiyo muryar sahura a can gidan, ya nufi gidan don haka kusan tare suka shiga gidan da Abba.

Alhaji cikin bacin rai yafada Abba da fada, abba bai katse shi ba har sai daya kai ga tambayarshi cewa me yasa yayi mata duka?

Yace, banyi mata duka ba alhaji marinta kawai nayi, umma ta ce mari kawai ne Abba?

Alhaji karami yace, to kan wane dalili ma zaka mare ta?

Abba ya koro musu komai, ya kara da cewa, wannan har zata ce an mata tsaki, zata yi duka ni wane irin zagi ne bata min ina hakura darajar iyayenta?

Ya nuna ta, wallahi in kika kai ni bango zaki koma gidanku don bazan iya ba na gaji, nan kuma su alhaji suka shiga bashi hakuri.

Ita kuma suka bata rashin gaskiya, sai dai duk da haka umma tai masa fadan kada ya sake daukan ummi ranar girkin bishira ya fita da ita, yace to.

Umman bashir taja bishira zo muje ai dama nasan baza suga laifin 'yar su ba.

To wllh marin da yamiki ki tabbata bashine.

Ko nan da yaushe ne ki rama shi kan ummin, in ba haka ba duk da banice uwar data haife kiba sai na tsine miki.

Alhaji karami yace, to katuwa mara lissafi, ke dai kinji haushin rayuwarki, to ki sani duk randa ta rama duka akan ummi ni kuma akan ki zan rama wa ummin inga ta tsiya.

Alhaji babba yace, kada kai ma kazama su mana aminu.

Tsohuwa tace, gskiya ne, in har tazama silar dukan ummi itama sai ya mata taji.

Umma tace, a'a duk abin ba zai kai haka ba insha Allahu, kai dai abba kayi ta hakuri sannan kadaina sa hannu kana dukan mace.

Yace, umma dukana fa tayi, sai kace wani soko zan tsaya mce tna dukana, umma tace, to ai tace ummi taje duka, yace ummin 'yarta ce?

Alhaji yace, tafi gidan kahadasu kayi masu nasiha, Abba yace ai baza ta tsaya ba, wannan yarinyar fa sai dai addu'a ni in nagaji kawai hakura za ayi, umma tace bana son jin wannan zancan, alhaji karami yace ai gskiyarshi ne, shi yasan irin zaman dayake da ita.

Alhaji babba yace, ai kuma darajar mahaifinta za aduba, da mutuncinsa, Abba yace ai dama alhaji ni banda mahaifinta da tuni nayar da kwallon mangwaro na huta da kuda.

Umman tace je ka gida Allah ya kyauta.

Nan dai ya musu sallama yanufi gida.

Ummi da gske tsoro ne da ita, da rana in ba kowa bta damuwa, amma da dare tfi son tdinga jiyo motsin bishira koda habaicin dta sabayi mata.

Soro taje ta tsaya tana yi tana leka waje, can ta hango bishira, don haka takoma daki ta kullo kofa aranta ta ce kada tazo tayi min duka.

Ummi tna jiyota lokacin data shigo tana cewa wllh kan yarinya zan rama marina, wannan dole ne koba dade saina ramashi.

Abba kan bai nufo gida ba, shagonsa ya wuce lokacin goma ta gota, yaran sunyi shirin tafiya, don haka ya amshi makullin ya shiga shagon saman teburin da suke yin yanka da guga ya hau ya zauna.

Tagumi ya zuba hummu biyu tare da sauke wata ajiyar zuciya mai karfi, me yasa ummi ta furta kalmar data tuna mishi cewa bata sonshi?

Sakankancewa dayanda ummin kenuna mishi yasa shi jin kamar sonsa take ashe dai shi yake shermenshi.

Ya tuno wani labari yaya tabaji na wani mutum da aka ara masa mata wadda bata sonsa, tazo tazauna dashi tsawon shekaru kuma tayi masa biyayya matuka.

Ga 'ya'ya sun haifa yaran sun yi girma sosai, suma sun zama magidanta, sai wata rana mutumin nan suna hira da matar, yace oh, wance dafa ba kya sona, yanzun gashi harmun tsufa kin manta dawata kiyayyah.

Tadubeshi, inji wa yace maka na manta?

Biyayya kurum nake maka amma har gobe bana sonka.

Abba yajinjina kai, lallai dole ne ya nutso, yadaina tunanin ummi tana sonshi kokuma zata soshi, shidai da kaddarar sonta tafada mishi sai yayi ta addu'a Allah ya bashi hakurin jure zama da ita ahaka.

Bai san adadin lokacin daya dauka awaje ba kuma baisan adadin tunanin dayayi ba.

Daga karshe yarufe shagon yanufi gida.

Ganin yanda garin yayi tsit shine yasa shi kallon agogon hannunshi, daya da minti shabakwai, lallai lokaci yatafi.

ZURFIN CIKI book 4 part 10
ZURFIN CIKI book 4 part 10
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:55
Yanufi dakin bishira aranshi yce da wanda yake
kinka gara mai sonka ko mahaukaci ne.

Gdon
yahau tagefe ya kwanta suka saka muhibba
atsakiya, ummi kuwa duk tsawon lokacin nan
tkasa bacci domin bata ga shigowarshi ba.

Idonta
biyu har sai daya shigo ta leka ta windo tana
kalloshi har yashiga dakin bishira ya rufo kofa,
sannan ta kwanta tare dayin ajiyar zuciya.

A fili
tace ina ga fa har dani alaifin nan, amma bari
gari yawaye inba shi hakuri durkusa ma wada ai
ba gajiyawa bane.

Bishira tafarka cikin dare taga
Abba kwance hannunsa na dama dore kan jikin
'yarsu, ta tsura mishi idanu tana son mijinta
sosai.

Ban dahaka data kaishi koto ya bata
takardarta koda mahaifinta xaimata baki
sanadiyar haka, amma shi yanzun yadaina sonta.

Takai hannu tadora a kumatunshi, ahankali
yabude idanu, suka kura majuna ido yace bishira
me yasa kike yin abinda zai samu mu samu
sabani bayan kinsan sone ya hadamu?

Idanuwanta suka kawo ruwa, Abba dane ka soni
kaji dani har alokacin ina ganin ba Wata mace
data kai ni dacen gwanin iya soyayya.

Amma
yanzun duk ka zuba ni a kwandon shara har kana
marina saboda ummi.

Ya ce, a'a ba sbd ummi na
mare kiba, saboda kin dukeni ne amma kiyi
hakuri.

Banason kina zubar da kanki a gurinta,
yawan fadanku zai sa raini ya shiga tsakaninku,
ni kuma ba zan so ta rainaki ba.
Chapter 5 · 0% Book details