← Book details Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 18

Sashe 7

Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dazai tafi
masallaci yske lekawa yaga IKI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 13
ZURFIN CIKI book 4 part 13
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 02:05
shikenan yanyun bata dawani aji agurin Abba
ummi da tsoron allura sam taqi tsayawa jiya ma
don agalabaice take Nurse din tace ke dai
shagwaba ta miki yawa A ce allura ma kin kasa
tsayawa kefa mace ce Wata rana ma haihuwa
zakiyi ummi fa taki tsayawa nurse tazo tace ma
Abba taki tsayawa abba yaleka dakin allura
menene haka ummi tsoron alluran ki yayi yawa
kitsaya mana Tadube shi fuska a shagwabe ya
Abba dazafi nikam na hakura da allurar nan Abba
ya shiga dakin ya kalli nurse din zo kimata ba
zanyi asarar kudina ba Ummi bata ankara basai
jinta tayi atsakiyar kirjin Abba shi kanshi sai jin
wani abu yayi yataso daga tafin kafarshi zuwa
tsakiyar kanshi Har yayi baya dasu tamkar zasu
fadi to bare ummi wadda jikin nata ya dauki rawa
Ya kalli nurse dinda idanuwanshi wadanda suka
canza kala nan da nan zo kiyi mata Yadaga
hajabinta tare dazame zanin daidai inda za ayi
mata allurar shigar allurar ta saka ummi cewa
wash tare da sake makalewa jikin Abba Don kuka
tasaka wanda daga jinshi kasan shagwaba ce
zalla ya lumshe ido lokaci daya ya kuma budesu
nurse din tace kai ke kam kin cika shagwaba
Abba ya dora yatsunshi guda adaidai gurin da
akayi allurar yana murza mata tare da rada mata
'sannu' akunnenta Rekicewa tayi sannan ta
kwace jikinta daga gare shi wani yanayi ta tsinci
kanta mai girgiza bawa Ya sauke ajiyar zuciya
sannan yace mu tafi suna cikin mota dukkansu
sunyi shiru Abba kasala ce da muradin matar shi
yasa shizama hakan Ita ko ummi mamakinta ba
yau Abba yasoma taba jikinta ba can baya yasha
rike ta yazane ta, yasha rungumeta ayi mata
allura, bata taba jin irin abinda taji yanzun ba Ta
jingina da kujera tare da lumshe ido sai take ta
tuno yanayin dataji lokacin daya mannata
ajikinshi.

Tsayawar motar ne ya sata bude
idanunta, azatonta gida suka zo,sai taga ashe
gurin kayan kwalama ne Ya kalleta, ina zuwa Ya
fita ya nufi zuwa ciki jim kadan ya fito da ledoji,
kaji ya siyo da madara mai tsafta, har da
kankarar dayaji tana tambayar umma yasai
musu.

Tace, gama fa kankarar umma tasai mana.

Bishira ta cika fam don takaici, kamal kaninsu
Abba yaduba mata ko ummi tana gidan umma, ya
fada mata bata nan.

Ta tabbatar suna tare, ta
cema umman bashir tunfa safe suka fita tare
umma tace tun safe wane iri?

Tace wai bta da
lpy yaje kaita asibiti Umman bashir tace Allah ya
tashe mu lpy Goben nan zan tafi kauye dama
gobe ta ce indawo gaje 'yar bori, ina fada miki
ummi dakanta zata bar gidan basai ance mata
ba.

Bishira tace dahaka zata faru zanfi kowa farin
ciki, umman bashir tace kece aida shegen kyamar
'yan kauye bakison mutane Matsalarki kenan da
ace zaki jure muje tare kiyi kwana 2 'yar bori da
bokan tsauni zasu cika miki aiki Bishira tace
zanje umma.

Biyan bukata ai yafi dogon buri
umma tace taki turo minshi ince masa sha'ani
zamu don kada yace zai hana, bishira tace to.

Sun sameta agidan ummi tayi dakinta da ledar ta
shikuma yashiga gurin bishira.

Ranar daya dawo
dakin ta kuwa tayi kyau cikin doguwar rigar
shadda ruwan kunkumadi, tun yana kallon ummi
asace harya kasa dauke idonsa Ummi talura ta
birgeshi sosai don haka tazauna bakin gado tana
fuskantarshi hira ce suke yi jifa- jifa itace ma
tasoma sako zancen Ya Abba zance ma alhaji
yasai min TV nagaji dazama shiru Abba yace a'a
banason haka ina sane zansai miki, tace to
Bishira dake labe ta girgiza kai aranta tace ashe
za ayi bala'i duk randa yakawo TV ai itama ai
iyayenta suka sai mata.

Tace to yaya abba
inason makaranta ya aje laptop din daya soma
budewa yamaimaita kalmar makaranta?

Ta ce eh,
yace sai nayi tunani Ummi ta marairaice tunani
ya Abba?

Kai dakake son inyi karatu?

Yace
shikenan haka sukayi ta hira har lokacin
kwanciya ummi tayi shafa'i da wuturi tayi shirin
baccinta takwanta Abba yau yakasa nutsuwa
tamkar yaje ga ummi, amma girman kai ya
hanashi.

Ranar sama-sama yayi bacci sau biyu
yna fita yana watsa majikinshi ruwan sanyi kozai
dan samu nutsuwa.

Har lokacin daya tafi gurin
aiki bashi da wani kuzari.

Ranar fati tazo lokacin
bishira ta tafi badadinta, ummi tahau fati
damasifa tare da fada mata yanda sukayi da ya
Abba.

Fati ta rantse tamaya kan cewa ba wanda
yasan zancen nan don bata fada ma kowa ba,
sukayi ta tunanin ta ina ne zancan nan yafita?

Fati tace to ko kiyi hankali koda Anty bishira tana
miki labe?

Ummi tayi shiru tna nazari, can tadubi
fati Bazan zargeta ba, domin ban taba ganinta ba
amma zansa ido fati tace gara kisa kam yanzun
harzuwa yau baku sasanta ba?

Ummi tace aini
bana bukatar sasantawa dashi tunda yace baiga
gurin kwanciya agadona ba Fati tasaka dariya ke
dai kada kicika baki,ummi tace kedai mu bar
wannan zancen inbaki kudin kayan don Allah?

Tati tace kibani dan bnida matsala mijina she ne
yakaini nasai nawa zance yakaini insai miki
kinason wanduna Ummi tace kinjiki da siket zaki
debo min Ai har gajerun wanduna ki kwaso min,
wulakanci zanyi a gidan nan.vels / ZURFIN CIKI book 4 part 15
ZURFIN CIKI book 4 part 15
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 02:12
Saidatayi sallah sannan tazauna gaban madubi
duk da shirin bacci take yi Saida tashafa manta
da hoda sannan tadan goga jan baki.

Tafesa
turarenta ta isa gurin kayan baccinta dake cikin
dirowar dora akwati, ta dauko duguwa tazira
sannan takama karshen kitsonta tahada su guri
daya ta tufke.

Zata ha gado yace, ga nama kizo
muci.

Ta fada gado tare da jan filo ta dora kanta
da kirjinta sannan tace nama saikace wata kura?

Dazun fana danci amiyar danayi.

Yace nida na
siyo shine nazama kuran ko?

Tace, a'a ya Abba
kaine ranar nan naji kace kura.

Kullum ake cin
nama?

Yayi murmushi aranshi yace, ok nan na
rama ne kenan, sannan yace toshi kenan bari in
ajiye miki naki.

Nan tayi kwanciyarta.

To 'yar
gidan tsohuwa, yafada danufin zolaya, tace kai
kuma dan gidan ummanka.

Cigaba yayi dashiga
yanar gizonsa, ita kam a gajiye take bacci
yasoma fizgarta.

Lokacin dayazo shima ya
kwanta akan gado, ta bude ido lpy Yaya Abba?

Ya dubeta tsakaninsu mutum daya zai iya
kwanciya.

Wace irin tambayace wannan mutum
da dakin matarsa da gadonta atambaye shi lpy?

Tatashi zaune, gani nayi ba guri agadona, yayi
shiru, wato ummi bata barin bashi, ta tsura mishi
ido tana jira jin mezaice.

Yatashi zaune, idanunshi
akan lebunanta, toni dai ga guri na samu, ta
sulale itama takwanta rigingine tare dajan bargo
tarufe rabin jikinta.

Shima hakan yayi, ummi
fargaba ce tasa tanemi bacci tarasa, shikam
addu'ar bacci yakaranta sannan yashafa
yalumshe idanu.

Duk su biyun bacci sama- sama
sukayi koda Abba baisamu nasarar kama kayan
ummi ba amma aranshi yace wannan sharar fage
ce.

Dasannu za'a kai ga muradi, ko washegari
daya kwana adakin dai bawani cigaba sai sake-
sake Abban yayi tayi azuciyarshi, na cewa
yakauda wata kunya ya fito mata amutum, amma
yakasa hakan.

Musamman yanda yaga ummin
tana da shegen wayo, ba kamar yan yazata ba.

Sannan gashi ta iya yin ado irin na tsokana.

Hakan yasa duk ranakun girkinta Abba yana
zumudi amma yakanyi kwanan rashin sukuni.

Wata jumma'a tsohuwa ta riski ummi da irn
wannan shiga tariga da gajeren wando, ta kawo
mata ziyarar data saba inta dawo masallaci.

Salati tasaka tare da cewa, yarinyar nan kece
haka kinzamo sai kace arniya?

Ummi ta tashi
tsaye tayi juyi tare da cewa.

Ynzun tsohuwa ban
birge kiba?

Ta ce kitson naki ne kurum yamin
kyau, amma wannan shiga dame tai kama?

Kuma
shimai sunan malam yakasa hanaki koke ma
yasoma tsoron nakine?

Ummi ta tuntsure da
dariya, ba tsorona yake jiba, shine ma yake son
kayan don shine ma yasai minsu.

Tsohuwa tace,
oho!

Eh lallai ta mike Allah ya taimaka, duk abin
ku dai baza ki koma baturiya ba, ummi tace oho
dai ke dai kuma baza ki iya wannan ba.

Tace,
Allah ya tsare nida wannan shiga, ummi ta dauko
dari biyu ganin tsohuwa ta mike, nizan tafi in dan
zazzaga in ziyarci jama'a.

Ummi ta kama
hannunta ta saka dari biyun, gana goron
jumma'a, Allah ya hadamu aladan ziyarar.

Suka
fito tana cewa.

Ke kullum nazo sai kin bani kudi
ummi, to Allah ya shi muku albarka, Allah kuma
yasa ki sauko lpy.

Murmushi ummi tayi duk 'yan
gidan su kallon mai cike suke mata.

Duk hirar
nan tasu bishira najinsu, ta cika tayi fam.

Dama
Abba yana kwana da ummi?

Ashe shine yake sai
mata kananan kaya?

Ashe har tana da ciki shine
yamata karyar cewa baya sonta?

Tana dawowa
raka tsohuwa, bishira ta kalleta, karamar yarinya
ta iya karuwanci, dube ki.

Ummi ta kalleta babba
fa ya rike girmanshi inba haka ba inhau in taka,
kuma niba karuwa bace, kema kalle ki.

Ta taso
zan zane kifa?

Ummi ma tadaga murya.

Sai kace
wata 'yarki?

Ba ki isa ba.

Bishira tazo zata
shakota, ummi ta daka tsalle taja baya.

Karki
sake ki taba ni.

Nan fa gidan ya kacame, bishira
sai ashar take zugama ummi, tana kiranta 'yar
matsiyata.

Ummi tace, banga kamannin masu
arziki ba a jikinki, nan makota suka shigo yin
rabo.

Ummi ko tana fada mata take ramawa, abin
da yafi yiwa ummi ciwo datace ummanki
matsafiya, nasan komai saboda bakin asirinta ne
sahabi yafasa aurenki aka mannawa mijina.

Don
shima ya fada min ba ya sonki, har yanzun bai
taba kwanciya dake ba.

Ummi tace, kazama mara
sallah me labe, kina labe min akofan don bakin
kishi, kuma insha Allahu sai Allah yasakawa
ummata tunda kika ce tana asiri.

Maman amir
kawar bishira tuni taruga takira umman bashir,
sai dai cikin sa'a tanazuwa Abba nayin parking.
Chapter 7 · 0% Book details