← Book details Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 18

Sashe 18

Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana gama karantawa tayi
wuri da wayar ba tare data bashi amsa ba, haka
ya tafi.

Bishira ta qwanqwasa ma ummi ta bude
suka gaisa, tace naga baki fito bane ina fata lpy?

Tace lpy lau bacci ne, tace yau baza kije
makaranta bane?

Ummi tace, zanje sai sha biyu.

Bishira tace kinji dadinki ni gashi nan ina tayi
masa zancen karatun amma ya share ni, ummi
tace inkin matsa zai yarda, tace ko za ki dan sa
min baki?

Ummi ta riqe baki, ni a wa?

Ke da yake
hannunki ai ke ce zai saurara, ni kin zo ne ma ki
zage ni.

Bishira tace wane irin zagi?

Ni dama ki
amshi mijinki ummi don gangar jikinshi ce kawai
agurina, amma ruhinsa yana gurinki.

Ummi ta ce,
ngd da zagi, bishira ta ce zancan gsky ne ba
wani zagi.

Haka suka yi ta rayuwa cikin kwanakin
ummi kam har rama tayi shima Abba ya rage
walwala don wanda yasan kan kula da shi
kamarta.

Yayi missing din abincinta.

Amma ya
gaji bazai jure ba.

Ya tuna bishira tace masa zata
ta yini gidan ummanshi.

Don haka yana gama
muhimman abubuwan da zai yi agurin aikin
yanufi gida.

Ummi tana shirin tafiya makaranta ta
dauko jakarta sai kurum taga mutum kamar an
jeho shi.

Ta daure fuska tamkar bata taba dariya
ba, yace ummi nagaji kin ji ko, na gaji da wannan
horon naki.

Laifin me nayi miki?

In don na dawo
da bishira ne sai in saketa, duk ba kece kika
takura min sai na dawo da ita ba?

Ummi tace, ni
karka doran jakar tsaba kasa kaji su bini, ka saki
matarka sbd ni?

Ba ruwana.

Yace, to ki dawo
yanda kike, kuma ki janye batunki na wai kin
haqura dani, niban haqura ba.

Ke ma kuma nasan
dole ki kasa kanki, ummi ta ce ni ban damu ba,
ya ce qarya ne gashi nan duk kin rame?

Ya
canza daga fada zuwa lallashi, ummi don Allah
na roqeki mu koma kamar da, haba bebyna.

Ya
lalubo hannunta ta qwace, don Allah ka tafi kada
bishira ta dawo ta same ka anan ta zargi wani
abu.

Haushi yakamashi sosai, ya daga murya da
qarfi, kin san Allah ummi zan hadaki da umma, ta
nufi hanya fita, nikaga kada kasa ni yi latti don
lokaci yayi nisa.

Ya ficiko ta ta dawo ba zaki
makarantar ba, ke an ma daina karatun tunda yafi
ni.

Ta zubar da jakar da hijabi ta nufi gado shi
kuma ya fita cikin zafin rai, gidan su umma yaje.

Bishira tana dakin umma tana sallah yabi umma
kicin, umma gurinki nazo, ta dube shi lafiya
Abba?

Ya turo baki, alamun ranshi bace baki,
yace umma ki sallami bishira, tace kamar yaya?

Yace taje can gidan ko muyi maganar agabanta?

Tace, kyale ta muje dakin babanku.

Abba ya fada
ma umma komai da ummi ke masa, tun dawowar
bishira ran umma ya baci tace ka barni da ita.

Banda shashancin ta da ita kadai take son
azauna?

Baga bishirar nan ba gidan nan ta gane
kuskurenta ko yau yarinyar nan sai da tace in
yafe ta nace ni dama ban riqe ta da wani abu ba.

Shine ita zata qirqiro fitina?

Yace, umma ai ba da
bishira take yi ba dani take yi, tace to zata gane
kurenta da dare kuzo kai da ita.

Umma ce ta kira
ta awaya tace tazo ita da abba, jikinta ya mutu
don tasan qararta aka kai, tana idar da sallar
isha'i taje gidan.

Can tasamu abba, nan ko umma
ta rufe tada fada, koda tsohuwa ta jiyo tazo
umma tafada mata komai sai ta shiga fada.

Wai
ai kishi halas ne, ke suwaiba tsakani ga Allah ko
ke bazaki so kishiya ba, bare ita yarinya.

Abba
yace to gata nan ita ce fata dame ne nida batun
in dawo da bishirar, yanzun na dawo da ita kuma
ni abin ya qare akaina?

Nan fa umma tayi mata
tatas, ta kuma sata anan ta ba Abba Haquri, aka
kira shi awaya ya fita.

Umma ta samu dama
taqara yi mata nasiha da cewa, in bnda shirmenki
yaushe zaki bar ladanki, hanyar aljannarki kice
kinyi fushi da ita kin barwa kishiya?

To kada in
sake jin haka, ki riqe darajarki da mijinki, ke
ganinki da ita.

Ta jima tana bata shawara kafin
Abba yadawo suka nufi gida.

Ya shiga gurin
Bishira ya fada mata cewa yau gurin ummi zai
kwana, nan ya bar ta da kewa yanufi gurin ummi,
tamkar yaune daren farkonsu hara sukai rayuwa
aranar. ** ** ** ** Kwanci tashi asarar mai rai,
shekara ta zagayo lokacin bishira da tsohon ciki,
Abba nason yara don muhibba taqi dawowa tafi
son umma dole suka haqura suka bar mata.

Ta
haifi 'yarta budurwa tubarkalla ranar suna ta ci
sunan sahura inda suka sa mata walida.

Ummi
nason yara, don haka in tana gida to tana manne
da walida, Abba yana damuwa da rashin samun
cikin ummi, wanda ita ummin ta barma Allah
komai.

Shekaru uku sun sake biyo baya, lokacin
Bishira ta sake haihuwar habiba takwara Abba
yayi wa ummi.

Tsohuwa an qara tsufa, 'yan
rigingimu sun qaru tace ita Abba yama takwara
amma bata son ya duke ta irin yanda yayi wa
ummi.

Abba kullum qara son ummi yake, umma
ta matsa masa sai da yayi qoqari ya sai fili rabin
filoti tace kuma a rage ciye ciyen dadin nan agina
sh矛.

Haka kuwa ya gina flat mai daki hudu, daya
ummi daya bishira, sai nashi sannan na yara.

Yayi qoqari gurin gyaran falon ita kuma ummi ya
canza mata kayan daki don bishira an canza
mata daza su tashi agidan su.

Yace tabishi bashi
in ya samu zai bata kudi amadadin kayan daya
saima ummi, tace ta yafe.

Ummi dake karantar
(BUSSINESS) har ta hada (H.N.D) dinta kuma
tayi bautar qasa.

Abba dai yace baza'ayi aiki ba
amma ya yarda tayi kasuwanci, Alhaji babba ne
ya bata jari inda take saro kaya zannuwa, lesuna,
takalma zuwa jakunkuna.

Abin ya amsheta don
har kayan aure tana hadawa, tana yin saqo irin
su kwatano da chaina, india, pakistan ko dubai,
ta hanyar wani wan kawarta.

Haka kawai ummi
ta samu kanta da zaban abinci, yawan bacci
kasala da dai sauransu, sam bata san
takamaiman lokacin al'adarta ba.

Don bata wani
lissafi in yazo shi kenan in bai zo ba bata damu
ba tama cire ranta daga batun ciki.

Abba ya kalli
nonuwanta, baby kwanan nan kirjinki ya cika
sosai, gashi kinyi haske ko kin canza mai ne?

Tace yaya yaushe kazama likita?

Yace, ummi kin
fa canza shirya muje asibiti, ta ce ya Abba don
Allah ka bar ni nagaji dazuwa asibiti.

Yace, to ni
zan je inya tambaya game da yanda ki ka canza.

Cikin jin haushi tace sai ka dawo.

Ga yara
atsakar gida sun ishe mu, yace ni naki nake
qawar in gani nasan addu'ar da nike yi bazata
fadi kara banza ba, sannan ga qoqarin danake yi,
shiru ta masa.

Dagaske yake yi yaje yayi wa likita
bayani, yace yadai kawo fitsarinta.

Sai da suka yi
tsiya da qyar bishira ta lallasheta ta yarda ta
bada fitsarin.

Rungume likitan yaya lokacin da
yake fada masa ciki ne in dai har fitsarinta ne.

Afalo gaban bishira da yara abba ya rungume
ummi yana murna, ji tayi tamkar tsokana amma
ganin ya zauna yana ta buga waya yanata
yadawa ta amince cewa gske ne.

Don haka ta
tashi ta shiga dakinta tayi alwala tazo tayi nafila
raka'a 2 cikin kuku take godewa Allah tare da
addu'ar ya raba lpy.

Ya bata mai albarka.

Tsohuwa ma kuka ta saka lokacin da labarin ya
riske su.

Ummi taga gata musamman daya
kasance cikin yazo da kumburi tayi sumtum.

Duk
kowa ya tsorata sbd tunanin ko hawan jininta ne
ya tashi.

ALLAH cikin Ikonshi data tashi haihuwa
saita santalo danta cikin gajeriyar nakuda, sak da
abba kwabo da kwabo.

Rungume ummi abba yayi
don murna, sunan alhaji babba ya sake maida wa
kuma walid din dai suke kiranshi.

Watan yaron
bakwai ummi ta sake rasa kanta, kuka wiwi ta
dinga yi shiko abba murna kamar yayi rawa.

Tasake samun da namiji inda yaci sunan alhaji
karami suka sa masa hibban.

Haka suka ci gaba
da rayuwa cikin haquri da juna, tsakanin bishira
da ummi, bama irin bishira saboda abba baya iya
boye son ummi.

Kan 'ya'yansu ahade ba kya
gane bambanci, bishira ta gane umma uwa ce
guda har da rabi, don haka hatta shawara saitaje
gurin umma kuma ko sabani suka samu da abba
gurin umma take zuwa.

Ita kuma umma ta dauke
ta babu bambanci da ummi, don bata taba fada
ma ummi sirrin bishira ba.

Sahura yanzun ta
yarda umma da alhaji sune rufin asirinsu, kuma
gatan Abba, bashi ma da yayi aure gidan dasu
ummi suka tashi nan ya zauna.

Dangin bishira
yanzun sunga bishira ta samu natsuwa sun
sulhunta.

Abba agurin aikinshi yana ta samun ci
gaba, lamuran sai godiya.

Ummi tashafa addu'ar
da takeyi sannan tamiqe tana linke dardumar tace
kallon me ka ishe ni dashi ne ya Abba, yace ina
kallo ne na kusan samun da na uku wannan
karon takwara zan ma kaina.

Ummi ta jefa masa
dardumar hannunta, daina min fata ni, yace ban
karanci likitanci ba amma ni likitanki ne.

Ta fada
kanshi, ya rike fuskarta yana kallonta cikin ido,
ummi lokuta da yawa ina zama inta tuna da,
musamman in na kalli 'yan yaranmu wadanda
suke matuqar kama dani, tace me kafi tunawa a
baya?

Yace, yanda kikayi ta kirana awaya kina
tsara ni suhaylan kaduna.

Suka sa dariya.

Ni kam
nafi tuna yanda ni da kai muka yi ta 'ZURFIN
CIKI' dason juna.

Yace Allah yabarni da ke har
abada matata.

Ta kwantar da kanta
amakwancinta ''Amin mijina''.

Muma Allah ya bar
mu da masoyanmu har gidan aljanna, ya bamu
lafiya dazama lafiya.

Ya zaunar mana da 'yan
uwanmu lafiya, Amin ya rabbi. ** ** ** ** Bayan
shekara goma naje nasamu yaya Abba nace
inason muhibba yace badamuwa yabani kyautar
gida da mota.

Ummi kuma ta hada mun kayan
lefe saboda namijin kokarin danayi na rubuto
maku wannan littafin aka daura mana aure da
muhibbata muka tare muka cigaba da soyayya
fiye dasu ummi ma.
Chapter 18 · 0% Book details