← Book details Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 18

Sashe 12

Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka kuwa
ya gina flat mai daki hudu, daya ummi daya
bishira, sai nashi sannan na yara.

Yayi qoqari
gurin gyaran falon ita kuma ummi ya canza mata
kayan daki don bishira an canza mata daza su
tashi agidan su.

Yace tabishi bashi in ya samu
zai bata kudi amadadin kayan daya saima ummi,
tace ta yafe.

Ummi dake karantar (BUSSINESS)
har ta hada (H.N.D) dinta kuma tayi bautar qasa.

Abba dai yace baza'ayi aiki ba amma ya yarda
tayi kasuwanci, Alhaji babba ne ya bata jari inda
take saro kaya zannuwa, lesuna, takalma zuwa
jakunkuna.

Abin ya amsheta don har kayan aure
tana hadawa, tana yin saqo irin su kwatano da
chaina, india, pakistan ko dubai, ta hanyar wani
wan kawarta.

Haka kawai ummi ta samu kanta
da zaban abinci, yawan bacci kasala da dai
sauransu, sam bata san takamaiman lokacin
al'adarta ba.

Don bata wani lissafi in yazo shi
kenan in bai zo ba bata damu ba tama cire ranta
daga batun ciki.

Abba ya kalli nonuwanta, baby
kwanan nan kirjinki ya cika sosai, gashi kinyi
haske ko kin canza mai ne?

Tace yaya yaushe
kazama likita?

Yace, ummi kin fa canza shirya
muje asibiti, ta ce ya Abba don Allah ka bar ni
nagaji dazuwa asibiti.

Yace, to ni zan je inya
tambaya game da yanda ki ka canza.

Cikin jin
haushi tace sai ka dawo.

Ga yara atsakar gida
sun ishe mu, yace ni naki nake qawar in gani
nasan addu'ar da nike yi bazata fadi kara banza
ba, sannan ga qoqarin danake yi, shiru ta masa.

Dagaske yake yi yaje yayi wa likita bayani, yace
yadai kawo fitsarinta.

Sai da suka yi tsiya da qyar
bishira ta lallasheta ta yarda ta bada fitsarinURFIN CIKI book 4 part 23
ZURFIN CIKI book 4 part 23
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:22
Sam bishira bata damu da barin mijinta da zatayi
gurin ummi ba, tunda ta jima da sanin cewa
ummi bata da wani ammafni.

Wannan ne ma
yasa tasha alwashin in taje zatayi addu'a Allah
yakara toshe ummin kada ta warke sam, tunda
umma Bashir ta fada mata duk addu'ar da tayo
kafin ta dawo an karba mata.

Ta kuma kara bata
shawara ta roko musu rigima suyi tayi har su
rabu, Bishira tace duk zata roko.

Ko ranar da
zasu tafi sai da ta yi wa ummi habaici, kawyenta
sun shigo wato makotansu a tsakar gida take
fada musu cewa mijinta kurum take tunani.

Wai
zai sha wahala kafin ta dawo.

Wata cikin su tace,
wahalar me ga shi da amarya?

Ta ce amaryar da
ta ke a toshe, ai bata da ammfani.

Ummi duk
tana ji, takaicin duniya ya isheta sai dai ita zata
so ace bishiran take ta roko ma kanta shiriya ko
Allah zai sa ta dawo ta kama sallah.

Dayar tace,
to Bishira ki roko mata sauki mana, cikin zolaya
tayi zancen, Bishira tace ba abinda zai kaini
makka in roko ma kishiya abin arziki.

Ummi ta
fito ta ce Anty Bishira zai fi kyau ki roko ma
kanki shirya ko in kin dawo kya fara sallah da
tsafta.

To ban san ma yanda zaki kwashe da
ibadar ba ko za a karba tunda ba yin sallah ki ke
ba.

Ta taso fuuu, kawayen suka reketa suka ce
kyaleta bakin ciki ne.

Abba ya fito wanka yana
cewa, Ok, za kuyi na bankwana ko?

Yana da kyau
hakan.

Ummi ta koma dakinta.

Tun bayan tafiyar
Bishira Abba ya shiga takura musamman irin
wannan lkc na sanyi.

Ya dawo da yiwa ummi 'yan
wasanni da ya daina, sai hakan yakara sa shi
damuwa don haka ya shiga lallashin ummi ta
fadawa umma.......

Kuyi hkr da typing din banda
lafia sstr dita nake sawa tana maku.els / ZURFIN CIKI book 4 part 24
ZURFIN CIKI book 4 part 24
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:24
Tace ita kam ba zata iya ba ranar wata juma'a
suka tafi da nufun su fadama umma matsalarsu,
sai dai har zuwa bayan isha'i da abban yazo don
su tafi sun kssa sanar da umman komai, har
sunyi sallama abba yayi kunar bakin wake yace
umma ta fada maki matsalarta?

Umma tace wa?

Yace ummi tace a'a suka koma suka zauna.

Abba
kanshi na kasa Yace umma dama bata da lafiya
ne?

Umma tace mike damunta kuma?

Yace ummi
fada mata.

Ummi ta sunne kai cikin cinya tare da
cewa shiya fada.

Cikin sa'a aka kira wayarshi,
nan yayi waje ya barsu, umma tasa ummi saita
fada.

Ummi ta rasa ta inda zata dauki zancen,
umma ta soma yi mata fada har tsohuwa ta leko
tambaya take lafiya ba sunyi sallama dama basu
tafi bane?

Umma tace wai bata da lafiya ne,
kuma ita da abban sun kasa fadaman shi yayi
waje, ita kuma ta kunshe kai cikin cinya wai injira
ya dawo ya fadaman.

Tsohuwa taja hannun
ummi zuwa dakinta, suka zauna bakin gado ta
riko hannunta.

Takwara fadaman abunda ke
damunki.

Ummi ta sunkuyar da kai ta kasa
magana.

Tsohuwa tace inda baki fadaman ba
akwai wanda zai taimaka maki ne?

Tunda naga
duk yarda mijinki yake da umman ku ya kasa
fadamata to abun mai girma ne.

Ummi ta daure
tace "Gabana ne fa a toshe....." tsohuwa ta rafka
salati, sannan tace yannan badai angurya ba?

Cikin tsoro ummi Tace, ni ma ban sani ba ko
shine.

Salati tsohuwa ne ta jawo hankalin umma
tazo dakin da sauri.

Tsohuwa Tace ina ga
yarinyar nan angurya ne a gabanta.

Umma Tace
shine don wauta daga ke har abban kukayi shiru,
dubi tsawon watanin da kuka dauka, tsohuwa
Tace yanzun yaya za'ayi umma tace ni ina nasan
yanda za'ayi, ai ni na zata yanzun babu masu irin
wannan ciwon.

Rabon da inji labarinshi tun muna
yan mata.

Tsohuwa Tace kai nima na jima banji
ba, amman kinsan dama wanzamai ke aikin.

Alhaji ya dawo daga sallar isha'i yaga abba tsaye
a waje, Yace a'a babana dama baku tafi ba, Abba
yace eh yanzun zamu wuce, ya biyo bayan Alhaji
suka shigo suka riski zancen dasu dasu umma
keyi.

Alhaji Yace lafiya?

Umma Tace yaran nan
ashe zaune suka da lalura, tame inji Alhaji, umma
Tace angurya ce ashe ta fito ma Ummi wai suka
zaune.

Alhaji yace meye kuma angurya Tace wani
abu ne dake toshe mace.

Nan fa suka shiga
tattauna yanda za'a shawo kan abin, tsohuwa
Tace wanzami za a kira ya yanka mata.

Alhaji
yace to gobe zai kira wanzami.

ZURFIN CIKI book 4 part 25
ZURFIN CIKI book 4 part 25
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:26
Abba da jin haka sai ya fito, kishi fal da
zuciyarshi, ya ce umma wanzami kuma?

Ta ce
eh, aikin sune.

Yace gsky umma ba za a kai ta
gurin wani wanzami ba , bagara muje asibiti ba.

Tsohuwa ta ce, kaci gdanku da asibiti komai ku
ce asibiti to wannan ba aikinsu ba ne.

Abba ya
ce, Nifa gsky ba xa a kai min mata gurin wani
wanzami ba, umma asibiti zamu.

Yanzu kai ya
waye wanzamai ba duka suke dafa kayan aikinsu
ba, haka kawai taje ta hadu da wata cutar?

Alhaji
yayi murmushi yasan kishi ne ke damun Abba, ya
ce Babana kada ka damu, goben sai kuje asibitin,
in sun ce ba su san shi ba to sai a zo a yi na
wanzam ko ?

Kunya ta kama Abba, Sam ya
manta Alhaji yana gurin ya ce to Tsohuwa ta ce
kuje in kun je ma dawowa za Ku yi dan me taurin
kan tsiya.

Abba ya ce naji kin ji ummi taso muje
gda Tsohuwa ta ce oho dai, kuyi ta tafiya in dai
akayi mata aikin ai dole ka barta ta warke .

Alhaji
da umma dai dariya sukayi ta yi musu, shi kuma
yayi musu sallama, ummi kam kasa magana tayi
don duk ta tsorata.

Suna fita ta rike hannun Abba
gam tana cewa.

Don Allah ya Abba kada kabari
wanzam yayi mini aikin nan, zan ji zafi.

Ya
rungumota, Ba zan amince ba wani ya ganmin
al'aurar mata, likita ma mace zan nema ko nawa
zan kashe .

Ummi ta ce, to zan ji zafi ya Abba?

Ya ce, made ki damu, in asibiti ne kila suyi miki
allurar kashe zafi amma in wanzami ne ina za ya
ga wata allura yayi mini.

Ummi sarkin tsoro ranar
kwana tayi cikin damuwa, washegari kuwa tun
bakwai suna asibiti.

Babban asibiti suka je sun
yanki kati likita me kula da fannin mata aka tura
su.

Mata dayawa suna ta kallon su ummi
musamman yanda Abba ke nan-nan da ita,
sannan wasu sungane shi kasan cewar shi dan
jarida mai farin mini.

Wasu mazan kuwa sai zuwa
suke suna gaida shi.

An kirata dakin ganin likitan,
ta mike zata Shiga Abba shima ya mike, wata
Nurse ta ce, malam jira mana, ya ce ai duk Mu
biyu ne bamu da lfy, ya shige likitan namiji ne ba
yanda ya iya dole ya yi masa bayani likitan yayi
ma ummi tambayoyi in da duk ta bashi amsa/ ZURFIN CIKI book 4 part 26
ZURFIN CIKI book 4 part 26
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:27
Sannan ya bukaci ta kwanta kan gado ya saka
safar hannu, juya kai abba yayi don gaskia ranshi
ya baci, lallai ya kamata mata musulmai su dage
suyi karatun likitanci don su taimaki yan uwansu
mata.

Sai da likita ya gama dubata sannan ya iya
dubansa, likita yayi wani rubutu ya mika abba
tare da cewa, an baku gado zayi mata aiki gobe
ko jibi.

Abba yace likita zan iya sanin wane ciwo
ne wannan?

Likita yace tsirone dake fitoma mata
dai daiku.

Sam abba bai fahimta ba don haka yayi
mashi sallama.

Umma ce a wurin ummi tana
shan magani kafin ranar aiki inda abba
hankalinshi ya rabu biyu rabi gurin aiki rabi garin
ummi.

Don ma umma ta koreshi da so yayi ya
rika kwana, addu'a kam yana yinta.

Ranar da
za'ayi aiki abba hankalinshi duk tashe.

Yana
zaune bakin gadon da take kwance ita kuma tana
can ana aikin.
Chapter 12 · 0% Book details