← Book details Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 18

Sashe 1

Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

IKI book 4 part 1
ZURFIN CIKI book 4 part 1
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:42
Inna harira tace, Allah ya kyauta ku tashi mu tafi.

Suka mike Suka nufi dakin ummi.

Duk da ummi a
da bata tunanin tana da lokacin bishira, yanxu
kam dole tasan zaman da zasuyi.

Su inna saratu
suka ce ma ummi duk abinda zatayi don allah
kada ki kulata.

Suka ce tayi harkokin gabanta tayi
biyayya wa mijinta shine abunda zai fisheta.

Ummi tace To amma a zuciyarta bata tunanin
zata zuba ido a rainata.

Suna tafiya fatima ta
shigo yiman sallama, ummi tace don allah fati ki
dan tsaya ni kadai fa zan zauna a dakin nan. fati
tace wayace kada kisan kawaye?

Ummi ta ce
wane kawaye, auren da a ka daura cikin yan
mintina?

Fati tace, Yau zakiji abinda mata kaji.

Ummi ta damko mayafin fati, ni fa inajin turo, wai
da gaske da wahala ko kina tsokanata ne?

Fati
ta kamo kunnen ummi tayi mata rada.

Ummi ta
zaro ido tare da cewa, Da gaske?

Fati ta sheke da
dariya tace sai nazo jin batun.

Ummi tace sirrine
ya za'ayi in fada miki sirrina?

Fati tace au ni
shine na fadamaki nawa ko?

Ummi tace kinyi
haram da kika fada fati tace, "ke kuma kinji
haram ko?

Suka sa dariya.

Duk yanda ummi taso
fati ta tsaya amman taki, don haka sukayi
sallama.

Fati ta shige dakin bishira don yi mata
sallama.

Bishira tace, fati fitar min daga daki
bana wasa dake, tunda kema naga kin koma
jam'iyar waccan yar iskar, fati ta fita, cikin ranta
tana cewa ba zanki yar uwata ba don kishinki na
banza tayi tafiyata.

Ummi tsuru tayi tanaji tsoron
abinda fati ta fadamata, amman sai wata zucia
tace keda ba sonki yake ba kila ma bazaibi ta
kanki ba, sannan ta samu yar natsuwa.

Abba ya
fito zai nufi gida sai kuma ya fasa ya nufi super
market, ya siyo audugar mata yana tsammanin
gobe ne zata tashi da al'ada a lissafinsa.

Tun
sanda ta soma bai taba mance ranar ba, haka in
ya chanza mata lokaci duk yana lissafe.

Ya sai
masu yan kayan masarufi sannan ya fito, gida ya
nufa amman gabansa yana faduwa kila har
yanxun ba a kai ummi ba.

Da yayi fakin sai kuma
ya nufi gidan su umma duk kowa ya watse.

Yayi
sallama tsohuwa tana alwala ta amsa.

Umma
daga kicin ta amsa, tsohuwa tace "wane kinibibin
kuma ya kawoka mai sunan malam?

Bayan an
kai maka ita?

Yace kaji tsohuwa da wata magana
da gurin ummi nake zuwa?

Ni gidan mu ne.

Tace
kadaiji shi, takwara dai kada inji kada in gani, don
nace mata duk abunda kuka mata tazo ta
fadamin.

Yarinyar nan tana kuka wiwi tabar gidan
nan.

Umma cikin dariya tace "toh ai tsohuwa in
don Abba baza ayi fada ba, ummin ce dai abin
jama kunnen.

Tsohuwa tace 'a' a daina zancen
nan suwaiba kada ma ya samu nayi.

Abba yace"
Toh bari in zo in hada maki kayanki mu tafi can
don kada wani ya zafin cewa.

Kinga kyafi tare
mata.

Tace ina gana nan din ma zanji.

Yace
Alhaji sun shigo kuwa umma?

Tace A'a basu
shigo ba.

Yace toh bari in isa gida.

Tace toh
Abba ummi ma dazun aka rakata.

Don allah Abba
ka kara hankuri a kan na da, sannan matarka
kuma kada kace zaka nuna mata bambanci a kan
ummi yar uwarka ce.

Ka kwantar mata da hankali
ka mata adalci, sannan kada ka bawa ummi kofar
da zata raina bishira.

Yace zan kiyaye insha allah,
kuma don allah umma ki kara mika godiata gurin
alhaji.

Tace haba Abba yaya kake fadin haka?

Alhaji ai mahaifinka ne karka dinga kallon
alakarka da ummi.

Yace haka ne duk da haka dai
a min godia, tsohuwa tace yaki godia ya samu
mata a sama don rashin imani mai sunan malam
ko gyauto bai sa mata ba, toh kasani tana binka
bashin lefe.

Abba Yace umma ni dai na wuce.

Umma cikin dariya tace "Toh Abba.

Yace tsohuwa
ni nayi gaba, don in na cika tsayuwa a nan kila
mu dambace, Tsohuwa tace kai dai jeka na baka
amana ya tafi yana dariya.

Koda ya kai kofar
gidan sai ya bude mota ya dauki kayan
masarufinshi ya nufi cikin gidan salam dai duk da
jarumta irin tashi gabansa ne ke faduwa.

Bai san
wace irin masifar bishira ta tanada ba.

Ya shiga
da sallama.

Bishira tana zaune akofar daki tana
goye da muhibba, amman bata amsa ba.

Duhun
magriba ya soma dan daf da a kira sallah a ke,
yace bishira ya ba a tada inajin ba?

Tace tunda
kazo yanxun ai sai ka tada kai.

Da kafin wata
tazo ai baka taba zuwa kace a tada inji ba.

"Abba
ya kalleta a zuciyarshi Yace" mata kenan masu
manta alhaji.

Ya aje ledodin hannunshi ya nufi
injin.

Bishira ta mike ta nufi ledodin tana fadin
Tun yanxu a aka shigo mata da kazar, alamun ba
za'ayi ada ba kenan.

Ni lokaci na sa wuraren tara
ya shigo ina lissafe da komai, ta bude ledodin sai
taga kayan masarufi d kuma audugar mata.

Tsaki
taja tare da dangwarar dasu yana kallonta da ya
kara mai ya tada injin sa yazo ya kwashe ledodin
ya shiga falonta.vels / ZURFIN CIKI book 4 part 2
ZURFIN CIKI book 4 part 2
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:44
Kujerun da aka chanza mata masu kyau, amman
a ran abba yace ya basu sati biyu.

Ya cire riga ya
fito yana son yayi wanka ne kafin a kira sallar
magana,yaja ruwa da sauri da sauri yayi ban daki
ya fito ya shiga falo ya kwalama bishira kira.

Tace minene kake damuna?

Yace ina aka kai min
akwatuna na?

Tace tace ina kuwa gasu can a
kicin da sauri ya fito, kicin din lafia?

Ya tsaya
yana kallonta bani da mutuncin da za'a sa min
kayana a daki?

Tace ni da aka guji dakina da
kayan a kace ni kazama ce, me zaisa in sake
kaine?

Daga baice komai ba ya nufi kicin ya
kwaso akwatuna shi da takalmin shi ya kai
falonta.

Bai tsaya chanza kaya ba, ya nufi
masallaci don zai rasa sallah.

Bai baro masallaci
ba sai bayan isha'i amman bishira tana zauna.

Ummi kam ta kasa fitowa don tana kyankyamin
ban dakin, gashi al ada ta sameta da yamman
nan, sannan duk tanajin abin da sukeyi da
matarshi.

Ya shigo gidan ya chanza kaya sabi fil,
ya feshe jikinsa da turarukkanshi wayar shi ta
soma ringing ya daga salis ne.

Yace aboki in ba
sallama akwai daga hannu ko?

Kace an kai maka
rabin ranka koda ba zamu rakaka ba ai kayi
mana sallama.

Cikin dariya Abba yace na yafe
salis yace To Allah ya bada zaman lafia.

Suka yi
sallama zai aje wayar kenan sako ya shigo.

Ya
duba ummi ce da wayar nan da ya bata ajiya
cewa tayi, ina da matsala, ina bukatar taimako.

Gabanshi ya fadi, sai kuma ya tuna kila al'adar
ce, don haka sai ya saka hularshi ya dauki ledar
audugar ya nufi dakinta.

Har lokacin bishira nan
zaune inda take, tace au tun daga yanxu za'a
soma rashin adalcin?

An dauki leda an nufi
dakinta?

Sam baiko waiwayo ba, yayi sallama ta
amsa tare da gyara mayafinta, ya shiga suka kalli
juna Cikin ido zukatansu sukayi fari kal.

Cikin
taushin murya yace, wane taimako kike bukatar?

Ta lumshe ido sannan ta juya masa baya domin
kunya ta rufeta.

Yace To karba ya mike mata
ledar ta waiwayo ta ansa da hannu biyu.

Mamaki
ya cikata ganin audugar, ya yayi har ya san tana
bukatar audugar kuma a ina yake sanin lokacin
al'adarta har idan ya chanza?

Tace nagode yayi
dan murmushi nima ina godia.

Ya juya har ya
daga labule tace "Em na ce....." ya waiwayo yace
kika ce mi?

Tace don allah inason maganin
wanke bayi ne, tayi maganar Cikin kyankyami,
sakamakon irin dattin da tagani a bandaki tare da
gamsa kuka.

Yayi murmushi wane iri kikeso?
(IZAL) yace ai akwai amman yanxu Bai kamata ki
shiga wankin bayi ba.

Tace zan wanke in dai
akwai.

Yace bari in wanke maki, da sa tace a'a
yaya Abba zan wanke.

Falon ya koma ya cire
rigarshi ya shiga jan ruwa.

Bishira tana zaune ta
mike ina badai abokitaina ba, in zaka kwashe
mata rijiyar kwashe, amman a juye ko in baras
kuma in dai ruwan da za'ayi amfani dashi ne
kakeja, To kesani nima duk lokacin da zanyi
amfani da ruwa saika dibar min, ehee.

Ummi ta
fito da bokitai don duk tana jinsu, tazo wurin
Cikin sanyin murya tace, Ya Abba don allah ka
bari in ja ruwan nan.

Ya kalleta, take ya manta da
duk bakin Cikin da bishira ta kunsa mashi.

Yanxun daga zuwa saiki fara jan ruwa?

Ummi
tazo ta kama igiyar gugar, ai ba zama nazoyi ba,
Ya Abba bauta nazo yi, Aljanna sai an dage.

Ya
saki dariya bishira ta dakatar dashi da ce wa
"Karuwanci za'a gwadaman?

Ta daga ruwan da
ya zuba a bukati zata watsama ummi, yace kina
watsa mata zan baki Mamaki.

Cikin tsawa yayi
maganar ta tsaya cak da bokitin yace, Sakarya
mai kishin hauka.

Yaci gaba da jan ruwan yana
zubawa abokitan da ummi ta fito dashi.

Bishira
ta aje ruwan sannan ta hankadar dashi a kasa,
Bai ko kalleta ba.

Ya zuba ruwan sannan ya fito
da izal da omo.

Daki ummi ta koma ta dauko
tsinsiyar da aka sai mata don wankin bayi, kin
tafiya Abba yayi tana wankewa yana zuba mata
ruwa har sai da taga bayin yayi yanda take
bukatar sannan ta hankura. kyankyami jikinta
takeji don haka taje ta hada kayan wanka har
lokacinzurfin Ya Abba yana wurin rijiyar.

So take
ya matsa taja ruwan amman yaki, don ya lura
bishira shi kadai take shakka zata iya zartar da
komai kan ummi.

Shine ya sake zuba mah ummi
ruwan wanka, sannan ya coge har ta gama ta
fito rufe da hijabi tayi dakinta, sannan ya dauraye
jikinsa yaje ya maida kayanshi ya nufi wane.
Chapter 1 · 0% Book details