← Book details Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 18

Sashe 15

Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umman tace, zuwa makkan naki dashi
gara babu, don nasan da kyar ne in za akarbi
wannan aikin nani ke da bakya sallah arniyar
banza qazama.

Ummi harda riqe ciki don dariya,
haka dai suka yi tayi wajuna gori har dai 'yan
kallon da suka taru suka soma bda haquri,
umman bashir tayi gida cikin kuka.

Tagayawa
'ya'yanta komai su bashir dasunce sai sunje sun
zaneta umman bashir din tace barta ku barta
kawai bari abban yadawo.

Da dare ta ritsa shi
agidan yasha mamakin wai yau mahaifiyarshi da
bishira ne suke fada yace hakane dama duk
zamantakewar da ba'a kafata don Allha ba wata
rana sai ta rushe.

Nan yayi tawa bishira fada da
cewa uwarshi sa'arta ce dazata tsaya ta dinga
gaya mata magana?

Nan fa aka sake kacamewa
har abba.

Yakai ga kwasa wa bishira mari,
sakamakon irin rashin kunyar data rike qugu take
tsulawa umman bashir din.

Ummi ganin abin yana
tsawo ta fita taja umman bashir tana bata haquri
ta zaci zata hantare ta amma sai taji tana cewa
ba komai ummi sakayya ce tunda na nuna ina
sonta dole tamin haka.

Abba yace ummi tasa
mayafi taraka umma gida, hakan ya qara qona
ran bishira gashi yanda taga Abba ya bata rai zai
iya yin komai, dole ta koma daki tana cizon yatsa
tare da tunanin mafita.

Ummi kuwa ahanya sai
lallashin umman take tare dayi mata alqawarin
cewa duk abinda take so ta tambayeta zata mata
shi tarakata har gida sannan tadawo.

Sabon kuka
umman bashir tazauna tanayi, takaicinta yanda
bishira ta zage ta taci mata mutunci agaban
ummi, tashare ido tare dayin ajiyar zuciya a fili
tace dani take magana.

Ynzun ummi tasan kishi
fiye da baya, don ta hau turbar ma'aurata kuma
tasan muhimmancin abinda ake yiwa kishi, don
haka zatayi komai na jan hankali don ganin taja
mijinta gareta.

Kuma inta lura cewa bishira ta
maqale mata aqofar daki sai tayi ta jan abba da
wasanni, don ta quntata ma me labe.

Amma
hakan baisa ta daina ba, don haka ta daura
aniyai saita mata abinda zata tona kanta ha abba
yasani.

Duk jumma'a abba yana dawowa gida
musamman in ranar girkin ummi ne don cin
abinci na musamman.

Jumma'a biyu kenan bata
fado kanta ba sai wannan, don haka tun alhamis
taje ta yarfo kitsonta, ta biyo ta gidan su gurin
tsohuwa tazo.

Don haka suna gaisawa da umma
tace gurin tsohuwa nazo.

Suka shige daki tace da
tsohuwa nazo ne indan samu dan wani sirrin.

Tsohuwa tace, name ummi?

Ta ce na gyaran jiki
mana.

Fati tace min kwanaki kin fada mata wasu
abubuwa.

Tsohuwa ta ce, ja'ira, kinga uwar bari?

Dama nace zaki same ni ina kyakkyawan zamana,
bada ina fada miki kina sharewa ba?

Ummi tace
haba tsohuwa banaso aji mu yanzun dai ki bani
shawara sannan ki fada min abinda zanyi inja
hankalin mijina.

Ta ce, toda farko ki dinga kula da
jikinki ta hanyar rufe shi ruf, kada kibar kofar
iska.

Banda tafiya ba takalmi, iska tana shiga
tanan kuma mace narage ni'ima banda zama ba
dankwali inso samu ne hatta tsarki ki daina yi da
ruwan sanyi, ki dinga yida ruwan dumi.

Sannan ki
amshi bagaruwa gurin ummarki ki dinga shiga
inkin tafasa da alif dakuma saiwar mata, sannan
inkinyi al'ada kin gama kinyi wanka toki dinga
matsa farin miski a ehem dinki.

Sannan ki samu
saiwar kankana, saiwar zogale, kanunfari,
mazarkwaila dazuma amma kisa kanunfari
dayawa sai ki dafa su su dafu kullum kisha kofi
biyu safe da yamma.

Sannan ki aya garinta,
kwakwa ma kiyi garinta, dabino ma kiyi garinsa,
sai ki dinga diban cokali bibbiyu ki zuba amadarar
ruwa sannan ki zuba zumarki mai kyau kisha, sai
ki samu kuma gwanda, kankana, abarba, zogale,
citta, lemun tsami, ki markada su kisha.

In anan
maki katsaya yarinya zakiji ki kin cika cindum
daruwan ni'ima sai kin samu martaba ta
musamman agurin miji dan zaijiki kin fita daban
da dukkan sauran mata.

Ki hada da biyayya
tsafta da kuma iya tsara girki mai dadi.

Ummi
tace, toni yanzun yaya zanyi nasamu saiwoyin
nan?

Tace, bari zanba matar ado dake yawan
zuwa kasuwar qauye zata zo miki dasu.

Amma
su gwanda gasu nan bakin titi ko shi sai kice ya
siyo miki, zogale kuwa baki rasa shi gurin
ummarki, har da cittar da alif din da bagaruwan.

Ta ce to, ta tafi gurin umma ta amsa har taje
gida bata daina mamakin tsohuwa ba, ya akayi
tasan duk wadannan hadin matan?

Amma data
tuna cewa 'yar katsina ce sai tace ba mamaki.

Tun ranar alhamis din ta soma aiwatar da
darussan da ta debo daga tsohuwa, safiyar
jumma'a ranar zai bar dakin bishira.

Ya fito tana
sharar tsakar gida ta gaidashi, ya amsa da fara'a,
tare dawani kallo mai fassarar in ba keba.

Cikin
muryar data adana don shi kadai tace, ya abba
ina son in je ayi min zanen fulawa.

Yace jiya kin
fita yau kam a'a. amma ki aika akira mai zanen
tazo ta miki.

Ta marairaice, towa zan aika yaya
abba?

Yace aike ni, ina ne gidan?

Tace layin su
umma ne yace to za'azo ai miki.

Bishira tafito
daga daki tazabga ma ummi harara, Tare dacewa
kisisina.

Abba yakalleta, kema sai tayi miki.

Tace
bana bukata, aikin banza, shikam yafice.

Ummi
kuwa tace gaba da aikinta, ita ko sai tasa kujera
tazauna tana sakin zantuka, eh don kwalliyar
tabanzanta tunda ba a iya biyawa miji bukata.

Allah dai yasa ya fada min komai, to ni me zai
dame ni don 'yar aiki kawai na dauki yarinya.

Tashare min gida, tayi wa mijina abinci, daga nan
fa?

Saita saki shewa, ummi ta ce aranta yau zan
bambance miki.

Birabiskon shinkafa tayi da miya,
ta wadata birabiskon da kayan lambu, miyar ta
dauki nama da bushasshen kifi.

Sannan ta hada
musu kunun aya yaji dabino da madara, ta
aikawa ummanta lokacin da kamal yazo daukar
na ummarsu.

Tasheka wanka taci doguwar rigar
shadda koriya mai duhu, ta kafe dauri tamkar yau
ne daurin aurensu.

Ga fulawar da yaje ya biya
akazo aka zana mata.

Tanajin rigimar muhibba
tafito tazuba mata adan kwano tazaunar da ita
akofar falon mamanta.bishira tafito kicin baki
tasaki tana kallon ummi da tazo wucewa harda
bangazar ummi, nan ko kamshi ya bude ta na
turarukan da ummi ta fesa.

Abba yana yin
sallama ummi tafito da sauri, oyoyo yayana,
bishira tana daga kicin dinta tana kallon su.

Ummi ta rungume shi, sannu dazuwa sahibina.

Ta amshi ledar hannunshi dajakar, yace yauwa
sannu babyna tace inazan kai ledar?

Yace akwai
ta bishira aciki ki ciro.

Ta mika mishi ledar ta
wuce dajakar dakinta.

Ya mika wa bishira lemo
da abarba da yayo musu tsaraba sannan ya wuce
danasu, awulakance ta aje.

Yana shiga ummi
tadan karo kofar yanda bishiran zata iya lekensu
sosai ta gefen kofan.

Ta cire masa hula ta aje
akan madubi sannan ta kunna fanka.

Ta shirya
masa abinci, yauni zan baka har ka qoshi.

Haka
suka yita baiwa juna abaki har suka qoshi.

Yakamo hannunta mai qunshi yana ta sumbata,
wai kamar kada su goge.

Kumatun shi ta shafa
nima yau kamin kyau, koda yake dama kai me
kyaune, ina sonka ya abba sosai.

Cikin jin dadi
ya mannota a jikinshi, nima ina sonki, ina manta
kowa da komai in muna tare, tace ina tsoron kada
wata rana ka juya min baya.

Ya saqalo
hunnuwansa cikin nata ina fata in mutu kafin
lokacin.

Ummi tasomayi masa wasu irin darussa
wadanda tasan yana saurin tada sha'awarshi
nanda nan kuwa tasa shi fita hayyacinsa yakama
surutai.

Ummi ta tabbata bishira tana wurin ta
labe, don haka tai murmushi ta bishi suka tafi
duniyar ma'aurata.

Bishira tamkar tayi hauka sai
kawai ta fado dakin tana fadin, maciya amana,
har yanzun ba afita daga lokacin girkina ba
munafiki.

Abba ya tashi sannan yaja riga yasaka,
ok dama kina labewa ne kiji sirrinmu?

Da taga ya
sauko da zafin rai saita gudu dakinta.

Yabita
yamata tatas, kuma ya fada mata cewa tazo ta
shiga dakin ta zauna ba labe ba, yanzun zai
komane yaci gaba daga inda ya tsaya.

Tayi ta
kuka gashi ba damar zuwa gurin umman bashir
dole ta tafi gidansu.

Shi kam abba shareta ya yi
kosu umma bai fadawa ba.

Sabuwar soyayya ma
ya balle agidan, su ci abinci tare, wanka tare, su
fita yawonsu a qafa ko amota.

In yana gurin aiki
bini- bini ya kira waya, ita kuma ko yaushe cikin
kirkirar girki da kwalliya tare da dadadan kalaman
dazata fada masa take.

Duk lokacin datayi masa
zancen bishira sai ya ce, don Allah ta bar ta ta
huta, ummanshi kuwa 'yar bin qwaqqwafi sai da
tabi ta gano bishira bata nan.

Don haka koda ya
shiga gaisheta sai tace kada ya yarda yaje yama
bata takardarta.

Ita ko tana can uwarta tace ma
mahaifinta abba sakinta yayi, shi kuma yace to
sai tazauna tunda zaman gidan take so.

Amma
su sani daga abinci sai ruwan gidanshi ya amince
tayi amfani dasu sai ko gurin kwana, amma bnda
wannan ko makilin dinshi ta taba bai yafe mata
ba, wannan hukunci yayi musu tsauri.

Ko wata
bata rufa ba taji gidan ya isheta don hajiya zainu
taso maidata makaranta amma yace tagama
boko.

Bishira na zaune ta zuba tagumi hajiya
zainu ta shigo dakiki tace tagumin menene kuma?

Tace, su sumayyah ne wai nace suyi ma muhibba
wanka sukace Allah yakiyaye.

Wai tunda nazo
dakinsu ya lalace da kazanta, hajiya zainu tace
aiba karya suka yiba, don haka ma maida
yarinyar nan za ayi ke kuma ki koma gidan
antynku ko ki tafi abuja gidan aisha.

Tace
baxanje gidan aisha ba, don itama bama shiri,
gara gidan antyn amma gsky ni abarmin 'yata
kuma fakinsan bai sakeni ba.

Tace, inda ubanki
yasan ba saki bne da tuni bai kora kiba?

Don
haka mubarshi haka amma batun 'ya nice zan
maidata.

Ranar da ummi takira ummansu tafada
mata cewa bishirafa tuntuni tayi yaji amma Abba
yaqi zuwa, umma ta kira shi tace inya dawo gurin
aiki tana son ganinshi.
Chapter 15 · 0% Book details