← Book details Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 16

Sashe 9

Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kabir ya ce"To gaskiya da wannan ma, indai shi Alhajin ya ji ya gani, ina ga gara ma kawai ta aure shi É—in, shi Abdul mu bi shi da Allah Ya isa kawai".

Baba ya ce"Yawwa É—an gari, ashe ka gane".

Nan suka gargaɗe ta akan kar ta sake ta amsa auren Abdul, wanda ta kalli maganar a wani abu da ba zai taɓa yiwuwa ba, domin tana ganin indai har sun yarda Abdul ne ya yi aika-aikar kuma suka zargi zai iya wulaƙantata bayan aure, to shi Alhajin waliyyi ne da zai ƙyale ta? Ta saka a ranta ba ta da mijin da ya fi Yaya Abdul ɗinta.

08028966015
[11/21, 6:01 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*

BY
SADIYA ABDULRAZAƘ

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY

PAGE 7

Yau kuwa kafin Nura ya dawo Hasana ta ci kwalliyarta, wata ƙaramar rigar bacci da ta daɗe ba ta saka ba, ita ta ɗakko ta saka, ta fesa turare, ta zauna tana jiran dawowarsa. Yana dawowa ya shiga wanka, kafin ya fito ta tafi ɗakin nasa ta haye katifa ta zauna, har da kunna kallo, ya fito daga wanka yana tura ƙofar ɗakin ya ganta zaune tana yi masa murmushi, ya haɗe rai ya ce"Lafiya?"

Ta ce"Lafiya ƙalau, an dawo lafiya?"

"Ƙalau" Ya amsa a daƙile.

Ta ce"Dama fira na zo taya ka, na ga ka dawo da wuri, ga wannan ɗan abun taɓawa ne".

Ta ƙarasa tana miƙa masa ɗan kwano mai ɗauke da ilokar da ta yi da rana. Ya yi tsaki ya ce"To wace irin fira cikin daren nan?"

Ta ce"Fira dai irin wacce kake yi a majalisa, na yi zaton ka fara dawowa da wuri ne saboda ka ba ni lokacina, mu dinga fira muna tattaunawa game da rayuwarmu da ta Æ´aÆ´anmu bakiÉ—aya".

Takaici ya ishe shi, shi kam ashe ya gudu bai tsira ba, yanzu haka daga wajen ƙawarta Ramla yake, kuma sun yi da ita za su yi vedio call su sha fira, sai ga shi ta kwaso jiki wai ta zo su yi fira, ya saka kaya ya nemi waje ya kwanta, ta ce"Baban Salim, ba ka sha ilokar ba".

Ya ce"Ki ajiye zan sha".

Ta ce"Ni kuwa Baban Salim sai na ga malaman makarantar yaran nan kamar sun fara shirme, sai a kwana uku ba a ba su home work ba".

Ya yi kamar bai ji ta ba, ta ce"Ni dai kamar na je na ji dalili, saboda...."

A fusace ya katse ta da faÉ—in"To tashi ki tafi! Wannan wace irin takura ce haka, na dawo gida kaina yana ciwo ba za ki bar ni na huta ba, wannan ai masifa ce! Ka ware É—akin ma ba ka tsira ba!".

Ranta ya ɓaci, ta ce"Allah Ya huci zuciyarka, ni dai ban ga abun faɗa a nan ba". Ta tashi ta fice ta janyo masa ƙofar.

Ya je ya saka sakata, yana tsaki, a ransa yana ayyana sai fa ya taka mata burki a kan shigo masa É—aki.

Hasana ta zauna a kujerar falonta, tana tunanin yadda za ta yi, har ga Allah ba ta son mijinta ya zama ɗaya cikin masu lalata tarbiyyar yaran jama'a ta waya, ta taɓa ganin chart ɗin banza sau ɗaya a wayarsa, har ta kasa shiru ta tare shi da maganar, ya yi mata kaca-kaca, daga nan ya saka key a wayar yake kuma taka-tsan-tsan da ita, tun daga nan take zarginsa, ko don yawan son matansa dama dole ta kasa yarda da shi, ta san sarai bai daina chart ɗin banzan ba, ballantana yanzu da ya ware ɗakinsa zai ci karensa babu babbaka, sai a ce mace ba ta jan mijinta a jiki, shiyasa yake yi da wasu matan ta waya, to idan da ba ta ja shi a jiki ba, yanzu ta yunƙuro za ta gyara zaman, don kayan baccinta da ta daina sakawa duk ta fito da su, kuma ya ƙi ya ba ta dama.

Ta jima tana wannan tunanin sannan ta tashi ta sake fita cikin sanɗa, ta leƙa shi ta windo, ta hango shi, zaune yana kallon waya yana magana fuskarsa ɗauke da murmushi, ta koma ɗaki ta ɗakko panadol da ruwa a kofi, ta je ta fara ƙwanƙwasawa. Nura yana jin daɗin firarsa, ga iloka yana rakawa da ita kawai ya ji bugun ƙofa, sai da ya zabura, sannan ya ce wa Ramla yana zuwa.

Ya tashi ya je ya buɗe yana cewa"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Hasana kaina fa ciwo yake yi, na samu bacci da ƙyar kin tashe ni".

Ta ce"Dama magani na ga ya dace na kawo maka".

Ya karɓa, ya mayar da ƙofar ya rufe, ta koma ɗaki ta yi addu'a ta kwanta, tana jin zafi a zuciyarta. Da asuba ta idar da sallah ta ɗan kunna data, kamar an yi mata umarni ta shiga status ɗin Ramla, ta ga ta saka "Jama'a namiji ya ware turakarsa fa duniya ne, mace tana can sake da baki tana yawun bacci, shi yana caskalewa" Ta haɗa da emojin dariya.

A na gaba kuma ta saka"Auren mijin wata akwai lada".

Nan take Hasana ta ji ta tsargu, kamar ta wuce sai kuma ta kasa, ta dawo ta ba ta amsa a kai, ta ce mata"Ƴan'mata kenan, ku dai dinga tuna yadda ake caskalewar da ku, an caskale da na gidan fiye da haka, kuma kar lokacinku ya zo ku yi mamaki" Ta haɗa mata da dariya.

A na biyun kuma da ta ce auren mijin wata da lada, ta ba ta amsa da "Musamman mai cefane da nama".

Wajen azhar da Ramla ta duba saƙon, ta ce mata"Ke dai ƙawata ku riƙe mazajenku da kyau, amma tabbas duk wanda ya kawo kanshi wajena sai na tatike shi".

Hasana ta ce"Ku dai bi a hankali, wani sai bayan auren za ki san ko wane ne".

Daga haka suka taɓa fira, aka bar wannan zancen.

Da rana yana cin abinci ta ce"Don Allah baban Salim kayan kwalliya nake so, hodata ta kusa ƙarewa, ina son siyan humra ma, kuma underwears ɗina duk sun tsufa".

Ya ce"Mata kenan, ku fa babu ruwanku da halin da ake ciki, a nemo a ba ku kawai, ana ta abinci ke kina ta wasu tarkacen da ba su zama dole ba".

Ta ce"Hmm! Ai tarkacen ne yake kwasarku ku je ku dinga rawar ƙafa a wajen matan waje, waɗanda ba kyau suka fi ni ba, na ji an ce ma an ce har wannan mai awarar ta bakin kasuwa ita ma son ta kake yi, wannan dai zubar da aji ne wallahi, ka rasa wa za ka so wannan kucakar? Wannan uban kurkur ɗin ne fa ya kwashe ka, amma ka faɗo wallahi".

Ya ture abincin yana nuna ta da yatsa ya ce"Ke ya ishe ki haka! Saboda tsabar raini ni za ki saka a gaba da zancen banza sai ka ce wani É—anki? Ba mai awara kaÉ—ai ba har mai dankali ma son ta nake, wannan mai gurasar ma yau zan je wajenta, ko za ki hana?"

Ya tashi yana cewa"Kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan langa, ina da kuɗin auren, kuma Allah Ya ba ni damar ƙarawa za ki hana ne? Idan na ga dama ma mai ƙosai zan auro wallahi, ta zo kuma idan kika yi wasa ta fi fada a wajena!".

Ta ce"Au kai har wata fada ce da kai?"

Ya ce"Da babu da ba a biyo ni da ilokar toshiyar baki ba".Ya fice daga gidan, yana ayyana dole ma fa ya tattara ƙaryar nan ya tsayar da mace ɗaya ya aura.

********

Ta yi wa Abdul saƙo ya kai biyar bai ba ta amsa ba, amma ya saurara, duka haƙuri take ba shi, tare da alƙwarin za ta jira shi ko shekara nawa ne. Da daddare Alhaji Hashimu ya zo, Baba yana rawar jiki ya zo ya kira Nuratu, tana jin haushi a ce wai mahaifinta ne ɗan aiken saurayinta, ta fito suka gaisa, ta sunkuyar da kai, ya ce"Ya ƙarin haƙuri?"

Ya ce"Da godiya".

Ya ce"Ya jikin naki?"

Ta ce"Na warware".

Ya ce"To ma sha Allah!Mun yi magana da Baba, gobe za a kai ki asibiti sai a cire cikin, bayan sadakar arba'in sai a saka rana ko wata biyu ne, zuwa lokacin na kamalla ginin inda zan saka ki".

Ta ce"Amma Alhaji Baba bai yi maka bayani ba?"

Ya ce"Na me?"

Ta ce"Shi saurayin nawa da abun ya faru sanadinsa, ya ce zai aure ni, kuma har an gama magana da Baba".

Ya yi shiru na É—an lokaci sannan ya ce"Amma bai faÉ—a mini ba".

Ta ce"To zai faÉ—a maka".

Suka yi shiru na ƴan sakanni, sannan ta cigaba"Alhaji na gode da ƙaunarka gare ni, sai dai ina so na faɗa maka ni Abdul shi kaɗai nake so, gaskiya duk wanda ya aure ni ba shi ba, zai iya yin nadama a gaba, saboda ba zai taba samun nutsuwa da ni ba, kai babban mutum ne mai mutunci, kuma kana da ƙima a idona, ba zan so yi maka abin da na tanadarwa namijin da ya yi gangancin aurena ba, saboda haka don Allah Baba ka kama girmanka, kai baban wasu ne, ba zan so yi maka ba daidai ba, tun da ba zan so a yi wa nawa uban ba, na gode sosai Alhaji".

Daga haka ta juya za ta shiga gida, ya ce"ÆŠan tsaya Nuratu".

Ta dawo, ya ce"Na ji duk bayaninki, kuma na fahimce ki, ita rayuwar aure ba a yin ta da tilas, kamar yadda kika ce na kama girmana, na kama in sha Allah, dama ni na zo da ƙauna ne, da kuma niyyar taimako duba da ƙaddarar da ta same ki, yanzu zan janye batun soyayya, zan kuma yi wa Baba bayanin da zai fahimta, idan har kina buƙatar wani taimako ƙofa a buɗe take za ki iya tambayata, a matsayina na mai tallafawa marayu. Sannan goben za a je cire cikin" Daga haka ya juya ya fita, ta shiga gida jiki a mace, amma sai ya kasa faɗawa Baba yadda suka yi, saboda ba ya son haɗa ta da mahaifinta.
Chapter 9 · 0% Book details