Sashe 14
Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ƙarasa da daka masa tsawa, wanda da ace a nutse yake ma tsaf zai iya gano muryarta. Amma da yake ba ya cikin hayyacinsa da sauri ya ce"Na ji, wallahi na ji, kuma zan yi duk yadda kuka ce".
Ta ce"Idan ka yi haka ka taimaki kanka, daga gobe mu fara ganin canji".
Ya ce"To, to,na gode". Ta buga ƙofar da ƙarfi, Nura ya kwanta ya lulluɓa yana ta salati. Da yake shi bacci ba a cin bashin shi, haka Nura ya dinga kokowa da shi, har dai ya samu wahalallen bacci ya kwashe shi, sau biyu yana mafarkin aljanu, sai ya farka a razane ya cigaba da addu'a.
Yana jin kiran sallar asuba ya fito, ya yi alwala ya tafi masallaci, da ya dawo É—akin Hasana ya wuce, ya shiga ya zauna a kujera ya yi shiru, ta gama azkar É—inta, ta tashi ta fita don kunna wuta, da ta É—ota ta dawo É—akin ta zauna ta ce"Baban Salim lafiya kuwa?Na ga ka fito da asubar nan".
Ya sauke numfashi ya ce"Babu komai yanayi ne kawai".
Can ya nisa ya ce"Dama ina son mu yi magana ne mai muhimmanci".
A zuciyarta ta ce"An zo wajen".
Ya ce"Ina so mu haɗu mu gyara rayuwar aurenmu ne dama,duk abubuwan da nake yi miki zan daina in sha Allah! Ke ma sai ki ɗan gyara wasu abun, ki guji ɓata mini rai, ina so mu samu zaman lafiya".
Hasana ta ce"To Alhamdulillah! Ni dama baban Salim ai tun tuni nake so mu yi irin wannan zaman, kai ne ka ƙi fahimtata, in sha Allah ni ma zan dinga kiyayewa".
Ya ce"To, me da me ma kika ci mini za ki siya kwanaki?"
Ta ce"Ban ce zan sayi komai ba".
Ya ce"A'a kin ce za ki canza underwears mana".
Ta ce"Ai ka ce ba ta shi ake yi ba".
Ya ce"Kuma yanzu ba gyara zama ake yi ba? Anjima zan ciro kuɗi na ba ki, sai ki siyo duk abin da kike buƙata".
Ta ce"To na gode, Allah Ya saka".
Ko amin ya kasa cewa don takaicin fitar da kuÉ—in yake yi. Haka kuwa aka yi, ya je ya ciro kuÉ—i, sai ga dubu hamsin kash ya kawowa Hasana, ta nuna farincikinta sosai kuwa, shi kuma jiki a mace, ta ce"Ni akwai wata hoda da Husaina take nema, ta ce za ta turo maka hotonta ta whatsApp".
Gabansa ya faÉ—i tunawa da whatsApp É—in, ya ce"Ta tura miki kawai ki nuna mini, ni na daina chart".
Ta ce"Ikon Allah, saboda me?"
Ya ce"Ba komai kawai na gaji ne".
Har zai fita ya dawo ya miƙa mata mukullin ɗakinsa ya ce"Yawwa daga yau ki dinga kwana a ɗakina, babu amfanin raba ɗaki yanzu, tun da mun fahimci juna".
Hasana ta ce"Oh! Baban Salim kana ta kashe ni da mamaki fa, ina godiya".
Ya ce"Ki godewa Allah kawai".
Ya fice, babu jimawa ya dawo da tarkacen magani, ya ce"Ungo wannan maganin basir ne ki dafa mini".
Ta karɓa tana daurewa saboda dariyar da ta zo mata, ita da ya ce basir ne da shi ta yi zaton ma ƙarya yake yi, kenan ya san da cutar amma ya ƙi neman magani, sai da ya ji uwar bari.
Ta ce"Baban Salim basir ne ya same ka?"
Ya ce"E" Ya fice ba tare da ya jira ta ce wani abu ba.
Ta dafa magani, da ya dawo da daddare ya kafa kai ya kwankwaɗa, ana idar da sallar isha'i ma ya dawo, ta kuwa ci kwalliyarta, cikin rigar bacci, tana ta jan shi da fita yana mazewa, da yaran suka yi bacci, sai ta ɗauki Aiman suka tafi ɗakinsa, shi dai addu'a ya yi ya kwanta, saboda baccin da yake idonsa, ita kuwa sai da ta yi kallo sannan ta kwanta, suka kwana lafiya ƙalau.
LITTAFIN NAN NA KUÆŠI NE A KAN NAIRA 500 KACAL!
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay bank
08028966015
[11/25, 8:33 AM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*
BY
SADIYA ABDULRAZAƘ
*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)
https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY
Marubuciyar
Wani auren
Iya ruwa
Da walakin...
Wutar ƙaiƙayi
Matar shige
Alhakin so
Mataccen buri
Mukullin nadama
Akwai ragi ga wanda ya sayi littafaina guda biyu ko fiye da hakan
08028966015
PAGE 11
Washegari misalin ƙarfe goma Nuratu ta haɗa duka kayanta a akwati, ta yi sallama da ƴan gida, Baba ya zaunar da ita ya ce"To Nuratu, kin ga dai duk wanda ya janyo ka jikinsa shi ba maƙiyinka ba ne ba, saboda haka dole ki bi umarnin Kabiru shi da matarsa, yi na yi, bari na bari, kar ki sake na ji an kawo wani ƙorafi a kanki, wallahi sai na saɓa miki, kuma sai dai ki nemi inda za ki zauna, ba dai gidan nan ba, ba zai taɓa yiwuwa na aurar da ƴa kuma ta zauna min a gida ba, ban da kin zaɓawa kanki haka ai da tuni kin auri mutumin arziƙi kina can ɗakinki hankali kwance, yanzu kuwa sai ki yi ta zama, ƙila ma har ki tsofe a gida bai dawo ƙasar ba, Allah Ya kyauta!" Kalaman da suka raba ta da Baba kenan, saboda haka ta tafi jiki a mace.
Ana kiraye-kirayen sallar azhar Nuratu ta sauka a gidan Kabir, lokacin ba ya gida, Nawwara ta tare ta da murnarta tana cewa"Babbar baƙuwa ta ƙaraso, kodayake ma yanzu kin zama ƴar gida, sannu da zuwa".
Ta ce"Yawwa Anti na gode".
Ta yi wanka ta yi sallah, tana cikin cin abinci sai ga kiran Kabir, ta É—auka ta gaishe shi, ya ce"Kin raho?"
Ta ce"Ai har na ƙaraso ma".
Ya ce"Ma sha Allah!".
Bayan ta gama ta fito falo, suna ta fira da Nawwara, nan take faɗa mata ta samu aikin koyarwa a wata primary, tana zuwa kullum daga ƙarfe bakwai zuwa ƙarfe biyu, Nuratu ta taya ta murna, Nawwara ta ce"Kin ga yanzu ke kaɗai za mu dinga bari a gidan kenan, sai na dawo".
Nuratu ta ce"Ai babu komai, Allah Ya taimaka".
Nawwara ba ta taɓa haihuwa ba, saboda tana da matsala a mahaifarta, suna zaune lafiya da Kabir, kuma tsawon shekarun da suka yi bai damu da matsalar rashin haihuwarta ba, mafi yawan lokuta ma shi ne yake nuna mata muhimmancin yarda da ƙaddara, yana kyautata mata da ba ta kulawa daidai gwargwado, sai dai akwai wata ɓoyayyiyar hallayarsa wacce hankalinta bai kai kanta ba, ballantana ta yi nazari, ba ta taɓa sanin Kabir mane min mata ba ne, saboda yana yin komai cikin tsari, sannan ba mai tsananin da za ta yi saurin ganewa yake yi ba. Sau uku tana ɗakko wata yarinyar cikin ƴan'uwanta, domin ta zauna a gidan ko za ta samu ta rage kewar zaman kaɗaici, sai yaran sun zo suna murnar zaman gidan, daga ƙarshe sai su rikiɗe su ce su ba za su zauna ba, duka su ukun ba ta gano dalilin barin su gidan ba, Kabir ba ya iya ɗauke kansa a kan mace, ƙananun yaran nan su uku duk ya gwada masa halinsa, amma bai samu cikar muradinsa ba, wannan halin nashi ne yake korar su daga gidan, dangi duk an sani, ana kallonta a fanko, domin har mahaifiyarta ta sani, amma ta ƙi faɗa mata, kuma ta hana a faɗa mata, sai dai ta taka mata burki a kan sake ɗaukar wata yarinya da sunan riƙewa, ta ɓoye mata ne saboda ta zauna lafiya da mijinta, sai dai tana yawan yi masa addu'ar shiriya, saboda Kabir yana da kirki, yana girmama murane, wannan halin ne kawai matsalarsa.
Da daddare bayan ya dawo sun gaisa da Nuratu, ya tambaye ta ta taho da kayan lefenta? Nan ta sanar masa ai bai yi mata lefe ba, sai kuwa ya hau faÉ—a yana cewa"Me yake nufi kenan? Wannan fa ya samu dama da yawa wallahi, ga cutarwar da ya yi miki kuma saboda samun sake lefe ma ba zai yi ba? Ki ba ni lambarsa".
Gabanta ya faÉ—i, saboda ba ta so wani ya gano Abdul shi kansa ba son auren yake yi ba, ta sunkuyar da kai ta ce"Yaya ba haka ba ne, ka san bai daÉ—e da tafiya ba, duka wata biyu kenan, yanzu ma albashin wannan watan ne fa ya ba da sadakin, ya ce gaba zai yi mini lefen".
Ya taɓe baki ya ce"Allah Ya kyauta, wannan auren amma sam inda an bi shawarata da an bar shi".
Nawwara ta ce"A'a ka daina cewa haka Honey, tun da suna son junansu komai zai daidaita".
Ya ce"Tashi mu je na samo miki kaya, na san nakin duk tsofaffi ne".
Nawwara ta ce"Mu je na raka ku, dama ina son siyan wani curry".
Ya ce"A'a rubuta mata dai ta É—akko miki, kullum sai kin fita ko gajiya ba kya yi?"
Ganin ta canza fuska kamar ba ta ji daÉ—i ba, ya yi murmushi ya ce"Ke wai ba ki gane me nake nufi ba ne? Ni dai ki tafi ki yi wannan shirin naki mai gigita ni, kawai ina dawowa na gan ki a turaka, ya fi miki wannan fitar".
Ta yi murmushi tana faÉ—awa Nuratu sunan curryn, suka tafi tana cewa sai sun dawo.
A hanya yake ce mata"Yanzu ke Nuratu kina tunanin nan da shekara nawa mijinki zai dawo?"
Ta ce"E to, da zai tafi cewa ya yi shekara biyu zai yi, yanzu tun da an yi auren ƙila ma ba zai kai hakan ba".
Ya yi murmushi ya ce"Kuma ke za ki iya riƙe kanki har tsawon shekara biyun?"
Ta ce"To Yaya ka ce zan zauna a gidanka ai, idan ma an kwana biyu zan iya komawa gidan yayan babata, sun ce na koma can, sai na jira sanda zai dawo, idan kuma babu dama sai na fara wata sana'ar na dinga yi wa kaina komai".
Ya ce"Nuratu kenan, ni fa ba wannan riƙe kan nake nufi ba, ai bai kamata mace ta dinga ciyar da kanta ba, ballanatana ma irinki wacce ta haɗa komai da najimi zai so".