← Book details Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 16

Sashe 16

Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Ta sauke gwauron numfashi, sai dai ta kasa cire rigar, don a ganinta rigar nan ta jikinta da ita da babu duk É—aya suke, ta yi vedion a haka da rigar, ta tura masa.

Tana turawa ta ajiye wayar tana jin babu daɗi, duk da ba haramun ba ne, sai can anjima ta ɗauki wayar domin ta ga amsar da ya bayar, ƙirjinta ya yi wata mummunar bugawa ganin kamar mutum biyu ta turawa, da sauri ta kalli lambar Yaya Kabir wanda har saƙon ya nuna blue tik alamar ya gani, ta miƙe tsaye tana ɗora a ka, ita ta ma manta da ana delete saboda yadda kanta ya ɗauki zafi, salati kawai take jerowa, wajen minti biyar kafin ta dawo cikin nutsuwarta, ta zo ta goge da sauri.

Kabir wanda daÉ—i ya gama rufe shi, don wannan alama ce da take nuna ta gama amsar tayinsa, tuni ya tura shi zuwa laptop É—insa don ya more kallo da kyau, saboda haka ko da ya ga ta goge bai wani damu ba, sai ma stikar godiya da ya turo mata.

Shi kuwa Abdul a na shi ɓangaren, yana kallon vedion zuciyarsa tana tafasa, wani kishi ne yake azabtar da zuciyarsa, a fili ya ce"Nuratu in sha Allah wannan vedion sai ya zama silar shigarki ƙunci na har abada, wannan vedion sai ya hana ki zaman aure, sai kin dawwama a gida kin tsufa kin mutu babu aure, babu ɗa babu jika, wannan ce hanya ma fi sauƙi da zan rama cin amanar da kika yi mini" .

LAST FREE PAGES!

To mutanena mu numfasa a nan, ko kun hango girman matsalar da Nuratu ta jefa kanta kuwa? Shin da gaske Abdul zai iya take ƙauna ya aiwatar da furucinsa a kan wacce ya fi so duk duniya, ashe ƙauna tana rikiɗa ta zama ƙiyayya? Yaya Kabir zai yi da wannan vedion? Shin zamanta a gidansa zai yi tsayi ko na ɗan lokaci ne? Na ba ku satar amsa? Nura zai yi ta aure-aure a wannan labarin, amma a ƙarshe ya zamansa da Hasana zai kasance? Akwai tarin ƙadarori a kan Nuratu, ku dai kar ku bari a yi babu ku, da ɗarinki biyar ki sha karatu.

8028966015
Sadiya Abdulrazak opay bank

Shaidar biya ta nan
08028966015
Chapter 16 · 0% Book details