← Book details Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 16

Sashe 5

Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ce"To ka faɗa masa jikin da sauƙi sosai, magani ma ya isa".

Ya faka motar, ya É—akko waya ya kira Alhaji, ya yi masa bayanin da Nuratu ta yi, Alhaji ya ce kawai ya wuce su tafi asibiti, idan ma maganin ne su ba ta a can".

Ba ta sake cewa komai ba, har suka ƙarasa asibitin. Tun kafin zu je Alhaji ya yi magana da likita, don haka kai tsaye direban ya rakata inda ya kwatanta masa, ta zauna a kujera sai raba ido take yi, hannunta yana dafe da mararta ta cikin hijjabi, gani take kamar likitan yana kallonta zai gane tana da cikin. Ya tambaye ta me yake damunta? Ta ce"Zazzaɓi ne kawai kuma ya riga ma ya sauka tun a hanya".

Ya ce"Ma sha Allah! Amma Alhaji ya ce ko abinci ba kya ci, ya ce a saka miki ruwa saboda ki samu ƙarfin jikinki, sannan zazzaɓin ƙila malaria ce, za mu yi miki gwaji mu gani".

Ƙirjinta yana ta dukan uku-uku ta ce"Likita, ni fa ina jin ƙarfin jikina, kawai ku ba ni magani ya isa".

Likita ya yi murmushi, don ya sabada mara lafiya mai gardama, ya ce"Ki yi haƙuri Hajiya, a yi miki yadda ya dace kawai".

Ya tura su wani ɗakin, wajen wata nurse, ita ta ɗibi jininta, sannan aka saka mata ruwa ta kwanta gabanta yana ta faɗuwa, tana ayyana ƙila yau ce ranar ƙarshe cikin ranakun farincikinta na gidan duniya.

A ɓangaren likita bayan sun fita sai ga kiran Hajiya Laila, uwar gidan Alhaji, suka gaisa ta ce"Doctor yarinyar da aka kawo daga wajenmu me yake damunta?"

Ya ce"Yanzu dai za a duba, zazzaɓi ne take yi, sai rashin ƙarfin jiki, an tafi saka mata ruwa".

Ta ce"Ok, don Allah kar ka bari ta tafi, sai ka samu adireshinta ko lambar waya, ka ajiye mini account deteils É—inka".

Ya ce"An gama Hajiya godiya nake". Suka ajiye waya.

08028966015
[11/20, 9:35 AM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*

BY
SADIYA ABDULRAZAƘ

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY

PAGE 4

Sakamako yana fitowa likitan Hajiya Kubra ya fara kira, ya sanar mata yarinyar ciki ne da ita na sati tara, sai kuma malaria. Hajiyar ta yi murmushi ta ce"Idan ka tashi sanar masa ka ƙara da cewar tana ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki". Likita ya amsa, amma a zuciyarsa yana ta auna yiwuwar hakan, domin babban laifi ne, har a cikin aikinsu, sannan yana gudun Alhaji ya bincika ya gane ba haka ba ne.

Har allurar bacci Alhaji ya sa aka yi mata, don ta samu hutu, ba ta san tsayin lokacin da ta ɗauka tana bacci ba, ta dai farka ne kawai ta ga Mama Karime zaune a kan sallaya, gefen gadon da take kwance, gabanta ya faɗi, ta tashi zaune, har an cire ƙarin ruwan, Mama Karime ta ce"Sannu Nuratu kin tashi?"

Sai ta kasa amsawa, kallonta dai take yi, tana son karantar fuskarta, don ta samu wani haske a kan zargin da take yi na fallasar sirrinta, sai dai ba ta ga komai a fuskar Mama ba, ta ce"Mama ba su sallame ni ba?"

Ta taɓe baki ta ce"Jira suke ki tashi, amma ke wannan gadon asibitin ai a yanzu sai ya fi yi miki daɗi fiye da gidanku".

Gabanta ya faÉ—i, tana rabon ido ta ce"Mama saboda me?"

Ta ce"Saboda cikin jikinki, da ƙyar aka fitar da babanki daga asibitin nan, don cewa ya yi sai ya kashe ki, da tuni sai dai ki farka ki ji ana man Rabbuka?"

Bugun zuciyarta ya tsananta, tuni tsoro ya dirar mata, ba ta sake shiga tashin hankali ba sai da Mama ta cigaba da faÉ—in"Babban abun damuwar ma asirinki ya tonu, don na san zuwa yanzu maganar nan ta fantsama cikin gari, tun da a gaban Zainabu aka yi komai".

"Innalillahi! Me ya kawo ta?" Ta tambaya tana sakin kuka.

Mama ta ce"Ta je gida kai miki abinci, aka faɗa mata kina asibiti, dama lokacin babanku ya ce gado aka ba ki, na ce ya kamata na bi ki, shi ne ta ce mu tafi tare, shigowarmu ke da wuya, muka samu ana kokowa da babanki. Nuratu kin ba mu mamaki, ba ki kyautawa Salamatu ba". Ta ƙarasa a raunane.

Ta kifa kai a cinyarta ta rushe da kuka, shikenan asirinta ya tonu, abin da take ta ɓoyewa yau ya fito fili, tunani take yi yanzu ya za ta yi? Wane bayanin za ta yi musu su fahimce ta? Da wane idon za ta kalli Abdul? Sannan idan ta faɗa masa dalilita zai yi mata uzuri kuwa?"

"Ina wayata?" Ta tambayi Mama.

Ta ɗakko ta miƙa mata, ta danna ta ga ƙarfe takwas da rabi na dare, ta sakko daga gadon, ta shiga banɗaki ta yo alwala, ta fara jero salloli, lafin ta idar Mama ta zuba mata abinci, ta miƙa mata tana cewa"Wannan abincin duk Alhaji ne ya aiko miki, wallahi Nuratu kin yi asarar miji kamar shi, don kuwa shi ma zuwa yanzu ya samu labari, ai da mutunci ma, idan wani ne na tabbata korar kare zai sa a yi mana daga asibitin".

Nuratu ta fara cin abincin a hankali, tana hawaye.

Mama ta cigaba"Idan kuma Allah Ya tarfa wa garinmu nono sai ki ga duk da hakan bai janye ba, tun da wasu suna sane ma suke auren karuwa, saboda huce takaici ta wani ɓangaren".

Sosai surutun Mama ya dame ta, saboda tana ruguza mata lissafin da take yi ta tafkawa a zuciyarta. Fatanta dai a ce yau a asibitin za ta kwana, indai lissafin da ta yi yanzu ya tafi daidai, to a tasha za ta kwana, washegari ta bar garin.

Ƙarfe tara da ƴan mintuna, sai ga direban ɗazu da ya kawo su, ya shigo ya ce"Hajiya za mu tafi, in ji Alhaji".

Nuratu ta ce"Sun sallame ni?"

Ya ce"E". Ya kwashi kanukan abinci ya wuce gaba.

Mama ta ce"Sai ki tashi mu wuce, ƙiyamarki ta tsaya cak yau".

Wani sabon kuka ya zo mata, duk nuƙu-nuƙun da ta tsaya yi don Mama ta yi gaba, abun bai yiwu ba, haka ta saka ta a gaba suka shiga mota, a ciki suka tarar da Alhaji Hashimu, sai kunyar duniya ta rufe Nuratu, duk da ba son shi take yi ba, amma ba ta so a ce zai yi mata kallon mara tarbiyya ba, haka motar ta yi tsit har suka ƙarasa gidan.

Baba da abokansa biyu suna zaune a ƙofar gidan, ya taso da sauri ganin motar Alhajin, sai dai Nuratu tana fitowa ya gimtse fuska, yana huci.

Wani mugun haushinta yake ji, gabaɗaya ta canza masa lissafi. Suka shiga daga ciki, a zaune Alhaji ya ce su tsaya, Nuratu za ta wuce ya ce ita ma ta tsaya, ta dawo ta tsugunna kanta a ƙasa tana hawaye.

Baba ya ce"Don Allah Alhaji ka yi haƙuri, wallahi da na san da wannan badaƙalar a jikinta da ban yi maka alƙawari ba, ɗan yau ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba!".

Alhaji ya ce"Na sani, kuma a yadda na samu labarin tarbiyyar Nuratu na san wannan ƙaddara ce, kar ku damu, ni tsakani da Allah nake son yarinyar nan, musamman yanzu da wannan ƙaddarar ta faru da ita, na san rayuwarta za ta iya shiga garari, saboda Baba ni na ji na gani, zan aure ta na kau da ido a kan komai, da an cire cikin shikenan".

Baba ya fara jero godiya har da kukansa, Alhaji yana cewa "Babu komai".

Sannan ya yi wa Nuratu nasiha sosai, tamkar tsakanin uba da ƴarsa, har ta ji a ranta wannan mutumin ƴaƴansa sun yi sa'ar uba, ba kamar ita ba, ya ƙara da roƙon Baba kan kar ya ce zai dake ta, ko wani hukunci, addu'a ita ce kaɗai mafita, daga haka ya tafi, ita ma ta shiga gida, ta saka sakata a ɗaki, duk bugun da Baba ya yi ba ta buɗe masa ba.

Ba ta taɓa zaton mutumin nan zai ce zai aure ta a hakan ba, ta san auren nasa rufin asirinta ne, amma ya za ta yi da soyayyar Abdul ɗinta? Sai ta ɗakko wayarta, ta yi masa sallama ta whatsApp, yana online bai duba ba har tsawon mintuna, sai ta danna voice, sai dai ta kasa cewa komai, har tsawon sakan goma, sai ta sake shi a hakan ya tafi, wannan karon da wuri ya duba, bai ce mata komai ba, ta ajiye wayar ta kwanta.

Can tsakar dare kuma ta tashi ta fara haɗa kayanta a wata tsohuwar akwatin Mama, wanda ta bar mata ita, kayanta ne dama a ciki, ta saka komai ta ajiye ta tsaf, sam ba ta runtsa ba, kiran sallar farko a kunnenta, ta fito a hankali, tana jan akwati ta fice daga gidan a hankali, ta karo ƙofar, ta fara sauri don gudun wani ya biyo bayanta, tafiya mai nisa ta kai ta tasha, ta tarar da tsirarun mutane, ta zauna ta fara hawaye tana fatan Allah Ya sa a karɓe ta a inda za ta je, sannan ta samu buta, ta yi alwala ta yi sallar asuba wanda har an kusa idarwa. Ta faɗawa kwandasta Kaduna za ta je, aka saka ta a motar, ta yi zaune tana jira ta cika, zuciyarta tana ta dukan uku-uku. A daidai lokacin ne kuma Mama Asabe ta leƙa ɗakinta, ta ga ba ta nan, nan ta hau cikiya a tsakar gida, kowa ya fito ana jajantawa.

********

Misalin ƙarfe goma Nura ya kira Hasana a waya, tana ɗagawa ya ce"Ke maza ki buɗe wannan ɗakin ki share shi tass! Gani nan zuwa".

Ta san dai ɗakuna uku ne a gidan, ciki da falon da take ciki, sai kuma falle ɗaya, wanda take saukar baƙinta, da kuma keken ɗinkinta a ciki, ta san shi yake nufi, amma hakan bai hana ta tambayarsa ba"Wane ɗakin?"

Ya ce"Wannan wace irin tambaya ce? ÆŠayan É—akin nan dai, da kike saka shirgi, ba na so na zo na tarar da komai a ciki".

Ta ce"To saboda me? Yanzu ina zan kai keken nawa?"

Ya ce"Wannan kuma ya rage naki, idan za ki kai shi bola zan taya ki". Ya kashe wayar.
Chapter 5 · 0% Book details