← Book details Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 16

Sashe 2

Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke dalla can kwashe shi ki fice mini!" Cewar mijin nata, ko a jikinta don inda sabo ta saba da halinsa na masifa, gabaɗaya shi kullum a zabure yake ba shi da lokacin nishaɗi tare da ita sai dai idan yana tare da yaransa ko kuma wayarsa, yaran da sai sun zama mutane yake fara son su, amma yaro indai ba ya tafiya ba ya magana to ba mutum ba ne a wajensa, ko kallo nai ishe shi ba, da safen nan idan tana can tana girki Aiman ya tashi, ta sha zuwa ta tarar ya dawo da shi falo, sauro suna ta cizonsa, idan kuma ta yi magana ya ƙure ta da zagi a gaban ƴaƴanta.

Haka ta goya yaron, ta tashi sauran yaran Salim da Amir ta shiga yi musu shirin makaranta, sanda ta kammala komai bakwai da rabi har ta yi, don sai ta dafa musu indomi wacce za su tafi da ita makaranta baya sun ci taliya a gida, sai lokacin Nura ya fito cikin shirinsa na fita, ya buga uban wanka ya sha wani yadi daga gani ma yau ya fara saka shi, ya kafa hula, kamar mutumin kirki, irin wankan da ya sace zuciyarta ya yaudare ta da daɗin bakin sama mata rayuwar soyayya mai cike da farinciki, sai ga shi ya kawo ta baƙin gidansa mai cike da ƙunci ya kulle, ba ta da wani amfani a idonsa sai na bautarsa shi da ƴaƴansa, suka karya a tare, ya ɗauki mukullin babur ɗinsa ya haɗa kan yaran za su fita, ta ce"Me za a dafa anjima? Babu kayan miya a gidan".

Ko kallonta bai yi ba, ballantana ta samu amsa, wannan yana É—aya daga cikin halinsa wanda ta saba da shi, suka fice tana tunawa yaran addu'ar fita daga gida.

Da rana ta dafa shinkafa da wake, sauran yajin nata ma kaɗan ne, ga shi ba ta da ko sisi ballantana ta ƙara barkonon, ƙarfe ɗaya yake ɗakko yaran daga makaranta, sai ya ci abinci ya koma kasuwarsa, wacce babu nisa da gidan nasu, dab da yaran za su dawo ƙawarta Ramla ta zo, ta ce daga kasuwa take shi ne ta biyo, ta zubo mata abinci, suna ta fira cikin nishaɗi.

Tana jin ƙarar babur ɗinsa gabanta ya faɗi, don ba ta son ya shigo gidan tana da baƙi, don kar ya yi mata faɗa a gabansu har a san halin da take ciki, don ma dai ya san Ramla.

Ya shigo da sallama, suka amsa, Hasana ta yi masa sannu, ya amsa idonsa a kan Ramla, wacce take kicikinar mayar da hijjabinta, ya kalli abincin da yake gabanta ya kalli Hasana ya ce"Ke wai Hasana wace irin mace ce mai taurin kai?"

Sai ta sha jinin jikinta ta sunkuyar da kai ƙwalla har ta kawo idonta, ya ce"Sau nawa zan faɗa miki ki daina dafa mai da yaji a cikin gidan nan? Ta ya zan dinga yin cefane mai kyau kina nunawa duniya gidana babu rufin asiri? Nama ya ƙare ba za ki sanar da ni ba?"

Ita dai ta yi shiru cike da takaici, don rabon da ta ga nama tun na babbar sallah.

Ya kalli Ramla ya ce"Wannan ƙawar taki don Allah ki dinga yi mata faɗa, wai idan kana da shi ba ka ci ba me za ka yi?"

Ta É—an yi murmushi ta ce"Gaskiya kam ba ta kyautawa".

Ya ce"Tsakani da Allah fa! A ce za ka yi baƙuwa ka dafa garau-garau, alhalin ba babu ba ce, Ina zuwa".

Sai ya fice.

Hasana ta sauke ajiyar zuciya, suka cigaba da taɓa fira, kafin ta tashi za ta tafi, ta rako ta tsakar gida, sai ga shi ya dawo da ledoji a hannunsa, ya ce"A'a Ramla kike ko wa? Ba dai tafiya za ki yi ba".

Ta ce"Tafiya zan yi baban Salim".

Sai ya miƙa mata ledojin ya ce"Ga wannan balangu ne da lemo, wallahi mai kaji bai fara gasawa ba, ba zai yiwu a zo gidana a ci garau-garau ba, alhalin Allah Ya hore mini".

Hasana ta san Ramla da kwaɗayi, ai kuwa babu musu ta karɓa har tana rusunawa, ta yi masa godiya.

Ya ce"Maman Salim bari na koma kasuwa, yau ba na jin yunwar ma".

Baƙinciki ya hana ta cewa komai, ta rufe ƙofar gidan, ta koma ta zauna tana jin zafi a zuciyarta, zuwa yanzu ta fara zargin Nura aljanun son mata gare shi, babu damar ta yi baƙuwa ya ƙyalla ido ya ganta sai ya ruɗe ya yi ta kaiwa da kawowa, yana siyayyar ƙarya wacce ita ba ya yi mata, ƙawayenta sun sha faɗa mata mijinta ya bi su gidansu yana son su daga haɗuwa a gidanta, wasu ma matan aure ne, sai dai idan ya bi su hanya su faɗa masa ba, shiyasa yanzu sam ba ta son ma ta yi baƙuwa mace indai ba ƴar'uwarta ta kusa ba ce, group ɗinta na makaranta duk ta fita saboda yadda ake yi mata habaici a fakaice kowa ya san mijinta na mamajo ne.

08028966015
[11/17, 9:28 AM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*

BY
SADIYA ABDULRAZAƘ

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY

PAGE 2

Nura ya jima kafin ya dawo, sai da ta shiryar yara suka tafi islamiyya, sai ga shi ya shigo yana haÉ—e rai, Hasana da zuciyarta take a zafafe bayan ya zauna ta kalle shi ta ce"Baban Salim yanzu haka daga gidan su Ramla kake ko?"

Sai kuwa ya haÉ—e gira ya fara zabure-zaburen borin kunya yana cewa"Ko kuma uwarta ba! Wai ke Hasana me kika mayar da ni ne? Yanzu rainin naki na lura kullum gaba yake yi ba baya ba!".

Hasana ta ce"Ai na fi kowa sanin halinka shiyasa na faÉ—a, idan ba haka ba meye na siya mata balangu, bayan rabon mu da nama a gidan nan tun watandar sallah?"

Ya fara jinjina kai, ya ce"Laifina ne, wallahi laifiina ne, saboda na fitar da ke kunyar ƙawarki ko?"

Ta ce"Ka fitar da kanka dai, ko kuma na ce ka shigar da kanka, don na tabbata ko ba daga gidansu kake ba, to za ka je".

Ya ce"Ai ke ba ki da hankali, bai kamata ma na biye miki ba".

Ya juya zai fita, ta ce"Ka tsaya na kawo maka abincinka".

A fusace ya ce"Ba zan ci ba". Ya fice yana ta mita da borin kunya.

Ba ta wani damuwa ba, saboda Nura ya sabarwa da zuciyarta irin wannan ƙuncin, ta ci abinci ta yi wanka ta ɗauku wayarta, tana kunna data ta ga Ramla online, ta ɗaga mata hannu, ta ce"Ya kika je gida?"

Ramla ta ce"Lafiya ƙalau, na gode fa sosai, kin gan ni nan ina cin balanguna hankali kwance".

Hasana ta tura mata stikar dariya. Sannan ta ce"Yau kin samu É—an rakiya ko?"

Ramla ta ce"Mijinki yana da kirki wallahi, kin ga har gida ya kawo ni fa, ku dai Allah Ya taimake ku, mu ga mu a gida ba karatun ba, ba auren ba, aure mai daɗi wai har faɗa ake miki don nama ya ƙare ba ki sanar ba" Ta haɗa maganar da emojim dariya da mamaki.

Hasana ta ce"Hmm! Ke dai Allah Ya ba ki na gari, auren wuri ba shi ne kwanciyar hankali ba, dace a gidan auren ko da an samu jinkiri shi ne".

Ramla ta ce"Hakane" Sai ta kashe datar, dama ta so ta san Nura ya kai ta har gidansu ne ko a hanya ya ajiye ta, tun da ta ji ya kai ta tana da tabbacin zai koma, sai dai za ta zubawa Ramla ido ta ga za ta kawo mata labari ko za ta karɓi mijin nata, tun da har ga shi tana yabonsa, sannan ta ƙosa da zaman gidan dama, da wannan tunanin ta kai yammaci, sai dab da magriba ta tashi ta dafa farar taliya, don har yanzu bai aiko mata kayan miyan ba. Ana idar da sallah ya shigo, ya ce ta kai masa ruwan wanka, bayan ya gama ya zo falo ya zauna,yana ta faman danna waya, ta kawo masa taliyar, ya buɗe ya yi tsaki, ya fara ci, duk rabin hankalinsa a kan waya yake, haka kawai ta zargi da Ramla yake chart, ta ɗauki tata wayar ta kunna data, sai ta ga Ramla ba ta online, ta sauke ajiyar zuciya, amma har lokacin tana fargaba, ta rasa ya za ta yi ya daina janyo mata abun kunya irin haka, ana fara sallar isha'i ya tashi zai fice, yana cewa Salim"Sai na dawo".

Salim ya ce"Daddy ina za ka tafi? Don Allah ka zauna yau kar ka fita".

Ya yi dariya yana É—aga Amir sama ya ce"Ai dole na fita, idan na zauna a gidan me zan yi Salim? Zuwa zan yi na gyara wasu abubuwa".

Salim kuwa da surutu ya ce"Wani abu?"

Ya ce"Kai yaro ne Salim, ina zuwa kar ka yi bacci ka ji?"

Ya gyaɗa masa kai, Nura ya fice yana kiran waya, idan ya yi irin wannan fitar sai ya kai sha biyu har ƙarfe ɗaya, kullum sai ta yi bacci yake dawowa.

Zuwa takwas da rabi yaran sun yi bacci, ta yi musu shimfiɗa a falo, ta yi musu addu'a, sannan ta rufe falon ta shige ɗaki, ƙofar gidan dama kodayaushe a rufe take, sai dai idan ya dawo ya saka mukulli ya buɗe, dayake tana da nauyin bacci ba kullum ba take jin dawowar tasa ba.

Ta sauke Aiman daga bayanta ta kwantar, ta yi masa addu'a, sannan ita ma ta yi, babu jimawa bacci ya ɗauke ta, haka take yi kafin ƙarfe tara ta yi bacci, saboda babu ɗan fira.
Chapter 2 · 0% Book details