← Book details Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 16

Sashe 11

Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta idar da sallar isha'i ta kasa tashi daga sallayar, gabaɗaya rayuwar ta yi mata zafi, ta rasa inda za ta saka ranta, a gaskiya ba ta son zaman gidansu Abdul, gabaɗaya ɗaki uku ne a gidan, na iyayen ɗaya, na Abdul da ƙannensa maza ɗaya, sai na ƙannensa mata, yanzu a ina za a saka ta kenan? Ba gara ma a bar ta a nan ɗakin babarta ba, idan ya zo ya dinga turo mata da kuɗin abinci. Da shi ya kamata ta yi shawara, amma ya ƙi sauraonta sam, ba ta da mafitar da ta wuce ta sake tuntuɓarsa, don haka ta ɗakko wayarta, ta kunna data, yawanci datarsa a kunne take, sai dai idan ya ji shigowar saƙo ya duba, ta same shi online, ta yi masa sallama, tare da stikar hawaye, ya duba bai ce komai ba, ta yi masa voice ta ce"Assalamu alaikum, Yaya ina wuni? Fatan kana cikin ƙoshin lafiya, a yau burin nan namu na tsawon lokaci ya cika, mun zama mallakin juna, sai dai kuma abun ya zo mana akasin hasashenmu, wannan yana rubuce cikin ƙaddararmu, ya kamata mu karɓe ta, Yaya tun da an cire cikin nan don Allah ka manta da komai, wannan ya zama tarihi, a tunanina soyayayyar da muke yi wa juna ta yi ginuwar da wannan ɗan saɓanin bai kai ya rushe ta ba, ina ƙaunarka har gobe angona".

Ya saurara bai ce komai ba.

Ta sake cewa"Yaya ya ka tsara bayan auren nan? Yanzu zan zauna a nan gidanmu ne, ko haya za ka kama mini?"

Sai ta ga ya fara typing bayan ya saurara, tana ta zumuɗin ganin me zai rubuto, sai ta ga ya ce"Ni na ba wa kura ajiyar nama? Kin san maza sannan kuma na kama miki haya? Mtwsss" Ya ƙarasa da tsaki.

Hawaye ya sakko mata, ta ce"Ko kowa na duniyar nan zai zarge ni, ban taɓa tunanin har da kai ba Yaya, tabbas na yarda a yanzu duniya ba ta da tabbas, na gode da komai, sannan zan ɗauki ƙaddarar zama da kai a duk yadda ka tsara zaman namu".

Sai ma ya kashe data ba tare da ya sake cewa komai ba, sabon kuka ya zo mata, ta rasa da wa kuma za ta yi shawara, wa zai saka Baba ya yarda ta yi zamanta a gidansu? Ta ya za ta fara zama a gidan su Abdul, bayan ko shi kansa bai damu da ita ba, ballantana ya tilasta wa Æ´an'uwan shi kula da ita? Ta samu kanta da kiran lambar Yaya Kabir, ya É—auka suka gaisa, ya ce"Amarya, dama ina da niyyar kiranki, É—azu Baba ya ce an É—aura".

Sai ta fara kuka ba tare da ta ba shi amsa ba.

Ya ce"Nuratu, akwai wata matsalar ne?"

Ta ce"E Yaya". Nan ta faɗa masa duk yadda Baba ya tsara, amma ba ta faɗa masa wulaƙancin da Abdul ɗin yake yi mata ba, ta ɗora da faɗin"Don Allah ka cewa Baba gara zamana a gidanmu, can gidan nasu ban ga inda za su ajiye ni ba, kuma ni ba zan iya zama gidan haya ni kaɗai ba".

Yaya Kabir ya ce"To zan yi masa magana in sha Allah! Ki daina damuwa".

Suna gama wayar kuwa ya kira Baba, yana jin wannan wata dama ce ta zo masa wacce zai cika muradin da ya daÉ—e a zuciyarsa, bayan sun gaisa da Baba ya tambaye shi, Nuratu ta tare? Baba ya ce"Ina fa? Babu ma mai zancen tarewar, ni dai zuwa gobe na ba su, ko ba su zo ba zan tura ta, ta tafi can gidan iyayen nashi".

Kabir ya ce"A'a Baba kar ka yi hakan, ni a ganina kamar Nuratu za ta takura a can É—in, me zai hana ta zo nan gidana ta zauna kafin a tsayar da maganar yadda za a yi?"

Baba ya ce"To indai za ta je ni ai ba ni da wata damuwa, ta tattara ta tafi".

Ya ce"To zuwa gobe zan turo mata kuÉ—in mota sai ta taho, kamar za ta fi samun nutsuwa a nan É—in". Suka yi sallama Baba yana ta godiya.

Sannan ya kira Nuratu, ya fala mata yadda suka yi da Baba, ta ce"Amma Yaya har tsawon wane lokaci zan zauna?"

Ya ce"Har sanda zai dawo ƙasar mana".

Ta ce"Amma Yaya babu takura kuwa?"

Ya ce"Wa za ki takurawa? Ni da nake É—an'uwanki ko matata wacce tun tuni take sha'awar ki dawo gidanta da zama?" Ta yi shiru.

Ya ce"Babu wata matsala, sai dai ko idan kin fi son zaman can gidan nasu, don ban ga alamar Baba zai yarda ki cigaba da zama a nan ba, idan kuwa ya yarda to nan gaba abinci ma sai ya gagare ki, ki dai yi tunani, idan kin amince ki turo account na saka miki kuÉ—in mota, idan ba ki amince ba sai ki sanar mini, daga haka ya katse wayar.

Nuratu ta zauna shiru tana tunani, ta san matarsa tana da hal mai kyau da son mutane, sai dai kuma wannan fa dogon zama ne, tana tunanin anya kuwa abun zai ɗore ba za ta ƙosa da ita ba? A zuciyarta dai ta ji ta amince, amma a yanzu a ƙarƙashin ikon mijinta take, saboda haka dole ta shawarce shi, ko ma a ce ta nemi izininsa, don haka ta kunna data ta yi masa sallama, ta rubutu ta ce masa"Yaya ina ta magana ka ƙyale ni, Baba ne ta ce bai yarda na zauna a gida da aurena ba, to ni ma ban goyi bayan ka kama mini haya ba, ko don ka samu nutsuwa a zuciyarka, amma na san gidanku babu inda zan zauna, ba wai na raina ba ne, kawai ba zan ji daɗin zaman ba, tun da zan takurawa ƙannenka, to yanzu dai an ce na nemi izininka na koka gidan Yaya Kabir da zama, har zuwa lokacin da za ka dawo. Ka amince?"

"Ki je duk inda za ki je, sai dai ina tunasar da ke, ki ji tsoron Allah!" Amsar da ya ba ta kenan, sai ta tura masa godiya.

Daga nan ta kira yayar babarta a waya, ta sanar mata halin da ake ciki, ta ce mata indai ta ga ana neman kai da ita ta dawo gidan kawun Hadi ta yi zaman ta, shi yayan Mama ne, Nuratu ta ce babu damuwa za ta je ta gwada zaman ta gani, idan da takura za ta dawo, ta yi mata nasiha sosai a kan ta kama kanta ta riƙe mutuncinta, sannan ta mu'amalanci kowa cikin mutunci, ta dinga kamawa Nawwara aikin gidanta.

Suna gama wayar, ta turawa Yaya Kabir account lambar, nan take ya turo mata dubu goma, ta tura masa godiya. Kabir ya sauke ajiyar zuciya, yana jin wani kaso na nauyin da yake ɗauke da shi a zuciyarsa tun lokacin da ya ji Nuratu tana da ciki, ya ragu, ya ce"Yanzu za a fara yaƙin".

LITTAFIN ZUCIYAR MACE NA KUÆŠI NE A KAN NAIRA 500 KACAL, ZA KU IYA FARA BIYAN KUÆŠIN KARATUNKU DAGA YANZU TA NAN

8028966015
Sadiya AbdulrazaÆ™ opay bank

Shaidar biya ta nan
08028966015
[11/23, 12:45 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*

BY
SADIYA ABDULRAZAƘ

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY
PAGE 9

GIDAN NURA

Zuwa yanzu Hasana ta saba da kwana ita kaɗai, ta yi nacin da za ta iya har ta gaji ta watsar, wataran haka za ta je ta ce masa ba ta da lafiya wai ko zai zo ya kwana a ɗakinta, amma bai taɓa yin hakan ba, sai dai ya ba kawo mata magani ya yi tafiyarsa, yanzu ko ta buga masa ƙofar ma ba ya buɗewa, washegari idan ta yi masa maganar sai ya ce shi ya yi bacci a lokacin, alhalin tana kallon shi ta windo. Daga baya sai take kunna datar ita ma, ta dinga tura masa stika ko ƙananun kalmomi irin su i love you, i miss you, sai ya duba ya yi banza da ita, wai ita a nufinta abin da ƴan'matan suke faɗa masa kenan, ita ma sai ta koya ta dinga yi, da haka har ta samu hankalinsa ya dawo kanta, ya ƙyale su, amma daga ƙarshe sai ya kafa mata dokar chart ɗin dare, ya ce duk inda aka idar da sallar isha'i ya ganta online sai ya hana ta chart ɗin ma gabaɗaya. Haka ta zuba masa ido yake ta shagalinsa, a tsawon kwanakin nan sau biyu ya kira ta ɗakin nasa, tana tunawa a farkon aurensu Nura ba ya taɓa kwana uku bai kira ta ba, amma yanzu sai ya yi sati uku har fiye da haka ma bai kira ta ba, to ita kanta ta san a yanzu babu wani gyara da take yi, saboda gani take asarar kuɗi ne, uwa-uba ma ba ta da kuɗin gyaran ne, a da bayan ya yo mata cefanen komai wataran haka kawai idan kasuwa ta yi kyau yakan ɗauki dubu ɗaya ko biyu ya ba ta, amma yanzu ta manta ma rabon da kyautar kuɗi ta shiga tsakaninsu, ko data Husainarta ce take saka mata, da kyautar katin waya.

Sannan zuwa yanzu ta yarda Ramla ita take yi wa habaici, ta gane da gaske mijinta yana soyayya da ita, abun yana yi mata ciwo sosai, indai wata ƙawarta za ta zo, ko kuma ƴan'uwanta to fa sai sun ba ta labarin Nura yana son wata wacce ta sani, ta rasa me yake damunsa, kamar wanda baki yake bibiyarsa. Daga baya ma Ramla sai ta saka a ka mayar da ita group ɗinsu na makaranta, ta yi habaici tana ba da labarin mijin wata ƙawarta ya maƙale mata, a ba ta shawara ya za ta yi da shi? Hasana sai dai ta yi shiru, don ta san ba laifinta ba ne, komai shi ne ya ja mata.Ta taɓa tambayarsa ina Ramla? Ya fara faɗa yana cewa"Wannan wace irin tambaya ce?"

Ta ce"To ai na ji labarin kun jone da ita, kuna soyayya, kuma ita da kanta ta faÉ—a mini".

Ya ce"To an yi É—in, Hasana ki É—auki mataki don Allah!".
Chapter 11 · 0% Book details