Sashe 4
Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya ce"To Allah Ya ƙara afuwa, ga wannan ki karɓa ki ci, da kuɗi a ciki ko za ki yi wata buƙatar, sannan duk abin da kike buƙata don Allah ki sanar mini, babu abin da ba zan ba ki ba, Allah Ya ji ƙan Mama Ya sa ta huta".
Ta amsa da amin, ya ba ta ledar ta karɓa ta yi cikin gidan, ta samu su Umma a tabarmar da ke tsakar gida tare da su Mama Asabe, suna mai da yadda mutuwar ta kasance. Ta duƙa ta sake gaishe su, suka amsa suka yi mata gaisuwa cike da tausayawa, Mama Karime da ta ƙyalla idonta a kan ledar ta ce"Kina zaune ke kaɗai a ɗaki, sai mutuwar ta dawo miki sabuwa ai, ki wuce ɗakina ki kwanta, bari na aika a samo miki ko kunu ne".
Ta ce"To" Ta shiga É—akin nata.
Sai Zainabu ƙanwar Abdul ta tashi ta bi bayanta, Khadija da Hannatu suna kwance a ɗakin, ta zauna tana ajiye ledar, Zainabu ma ta zauna ta miƙa mata ledar da ke ƙunshe a hijjabinta tana cewa"Yaya Abdul ya ce na kawo miki"
Sai ta ɗakko wayarta ta danna ta kunna mata voice, sai ga muryar Abdul ɗinta ta bayyana, daidai inda yake cewa"Nuratu ga saƙona nan, jikina ya ba ni ba ki ci komai ba wunin yau, na yi nisan da zan ba ki wata kulawar da ta dace, amma ga ƙanwata nan a madadina, idan a baki kike so sai ta ba ki, don Allah ki ci wani abun".
A nan maganar ta ƙare, Zainabu ta miƙa mata ledar, bayan ta ciro yougurt ta buɗe ta matso ta kai mata baki, Nuratu ta yi guntun murmushi ta ce"Wato Zainabu biye masa za ki yi ko?"
Tana dariya ta ce"To ai ni Æ´ar aike ce".
Nuratu ta karɓa ta fara sha, ta sha kusan rabin jarkar, daidai sanda su Umma suke cewa Zainabu ta fito su tafi, Nuratu ta ji cikina ya fara hautsinawa, yawu ya taru a bakinta, da sauri ta fita tsakar gida ta fara kwarara amai, suna ta yi mata sannu, Zainabu tana cewa daga shan yougurt, Mama Asabe ta ce"Ƙila don ta jima ba ta ci komai ba ne, sannu Nuratu kin ji" Ta gyaɗa kai, ta gyara wajen ta koma ɗaki, su kuma suka yi musu sallama suka tafi.
Tana shiga ta kwanta, a kan sallayar da take wajen, Mama Asabe ta shigo tana yi mata sannu, ta ɗauki yogurt ɗin tana cewa ke ma ai ba za ki sha abu mai sanyi ba yanzu, tun da ƙila rabonki da abinci tun jiya, ta ce da Kadija"Dije tashi ki siyo mata kunu, ko ruwan bunu a wajen Mati mai shayi".
Nuratu ta ce"Gara ruwan bunun Mama".
Khadija tana fita, Mama ta janyo ledar wajen Zainabu, ta ga wani yougurt ɗin ne, da lemuka biyu, sai shawarma guda biyu, ta janyo ta wajen Alhajin, ta fara cin karo da ƴan ɗari biyar biyar a dunƙule, ta faki idonta ta soke su a zani, ta duba sauran kayan, har da kayan shayi, da biredi da manyan biskit ga kuma kaza da lemo babba, ta jinjina kai ta ce"Lallai ana gatale ki Nuratu".
Nuratu saman É—akin kawai take kallo, ta yi nisa a duniyar tunani, Mama ta ce"Wai ni kam dama babanki bai raba ki da Abdul É—in nan ba?"
Nuratu ta ce"Mama ni fa wannan Alhajin dole sai dai ya haƙura".
Mama ta ce"Hmmm! Yaro man kaza, lallai kina da ƙarancin hankali Nuratu".
Ana kawo shayin Mama ta É—akko kofi ta haÉ—a mata mai kauri, ta sha, sannan ta ci shawarma guda É—aya, ta ba su sauran, kayan shayin da biskit kuma ta É—auka ta tafi É—akinsu, Mama tana cewa ta kwana a nan ta ce a'a.
Ta shiga ta zauna, kawai sai ta fara kuka, ga ta yau za ta kwana ita kaɗai babu Mama, wayarta ta yi ƙara, ta duba ta ga Abdul ne, ta ɗaga a sanyaye, ko gaisawa ba su yi ba ya ce"Nuratu wane ne wanda kuke tsaye ɗazu?"
Ta sauke numfashi tana lumshe ido, da tunanin ta inda za ta fara yi masa bayani.
Ya ce"Kar ki yi mini ƙarya".
Ta ce"Wani ne, sunan shi Alhaji Hashimu, yana sona ne, ya fara zuwa sati biyu da suka wuce..."
Ya katse ta da faÉ—in"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!" Sai ya kashe kiran ba tare da ya ce komai ba.
Ta bi wayar da kallo, ta so ya tsaya ta ƙarasa, ta yadda za su fahimci juna, dama ta sani za a yi hakan, ga shi ba ta da katin kiran wata ƙasar, sai ta kunna data, ta kuwa ganshi online, ta yi masa voice ta faɗa masa komai tun farkon haɗuwarsu, ya duba bai ba ta amsa ba, ta yi ta jira har ta gaji, ta kashe data, ta saka sakata a ɗakin ta kwanta, tana jin wani abu mai kama da tsoro tare da kewar mahaifiyarta, sai ta kasa baccin, sai hawaye da suka ƙi tsaya mata.
Haka ta yi bacci rabi da rabi, saboda kewar mahaifiyarta. Da asuba bayan ta idar da sallah ta kunna data, duk yawan saƙonnin da suke tururuwar shigowa na Abdul kawai ta kai hannu ta buɗe, "Ba zan fahimce ki ba Nuratu sai na kammala bincike a kanku. Fatana dai kar ki manta da alƙawarinmu, ke kaɗai ce macen da nake ƙauna da fatan aurenta duk duniya Nuratu, kar ki butulce mini". Abin da ya rubuto mata kenan, a maimakon ta ji daɗi irin yadda ta saba a yau sai zuciyarta ta yi rauni, ta fara hawaye.
Ta koma ta kwanta tana jin yadda gidan nasu ya kaure da hayaniya, da alama har kowa ya cigaba da sana'arsa kenan, kwana É—aya bayan mutuwar mahaifiyarta, kodayake idan ba su cigaba da nema ba, waye zai ba su abin da za su ci?
Sai a lokacin ta É—an samu bacci ya É—auke ta sama-sama, Mama Karime ce ta shigo ta tashe ta, ta tashi zaune tana gaishe ta, Mama ta amsa tana cewa"Sannu Nuratu, kin karya?"
Ta girgiza mata kai alamar a'a. Mama ta ce"Fito ki karɓi koko da fanke ga shi na rage miki".
Ta ce"Idan da ruwan shayi dai zan karɓa". Ta tashi ta bi bayanta, tana jin yadda sanyi yake ratsa ta, saboda zazzaɓin da yake jikinta.
Ƴan'uwa da maƙota ɗaiɗai ana ta shigowa ana yi mata gaisuwa, daidai lokacin Abdul ya kira ta, ta faɗa masa zazzaɓi take yi, ya ce zai turo abokinsa ya ɗauke ta su tafi asibiti, ta ce a'a ya bar shi, ya ce to zai turo Isa ya duba ta, Isa shi ma abokinsa ne, yana da chamest a ƙasan layinsu, ta ce kawai ya bar shi za ta sayi maganin zazzaɓin, suka yi sallama, saboda ba ya son jan magana.
Suna gama wayar ta tuna jiya Alhaji ya ce da kuÉ—i a ledar nan da ya ba ta, sai ta É—akko ta dudduba, ba ta ga alamar kuÉ—i ba, sai ta raya ko mantawa ya yi bai saka ba, ta san halin gidansu da sata, amma yanzun ba ta kawo wata ce ta É—auka ba, to idan ma É—aukar aka yi, ita yanzu ba ta su take yi ba, ta koma ta kwanta.
Wajen azhar tana zaune tana cin abincin da ƙanwar Mama ta kawo mata, sai ga Isa ya zo da leda har da ruwa wai zai saka mata, Baba yana ƙofar gida Isa ya gaishe su, ya shige, don haka ya biyo bayansa, daidai sanda Nuratu ta fito tsakar gida.
Baba ya ce"Kai yaro lafiya wajen wa ka zo?"
Ya ce"Baba aiko ni aka yi zan duba Nuratu".
Baba ya ce"Ikon Allah! Kai kuwa yaro wane hamshaƙin ne ya aiko ka?"
Ya ce"Abdul ne saurayinta".
Baba ya ce"Ka ce dai tsohon saurayinta, to wuce ba ta buƙata, sannan ka faɗa masa kar ma ya sake asarar kuɗinsa a kan matar da ba ta shi ba, ni na riga na ba da ƴata ga wanda ya dace, lokaci kawai muke jira, ba don mutuwar nan ba ma, da a cikin satin nan za a tsayar da rana".
"Ok" Isa ya faÉ—a yana juyawa ya fice daga gidan.
Nuratu da duk ranta ya gama ɓaci, ta ce"Haba Baba..."
Ya ce"Buhun ubanki! Ba ki da lafiya shi ne ba ki faÉ—a mini ba? Duk duniya yanzu kina da wanda ya fi ni ne?"
Ya ja tsaki, ya ciro waya, ya yi danne-danne ya kara a kunne, can ya washe baki ya ce"Wa alaikumus sallam, Alhaji ina kwana?"
Alhaji dake zaune tare da matarsa tana zuba masa abinci ya amsa da"Lafiya lau Baba, ya ƙarin haƙuri?"
Baba ya ce"Da godiya. Wallahi Alhaji dama mutumiyar taka ce dama babu lafiya, wallahi zazzaɓi jiya ba mu yi bacci ba, shi ne na ce to bari a sanar maka..."
Alhaji ya ce"Subhanallah! Bari yanzu zan aiko sai a É—auke ta a kai ta asibiti".
Daga nan sai Baba ya dinga jera godiya, har yana rusunawa kamar yana gabansa.
Ya kalli Nuratu ya ce"Tafi ki shirya, zai aiko a kai ki asibiti yanzu, ai ke dai Allah Ya dubi maraicinki da ya kawo miki wannan bawan Allah mai karamci".
Nuratu da ta shiga tashin hankali, ta marairaice ta ce"Baba ɗan zazzaɓi ne fa, ni ba sai mun je asibiti ba".
Baba ya ce"Ai ke shashasha ce, har ki samu mau jiɓantar lamarinki amma ki tsaya shashanci, maza shirya".
Ta shiga ɗaki, ta zauna, sai ta fara hawaye, ta san manyan asibitocin nan da ƙirƙire-ƙirƙire, tsoronta ɗaya kar a ce za a yi mata wani gwajin da zai fallasa sirrinta.
Babu jimawa Baba ya shigo ya ce ta fito su tafi, yayarta Rahma Æ´ar Mama Karime tana tsakar gida Baba ya ce"Ke Ramatu wuce ki raka su".
Har da saurinta ta sako hijjabi, suka fita, Nuratu tana jin kamar ta ce ba za ta je ba.
Har da buÉ—e mata murfin motar, ta shiga ya ja suka É—auki hanya. Dab da asibitin ta ga wani babban chamest, ta ce"Bawan Allah kawai ka tsaya ka siya mini magani a nan, ba dole sai an je asibiti ba".
Ya É—an yi jim, sannan ya ce"To Hajiya ai ni umarni nake bi, sai dai na tambayi Alhajin, duk yadda ya ce".