← Book details Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 16

Sashe 3

Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayin da Hasana ta saki baki take sharara bacci, shi kuwa Nura yana fita masallaci ya tafi sallar isha'i, bayan an idar ya hau babur ɗinsa ya tafi gidan su wata Hafsa, wacce ya karɓi lambarta tun shekaran jiya da ta zo shagonsa siyan kayan kwalliya, tun a ranar ya so zuwa, amma yana da wasu alƙawuran, sai yau layi ya zo kanta, Ramla ma ya je ganin gidansu ne kawai amma sai zuwa jibi zai koma. Fira sosai suka yi da Hafsa, wacce bai ɓoye mata yana da mata da ƴaƴa uku ba, sai dai ya faɗa mata sam bai yi dacen mace ba, Hafsa ta ce"Ikon Allah, amma dai auren wuri ka yi, wallahi ban yi zaton kana da aure ba".

Ya yi wani murmushin ƙasaita ya ce"Wallahi da aurena, kawai dai tsabar tsafta ne da kula da kai, sannan kin san idan mutum yana cin guminsa yadda ya kamata ya ci mai kyau ya sha mai kyau, dole za a gan shi tsaf".

Hafsa ta ce"Hakane" Don ita ta tsani kishiya, ba za ta iya auren mai mata ba, ta yi soyayya da masu mata wajen su uku, duk mammaƙo gare su, ba sa ɓarin kuɗi saboda hidimar gidansu ma ta ishe su, sai dai shi wannan ta ji yana zancen yana cin mai kyau.

Nura ya ce"Wallahi Hafsa a hakan ma da kika ganni don ma dai ina da matsala ne a gidana, ban yi dace da mace ba, kin san ita rayuwa idan ka yi dacen mace ta gari wacce ta haɗa komai kamar dai ke ɗin nan, to fa har wata ƙiba kake yi".

Hafsa ta ce"Kuna samun matsala da ita kenan".

Ya ce"Idan kin ji matsala ɗaya kenan, matsaloli ne da yarinyar nan birjik wallahi, kin ga dai irin kayan kwalliyar da nake siyarwa, amma wallahi sai na yi wata ban ga hoda a fuskarta ba, kuma duk order da na yi sai na dara kai mata ta zaɓi kaya kafin na kasa a kasuwa, ɗinki duk wata sai na yi mata ita da yara, amma indai kin ga ta saka sabon kaya to fita za ta yi, nama a firji sai dai wani ya tarar da wani, amma idan ta kwaɓa girkin kare ma ba zai ci ba, gaskiya mata kuna da matsala, yawanci ku ne kuke saka mazanku ƙara aure".

Hafsa ta ce"Wasu matan dai, amma ni yaushe zan samu mijin da zai yi mini komai na ƙi faranta masa?"

Ya ce"To Allah Ya sa kakata ce ta yanke saƙa".

Ta ce"Hmm! Idan da gaske kake ba".

Ya ce"Kamar ya?"

Ta ce"To ai na ga haka kuke masu matar nan, yawancinku kuna zuwa wajen zance ne don ku rage dare ba don aure ba, sai an ce ku fito sai ka ga wani matarsa ta fi ƙarfinsa, wani kuma gidan nasa ma da ƙyar ake cin abinci sau uku a rana, ba shi da halin ƙara auren, ni fa shiyasa ban fiya sauraron mai mata ba".

Nura ya yi wata dariya ya ce"Baby Hafsa kenan, kin sanfa akwai maza, akwai muna maza, wallahi ni kam namiji ne a gidana, na fi ƙarfin gidana, sannan idan da yunwa a gidana a jikina za ki gani".

Hafsa ta ce"A jikin matarka dai, ko tana da matsalar gyara jikinta na san tana cin abinci ta ci ko ba daÉ—i".

Ya ce"To ni dai ki gwada ni ki gani, na tabbata ba za ki yi nadamar ɓata lokacinki ba".

Ta ce"Zan yi bincike dai".

Haka suka dinga fira, yana ta kushe Hasana, da ƙarairayi, don rabon davya ɗauki hoda ya ba ta kyauta har ta manta, ita yanzu sam babu kwalliyar ma a gabanta tun da ko ta yi ba ya ganin ƙoƙarinta ballantana ya yaba, sai dai idan ta yi wanka ta shafa hodar da man leɓe, don kanta ba dai don miji ba.

Sai ƙarfe goma ya bar wajen Hafsa, ya zarce majalisarsu ta bakin titi, ana ta fita sai sha biyu ya koma gida, ya buɗe ya shiga, ya saka sakata, ya tura ƙofar falon ya shiga, yana haska yaransa, ya gyara musu kwanciya, don ɗaya ya ɗorawa ɗaya ƙafa, sannan ya shiga ɗakin, ya canza kaya ya hau gadon, ya haska Hasana da take ta sharar bacci, Aiman a kusa da ita, ya taɓe baki ya kwanta, a yanzu ba shi da burin da ya wuce ya ƙara aure, yana buƙatar ƴar sawalwala wacce dare yana yi zai ji yana ɗokin dawowa gida su sha soyayya, babu ciki babu goyo babu yaran da za a jira su yi bacci.

*******
Ƙarfe takwas da rabi wayar Nuratu ta fara ƙara, ta duba ta ga lambar ce daga Saudiya, ta san Abdul ne mai kira, don yana aron wayar mutane ya kira ta idan ba ta hau online ba, saboda ba kasafai yake saka kati ba, Abdulmalik mutum ɗaya da take gani a matsayin sanyin idaniyarta bayan mahaifiyarta, ta san bai ji rasuwar da wuri ba shiyasa bai kira ta ba, ta ɗauki wayar da sallama, ya amsa, sannan ya ɗora da faɗin"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!".

Nan ta ji wani sabon rauni ya taso a zuciyarta, ta fara kuka, ya ce"Ashe Mama lokaci ya yi" Sai ta kasa magana.

Ya ce"Ki yi haƙuri Nuratu, duk mai rai mamaci ne dama, Allah da Ya ɗauke ta ya fi mu son ta..."

Cikin kuka ta ce"Yaya Abdul ina buƙatar Mama a rayuwata, ina buƙatar uwa, yanzu da wa zan zauna a wannan bahagon gidan namu mai cike da takaici kala-kala?"

Ya girgiza kai kamar tana ganinsa ya ce"A'a kar ki sake faɗar haka, Mama ba ta yi gaggawa ba, mu ma wataƙil yau ko gobe ne, duk mai rai gawa ne shi a tafe. Sannan Allah Yana sane da yanayin gidanku Ya ɗauke ta ɗin ya bar ki, sai mu bar hakan a matsayin wata jarabawar rayuwa Allah Ya ba mu ikon cinyewa".

Hawaye mai zafi suka fara tunkuɗo juna daga idonta, Yaya Abdul ɗinta ne kaɗai mai mai da damuwarta tasu su biyu, sai dai wannan ƙaddarar da ta afka a dare ɗaya ta dalilin inganta rayuwarsa, sai dai tana zargin hatta shi Abdul ɗin ba zai iya karɓarta ba, da wane idon za ta kalle shi idan ya gane tana da ciki? Ina zai saka kansa a ranar? Ta fi kowa sanin zafin kishin shi, shiyasa yake tsaye tsayin daka a kan ƙananun buƙatunta wanda ba su gagare shi ba, ko wannan tafiyar da ya yi dominta ne, yana can yana bauta don ya tara kuɗin aurensu, kuma ya samu jarin da zai riƙe su, don su yi rayuwa mai inganci.

Suna cikin waya ta ji muryar Baba yana ƙwalla mata kira, ta yi saurin cewa Abdul"Ina zuwa ka ga Baba yana kira".

Ya ce"To ki yi masa gaisuwa, anjima zan sake kira".

Kafin ta fito Baba har ya bankaÉ—o labulen yana cewa"Wai uwar me kike yi ne da kika share ni?"

Ta fito jiki ba ƙwari tana cewa "Gani nan Baba".

Ya ce"Ga Alhaji can a zaune, sai ki je ku tattauna".

Ta ce"To".

Ta bi bayan Baba, ta tarar da Alhaji Hashimu tsaye yana danna waya, ta tsaya tana kallon fuskarsa da wayar ta haska, babban mutum ne zai doshi shekara sittin, sati biyu kenan da haɗuwarsu, ya kawow malamin makarantarsu sadaƙar da yake kawowa duk wata, ya ganta, a ranar sai ga Malaminsu wato shuganan makarantar ya zo har gida wai an aiko shi, ya zo neman alfarma, ya faɗa mata Alhajin yana sonta, kuma matansa uku, nauyi da kunyar Malam Isma'il bai hana ta faɗa masa tana da wanda take so ba, don haka Malam ya samu Baba ya faɗa masa, a ranar Baba faɗa kamar zai ari baki, ya ce dole kuwa ta manta da kowa ta aure shi matuƙar da gaske yake, duk kuwa da kafin Abdulmalik ya bar ƙasar nan sai da iyayensa suka zo suka yi magana akan bayan shekara biyu zai dawo sai a yi auren, a lokacin Baba murna ya dinga yi, saboda yana ganin Abdul zai tara arziƙi kafin shekara biyun, amma bayan zuwan Alhaji Baba har yana cewa"Wane shirmen banza ne ki zauna jiran wanda ya tafi Saudiya? Ai sai ya shekara goma bai dawo ba, idan ya dawo ma ya ce kin tsofe ya samu wata ya aura, don haka ba za a yi wannan shashanci da ni ba".

Mama ta yi iya yinta don a bar zancen Alhaji Baba ya kafe, tijarar safe da ban ta dare da ban, har ƙarar Mama ya kai wajen yayyunta tana hurewa ƴarsa kunne, shi ne ta ce kawai Nuratu ta haƙura ta aure shi, to a nan ne fa ta sanar mata zancen cikin jikinta, wanda ta same shi silar taimakon Abdul.

08028966015
[11/18, 1:06 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*

BY
SADIYA ABDULRAZAƘ

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY

PAGE 3

"Barka da fitowa". Muryar Alhaji Hashimu ta dawo da ita nutsuwarta.

Ta ce"Ina wuni".

Ya ce"Lafiya lau, sannu Nuratu ya haƙuri?"

Ta ce"Da godiya".

Ya ce"Allah Ya yi mata rahma Ya sa aljanna makoma, sai ki yi ta haƙuri kin ji ko?"

Ta amsa da amin, suka yi shiru na É—an lokaci, kafin ya ce"Kin ci abinci dai ko?" Ta yi banza da shi, ya sake cewa"Me kike son ci? Kar damuwa ta saka ki zama da yunwa, sai ya haifar miki da wani ciwon, na zo miki da abinci ki daure ki ci".

Ya ƙarasa yana miƙa mata babbar ledar da take hannunsa, ba ta karɓa ba, kuma ba ta ce komai ba, sai hawaye da suke ta gudu a fuskarta. Ana haka sai ga sallamar baƙi gidan, suka wuce su a zauren bayan ta gaishe su, sarai ta gane Umma ce mahaifiyar Abdul, tare da abokiyar zamanta, sai ƙanwarsa, su ma kuma sun gane ta, don da fitila a hannunsu suka shigo zauren, gabanta ya dinga faɗuwa, saboda tana fargabar Abdul ya ji labarin an ganta da wani, ga shi mutanen da ba ta isa ta ce masa ƙarya suke yi mata ba ne suka ganta, duk hankalinta ya yi cikin gidan, ta ce masa"Zan shiga gida".
Chapter 3 · 0% Book details