Sashe 12
Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ce"Babu wani matakin da zan ɗauka, kawai dai zan ba ka shawara ne, ya kamata ka riƙe mutuncinka, ni ma kuma ka sama miji aji a cikin jama'a, ana ta zagina a gari saboda wannan halin naka na son mata, wai da me na rage ka ne don Allah? Ka sanar da ni matsalata sai na gyara..." Ta fashe da kuka.
Duk da jikinsa ya É—an yi sanyi, amma ya danne bai nuna ba, ya ma tashi ya bar mata É—akin, shi dai bai ga wata matsala ba saboda yana kula mata, ai namiji mijin mace huÉ—u ne, yana da ra'ayi da burin auren mata huÉ—u idan har ya samu dama, saboda haka ba ta isa ta hana shi ba.
Daga baya ta yanke hukuncin jan hankalinsa don ta gane wace kalar mu'amula yake yi da mata a wayar? Sai ta saka Husainarta ta aiko mata d sabon layi, saboda akwai ƙanin mijinta wanda yake siyarwa, ta saka a wayarta, ta saita sabon whatsApp da shi, ta nemi lambar Nura ta yi masa sallama, ya amsa suka gaisa, ya ce bai gane mai magana ba, a rubuce ta ce"E dama ba ka san ni ba ai, yanzu dai nake ganin lokaci ya yi da ya kamata ka san ni, saboda ka daɗe kana azabtar da zuciyata da soyayyarka, burina ko yaya ne na samu matsuguni a zuciyarka, wanda za ka dinga tuna ni ko da sau ɗaya ne a sati".
Sai ya tura stikar murmushi, ya ce"Ikon Allah! Da farko dai ya sunanki?"
Ta ce"Sunana Suhaila, kuma a kasuwa nake ganinka, wallahi kana burge ni sosai, na daɗe da samun lambarka, amma sai na yi ta jujjuya ta, na kasa yi maka magana, saboda a zotona za ka yi wulaƙanci duba da ganin yadda ka haɗun nan kake da aji, na ji an ce ma mata ba sa gabanka, shi ne nake ta fargaba".
Nura ya yi murmushi ya ce"Wannan dalilin ai ba shi zai saka mutum ya yi wulaƙanci ba, sai dau idan dama can halinsa ne, ita mace ai ba abar wulaƙantawa ba ce, mace abar riritawa ce da tarairaya, kuna buƙatar kula ta kowane fanni, wannan shi ne burin da na ci a kan matar da zan aura har tsufanmu".
Ta ce"Kenan yanzu ba ka da aure? Zan so a ce ni ce zan samu wannan kulawar".
Ya ce"Ina da aure har da yara, sai dai wancen burin nawa yana neman zaɓa tarihi, saboda wata kidahumar mace Allah Ya haɗa ni da ita, wallahi sam ba ta san kanta ba, ballantana ta san mijinta".
Kalmar kidahuma ta daki zuciyar Hasana ba kaɗan ba, nan take ranta ya yi baƙi, sai ta ji kamar ta yi voice ta faɗa masa ita ce, sai dai kuma ba wannan gaɓar take nema ba, don haka ta daure zuciyarta suka cigaba, ta ce"Ikon Allah! Yanzu duk wannan haɗuwar taka ba ka yi dacen mace ba? Amma ai kai ya kamata ka canza ta, ka mayar da ita yadda kake so ku zauna".
Wannan karon voice ya yo, yana ƴar dariya ya ce"Malama Suhaila kenan, wato ba ki san wace ce matata ba, shiyasa kike zaton za ta canza hali, yanzu haka zancen da nake yi miki fa kin gan ni kwance a ɗakina ni kaɗai, na kasa bacci saboda tsananin buƙatarta nake, amma na kirata ta ƙi zuwa, yanzu ya dace a ce mace ta dinga nisa da ɗakin mijinta wai sai sanda ya kira ta?"
Hasana ta daskare da mamaki, sai ta kasa riƙe hawayenta, ashe dama haka Nura yake tona wa aurensu asiri? Kuma ma duk bin ta yake yi da sharri, indai har wacce ta fara yi masa magana yau bai santa ba, bai san inda take ba, zai saki jiki ya dinga tsara mata wannan ƙaryar, to ina ga wacce ya saba da ita har ma yake zuwa gidansu? Yanzu haka yake faɗawa Ramla ma? Tabbas dole ta raina ta.
Ta share hawaye ta É—auki wayar, sai ta ga ya turo mata stika, tana buÉ—ewa ta ga mace ce da namiji rungume da juna suna bacci, ta daure ta rubuta masa"To ko ni É—in na zo na taya ka baccin?"
Ya tura mata dariya ya ce"Da gaske ba za ki ji tsorona ba?"
Ta ce"To tsoron me?"
Ya ce"Ai za ki zo ne matsayin mai É—ebe mini kewa".
Ta ce"Hmm, za ka same ni fiye da matarka, kwatanta mini gidan naka yanzu zan zo".
Ya ce"Ki dai gwada ta waya don na yarda idan kin zo ɗin za ki iya taɓuka abun arziƙi".
Sai ya turo mata wani vedio, tana buɗewa, ta yi saurin kifa wayar, ganin blue film ne ƙarara, ta dinfa maimaita "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!", ta kashe wayar duka ba tare da ta ba shi amsa ba, sai ta samu kanta da fashewa da kuka, ashe irin mijin da take aure kenan?
A daren nan da ƙyar bacci ya ɗauke ta, da safe har ta makara, sai da ya tashe ta, har da faɗansa yana cewa"Wannan wani sabon salon ne kuma salon yara su makara?"
"Ba ni da lafiya ne" Abin da ta ce kenan kawai, wani irin mugun haushinsa take ji, ji take kamar ta kama shi ta shaƙe, ta tambaye shi me yasa yake zaune da ita ba zai sake ta ba? Ta je ta kunna wuta, sai dai tunawa da kalmar kidahuma ya sa ta fara hawaye, idan ya tashi wulaƙancinsa har jaka yana ce mata, amma a jiya fa wata yake faɗawa ita kidahuma ce, tabbas ta san duk wacce zai auro nan gaba ba za ta kalle ta da mutunci ba.
"Kukan me kike yi?" Ya tambaye ta yana yamutsa fuska.
Ta ce"Na ce maka ba ni da lafiya".
Ya ce"To Allah Ya sawaƙe, sai ki yi ƙoƙari ki dafa shayi, bari na siyo biredi".
Ya fita, ta bi bayansa da kallo, tana tuna wannan ƙazamin vedion, wa ya san adadin matan da ya turawa shi? Wa ya san adadin yawansu a wayarsu, lallai wata wayar za ta iya yi wa mutum jagora zuwa jahannama, haka ta dafa shayin, suka karya, ta shirya yara, tana yin komai a sanyaye, yana taɓa aljihunsa ya ce"Ga shi ba ni da kuɗi da kin tafi asibiti".
Ta ce"Ciwon kai ne, zan sha magani yanzu".
Ya ce"Allah Ya sawaƙe ya fice".
Wajen ƙarfe goma ta kunna data, ta gan shi online, zuciyarta tana ba ta shawarar ta ajiye layin nan, tun da har ta san wane ne mijinta, ta samu abin da take so, wani ɓangare na zuciyar kuwa zugata yake yi, a kan ta cigaba don ta gano iya waya abun nashi ya tsaya ko zai yarda su haɗu a zahiri? Ta fi yarda da wannan don haka ta yi masa sallama, sai da ma ya duba chart ɗin baya har farko, sannan ya tuna ta, saboda yawan matan da yake chart da su, ya amsa ya ce"Matsoraciya jiya sai kika gudu ko?"
Ta ce"La ba fa guduwa na yi ba, wayar ce ta mutu, caji ya ƙare, ban ma kai ga ganin me ka turo ba".
Ya ce"Kin bar ni da kewarki, har da mafarkinki na yi".
Ta ce"Daga haÉ—uwa?"
Ya ce"Ai haÉ—uwar ce ta yi daÉ—i shiyasa, yau za ki rage mini dar ko?"
Ta ce"Me zai hana? Ni fa da gaske nake, ka ga ni ban saba ta waya ba, a ina za mu haÉ—u?"
Sai ya tura mata dariya ya ce"Kamar gaske".
Ta ce"Tun da ba ka shirya ba shikenan mu bar zancen".
Ya ce"Wai ke ba kya yin voice note?"
Ta ce"Ai ni kurma ce, ba na magana kuma ba na jin komai".
Ya tura stikar dariya ya ce"Ban yarda ba, sai ranar da na ganki a zahiri".
Ta ce"To yaushe zan zo taya ka kwana?"
Ya ce"Yau".
Ta ce"Za kuwa ka gan ni, da gaske fa".
Ya yi dariya.
Ta ce"Zan zo ƙarfe sha ɗaya daidai, saboda haka ka koma gidanka da wuri yau".
Ya ce"Allah Ya kawo ki, zan shirya miki abubuwan mamaki kuwa".
Daga haka ta kashe data, ta tashi ta ɗora girki, a ranta tana ayyana tabbas yau ɗin kuwa za ta je, ta fito masa a mutum, don ya san ta gane badaƙalar da yake yi a wayarsa. Da ya zo cin abincin rana ba ta nuna komai ba, sai dai sam ba ta da walwala, da daddare yana dawowa ya gama komai ya shiga ɗakinsa, ta kunna data, ta ga saƙonsa ya shigo, yana ce mata"Kyaun alƙawari dai a cika, yana jiranta".
Ta ce"Ka tashi ka buɗe ƙofa yanzu za ka ji na turo na shigo".
Ya ce"Na buÉ—e".
Ta ce"Ba ka buÉ—e ba, ina kallonka fa, kana kwance a katifa da gajeren wando bulu".
Ya yi Æ´ar dariya ce"Kuma wallahi kin canka".
Ta ce"Na ce fa ina kallonka, yanzu na ƙaraso ƙofar ɗakin zan ƙwanƙwasa, ka buɗe, amma don Allah ko a yaya ka gan ni kar ka ji tsorona, wallahi ni mai sonka ce".
Ya ce"Kai Suhaila kenan".
Hasana ta buɗe ƙofarta a hankali, ta fito, ta fara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Nura da ƙarfi, gabansa ya faɗi rass, ya ce"Wane ne?"
Ta tsaya da bugun ta rubuta masa cewar"Ni ce mana, ya kake haka, ko na shigo ta saman É—akin?" Sannan ta cigaba da bugawa.
Nura bai san sanda ya yi wulli da wayar ba, ya fara karanto duk addu'ar da ta zo bakinsa, ya yaye zanin gadon da aka shimfiɗa a katifa ya lulluɓa, yana ta addu'o'i.
LITTAFIN NAN NA KUÆŠI NE A KAN NAIRA 500 KACAL! ZA KU IYA FARA BIYAN KUÆŠINKU TUN YANZU TA NAN
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay bank
Sahaidar biya ta nan
08028966015
[11/24, 1:16 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*
BY
SADIYA ABDULRAZAƘ
*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)
https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY
PAGE 10