Sashe 1
Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[11/16, 6:31 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*
BY
SADIYA ABDULRAZAƘ
*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATOIN*
PAGE 1
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ihu jama'a, a kawo ɗauki!".Hayaniya da ihun mutanen gidansu ya ta tashe ta daga baccin safenta mai ɗan karen daɗi, ta ja dogon tsaki tana jan yaƙunannen bargonta don ta rufe fuskarta, wai ko za ta samu damar rage tasirin hayaniyar, gidansu gidan yawa ne, mai cike da hargitsi, sun saba da hayagaga mara dalili, sai dai ta yanzu ta fara zargin da dalilin, duba da yadda yara da manya suke ihun babu ƙaƙƙaunatawa, "Yekuwa jama'a! Salamatu ta faɗa a rijiya, ku kawo mana ɗauki!." Maganar Mama Karime ta daskarar da duk wata na'ura ta jikinta ta dakata da aiki na wucin gadi, a hankali ta juyo da kanta ta yi wa idanunta matsuguni a gefen shimfiɗar Mamanta, da fatan Allah Ya sa ba ita Salamatun ake nufi ba, duk da ta san babu wata a gidan mai irin sunata, nan ta ga wayam babu kowa a kai, ta tashi a firgice daidai sanda Nusaiba ta bankaɗo ɗakin da take tana haki tana cewa"Ke Nuratu, tashi babarku ta faɗa a rijiya!".
Da wani irin hanzari ta fice a guje har sai da ta yi fatali da Nusaiban da ta kawo mita rahoto, maƙota har sun fara shigowa ana ta salati, ta yi tsalle da nufin faɗawa rijiyar don ta ceci Mama, ganin an tsaya kame-kamen yadda za a yi, kamar ba su ɗauki ran nata a bakin komai ba, Baba ban da salati ba ya yunƙurin taɓuka komai, aka cafe ta ana ba ta haƙuri, ta ɓarke da kuka tana kiran sunanta cikin fitar hayyaci, "Maaamaa!" Tsayin mintuna kafin Malam Haruna ya zo, wanda masani ne sosai a kan harkar haƙan rijiya, su biyu suka shiga, aka samu nasarar ciro ta, aka shimfiɗa tabarma aka zube ta aka shiga ba ta taimakon gaggawa, sai dai ta ƙi numfasawa, Baba ya ƙarasa ya kasa kunnensa a saitin zuciyarsa, sai ya ɗago ya ɗora hannu a ka yana cewa"Ƙalu inna lillahi wa inna ilaihir raji'un, Salamatu ta tafi, ta tafi ta bar mu, an yi mana mutuwa ni da Nuratu!". Nuratu ta yi kanta a guje, tana jijjigata haɗe da gunjin kuka, amma ko motsi ba ta yi ba.
Gabaɗaya gidan aka hau salati, wasu suna cewa ba ta mutu ba, a tafi asibiti, Baba ya hau faɗa yana cewa"To wane asibiti ana zaune ƙalau? Ni ƙaramin yaro ne da ban san mutuwa ba? Na binne uwata na binne ubana, na binne matata, na binne ƴaƴana huɗu sannan a ce ban san mutuwa ba, aradu Salame ko ba ta mutu ba na tabbata ba za ta tashi ba sai ta ƙarasa".
Nan aka yi masa ca, ana nuna masa muhimmancin zuwa asibitin, abin takaici Baba sai ya zaro aljihun rigarsa duka biyun yana kaɗewa yake cewa"To wai da shekaruna zan kai ta asibiti? Ga shi dai ko ƙarfanfana babu a aljihuna".
Ta sake fashewa da sabon kuka, nan wani maƙocinsu ya sunkuci Mama ya fice da ita, sannan Baba da sauran mutane suka mara masa baya, haka ita ma ta bi su ko ɗankwali babu a kanta, sai ƙanwarta ce ta cire hijjabin jikinta ta saka mata, ta bi su titi a guje, ta tari adaidaita sahu ta shiga, ya bi bayan nasu, a tare suka shiga asibitin ko ta kan kuɗin mai adaidaitan ba ta bi ba, shi ma bai tambaya ba ganin halin da take ciki.
Bayan jira na ɗan lokaci aka tabbatar musu da rasuwar Mama Salamatu, Nuratu ta zauna a ƙasa dirshan tana gursheƙen kuka, ana ta ba ta baki, don Mama Karime ma ta ƙaraso asibitin, nan aka ja lissafin kuɗin asibiti da na ɗaukar gawa, wanda Baba ya ce ba shi da shi, sai karo-karo aka yi aka ɗauki gawar zuwa gida, sai ta shiga ɗaki ta zauna ta zama kamar mutum-mutumi sai hawaye da ta kasa dakatar da su, da ƙyar ƴan'uwan Mama suka ja ta zuwa kan gawar bayan an gama yi mata sutura, suka ce ta yi mata addu'a, kuka ta fashe da shi, da ƙyar ta iya buɗe baki cikin in'ina ta ce"Ma...Mama, Allah Ya yi miki rahma, Allah, Allah Ya sa can ya fi nan". Sai ta rushe da kuka, wata zuciyar tana raya mata Mama ba ta farinciki da addu'ar nan tata, saboda ta mutu tana tsananin fushi da ita, da ƙyar aka ja ta a ka mayar gefe, tana kallo aka fice da gawar, zuciyarta na tururi tana yi wa mahaifiyarta kallon ƙarshe.
Ƙullin wainar siyarwar da Mama take yi, na yau sai ya zama na sadakar mutuwarta, Nuratu ta tuna jiya da daddare sanda take haɗawa, ko markaɗe da kanta ta kai, saboda tana fushi da ita, dama haka take yi idan ta yi mata laifi ba ta yarda ta taya ta aiki.
Zuwa azhar ƴan'uwa sun cika gida, har an gama kuka an shiga hada-hadar rabon abinci, wanda Alhaji Hashimu ne ya kawo, ƴan gidansu har da masu faɗa a kan abinci, yayin da Nuratu kuma yawun bakinta ma ya yi mata ɗaci. Mutuwa ta yi mata yankan ƙauna, Mama ta tafi ta bar ta a gaɓar da take ƙishi da yunwar kasancewa da ita, a lokacin da ta fi buƙatar taimakonta da samun kusanci da ita, ta rasu tana fushi da ita, ba ta tsaya ta fahimci uzurinta ba, ba ta yarda da hujjojinta ba, idan aka ce baƙin cikin abin da ta aikata ne ya yi silar mutuwarta ba za ta yi musu ba, domin kuwa tun shekaran jiya da ta sanar da ita ƙaddarar da ta faɗa mata take cikin tashin hankali da ɗimauta, tana yin komai ne da ƙarfin hali, sannan a yadda Mama Karime ta ba da labarin yadda ta faɗa rijiyar ta san ba ta cikin hayyacinta ne, sannan Mama da asuba take fara suyar waina, amma a yau ɗin har gari ya waye ƙullin yana ɗaki ba ta fara ba, ita kuma sai wani shegen bacci ne mai daɗi yau ya ɗauke ta, cikin bargon da take kwance zazzaɓi yana nuƙurƙusarta, ta kai hannu ta dafa mararta tana tunanin yadda zan yi idan abun ɓoye ya fito fili, da wane ido za ta kalli duniya idan ta fahimci da ciki a jikinta na watanni biyu? Mahaifiyarta ma ba ta fahimce ta ba ballantana kuma duniya? Sai ta saki siririn kuka, don zuwa lokacin muryarta ta dashe sosai.
Ƴan'uwan Mama da suke ɗakin sun yi iya yin su ta ci abinci ta ƙi, can bayan la'asar mata duk ana zazzaune, wasu suna shirin ɗora tuwon dare, sai ga Baba ya shigo, fuskar nan a dagule ya kalli Inna Asabe yayar Mama ya ce"Asabe yaya na ga ana shirin kunna wuta?"
Ta ce"E abincin dare za a É—ora".
Ya ce"Au! Wato kenan ku banza ta faɗi, kowa ya samu wajen fakewa ya ci abinci ko? Ɗan abincin sadakar da aka kawo mini don rage raɗaɗi tun da ba fita nema zan yi ba, a zage ni a gari a ce ban zauna karɓar gaisuwa ba, shi ne za ku saka abincin a gaba ku cinye, ku bar mu da tagumi ni da ƴar marainiyar Allah?"
Sai ya zo tsakiyar gidan ya É—aga murya ya ce"Kowa ya buÉ—e kunnenaa da kyau ya ji ni! Daga yau an rufe zaman makoki, kowace mace ta shuri takalminta ta tafi gidanta, gaisuwa ce an yi na gode, amma kar wacce ta sake zuwa gidana daga yau!".
Mama Lami wacce ita ma matar Baba ce, ta taso tana cewa "Haba Malam..."
Ya É—aga mata hannu yana faÉ—in"Kin ga Lami ki kiyaye ni, ni na gama magana!".
Sannan ya shiga ɗakin mai rasuwa inda aka ajiye kayan abincin ya dinga ɗibowa yana kai wa ɗakinsa, ya rufe da mukulli ya fice, nan mata aka dinga ƙananun maganganu, aka fara silalewa ɗaya bayan ɗaya.
Inna Asabe ta shigo É—akin tana cewa"Kaico! Amma wallahi wannan Iro an yi mara mutunci, yanzu ban da zub da mutunci a gidan mutuwar ma sai ya nuna halinsa? A kan abinci zai hana zaman makoki?"
Mama Suwaiba ta ce"To ke za ki dinga ci da mutane idan kin ce su daina zuwa? Babu wanda bai san halin Iro ba, don haka wannan ba wani abun damuwa ba ne, ni kin ga tafiyata".
Ta kalli Nuratu ta ce"Nuratu ki yi haƙuri ki bar kuka haka, Allah Ya yi mata rahma Ya zama gatanki". Sai ta gyaɗa mata kai alamar ta ji.
Haka duk aka yoye aka tafi ana yi da Baba, ɗakin ya rage ita kaɗai, ta tuna jiya iyanzu tana kallon Mama zaune a cikin ɗakin, fuskarta cike da damuwa, sai ta fashe da kuka tana cewa"Allah Ya yi miki rahma Mama, amma kin bar baya da ƙura".
Kiran sallar magriba ce ta fito da ita daga É—akin, har jiri take yi saboda yunwa, ta tarar da Baba ya fito daga banÉ—aki, yana gyara tazuge, ya ce"Yawwa ke Nuratu, É—azu Alhaji Hashimu ya zo, duk shi ya kawo kayan abincin nan ma, ya ce anjima zai zo ya yi miki gaisuwa".
"To" Kawai ta ce, ta É—auki buta ta fara alwala, tana tunanin da wane yaren za ta faÉ—awa Baba tana É—auke da ciki a jikinta ya gane abin da take nufi?
*******
Kamar kullum tana idar da sallar asuba, ta fito tsakar gida, ta fara kiciniyar kunna wutar gawayi, shayi ta fara dafawa sannan ta ɗora farar taliya, ta zauna tana ta fifita wutar ta ji kukan Aiman ƙaramin ɗanta ɗan wata biyar ya farka, tsakanin kukan da ƙwalla kiran da mijinta ya yi mata ba ta ma tantance wanda ya riga wani ba"Ke Hasana! Hasana". Ta tafi da sauri, ta shiga ɗakin tana raira ƴar waƙarta"Aiman ya tashi, manya sun tashi".