Sashe 13
Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jin shiru ya sa Hasana ta leƙa shi ta windo, nan ta hango shi ya naniƙe bango kamar ƙadangare, dariya ta zo mata, amma ta daure ta riƙe ta, ta matse murya tare da dakushe ta tamkar ta tsohuwar da ta gaji da duniya ta ce"Kai yaro kai fa ka ce kyaun alƙawari a cika, mu ba ma karya alƙwari, kai yaro yanzu za mu ɗage ka, kai da katifar mun kai ka tsakiyar sansanin karuwan aljanu, zan nuna musu masoyina, a can za mu rage dare na zo maka a matsayin matarka kamar yadda ka ce".
Wani irin hautsinawa kayan cikinsa suka fara yi, ya yi adungure ya diro daga katifar, ya buɗe sif ɗinsa ya shige lokar ƙasa yana tsananta addu'arsa.
Hasana ta sake cewa"Sakan ɗaya na ba ka, ka fito daga sif ɗin nan idan ba haka ba, zan rufe ta da mukullin garƙam na kakana na goma sha tara, babu wanda ya isa ya buɗe sai bayan shekara ɗari da saba'in".
Kafin ta rufe baki, sai ga shi ya faɗo daga ciki kamar an jefo shi, ya kalli gabas da yamma, ya fashe da kuka yana cewa"Na tuba, wallahi na tuba don Allah ki yi haƙuri?"
Ta ce"Me ka yi kake tuba?"
Ya ce"Ni ɗan iska ne wallahi, amma daga yau na daina ba zan ƙara ba".
Ta saki wata muguwar dariya ta ce"Yanzu kana nufin ka haƙura da rage daren?"
Da sauri ya ce"E wallahi, dama ƙarya nake yi, ban san ma yanda ake rage daren ba, ki yafe ni".
Ta ce"Ni sunana Aljana Salsabilatul-silsilatul-sakafilatul-salwaisus, ya na ce sunana?"
Nan Nura ya ruÉ—e ya fara jero baragada, S kawai kake ji tana tashi, ga shi kuma yana kuka".
Hasana ta kasa daurewa ta yi nesa da ɗakin, ta yi dariya a ciki-ciki, sannan ta daidaita kanta ta dawo ta sake buga ƙofar, ya zabura, yana ba da haƙuri, ta ce"Yi min shiru, munafukin banza!" Daidai nan kuma ta fara jiyo kukan Aiman.
Ta ce"Ka ci sa'a, yau muna da mitin namu na ƙungiyar karuwai, amma ka sani zan dawo gobe domin mu tattauna game da ƙuntatawar da kake yi wa matarka, da sharrin da kake yi mata, sannan duk chart ɗin cikin wayarka ka tabbata ka goge su, ka goge whatsApp ɗin duka mun haramta maka shi har abada, tun da tarbiyyar yaran mutane kake ɓatawa".
Ya ce"To zan goge, na ma goge wallahi, ni da charting har abada Kaka".
Ta ce"Kai yaro, bar ganin muryata haka kake ce mini Kaka, ni matashiyar aljana ce, shekaruna É—ari uku da ashirin da uku, kawai ina yi maka kalar muryar da kunnenka zai iya É—auka ne".
Ya ce"To na gode, na gode".
Ta ce"Gobe zan dawo mu tattauna, sannan duk wanda ka ba wa labari, to ka tabbata ka furta kalamanka na ƙarshe kenan, domin daga ranar zan fansar da harshenka ga saurayina, ba za ka sake magana da bakinka ba. Yanzu ka tashi ka yi ta tsallen kwaɗo har sai gari ya waye, idan ka fito kafin kiran sallar asuba, sai dai ka ga kanka a tsakiyar barikin aljanu".
Ta leƙa ta windo ta gan shi yana ta tsallen kwaɗon har da kama kunnensa kamar a makaranta, ta buga ƙofar ɗakin da ƙarfi, Nura don tsoro har sai da ya faɗi, sannan ya tashi ya cigaba da yi, ta yi wani irin abu da muryarta, sannan ta tafi cikin sanɗa ta buɗe ƙofar ɗakinta, ta shiga, ta hau gadon ta ɗauki Aiman, ta fashe da dariya, ashe ita tana da maganin Nura ta tsaya take ta shaƙar takaici? Har ta fara hasashen azabar da za ta ba shi gobe, tabbas sai ta huce takaicinta. Haka ta kwanta bacci ranta fes.
A ɓangaren Nura kuwa, ya kai awa biyu yana ta tsallen kwaɗo, yana yi yana addu'a, ya gaji matuƙa, amma tsoro ya hana shi tsayawa, ƙarshe dai da abun ya ishe shi, sai ya yi shahada ya daina yi, ya rarrafa ya kunna kayan kallo, ya nemo tashar da ake yin karatun Qur'ani, ya manta rabon da ya saurari Qur'ani sai yanzu da yake neman tsira, ya zauna yana bin karatun duk da ma bai iya surar ba, a haka har asuba ta yi, bai runtsa ba. Yana jin fitowar Hasana za ta yi alwala, amma tsoro ya hana shi fitowa, ya ce"Hasana!"
Ta amsa tana tahowa É—akin.
Ya ce"Don Allah samo mini buta da roba mai faÉ—i haka, alwala zan yi, ki haÉ—o da fo ma".
Ta ce"Subhanallah! Baban Salim karyewa ka yi ne?"
Ya ce"Dalla idan ba za ki kawo mini ba ki faÉ—a mini!".
Ta ce"A'a ni ba ni da fon da ƙato zai hau, ga dai buta nan" Ta miƙa masa butar hannunta da roba ta fice.
Can dai ya yi shahada ya fito, ya yi alwala ya tafi masallaci, sai da gari ya waye sosai sannan ya dawo, yanzu tsoron ɗakin yake ji, wayarsa kuwa bai kula ta ba, sai da suka gama cin abinci, gabansa yana faɗuwa ya ɗauka, ya goge whatsApp ɗin duka, ya saka a aljihu ya fita, a kasuwa ma jikinsa duk a sanyeye, haka ya dawo cin abincin rana Hasana tana lura da yanayinsa, da zai fita ya ce"Yau kar ki rufe ƙofar nan, a nan zan kwana".
Ta ce"A nan za ka kwana kuma? Kai kuwa me ya yi zafi?"
Ya ɓata rai ya ce"Ban sani ba! Ko ni da gida za ki yi mini iyaka ne?"
Ta ce"A'a, amma dai da mamaki, a ce wai kai da kake kora ta kuma yanzu za ka baro lafiyayyen ɗakinka ka zo nawa, gaskiya da wata a ƙasa".
Ya yi banza da ita, ya fice.
Ana yin sallar isha'i, Hasana ta garƙama sakata a ƙofarta, ƙarfe takwas sai ga shi ya dawo gidan, gabansa yana ta faɗuwa, ya ga abincinsa a ƙofar ɗakinsa, ya je ya fara ƙwanƙwasa ɗakin Hasana tare da kiran sunanta, tana ji ta yi banza da shi, ya dinga bugawa, ƙarshe har Salim da Amir yake kira, ya ji shiru, sai ya kira ta a waya ta ƙi ɗagawa, abun duniya ya ishe shi, shi bai taɓa jin haushin wannan nauyin baccin nata ba kamar yau, ya zauna a tsakar gida duk da gabaɗaya gidan ma tsoro yake ba shi, Hasana ta ɗakko wayarta ta rubuta mata saƙo, ta ce"Ko ka tashi ka shiga ɗakinka mu tattaunawa ko kuma mu yi sama da ƙoƙon kanka yanzu".
Sai da gabansa ya faɗi da ya ji shigowar saƙon, ai kuwa yana karantawa ya tashi a guje ya nufi ɗakin Hasanar yana ta bugawa haɗi da addu'a, Hasana da take ta dariya, ta sake rubuta masa"Muna kallonka kana buga ɗakin baiwar Allah, nan muka aike ka?"
A guje ya je ya buɗe ɗakin nasa ya shiga, yana ta addu'a. Ya tsugunna kamar ɗalibi a gaban Malami, ki mai laifi a gaban jami'an tsaro, ya fara cewa"Don Allah ki yi haƙuri ki yafe ni, wallahi na tuba".
Hasana ta buɗe ɗaki ta fito, karaf a kunnensa, sai kuwa ya daddage yana ƙwala mata kira cikin kuka, "Hasana! Hasana don Allah zo ki cece ni".
Maganarsa ta guntse jin an buga ƙofar ɗakin da mugun ƙarfi, ya yi tsalle ya haye katifa yana "Wa innahu Sulaimanu".
Hasana ta fara irin muryar jiya ta ce"Wato matar taka da kake cuta ita za ta zo ta cece ka ko? To fitsari ta fito, kuma mun juya mata ƙwaƙwalwarta mun mai da ita ɗaki, sai kuma wa za ka kira?"
Da sauri ya ce"Babu, wallahi babu wanda zan kira".
Ta ce"Me yasa kake chart É—in banza da Æ´aÆ´an mutane?"
Ya ce"Ƙaddara ce, amma na daina wallahi, har abada".
Ta ce"Mun gama da wannan shafin, to me yasa kake ƙuntatawa matarka? Kake zaginta idan ka je zance wajen ƴan'matanka?"
Ya ce"Babu komai wallahi, na daina".
Ta ce"Bayan ƙungiyar karuwan aljanu, ina cikin ƙungiyar masu ladabta bil-adaman da suke ƙuntatawa matansu, saboda haka zan ɗauke ka na kai ka can ofishinmu na aljanu masu kare haƙƙin matan bil-adama! A tarihin sama da shekara dubu, babu bil-adaman da ya shiga ofishinmu ya fito da rai"
Cikin tashin hankali Nura ya fara"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Don girman Allah ku yi haƙuri, wallahi na daina, daga yau ba zan sake yi mata komai ba, zancen ma na daina zuwa".
Ta yi wata dariya ta ce"Muna sane da abubuwan da kake yi mata, ba ka ba ta kayan kwalliya, amma kana ba wa matan waje, kwanaki ta tambaye ka me kake so ta dinga yi don ku zauna lafiya, ka ƙi faɗa mata, ta ce ka ba ta kuɗi ta sayi ƙananun kaya nan ma ka ƙi, haka kawai sai ka fara yi mata masifa, sannan kuma ba ka ba ta ɗan kuɗin kashewa, kuma duk baƙin da ta yi sai ka ce kana son su, hakane? Ka raba ɗaki, ka hana ta dinga biyoka"
Da sauri ya ce"Hakane, hakane wallahi wannnan duk halina ne, amma na tuba yanzu".
Ta ce"Sannan sai ka yi wata ba ka kira ta ba, to idan ba ka buƙatar mace mu za mu turo maka aljana shafumuleratu, ta shafeka".
Da sauri ya ce"Ku yi haƙuri don Allah! Wallahi zan gyara zan daina".
Ta ce"Kenan da kana sane? Matan waje kake bi ko?"
Ya ce"A'a wallahi ba na bin kowa, basir ne da ni".
Ta ce"Mun ba ka wata É—aya ka nemi magani!" .
Ya ce"To, zan nema, gobe zan siyo".
Ta ce"Ina kuÉ—in auren da ka fara tarawa? Yanzu sun kai nawa?" Ta tambaya, don a cikin satin ta ji wata Æ´ar'uwarsu ta ce kuÉ—in aure ma zai kai.
Ya ce"Dubu hamsin ne dama za a kai ranar Lahadi, amma yanzu idan kun ce na fasa shikenan".
Ta ce"Ba mu ce ba, amma wannan kuɗin ka ɗauke su ka ba wa matarka ta sayi underwears da kayan kwalliya, kuma ka ba ta haƙuri ku gyara zaman aurenku, sannan daga yau kullum za mu na kawo maka ziyara, idan muka zo muka ganka kana bacci kai kaɗai, sai dai ka farka ka ganka sansanin karuwan aljanu, daga yau ka kira matarka ku dinga kwana tare, ko ba ka ji ba!?"