← Book details Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 16

Sashe 15

Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya gangara gefen titi ya faka motar ya kashe ta, ta kalle shi da alamar tambayar dalilin tsayawar, sai ya kafe ta da kallon da ya saka ta tsarguwa da kuma faɗuwar gaba, ta kau da kai daga kallon shi, a bazata ta ji hannunsa a kan nata, ta kalle shi da sauri, sannan ta kalli hannun nashi, a hankali ta zare hannunta, don ba ta manta wane ne shi ba a wajenta, shi ba muharraminta ba ne, ko ba ta da aure haramun ya taɓa ko da hannunta ne, ta ce"Yaya mene ne?"

Ya ce"Wato Nuratu akwai maganar da nake son mu yi da ke mai muhimmanci, shiyasa na nemi mu fita mu biyu".

Ta yi shiru tana sauraronsa.

Ya ɗan yi shiru yana jujjuya kalaman da zai furta, sannan ya ga kunyar mara kunya ai asara ce, don haka ya fara magana kai tsaye"Nuratu wani auren ana yin shi ne kawai saboda rufin asiri da neman kamala a idon jama'a, kin gan ni a haka kamar ina samun cikakkiyar nutsuwa da matata, amma a baɗini ba haka abun yake ba, wallahi Nawwara sam ba ta san zaman aure ba, don dai ina da haƙuri ne kawai shiyasa har muka kai haka, dama can maleji nake yi, ballantana kuma yanzu da ta fara fita koyarwar nan, idan ta dawo ta yi girki dare ya yi, da na matso kusa da ita za ta fara ƙorafi, tana cewa ita fa duk a gajiye take, cikin kwanakin nan lamarin ya dame ni, ina tsoron na kasa jurewa. Nuraru na san a yanzu kin riga kin san maza, wannan mara kirkin mijin naki ya cuce ki, ya lasa miki zuma a baki".

Ta dai yi shiru tana so ta ji ƙarshen zancen, ta gama sakankancewa so yake ya saka ta, ta nemi saki a wajen Abdul, don ta samu wanda zai aure ta su yi rayuwa mai inganci, sai dai tana nazarin me yasa zai sanar da ita matsalar iyalinsa?

Kabir ya cigaba da faɗin"Nuratu ke ƙanwata ce, na san ba za ki kasa taimakona ba, wannan alaƙar da nake son mu ƙulla ni da ke sunanta taimakon juna, domin za mu dinga yin abin da Hausawa suke cewa ban gishiri, na ba ka manda".

"Yaya alaƙa?" Ta tambaya da mamaki.

Ya ce"Alaƙa mai ƙarfi ma kuwa, ina roƙon wannan alfarmar a wajenki Nuratu, mu dinga ragewa junanmu zafi, tun da ke kin saba da maza kuma yanzu babu damar samun su, ni kuma ga yanayin matata, kin ga ke ƙanwata ce, kuma matar aure, babu wanda zai kawo wani tunani mara kyau a kanmu, amma ya kike gani?"

Ƙwalla ta cika idonta taff, ta ma rasa me za ta ce, gabaɗaya ya ɗaure ta da jijiyoyin jikinta.

Ya ce"Na yi miki alƙawarin duk watan duniyar nan zan dinga ƙirga dubu ashirin ina ba ki, na tabbata kafin mijinki ya dawo kin haɗa kuɗin kayan ɗaki, kin ga ba ganewa zai yi ba, tun da dama can ya gama lalube ki, ya kike gani?"

Tuni hawaye suka wanke mata fuska, ta rasa wane irin zamani ake ciki wanda mutane ba sa jin tsoron Allah, ba sa yin taimako domin Allah, indai wanda ke da matsayin É—an'uwanta na jini zai so lalata rayuwarta to ina ga Agent wanda ba su haÉ—a komai ba? Tambaya take yi wa kanta wai meyasa maza suka mayar da kansu tamkar Æ´an taure?

Kabir ya kalli agogo a wayarsa yana cewa"Lokaci yana tafiya, na san maganar tana da nauyi, amma zan ba ki dama ki yi tunani, za ki samu ci da sha, har ma sutura a gidana, babu abin da ba zan yi miki ba, duk abin da kike buƙata kawai ki sanar da ni, sannan wannan ba wani abu ba ne mai wahala, da safe idan ta tafi gantalin koyarwarta, ni kuma sai na dawo gida, kamar ƙarfe goma haka, mu samu ko minti talatin ne".

Ta ce"Yaya Kabir mayar da ni gida".

Ya tashi motar yana cewa"Mu je ki yi siyayyarki, ki zaɓo kayan bacci ma su kyau".

Takaici ya hana ta cewa komai, har suka ƙarasa babban shop ɗin, duk yadda ya yi da ita, fir ta ƙi fitowa daga motar, sai shi ya shiga ya siyo mata kayan, wanda yawanci riga da wando ne da riga da siket na roba, sai atamfofi kala uku, da ƙananun abubuwa, irin su towel, soson wanka, brush, da saitin man shafawa da subulai, haka dai kaya rigijib ya kawo mata, sai ta kasa yi masa godiya tun da zuwa yanzu ta fahimci ba don Allah yake yin komai ba.

Da suka dawo gida sun tarar da Nawwara a falo, ta yi mamakin ganin shi ne ya ruƙo kayan ba Nuratu ba, sannan ba ta ce komai ba, ta wuce ɗaki, shi ma sai da ya ji ƴar fargaba, Nawwara ta ce"Lafiya kuwa, na ga ranta a ɓace?"

Ya ce"Wallahi wani ne ya biyo mu wai yana son ta, na faɗa masa matar aure ce, to shi ne fa a mota har da kukanta, tana cewa ban da ƙaddara da tana tare da mijinta ai da wani bai ganta ba ma, ballantana ya ce yana sonta".

Nawwara ta yi murmushi ta ce"Nuratu kenan, ni dai ban ga abun fushi a nan ba".

Ya ajiye kayan, ta É—auka ta buÉ—a tana cewa"An samo curryn?"

Ya ce"To ina ma ta bi ta kan wani curry, lokaci É—aya fa ta birkice kamar mai aljanu".

Nawwara ta ce"To Allah Ya kyauta". Ta kwashi kayan ta miƙa mata, ta tafi ɗakin mijinta.

Nuratu ta zauna tana ta tunanin mafita, indai wannan manufar ce tabsaka Yaya Kabir ya nemi ta zo ta zauna a gidansa, to kuwa gara ma ta zauna a gidan su Abdul ɗin, ba ta fatan ta sake aikata wani kuskuren a kan wanda ta yi, zina babban bala'i ce, ga shi ta sanadin aikatata sau ɗaya ta shiga masifar da take neman yi wa rayuwarta juyin waina cikin baƙar tanda, lallai gidan Yaya Kabir ba wajen zamanta ba ne, ya zama wajibi ta tattara ta koma inda ta fito.

Bayan ta gama shirin bacci, sai ta ɗauki wayarta, ta kunna data, ta yi wa Abdul sallama ta gaishe shi, sannan ta ce"Na sauka lafiya tun ɗazu, da fatan kana cikin ƙoshin lafiya".

Yana dubawa sai ta ga ya fara typin, daÉ—in zai kula ta da kuma fargabar abin da zai rubuto suka dira a zuciyarta lokaci É—aya, yanzu har tana fargabar jin furucinsa a kanta, saboda ba ya faÉ—a mata magana mai daÉ—i.

"Ke da waye yanzu a É—aki?" Abin da ya rubuto kenan.

Ita ma rubutun ta yi masa ta ce"Ni da kewarka ne, ka san gidan babu yara, ni kaÉ—ai ce a É—akin da aka sauke ni".

Ya ce"Za ki iya yi mini vedion kanki a halin yanzu?"

Ta ce"Gaskiya ba zai yi ba, saboda wayar babu flash".

Ya ce"To gobe da safe ki yo mini vedion jikinki, ban ce ki saka kaya ba, saboda ina buƙatar ganin halal ɗina ne".

Sai da ta ji gabanta ya faÉ—i da ta karanta, ta sake maimaita karantawa, ta yi mamaki, tun da ta ga yana ta nuna rashin damuwarsa a kanta, sannan ma ta lura kamar dole ce ta saka ya yarda da aurenta, amma har a ce yana jin kewarta da ta kai har yana neman ganin ko da hoton jikinta ne?"

Ganin ta duba saƙon ba ta ce komai ba, ya sake rubuto"Ko ba zan samu ba?"

Ta rubuta masa"Allah Ya kai mu goben".

Ta ma rasa ta ina za ta fara wannan abun da ba ta taɓa yi ba, amma ta sani a yanzu Abdul mijinta ne, wannan ba haramci ya nemi ta aikata ba, sai dai tana jin nauyi kuma ta ga abun banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Tana cikin duba saƙonni sai ga saƙon Yaya Kabir ya shigo, stika ce ya turo mata ta mace da namiji rungume da juna, sannan ya yi gajeren rubutu ya ce"Zan kwana da kewarki". Don takaici ba ta san sanda hawaye ya sakko mata ba, ta kashe data ta kwanta tana jin zuciyarta babu daɗi, ga kuma rashin nutsuwa a tare da ita, ta san a yanzu idan ta ce za ta koma gida ba ƙaramin yaƙi ta ɗakko ba tsakaninta da Baba, da haka ta yi bacci kanta a cushe.

Washegari da sassafe ta ji motsin Nawwara, ta fito ta gano ta a kitchen, ta shiga ta gaishe ta, sannan ta fara taya ta aiki, suna gama komai ta koma É—aki, sanda suka fito karyawa Nawwara ta zo ta kira ta, ta ce"Anti sai anjima zan karya".

Saboda ko ganin Kabir ma ba ta son yi.

Bayan sun gama karyawa Nawwara ta leƙo tana ce mata "Za mu tafi"

Ta ce"To Anti, me za a dafa muku kafin ku dawo?"

Ta ce"Ki dafa duk abin da kike ra'ayi, sai mun dawo".

Ta ce"A dawo lafiya".

Bayan sun tafi, ta fito ta ci abinci, ta yi wanke-wanke, ta share gidan ta gyara komai tsaf, maganar Abdul tana maƙale a zuciyarta, don haka ta tashi ta yi wanka, ba ta ji a zuciyarta za ta iya yin vedion kamar yadda ya ce ba, don haka ta yanke za ta saka rigar bacci, sai kuma ta tuna ba ta da wata rigar bacci, rigunanta marasa nauyi ma duk sun tsufa sun ji jiki, ba za ta iya yi wa miji kwalliya da su ba, ta tsinci kanta da duba ledar kayan da suka siyo jiya, ta kuwa ga kayan bacci kala uku, ciki har da wata riga ta net mara kirki sosai, sai ta saka ta, ta ɗauki kanta a hoto, ta kunna data, da saƙon Kabir ta fara cin karo, da alama tun jiya ya turo, don cewa yake yi"Na zo na taya ki bacci?"

Ta yi tsaki, ta shiga lambar Abdul ta yi sallama ta gaishe shi, sannan ta tura masa hoton da ta É—auka yanzu, yana dubawa ya ce"Mene ne wannan?"

Ta ce"Ba zan iya yin hoto babu kaya ba".

Ya ce"Amma za ki iya ba wa wanu kanki ai ko? Kuma vedio na ce, sannan ina son ganin fuskarki sosai a vedion".
Chapter 15 · 0% Book details