Sashe 8
Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ajiye wayar tana tuna ranar da ya zo ƙofar gidansu, jikinsa a mace, yana faɗa mata Agent ɗin ya ce yau ce rana ta ƙarshe, idan bai kawo kuɗin nan ba, babu shi a tafiya, sai dai ya sake nema a gaba, abokansa uku duk sun biya, shi ne kaɗai ba shi da shi, ga shi mahaifinsa yana zaune a gida, jinya ta saka shi a gaba, a ƙa'ida ya kamata a ce yana asibiti, amma yanzu yana gida sai maganin Hausa ake ta banka masa. Ya ce"Nuratu macuta sun yi yawa a ƙasar nan, a gabana ya cikewa mata biyu, kuma ina zargin sun ba shi kansu ne, ɗayar ma buduruwa ce, tsananin rayuwa ya sa take son tafiyar, na ga bayan ta fito ta tsaya tana kuka, ita da ya kamata ta yi farinciki, ni kuma da nake namiji kuɗi ne kaɗai zai fitar da ni, na rasa yadda zan yi, ba na so tafiyar nan ta kufce mini, domin na san haka ke ma za ki kufce mini".
Nuratu ta ce"Allah Ya kiyaye, wallahi ba zan taɓa kufce maka ba Yaya Abdul, zan jira har ka samu aiki".
Ya yi guntun murmushi ya ce"Wa ya san nan da shekara nawa za a samu? Ai ni ma ba zan so tauye miki rayuwa ba".
Ta ce"Yanzu babu wata hanyar?"
Ya ce"Ba ni da komai wallahi, kin ga babata duk ta siyar da kayan É—akinta, akan tafiyar nan idan ba ta yiwu ba akwai damuwa".
Haka suka dinga tattaunawa, ƙarshe da zai tafi ta ce ya ara mata wayarsa za ta yi kallo, dama yana ara mata, don haka ya miƙa mata ya tafi. Ta shiga ɗaki ta yi zaune da wayar tana tunanin mafita, kafin ta bi shawarar zuciyarta ta ɗauki lambar Agent ɗin, shi ne wanda suka yi waya na ƙarshe, ta saka a wayarta, ta danna kira, ya ɗauka suka gaisa, ta ce"Ni ƴar'uwar Abdul ce".
Ya ce"Wane Abdul?"
Ta ce"Abdulmalik, wanda kuka yi waya É—azu, wanda bai samu ya cika kuÉ—in tafiyarsa ba".
Ya ce"Ok ya aka yi?"
Ta ce"Dama ina son mu haɗu, akwai alfarmar da zan roƙa idan zai yiwu".
Ya yi mata kwatance, Allah Ya taimake ta Mama ba ta nan don haka ta saka hijjabi ta tafi. A bakin titi ta tsaya, ya turo aka shiga da ita, ta shiga har ofishinsa, ta zauna ta gaishe shi, ta sake yi masa bayanin kanta, sannan ta É—ora da faÉ—in"Abdul yana cikin matsalar rayuwa, shi ne babba a gidansu, ga mahaifinsa ba shi da lafiya, don Allah ka taimaka masa ya samu tafiyar nan, daga baya sai ya biya ka".
Ya ce"To ƴan'mata ai haka tsarin yake, mu babu ruwanmu da ƙarfin matsalar mutum, kamfani ne, dole yadda aka tsara ake yi".
Ta ce"To amma me zai hana ka ɗauke ni a nan ɗin ko na shara ne, sai ka dinga riƙe albashin nawa da haka har ya biya ka?"
Ya yi ɗan murmushi ya ce"Wannan lokaci ya ƙure masa ai, yau ce kaɗai damarsa, ni kuma ba zan yi masa aiki bashi ba".
Idonta ya kawo ruwa, ta karaya sosai, ta tashi tana cewa"Shikenan na gode".
Har ta kusa fita, ya kira ta, ya nuna mata kujera ta zauna, ya ce"Ya kuke da shi?"
Ta ce"Yayana ne".
Ya ce"To indai da gaske kike son taimakonsa, ai kina da abin da za ki taimake da shi" Ya ƙarasa yana yi mata kallon ƴan bariki.
Ta ce"Inda ina da shi, da ban zo neman alfarmar nan ba".
Ya ce"Idan har za ki amince mu tsallaka wancen hotel É—in na kusa da mu, cikin mintuna za ki taimaki yayanki".
Gabanta ya faÉ—i, ta ce"Amma sai wannan kaÉ—ai?"
Ya ce"E, idan kin duba ai ba wani abu ba ne mai wahala, saboda idan ya tafi zai yi miki alheri fiye da yadda kika yi masa, ƙila ma idan aurenki ya zo shi ne zai yi miki kayan ɗaki, sannan kamar kin taimaki iyayenki ne".
Ta ce"Zan yi shawara".
Ya ce"No, ki je kawai, na faÉ—a miki yau ne last".
Ya É—auki waya ya yi danne-danne ya kara a kunne, ya ce"Wannan list É—in ku cire sunan Abdulmalik Ibrahim, zan tura muku sunan da za ku saka a kai".
Hawaye ya zubo mata, ta ce"Don Allah Oga ka taimake mu, zan dinga kawo maka kuÉ—in a hankali".
Ya ce"Ki je kawai, ba shi da rabon tafiyar".
Ta tuna wane ne Abdul da yadda yake ƙaunarta, sai ta ga ya cancanci har sadaukarwar rayuwa ta yi masa, don haka ta ce ta amince, nan take suka fita, suka je Nuratu ta miƙa kanta, babu shawara babu tunanin ta tafka kuskure, ta manta wane ne namiji, ba ta tunanin ba kowane zai iya yi maka halakci har ƙarshen rayuwarku ba.
Shigowar Nawwara ce ta katse mata tunani, ta kai hannu ta share hawayen fuskarta, Nawwara ta ce"Ki fito falo yana jiranki, fita zai yi".
Ta tashi ta bi bayanta. Ta zauna kanta a ƙasa, Kabir ya ce"Nuratu me ya kawo ki? Ni ma gobe nake shirin tafiya gaisuwar fa, aiki ne ya yi mini yawa".
Sai ta fara kuka, Nawwara ta ce"Ɗan'uwanki ne, tun da kika zo wajen shi na tabbata kina da yaƙinin samun sassaucin damuwarki, saboda haka bai kamata ki ɓoye masa komai ba" Sai ta tashi ta shiga ɗakinta, don ta ba su waje.
Nuratu ta kasa faɗa masa komai, sai kuka da ya ci ƙarfinta, ƙarshe ya ɗauki waya ya kira Babanta, wanda ke a matsayin ƙanin uba a wajen shi, wato dai ɗan wa da ɗan ƙani suke da Nuratu, amma Allah Ya haɗa jininsu sosai, har ma ya so ta koma gidansa da ya yi aure, sai Mama ta hana, sai dai ta je hutu ta kwana biyu ta dawo gida.
Suka gaisa da Baba, ya ƙara yi masa gaisuwa, sannan ya faɗa masa ga Nuratu ta zo tana kuka, ta ƙi faɗar komai.
Baba da yake kwance a ɗakinsa abun duniya ya ishe shi, ya miƙe zaune yana cewa"Alhamdulillah! Gidanka ta zo ashe?"
Ya ce"E ga ta nan".
Nan Baba ya kwashe komai ya faɗa masa, Kabir ya yi mamaki sosai, saboda duk cikin ƴan gidansu ya fi ganin nutsuwarta, ya shiga yi mata faɗa, tana ta kuka, ƙarshe ya tambaye ta wane ne ya yi mata haka? Nan ma dai ta ƙi faɗa, don takaici ko sallama bai yi wa matarsa ba ya fice daga gidan, a waje Baba ya sake kiransa ya ce lallai-lallai gobe ya sako Nuratu a mota su dawo, ya ce masa da kansa ma zai kawo ta.
Haka ta wuni a ɗaki, duk yadda ta so Abdul ya fahimce ta abu ya ci tura, babu kalar bayanin da ba ta yi masa ba, amma yanzu ya ma daina duba saƙon, kuma yana online.
Shi kuwa a ɓangarensa shi kaɗai ya san halin da zuciyarsa take ciki, yana da matuƙar kishi, musamman a kan Nuratu da ya yanke a ransa da ita kaɗai zai rayu, ya kasa ganin da gaske halakci ta yi masa, ballantana ya yi mata sassauci a hukunci, abu ɗaya kawai yake yawo a kansa, Nuratu ta yi masa butulci, kuma zuciyarta ba mai kyau ba ce, yana tunanin da aurensu ma za ta iya aikata hakan, da sunan taimako.
Amma ta duniya za ta kalle shi da iyayensa, idan aka ji domin shi ta aikata? Saboda haka zai yanke wani hukunci, zai aure ta na É—an lokaci, daga nan duk wanda zai ji tarihinta a bazawara zai santa, kenan ba za ta samu wata matsala ba a duk yadda mijin da za ta rayu da shi ya same ta.
Ya kira mahaifiyarsa a waya, ya tausasa murya, ya fara roƙonta yafiya, ya yi mata shimfiɗar ƙaddara, sannan ya faɗa mata kafin ya tafi shaiɗan ya shiga tsakaninsu da Nuratu, har ma tana da cikinsa, mahaifiyarsa ta shiga tashin hankali sosai, ta san idan ta sanarwa mahaifinsa zai iya ƙarasawa, don haka ta faɗawa ɗan'uwansa, wanda yake waliyin Abdul ɗin, duk faɗan da aka yi wa Abdul ya yi haƙuri ya jure, a ganinsa wannan ne halakcin da zai yi wa Nuratu kawai, ya rama wa kura aniyarta.
Haka ƙanin babansa ya je wajen Baba da daddare ya faɗa masa halin da ake ciki, Baba ya dinga sababi, don dama Abdul ɗin kaɗai ya zarga, tun da ba ta kula kowa bayan shi, nan ya rarrashe shi, ya ce Abdul zai turo sadaki a ɗaura auren cikin satin nan, idan ya dawo sai ta tare, nan Baba ya ce bai yarda ba, su je kawai Allah Ya isa, amma ita Allah Ya rufa mata asiri, tana da miji.
Washegari Kabir ya saka Nuratu a gaba suka dawo, nan suka zauna da Baba a gabanta yake sanar masa Abdul ne ya yi mata ciki, kuma ya ce zai aure ta. Ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi, sai ta rasa farinciki take ciki, ko akasinsa? Ashe Abdul zai jiɓanci lamarin nan, har ya amsa laifin da ba nashi ba? Ta babbata ita da Abdul ruhi ɗaya ne a gangar jiki biyu, ashe ya nuna fushi ne kawai saboda ya hora ta, sai ta ji kamar ta fita daga duka damuwar ma.
Kabir ya ce"To Baba ai ta kwana gidan sauƙi, dama wanda ya dama kunun ai shi ya kamata ya shanye, kuma suna son junansu, tun da ta ga za ta iya jiransa sanda ya bushi iska ya dawo sai su tare".
Baba Ya ce"Ai ba a nan gizo ke saƙar ba!". Nan ya ba shi labarin Alhaji Hashimu, ya ɗora da faɗin"Ka ga shi ya ji ya gani, sannan babba ne mai hankali, ba kamar Abdul ba da ƙuruciya, bar ganin shi ya yi aika-aikar, tsaf zai wulaƙantata a hakan hakan, shi kuwa wannan mai rufin asiri ne, wulaƙanci mai kuɗi ya fi na talaka sassauci a zuciya, ko banza dai a gidansa za ta fi ƙarfin komai, sannan yanzu ta riga ta san daɗin namiji, ba lallai ta nutsu ba, ƙila ta cigaba da shashancinta shi yana can, tana kwasar zunubi, kuma ni ina ma zargin tilas za a yi masa, idan ya ƙi dawowa ya zan yi da ita?"