← Book details Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 16

Sashe 10

Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washegari da safe direba ya zo ya ɗauke ta, tare da wata yayarta, suka tafi asibiti, gabanta yana ta faɗuwa, tana jin kamar ta gudu, a hannun likitan farko dai ya damƙa ta, da alama shi ɗin amintaccensa ne, shi da kansa ya yi mata allurar zubar da cikin, sannan ya ba ta gado. Bayan ya kammala ya kira Hajiya Kubra a waya ya sanar mata.

Zuwa yamma komai ya kammala, cikin ya fita duka, aka sallame su direba ya mayar da su gida. Tun kafin su ƙarasa likita ya kira Alhaji suka gaisa ya ce"An kammala aikin cikin nasara".

Ya ce"To Alhamdulillah!".

Likita ya ce"Sai dai fa akwai wata matsala".

Ya ce"Ta mene ne?"

Likita ya ce"To ban sani ba ko ka san yarinyar tana É—auke da cuta mai karya garkuwar jiki".

Gaban Alhaji ya faÉ—i, ya kaÉ—u sosai da jin kalmar nan, ya ce"Ok babu damuwa, na gode".

Ya katse kiran, nan tausayinta ya ƙara kama shi, ya kuma raya a zuciyarsa lallai yaron nan ya cuci Nuratu, ko ta san tana da cutar a jikint? Da ya yi tunanin sanarwa Baba, sai kuma ya ga tun da yaron ne zai aure ta gara ma ya bar zancen don kar abun ya yi wa Baba yawa, ya tausaya musu sosai, ya kuma gode Allah da aka gano hakan, bai aure ta ba ya sakawa matansa.

A ranar da daddare ya je ya kai kayan abinci da yawa, sannan ya kai wa Nuratu kayan shayi, da fruit, ya haɗa mata da kuɗi, ya zauna da Baba ya ce masa"Baba haƙiƙa na so na taimaki Nuratu ta hanyar aurenta, to kuma sai aka samu wata ƴar matsala wacce ba zai biyo na ƙara aure nan kusa ba, saboda haka ka yi haƙuri ni na janye zancen auren, idan ta samu miji kawai ka aurar da ita, sannan ina ba ka shawarar indai wannan yaron da ya yi mata abun ya amince zai aure ta, to kar ka ƙi, domin shi ne ya fi cancanta".

Baba jikinsa ya yi sanyi ƙalau, ya ce"Amma Alhaji wannan wace matsala ce?"

Ya ce"Matsalar iyali ce, na yi iya yina na ga abun ba zai yiwu ba, ka yi yadda na ba ka shawara kawai". Ya ɗakko dubu hamsin ya ba shi, ya ce ya ƙara a jarinsa don kula da iyali. Baba ya dinga godiya, har da ƙwallarsa, ya bi Alhaji da kallo cike da jajantawa Nuratu na asarar da ta yi.

08028966015
[11/23, 12:44 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*

BY
SADIYA ABDULRAZAƘ

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY

PAGE 8

Baba yana shiga gida ya shiga ƙwala wa Nuratu kira, ta fito gabanta yana faɗuwa, ya ce"To yau dai burinki ya cika, Alhaji Hashimu ya fasa aurenki, sai ki je ki auri yaron da ba a san ranar dawowarsa ba ma".

Ta ji sanyi a ranta, ba ta ce komai ba, har ya gama faÉ—ansa ya fice.

Tsawon sati ɗaya tana fama da Abdul ya ƙi sauraronta, sai dai ya duba saƙonta ya yi shiru babu amsa, har ta gaji ita ma ta ƙyale shi zuwa sanda zai huce, sai su sasanta. Wasu daga cikin ƴan'uwan Mama sun gane ta yi ɓarin ciki, saboda duk da Baba ya hana zaman makoki, suna zuwa kullum su ga Nuratu, su kuma taho mata da abinci, don haka ba ta ɓoye musu ba, saboda ta san dole zancen ya fita gari, ko ƴan gidansu za su iya fitarwa, ballantana kuma ƴan'uwan Abdul, ƙanwar Baba sai ta gyara mata jiki daidai gwargwado, bayan sun yi mata faɗa da nasiha.

Bayan kwana arba'in da mutuwar Mama, zuwa yanzu har ta fara sarewa da lamarin Abdul, domin kuwa har yau bai saurare ta ba, ta yi nacin da magiya iya iyawrta ta gaji, don haka ta zuba masa ido, a kwana arba'in ɗin nan ita kaɗai ta san halin da take ciki na ƙunci, kullum a ɗaki take wuni, don kunyar fita waje take yi, gani take kowa yana ganinta zai gane ta zubar da ciki, idan an yi abinci ana miƙo mata, wataran duk su biyun su ba ta, wataran mutum ɗaya ta ba ta, wannan duk albarkacin kayan abincin da Alhaji ya kawo ne, don a baya Baba bai damu da cefanen gidansa ba, sai dai kowacce mace ta yi sana'arta, ta ci da ƴaƴanta, shiyasa Mama ma ta kama sana'ar waina kafin rasuwarta, ga shi yanzu har an ɗora Khadija a kai, dama tare suka yi Candy da Nuratu, kuma babu maganar miji, ballantana cigaba da karatu.

A cikin satin da aka yi arba'in, sai ga Baba ya zo cikin gida da zancen gobe iyayen Abdul za su kawo sadaki a ɗaura aure, zuciyarta ta dinga dokawa, sai ta nemi farinciki ta rasa, ba ta taɓa hasashen aurenta da Abdul zai zo ta wannan yanayin ba. Matan na shi suka tambaye shi za a yi biki ko ita Nuratu za ta yi ƴar walima? Ya ce babu wani taron banza da za a yi, a wannan auren na larura, da an ɗaura aure a masallaci shikenan, shi babu wani gayyata da zai yi ma. Duk da haka sai da suka kira ƴan'uwan babarta da na Baban suka sanar da su, washegari misalin ƙarfe biyu na rana aka ɗaura auren Nuratu da Abdulmalik a kan sadaki naira dubu hamsin, duk da an ce babu taron sai da ƴan'uwa na kusa suka zo, ƴan'uwan babarta suka auno shinkafa kwano biyu aka dafa kowa ya ci, an yi sa'a Baba ya zo ya damƙa mata kuɗin sadakinta, ta ajiye a gefe tana kuka, yayar babarta ta ce"Kawowa za ki yi a adana miki, wannan uban naki tsaf zai biyo ya ce ki bada".

Wata ƴar'uwarta ta ce"Kamata ya yi a dinga juya su, ƙila zuwa sanda zai dawo ta tare su isa a siya mata katifa mai inganci". Duk suka yarda da shawarar.

Nan suka tambaye ta batun lefe,ta ce ita ma ba ta sani ba, suka hau faɗa suna cewa wannan ai rainin wayo ne, babu lefe kuma ya ba da sadaki dubu hamsin? Ai arahar ta yi yawa, ita dai ba ta ce komai ba, domin ta san ita ce ta ja komai, a ganinta Abdul ya yi mata halakci ma da ya yarda zai aure ta, ya kuma ɓatawa kansa suna a duniya, don haka ba ta da ta cewa, zuwa magriba kowa ya kama gabansa. Da daddare sai ga Baba ya shigo yana kiran Nuratu, ta zo ta tsuguna, ya ce"Ina kuɗin sadakin? Ai sai ki kawo gobe a siyo miki katifa".

Ta ce"Baba ai na za ta sai ya dawo".

Ya ce"Au dama nufinku auren kawai aka ɗaura, na siyar da akuya kuma za ta cigaba da cin dangata? To wallahi ba zai yiwu ba, ko dai ya kama miki haya, ko ki tafi can gidan iyayensa ki tare, ni dai tun da na aurar da ke, to ya zama dole na gani a ƙasa, me za ki zauna ki yi a gida, da aurenki? A'a ba za a yi wannan shashancin da ni ba!".

Nuratu jikinta ya yi sanyi, har ta fara hawaye, ta kuma kasa cewa komai.

Baba ya ce"Ni shiga ki fito mini da kuÉ—in, na kama gabana!".

A raunace ta ce"Ƴan'uwan Mama sun tafi da shi, su ma katifar za su siyo mini yau".

Sai kuwa Baba ya rafka salatin da har mutanen gidan suka fito, ya ce"Yanzu ni na haifi ƴar, babu shegen da ya san cinta da shanta, har ta kawo moro, a ce ni ban kai a yi shawara da ni ba a kan sarrafa sadakinta!? Saboda tsabar rainin hankali! To maza shige mu je ki karɓo su!".

Mama Karime ta ce"A'a Malam, wannnan fa ba wani abun tayar da jijiyar wuya ba ne, ni na tabbata mutanen nan ba za su cinye mata kuÉ—i ba".

Mama Asabe ta ce"Wannan gaskiya ne, kuma su ma suna da haƙƙi a kanta, bai kamata a ce don an ba su kuɗi ka je ka karɓo ba".

Ya ce"Cikinku nan akwai wacce ta siya mata wani abu na gudunmawa? Ko za ku bayar nan gaba? Ku fita harkar Æ´ata, babu ruwanku da tsarina!"

Ya kalli Nuratu"Ke wuce mu je!".

Dama da hijjabi a jikinta, sai ta wuce ya bi bayanta, suka tafi, suna zuwa ƙofar gidan ya tsaya, ta shiga a sanyaye, Mama tana ganinta ta ce"Nuratu! Lafiya kuwa cikin daren nan?"

Ta fara kuka ta faÉ—a mata yadda suka yi da Baba, ta ce"Ai dama na san ba zai bar wannan kuÉ—in ba, ai shikenan dole a bi yadda ya tsara, kunya ce dai za a sha ta daga baya".

Ta ɗakko kuɗin ta ba ta, tana cewa"Ki yi haƙuri da duk abin da za ki gani Nuratu".

Ta karɓa ta fita ta miƙa masa, sai da ya ƙirga su cif sannan ya saka a aljihu suka tafi, a hanya ma yana ta sababi yana cewa zuwa gobe ya ba su, dole su zo su san inda za ta tare.
Chapter 10 · 0% Book details