← Book details Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 16

Sashe 6

Zuciyar Mace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta zauna tana mamakin me zai saka a cikin ɗakin? Ta san halinsa yanzu sai ya zo ya fara yi mata hayaniya, don haka ta tashi, ta fito da komai, ta share kamar yadda ya ce, ta janyo ƙofar ta koma ɗakinta, can anjima sai ga shi yana shigo da kaya, katifa ce madaidaiciya, da kayan kallo, har da ƙaramin firji, ta cika da mamaki, tana tsaye ya fara shiga da kayan yana ƴar waƙarsa, da alama yana cike da nishaɗi, ganin ko kallo ba ta ishe shi ba, sai ta shige ɗakinta, tana jira ya gama ta ji bayanin da zai yi mata. Ai kuwa yana gamawa ya ƙwala mata kira, ta fito tana amsawa, ya ce"Shigo mana".

Ta shiga tana ƙarewa ɗakin kallo, ya ce"To yanzu saurana sif, zan sa a yi mini sif mai biyu ƴar madaidaiciya haka, wacce zan zuba kayana a ciki, kin ga komai na zai zauna lafiya, idan zan fita na rufe ɗakina shikenan".

Da mamaki ta ce"Kamar ya É—akinka? Au wai nan turaka ce ka ware kenan?"

Ya ce"Ai ya wuce wai, ni na gaji da yadda nake bacci rabi da rabi, yara su hana ni bacci su hana ni sakat, tsakar dare a farka a yi ta kuka, don haka na ware É—akina".

Hasana ta ce"Baban Salim kenan! Kuma ban da abunka na ga dai yaran nan naka ne, sannan abu ba na farko ba, ba na biyu ba ai ya kamata zuwa yanzu a ce ka saba, kuma ma yanzu don ka yi hakan ai ba shi zai hana ka jin kukan Aiman ba, tun da dai ka san ba zan zo na kwana a nan na baro yaro ƙarami mai shan nono ba, dole da shi zan dinga tahowa".

Nan take fara'ar fuskarsa ta gushe, ya ce"Ki taho ina? Wai kina nufin saboda na ware ɗaki sai ki kwaso jiki ki biyo ni? Kenan ma na gudu ban tsira ba! A'a ba zai yiwu ba, ki yi zamanki da yara, ni duk sanda na buƙace ki zan kira ki, amma gaskiya ba don mu tare mu biyu na ware ɗakina ba".

Ta ce"To shikenan!" Ta juya ta fice, ranta bai so ba, sam ba za ta samu nutsuwa ba, saboda zarginsa da take yi ne zai ƙaru sosai, haka kawai ma tsakar dare farkawa take yi ta ga ba ya ɗakin, sai ta ji shi a tsakar gida yana waya, ko ta gan shi a falo yana vedio call, sai ya ganta ya yi tsaki, ya koma ya kwanta, to ina ga kuma ya ware ɗakinsa shi kaɗai? Tabbas zai ci karensa babu babbaka kenan, ta san ba ta isa ta ja da shi ba, amma kuma za ta yi iya yinta ta saka masa ido, don ganin bai kauce hanya ba, don haka ta ayyana bacci da ido ɗaya ya kama ta.

Haka ya wuni yana shige da fice, ya saita kayan kallo tsaf, dama akwai babbar setilait a tsakar gidan, tun da risibarsu ta lalace take ajiye kawai, bai kai musu gyara ba, yanzu sai ya sa aka saita da sabuwar risibar da ya siyo, firji ma nasu ya lalace bai kai gyaran ba, don ya ce ya gaji da gyarawa suna lalatawa, ita kuma a ganinta tsufa ya yi, tun da tun na aurenta ne, shekararsa takwas kenan.

Ya É—akko yara daga makaranta, suna zaune suna cin abincin rana, yake cewa"Ma sha Allah! ÆŠakina ya haÉ—u, yanzu mun yi magana da wani kafinta, zuwa jibi sif É—ina za ta zo, sai na samu É—an kafet, na saka a tsakiyar É—akin, ina ga ma sai na sayi senta tebur".

Hasana ko kallonsa ba ta yi ba, saboda takaici duk ya ishe ta.

Ya cigaba da cewa"Yadda tsarin gyaran É—akin zai kasance, da safe idan na gama shiryawa, ina zaune ina karyawa, ke kuma sai ki shiga ki gyara, idan zan fita na rufe abuna, salun-alun karatun yankan jaki".

Har yanzu dai ba ta ce komai ba. Sai ya ajiye kofin hannunsa yana haÉ—e gira ya ce"Wai ni Hasana me kike nufi ne? Ya ina magana kina manna mini hauka? Ko hassada kike yi da É—akin nawa?"

Ta ce"Hmm! A kan me zan yi maka hassada? Kawai dai gani na yi tsarin kamar bai yi ba, a ce kana da mata ita tana É—akinta, kai kana naka, wai sai ranar da ka kira ta? Ka manta sai ka yi wata ba ka kira ni ba?"

Ya ce"To mene ne? Ke ba hutunki ba ne ba ma? Ki sake a É—akinki, na sake a É—akina".

Salim Ya ce"Abba wane É—akin?"

Gwab! Hasana ta buge bakin yaron, tana cewa"Ban hana ka saka mana baki a magana ba? Waye sa'anka a nan?"

Sai kuwa Nura ya hartsuƙo kamar zai dake ta, yana cewa"Kar ki sake ki ƙara dukan shi, saboda ya tambaye ni? Da ke yake? Ba ki iya komai ba sai shirme!".

Ya tashi yana ɗaukar mukullin babur ɗinsa ya fice zuwa tsakar gida, yana kiran Salim ɗin, ya je ya buɗe masa ɗakin suka shiga, sai da ta ga za su yi lattin islamiyya sannan ta leƙa tana cewa"Ku zo ku tafi makaranta".

Salim Ya noƙe kafaɗa yana cewa"Daddy ni yau ba sai na je ba".

Hasana ta ce"A kan me? Ai kuwa ya zama dole ka je!".

Nura ya ce"Ƙyale shi, ƙila ya gaji ne".

Ta juya ta koma ɗaki, tana jin sanda suka fita, ya siyo musu biskit ya dawo da su, tana zaune ranta a ɓace, saboda ta gaji da yadda yake ɗaurewa yaran akan rashin son karatun addini, ya ce"Ki biya musu karatun, tun da ba su samu zuwa ba".

Ko kallonsa ba ta yi ba, ya fice daga gidan. Ta ja kunnen yaron ta murÉ—e tana cewa"Idan ka girma za ka gane ba gata yake yi maka ba!".

Ƙarfe sha biyu na dare, Hasana ta kasa bacci, tana tunanin me Nura yake yi a halin yanzu? Ya yi bacci, ko yana ta waya da ƴan mata? Tunanin ya kasa barinta, don haka ta tashi, ta saka hijjabi, ta buɗe ƙofa a hankali ta fito, ta je daidai windon ɗakin ta leƙa, ta kuwa hango shi zaune ya yi ɗaiɗai a kan katifa, yana ta danna waya, wani abu ya zo ya dunƙule mata ƙirji, kamar ta buga masa ƙofar, sai kuma ta ga me ma za ta ce masa? Ta daɗe tana kallonsa ba tare da ya sani ba, sannan ta juya ta koma ɗaki, ta kwanta, sai ta ji ɗakin ma yau ya mata girma, gadon ya yi mata faɗi, duk da dama yawancin daren da bacci suke raya shi, amma duk ranar da ba ya nan tana jin babu daɗi.

08028966015
[11/20, 3:36 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*

BY
SADIYA ABDULRAZAƘ

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee

PAGE 5

Washegari da safe Hasana ta gama haÉ—a abun karyawa, tana shirya yaran, Nura ya shigo yana cewa"Ki je ki gyara mini É—akina".

Ta yi kamar ba ta ji shi ba, ya sake cewa"Hasana magana fa nake yi".

Ta ce"Ni fa wannan raba É—akin ba lallai ya zama maslaha ga rayuwar aurenmu ba, saboda haka ya kamata a sake sabon tsari".

Ya tsaya yana kallon ta da mugun mamaki, ita kuwa da ba kallon shi take yi ba, ballantana ta lura da yanayinsa, ta cigaba da faɗin"A gaskiya sai dai ni ma na koma can ɗin, idan saboda Aiman ne, ni zan dinga yin shimfiɗata a ƙasan katifar mu kwanta".

Takaici ya ma hana shi tsayawa jayayya da ita, dogon tsaki kawai ya ja, ya ce"Allah Ya raba mu da jahilci".

Ta ce"Ni ce jahilar!?"

"Duk yadda kika É—auka haka nake nufi!" Ya faÉ—a yana jan kwanon abincinsa.

Ta shige ɗaki ta yi zaune a bakin gado, ta rasa ta hanyar da za ta bi ta daƙile wannan sabuwar badaƙalar da yake son ƙullawa, sam ba ta yarda da shi ba, ta san bayan uzurin da ya kawo mata, dole yana da wata manufa ta raba ɗakin nan da ya yi.

Haka suka gama karyawa suka fita tare da yaran, ya kulle É—akinsa yana mamakin sabon hali na raini da take son tsiro da shi a zaman nasu. Da azhar da ya É—akko su daga makaranta, yana shigowa fuska a murtuke, ya É—auki tsintsiya ya share É—akin, sannan ya haÉ—a ruwan mopping, har ya fara zuciya ta ciyo shi, shaiÉ—an ya yi zuga, ya fito a fusace, tana cirewa yaran unifom ya ce"Ke Hasana wai me kike nufi ne? ÆŠan iska kika mayar da ni ko yaya?"

Ta ce"Kamar ya?"

Ya ce"Ta ya za a ce ga ki a gida ni zan share É—akina? Mene ne amfaninki!?"

Ta ce"Ka fi kowa sanin amfanina".

Ya ce"Ki je ki gyara mini ɗaki Malama, ku mata sam ba ku da tunani wallahi, ba dole ma mutum ya ƙara aure ba? Hmm Allah dai ya hore, zan huce takaici tabbas".

Hasana ta yi murmushin takaici ta ce"Ai wallahi ni na fi so ma ka ƙara auren, ta nan za ka san haƙurin da nake yi da kai".

Ya ce"Ki kwantar da hankalinki, ai in sha Allah aski ya zo gaban goshi, wallahi da wannan siyayyar da na yi, kuÉ—in aure zan kai, to kawai na fi so lissafin komai ya tafi daidai shiyasa na jinkirta, amma kar ki damu indai aure ne dole zan yi shi".

Ta ce"Allah Ya nuna mana".

Ya yi ƙwafa, ta fice ta shiga ɗakin, ta ga wayarsa a kan katifa, ta raya ƙila mantawa ya yi, ta yi saurin ɗauka, sai dai da pasaword kuma ba ta san mene ne ba, ta yi ƙwafa ta ajiye ta, ta gama gyara ɗakin ta fito.

Ta same shi a falo ta ce"Yanzu haka za mu dinga ganinka kai kana yin kallonka mu ko oho?"

Ya ce"Tun da haka kika zaɓa ba!Na gaji da kai gyaran kayan kallo wallahi".

Amir ya ce"Don Allah Daddy a gyara mana".

Salim ya ce"To ai sai mu dinga yi a É—akin Daddyn".

Bai ce komai ba, ta kawo musu abincin rana suka fara ci, Nura ya yi kamar cokali uku ya taɓe baki ya ce"Abinci ma ba za a nutsu a yi shi ba, Allah Ya kyauta".
Chapter 6 · 0% Book details