← Book details Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 27

Sashe 9

Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Don haka cikin lokaci kankani komai ya kammala bayan dad yasanarwa da yan'uwansa komai, abin mamaki amma be sanarwa mon ba ko meyasa?.. haka nan jirginsu konace jirginmu yadaga zuwa
American domin nima dole naje dauko maku rahoto😉.

*_American_*
***""*****
Duk wani bincike daya kamata ayiwa kwakwalwar *Blue* din anyi mata amma babu abinda suka gano, sai allurai suke masa tare da bashi magungun wanda suke tunani Koda akwai wani matsala a brian din to maganin zasu iya bayyana wa saidai kuma babu abinda suka gano har tsawon sati uku, da kwana hudu don hakan ne yasa suka salleme shi yayinda suka kwasa zuwa Germany wani.

"A germany dinma dai bata canja zaniba results din kenan guda, kimani kusan sati uku ana bincike amma shuru gashi ciwon na *Blue* sai kara gaba yake abin gwanin tausayi, hauka tuburan baya be iyayin komai sai anyi masa tamkar yaro dan yaye,

Duk yarame yayi duhu hakan yasa dad sake shiga cikin tashin hankali fiye da tunani me karatu, hakama *Bulama* duk suma sun rame sunyi duhu tsabar tashi hankali, daga germany suka kwasa zuwa Spain acan dinma haka ne duk da na'urorin sai sunyi kamar zasu nuna wani abin sai kuma asamu akasin haka,

Nan ma dai sun kwashi tsawon sati uku da yan kwanaki ana binciken brian dinsa amma basuga komai ba, har papa da dad Lagos wato yayan dad suka kai masu ziyar inda papa yadaure yasake yin magana cewa ciwon nan fana *Blue* kamar shafar aljanu don haka bana asibiti bane, aikam dad yarufe ido yace shifa bayason yana danganta yaron sa da wasu aljanu don haka papa yayi shuru, tunda harda dad Lagos yagoyi bayan dad kwana uku sukayi suka dawo gida najeriya saboda duk kansu sunada shari'a me mahimmanci.

Yayinda suka bari ana sake binciken brian din *Blue* saida still basuga komai ba wanda hakan yaba likitocin mamaki don haka suka sallame su, mom ma ta ziyarce su tayi kuka sosai sakamakon yanda taga lilon d'anta yakoma, tace ma dad su dawo gida ayina gargajiya itama yatubure akan shibai san wannan zancen ba,

don haka suka rabu baran-baran haka tadawo gida najeriya zuciyar ta cike da kunci, saidai aranta tayi alkawarin yiwa d'anta addu'ar samun lafiya.

"Atakaice dai saida dad suka kwashi kusan wata biyu da wasu yan sittika suna ziyartar asibitoci kasa-kasa, kusan kasa biyar sukaje amma results din kenan daya don haka dad yace da *Bulama* sukoma gida yaje yafara aikin sa karsu taru aguri daya,

Kacan cewar dad da papa sun gina masu kamfani idan sun dawo zasu fara aiki to sai kuma ga laluran data samu *Blue* din, so haka akayi bayan sun dawo *Bulama* yafara gudanar da aiki akamfani su,

yayinda dad shima yacigaba da aikin sa bayan yasamar wa *Blue* masu kula dashi har mutun uku zaya dinga biyansu, tunda yakoma tamkar karamin yaro dan yaye irin masu shegen shagwab'a da saurin kuka baya iyayiwa kansa komai sai anyi masa harda abinci abaki ake bashi, wanka kad'a yakeyi dakan sa koshi facaka kawai yake da sabulu daruwa yafito,

"Wanda arana sai yayi wanka fiye da biyar domin har yanzu yana nan da mugun son tsafta bayason kazanta ko kad'an dotti yataba kayansa yadinga ihu kenan sai ancire masa ansa wasu, shiyasa kullun masu kula dashi cikin gyarasa suke Wanda inba kasan shi kagan shi saika rantse me hankali ne,

Allah sarki *Blue* gentleman duk yakoma wani iri gwanin tausayi😥.

*_Bayan wata uku_*
****"""*****
Sannun ahankali komai yake tafiya yanda Allah yatsara akuma lokscin da yaso,

Kamar su *Beenazeer* masuna nan suna rayuwa ayanda Allah yaso wato ba wuya ba dad'i, zance zuwa makaranta boko kam babu shi tunda basuda kudin biya don haka suka hakua saidai islamiya kam suna zuwa sosai,

Amma zance zuwa gurin kawu muda kuwa babushi domin duk yanda Ammun tayi yin kurin zuwan don karbo hakkinta, abbu yahana don haka ta hakura amman badan ranta yasoba saidai kawai don biyyyawa mijinta.

Misalin karfe 7:00am na ranan wata laraba wacce malam bahaushe kema kirari da laraba tabawa ranan samu, duk wanda yai samu acikin ta sai yakara, haka duk wanda yairashi aciki ta sai yakara to hakan ne takasance dasu *Beenazeer.*

Kamar koda yaushe bayan sun gama karatun su sund'an taya ammu aiki sai suka karya kumallo sannan suka shirya zuwa gurin aiki, har sun sallami iyayan su zasu tafi, sai Ammu takira *Beena* d'akin ta cikin sanyi murya tace idan kundawo baku iskeni ba natafi abuja....

Dasauri tad'ago kai ta kalli amman yayinda taji gabanta yayi mummunan fad'uwa, cikin tashin hankali tace Ammu yanzu abujan zaki koma gurin "kawu Muda?...kai ta gyad'a mata tare da cewa dole nakoma *Beenazeer* domin bazan iya cigaba da jure ganin mijina uban y'ay'ana cikin kun wannan halin ba,

Kuma gaskiya nagaji daganin ku zaune ba zuwa makaranta,

Cikin rawar murya *Beena* tace don Allah Ammu kiyi hakuri ki kyale "kawu muda tunda yaki baki, indai danmu ne mun hakura da karatun bokon tunda badashi zamu tafi lahira ba,

cikin rawar murya itama tace to naji idan harku kun hakura da karatun ku to shi Abbun ku haka zaya dauwama cikin ciwo?....kai ta gyad'a alamar a ah yayinda hawayen dasuka cika mata ido yazubo yasharrrrr!

tace to kingani don haka dole naje, cikin kuka tace Ammu kiyi hakuri karkije Allah fa yasan halinda muke ciki inshallah zaya yaye mana, cikin sanyi murya tace haka ne rokon danake kenan kullun saidai kisani nima dole zatasani zuwa amma nayi maki alkawari daga wannan zuwan idan har be baniba zan barsa da Allah, kedai kawai kiyimun addu'a keda yan'uwanki kinji ko?...

Cikin sanyi murya tace to ammu saikin dawo Allah yasa adace tace amin, to tashi kutafi don Allah ki kula da yan'uwanki sosai da Abbun ku kinji yar albarka murmushi tayi tare da cewa inshallah ammun mu sannan tafita.

Bayan ammun tashirya sai tashiga dakin abbu don ta sallame shi kasan cewar dama tariga taroke shi akan yabarta tasake zuwa gurin kawu muda, wanda dak'ar yabarta koshi saida tayi masa alkawari daga wannan zuwan idan har be bataba bazata sake zuwa, bayan ta sallame shi sannan tafito ta tafi,

Kamar koda yaushe Ammu ta'isa abuja lafiya saida agajiye ruwa kawai Safara'u ta bata, wannan lokacin ma bata iske kawu muda ba don haka saita tsaya jiranshi, can sai gashi yashigo yana ganinta yahad'e fuska kamar yaga mutuwar sa cikin sanyi murya tace inawuni yaya Mudassir?....

Cike da bacin rai yace bansani ba tace Allah yabaka hakuri, dama nasake zuwa karban hakkina ne... don Allah kayi hakuri kabani wlh muna cikin matsananci hali, zama yayi yad'ora kafa daya kan daya tare da fad'in kinyi kokari dakika sake dawowa so yau zakufita cikin halin dakuke, don haka bari nasa akawo maki hakkin naki yanxu,

Dasauri tad'aga kai ta kalle sa wani kila murmushi yasakar Mata sannan yasa hannun cikin aljinun rigarsa yaciro wayarsa, tare da danna lamba yakara akunne can yafara fad'in nomasi eh yauwa to Ina jiranku ok kuyi sauri ok sai kunzo sannan yakashe wayar,

Yana zubama ta wani mugun kallo sai karkad'a kafa yake hakan yasa Ammu jin fad'uwar gaba me tsanani,

Suna nan zaune saiga wasu karatan mutane su hudu sun shigo kallo daya zakai masu, ka kauda kai saboda tsoro domin fuskar su bakikirin babu annuri ko kad'an, yace yauwa nomasi kun iso ko?...

Cikin wata irin murya mara dad'in saurare yace ehhhh! Alh yace kunga wannan?...yafad'i tare da nuna masu Ammu dake zaune tana kallon abinda kawu muda yake kokarinyi, sukace ehhh alh munganta yaza'ai?...yace to tashiga gonata tayimun kane-kane don haka inason kub'atar mun da'ita adoron kasa banason asakejin labarin ko me kama da'ita cikin tashin hankali ta kalle shi tare da cewa.....

Muje zuwa

A

Alkalamin

✍🏼

*_LUFHAT_*

🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍

🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_

🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍

Page1️⃣7️⃣to1️⃣8️⃣

WRITTEN
By

🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍

OR

🎍 *MEENAT*🎍

Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*

SADAUKARWA GA

*_My lovely blood sisters 👩‍❤‍👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi out last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*

Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN ko AIRTEL na 200 a wannan 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi duk zaku iya tuntuban layin sai abaku account no ba nagode.

_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

*_FREE PAGE_*

✍🏼

_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_

"Yaya muda me kake nufi?....cikin tsawa yace abinda kikaji haka nake nufi, aina fad'a maki muddun kika sake tako kafarki gidan nan sai nayi maki abinda zakiyi dana sanin sanina arayuwar ki,

don haka nomasi kuyi aikin ku mana dasauri ya amsa da to Alh sannan ya kalli daya daga cikin su yace mugu eye oga, me kake jirane?...aikam kafin duk ammu tayi wani dogon motsi tuni yaciro wani farin kyalle acikin aljihun sa, yasama ta ahanci take tashake sai inda numfashin ta yadauke jikinta yasaki zata fadi,

"Sai yariketa cak yadauke ta yadora akafada daya yadauki jakar ta yayinda sauran biyun suka bisu abaya, cikin bacin rai kawu muda yatashi yanufi ciki yana fad'in aina fad'a maki yayinda Safara'u tabishi, kasan cewar duk abinda yafaru tana zaune agurin,

tace kai! yau kam mun yarda kwallon mangwaro mun huta da k'uda haba "mata sai shegen nacin tsiya kai! haba, ya amsa da to ai yau taga karshen naci.

"Su nomasi kam suna fita da ammu sai suka nufi wata k'atuwar mota me bakin gilas irin wanda naciki yana ganin nawaje yayinda shi kuma nawaje baya ganin naciki, Allah sarki baba megadi yana ganin su yai maza ya'isa gurinsu cike da tashin hankali yace don tsarkin mulkin Allah karku kashe wannan baiwar Allah,

harara nomasi yawatsa masa tare da cewa aiba irinmu ake roko ba domin munan daka ganmu bamayin afuwa ga duk wanda aka bamu kudi mukashe yasen kuwa, da sauri yace to don Allah kuyi mun wannan afuwar badan niba ciki bacin rai yace kai! tsohon nan kafara batamun rai fa,
Chapter 9 · 0% Book details