← Book details Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 27

Sashe 4

Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Direct wani babban daki suka shiga inda suke tattaunawa especially idan irin haka tafaru, sosai ake tattaunawa akan wannan lalura da tasamu Dan abokin aikinsu, nan Dad yake fadama su yanda abun yafaru, sai daya daga cikin likitoci yace niko sai nake gani kamar aljanu ne suka shafe s....

Zumbur Dad yamike cikin bacin rai yace haba Dr lbrahim wannan wace irin magana ce....? D'an nawa ne aljanu suka shafa?...to kasani ni 'Dana ba buwasu aljanu dasuka shafe "sa, asalima ni mabansan akwai wasu aljanu aduniya ba,

Sannan yafita rai bace daga dakin daya daga cikin likitoci yace humm! Dr I b kenan kaima kasan cewa "Dr L U be yarda da duk wani abu daya shafi gargajiya ba,

Amma tabbas ciwon "yaron sa yayi kama da shafar aljanu, Dr I b yace "uhumm kaima kafad'a yanzu dai mubari yatashi musake ganin yanayin sa tukun ko?..suka amsa da eh haka za'ayi sannan suka fito kowa yanufi office dinsa zuciyar sa cike da tunani halinda *Blue* yake ciki.

Dad ma koda yafita direct office dinsa yanufa da sauri *Barrister* tareda *Bulama* suka bishi, alokaci daya suka zazzauna cikin tashin hankali *Bulama* yace Dad meye samu my *Blue?...* *Barr* ma irin tmbyr yayiwa Dad,

Shuru Dad yayi kafin cikin bacin rai yace kai kaji "Dr I b wai aljanu suka shafi my "boy da sauri cikin harshen turanci *Bulama* yace Dad
meye kuma haka..?wai evil, tsaki yayi yace karya ne Dad me I don't believe this wooo! Dr yace me to my boy,

Shikam *Barr* shuru yayi yana nazari lamarin can sai yace Dr lamarin fa akwai kamshi gaskiya, da sauri Dad yace haba *Barr* kamar ya fa?...

yace naga yanda yake irin yadda aljan...dasauri Dr yace enough! enough!! enough!!! *Barr* banaso kana alakanta "boy da wayan nan shirmen da ni kwata-kwata banyi believe dasu ba, yace sorry bawai nace sudin bane amh! to yanzu dai ya jikin nasa"?...

Cikin had'e buska Dad yace him in bad condition, yanzu ma saida mukayi masa alluran barci me karfi wanda zata iya kaiwa gobe so idan har yafarka banga wani cigaba ba zanfitar dashi waje, *Barr* yace to Allah yabashi lfy,

Dad yamike tare da cewa Amin mujen ku gida inason nad'anyi wani bincike akan ciwon boy, *Barr* yace ok *Bulama* yace Dad ni zan tsaya gurin my *Blue* murmurshi yayi tare da dafa kafad'ar shi yace karka damu my boy akwai masu kulashi so muje ka huta kaji..?

Yace yes Dad, Sannan Dad yafara fita sai *Bulama* da sauri *Barr* yakama kunnan shi aikam yasaki yar kara kadan cikin shagwaba yace ahhh! papa akwai zafi fa,

Kasa-kasa yayi da murya yanda Dad bazaya jiba, yace l know meyasa bakaji ina rabaka da wannan akida kana ko karin yiko?..yace papa me nayi?..yace gidan ku, cewa fa kayi bakayi believe da aljanu ba, yace gaskiya papa ni ban yarda da wasu aljanu ba, yace to dan ubanka ko ka yarda kokar ka yarda akwai aljanu,

Yace to papa ni ban taba ganin su bafa taya zan yarda akwai su?..,da sauri yace Dan ubanka karkayi fatan ganinsu domin ganinsu arayuwa ba alkhairi ba ne,

Kai! tsaya ma tukun kanayin addu'a kuwa?..yace papa inayi shimafa my *"Blue* yanayi sosai har yafini yifa, yace kaidai shashasha ne to wlh gara kadage dayin azkhar domin suna tsare mutum daga bad evil kaji ko?..

Yace to dai-dai lokacin da suka karasa gurin mota escorts suka bude masu, suka shiga
kasan cewar tuni Dad yashiga don haka sukaja suka tafi......

*WAI WANENE BLUE*?........

_Muje zuwa yanzu za'afara_

So
More
Comments more
typing pls share
it

*_LUFHAT CE_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*® _PEN: WRITER'S ASSOCIATION_*

*~_Only the exquisite_~* *~__and whizkid_ _writers_~* ~*_are_* *_opportune to_* *_be__*~
*~_pen writers_~*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍

🎍 *_ZAUJUN MAJNUN_*🎍
( _Miji mahaukaci_)

🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍

Page7️⃣to8️⃣

WRITTEN
By
🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍

OR
🎍 *Meenat*🎍

Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*👇🏼
and now
*ZAUJUN MAJNUN*

SADAUKARWA GA

*_My lovely blood sisters👩‍❤️‍👩Hadiza (Aunty) and Nana firdausi our Last born do u know what...? sisters humm l really love love love yours irin babu adadin nan fa irin so muchhh love_*.💋💋💋

Littafin nan na kudi ne duk me bukata zaya iya turo katin mtn k airtel 200 a wannan 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi duk zaku iya tuntuban layin sai abaku acc no ba nagode.

*_FREE PAGE_*

✍🏼

*_Bismillahirrahamanirraheem!!!_*

*BILAL LAWAL USMAN* shine cikakken sunan sa sai abokan sa suna kiransa" *BLUE*, yakasan ce d'a ne ga Alh Lawal Usman kona ce Dr wato Dad asalin sa mutumin kano ne aiki ne yakawo shi zaria, gaba daya zuri'ar su Dad yan'boko ne na bugawa ajarida irin masu komai dabi'ar su ta bature ce

Kuma asalinsu fulani ne mahaifin Dad prof Lawal Bilai yarike mukamai sosai akasa najeriya yana daya daga cikin mutanen dasuke fad'a aji kasar nan, don haka zuri'ar su manyan mutane ne kuma masu kudi ne sosai Dad su uku ne kawai agurin iyayen su kuma duk kansu manyan ne acikin gwamnati, Kabeer shine babba wanda yake zaune a Lagos da iyalan sa matarsa daya da yaran sa biyu duk maza kuma shi din babban Lawyer ne,

Sai me bimasa macece me suna Sadeeya itama babbar Dr ce tana zaune abuja da mijinta da yaranta uku maza biyu mace daya, sai Dad Wanda shima babban Dr ne acikin asibitin shika da kuma Abuja Dad yaran sa biyu Aunty Aseeya itace babba wacce suke kira da Bebe kasan cewar sunan mahaifiyar Dad taci,

yanzu haka tana abuja tana auran wani babban Lawyer gwanati tanada yaranta hudu duk mata tana aiki ababban asibitin Abuja,

Sai *Bilal* amma ba maman su daya ba domin Aunty Bebe tanada shekara 8 aduniya ciwon kansar mahaifa yakashe mahaifiyar ta me suna Hafsatu, bayan shekara daya da rasuwar ta sai Dad ya auri mahaifiyar *Bilal* me suna Hauwa wacce take shuwa arab ce kyakkawa ce, suma asalin su yan boko ne sosai sannan sunada kudi.

Dad yana matukar son Hauwa domin tanayi masa biyayya sosai kusan duk, abinda yakeso tanaso saidai ra'ayin su yasha bambam kad'an,

Dad yanada akidar boko sosai komai nasa na boko ne itama tanada shi saidai shi yafita, amma kuma duk da haka basa fad'a akan bambamcin ra'ayi, saidan kaji fadan su akan *Bilal* domin tun da aka haife shi bata sake haihuwa ba hakan be damu Dad ba tunda dama shi bayada ra'ayin tara yara dayawa,

don haka yadauki so da kaunar duniya yad'ora akan *Bilal* sosai yake matukar son shi bayason abinda zaya bata masa rai ko kad'an, hakan yasa duk abinda *Bilal* yakeso shi yakeyi shiyasa yatashi shagwababb'e domin Dad yabashi gata sosai,

wanda hakan shike hadasu fad'a da Mom dinsa kuma idan tana koya masa akidar gargajiya tareda ta addini sam Dad bayaso amma duk da haka saida ta matsa ya sauke al'qur'an yakuma sannan wasu littafain addini,

Tun *Bilal* yana yaro suke rigima akan haka har ya girma ba adaina ba wanda shine dalilin rabuwar su,

Saidai tunda suka rabu ba wanda yayi aure cikin su har yanzu, tun *Bilal* yana secondary har yayi digren nafarko akan pharmacy wanda ra'ayin Dad ne, inda yaje chana yayi digren sa na biyu akan business administration Wanda ra'ayin sa ne wannan dawowar su kenan, wannan bakon al'amari yafaru dashi wanda bamusan komene ba amma dai bari mubisu asannun muji.

*BUHARI TAHIR BULAMA* shine cikkakken sunan shi sai abokan suna kiran shi *Bulama* kawai,
D'a ne ga papa wato *Barrister* Tahir Bulama asalin su mutanen barno ne tajahar meduguri aiki ne yakawo sa zaria,

Shidin kuma babban Lawyer ne me zaman kanshi shima d'an boko ne sosai saidai bashida ra'ayi irin na Dad,

Aminaine sosai shida Dad tun suna makaranta har yanzu, papa d'an sa kenan kwara daya wato *Buhari* wanda suka haifa tare da matar sa me suna Falmata.

*Blue* da *Bulama* suma aminan juna ne sosai tun suna yara tare sukai karatu tun daga primary har degree saidai shi *Bulama* law yayi a degree farko Wanda shima ya'ayin papa ne, domin duk suna San yaransu su gajesu sai degree na biyu shine yayi business administration shima ra'ayin sakenan,

Don haka kusan ra'ayinsu daya nason akidar boko shida *Blue* saidai halinsu yasha bambam, *Blue* ya kasance dan gaye miskili ne sosai ya'iya daukar wanka don haka yanada mutukar tsabta ga masifar kyankyami bakomai keyi masa ba,

yanada mugun high test yana kuma matukar kyamar zina shiyasa yake gudun yanmata don gudun afka mata, yayinda su kuma suke mugun son shi sosai suke bibiyar sa amma baya kulasu ko kad'an basa gaban sa.

Shima *Bulama* yana da tsabta sosai Dan gaye ne ya'iya daukar wanka kamar *Blue,* saidai shikam mutun ne me barkwanci sannan yana kula yanmata sosai shima yana kyamar zina saidai yana buga soyayyar shan minti da su, wannan kenan.

*Cigaba*
******
Su Dad kam basu tsaya ko'ina ba sai anguwar tudun jukum duk dacewa Dad shima yanada gida anguwar amma beyi nufin shigaba saidai kawai aka sauke su *Bulama* ,

Sannan yanufi gidan shi dake anguwar kwarbai suka nufa wani tsararran gida suka shiga bayan me gadi yabude masu get, bayan driver yabude masa kofa yafito direct yanufi cikin gidan yayinda escorts din sa sukabi shi abaya dauke da tarkacen *Blue*.

Masha'allah wani tsararran falo suka shiga wanda yasha blue and white din labule, gawasu manya manya set din kushin masu asalin kyau dasuka zagaye falon suma blue and white ne kai gaskiya falon ya tsaru wanda tsayawa fadin tsaruwasa bata lokacine,

Bayan escorts sun ajiye kayan sai suka fita yayinda Dad yashiga bedroom be dad'e ba yafiti sanye da jallabiya fara hannun sa dauke da wayoyi, wani table yanufa me dauke da manya manyan littafain,

zama yayi akan kujeran dake gaban talble din tare da ajiye wayoyi sannan yabude wani babban littafi,

Dai-dai lokacin da wani me aiki yashigo cikin girmamawa yaduk'a yace wlcm Sir....yace yauwa peter yace Sir u need something?..

yace no peter I want to be alone ok Sir" yajuya yafita dai-dai lokacin da daya daga cikin wayoyin sa tayi kara, ganin sunan daya bayyana akan wayar ne yasa yai murmurshi be dauka ba saidai yayi receive tare da bud'e kara,
Chapter 4 · 0% Book details