← Book details Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 27

Sashe 13

Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace magani ne nagargaji takarbo ma *Blue* idan zayaci abinci yazuba masa yaboye kar yabari dad yagani don idan yagani bazaya bari abashi ba, koma karya yazuba masa yabari sai idan dad yafita tukun, tace karyayi wasa gurin zuba masa domin maganine me kyau ance idan ana bashi zaya warke daga wannan rashin lafiyar da yake fama dashi,

aikam peter yanata jin dad'i domin shikam yamatsu *Blue* yawarke saboda yana tausayi halinda ubangidan shi yake ciki.

Saidai aranan da peter ya zubawa *Blue* magani yaci kamar zaya mutu domin kuwa ihu yadin gayi yana rike da kansa tare da wuyan sa, duk peter yatsora ta sai kuka yake yayinda masu kulada shi suke tafaman dariya abin gwanin tausayi da sauri yaje yakira aunty *Beebe* awaya kasan cewar tabashi lambarta,

tace duk abinda yafaru da *Blue* yakira yafada mata cikin kuka yafad'a mata abinda *Blue* yakeyi daya bashi maganin, sai tace kar yadamu zaya daina wai dama me maganin yace" zayayi haka, cikin sanyi murya yace mata to tare da kashe wayar

*Blue* kam saida yadauki tsawon lokaci yana faman shan wahala kafin yabar ihun, Allah sarki sannan barci yadauke sa gefe peter yakoma yana kallonsa gwanin tausayi.

*****
Yau laraba dad baije gurin aiki ba don haka yana gida shiyasa masu kula da *Blue*, suka maida hankali gurin aikinsu na kula dashi bayan yafito daga wankansa na banna da ruwa, sai suka fito masa da kayansa nasawa kamar yanda suka saba,

yauma haka sukayi bayan yasa shimi da gajeren wando, wanda da taimakon su yasa, sannan suka bashi wata shadda me kyau da tsada kalan sararin samaniya irin dinki da yawancin samari keyi gajeren riga me aljihun gefe da gefe, bayan yasa sai suka feshesa da turaruka sannan suka fito dashi falo gurin dad,

yana ganinsa yayi dariya cike da farin ciki yace dad murmushi dad yayi zuciyar sa cike da tausayi yaronsa cikin sanyi murya yace ya'akayi ne yarona?..bece komai ba saidai baki da yaketa washewa yana nuna masa kayanji kinsa, kamar yanda yara sukeyi idan ansaka masu sabon kaya dariya yayi yace kayi kyau yarona,

suna cikin haka
sai akakira dad asibiti anason ganinsa da gaggawa don haka yatashi yatafi bayan angama rikici da *Blue* wai sai yabishi, kasan cewar tunda masu kulada shi suka fara bashi wahala sai idan dad zaya tafi gurin aiki yaita ihu sai yabishi, wanda da ba haka yakeyi ba abin yana damun dada musamman yau don haka yatafi zuciyar sa cike da mamaki had'e tausayi Dan nasa,

Bayan fitar dad sai suka fito dashi gurin wasan dake cikin gidan gurin inda suke buga kwallo sukaje, sai suka fara bashi wahala kamar yanda sukeyi, yau ta hanyan buga masa kwallo idan wannan yabuga masa sai wannan yabuga masa haka sukai tayi saida suka tabbatar ya galabaita ga yinwa sannan suka kyalesa,

Sannan dayan yace maza yakamata fa mucika aikin mu yau mukara gaba ko yakuka ce ne?.. dayan yace gaskiya tunda gadama tasamu to yaza'ayi?...dayan wanda da'alama shine babban cikin su yace kutsaya ku gani, kwallon yadauka tare nufar inda *Blue* yace zaune akasan ciyawa duk yagaji matsawa baya yafarayi cike da tsoron sa, tsawa yadaka matsa hakan yasashi tsayawa dagosa yayi tare da mika masa kwallon da sauri *Blue* yakarba jikinsa sai kerma yake kamar zayayi,

sai mutumin yace yauwa zakaje "dad ko?..kai ya gyad'a da sauri alamar eh yace to zomuje bakin get suka nufa dukkansu *Blue* yana biye dasu rike da kwallon gwanin tausayi, cikin sa'a basu iske megadi ba da'alama yaza yagaya ban d'akine don haka sai suka kalli juna tare da d'aga babbar yatsansu, sannan suka bud'e kofar ahankali sai daya yakama hannun *Blue* yafita dashi wata hanya yanuna masa tare cewa kabi tanan zakaga dad kaji?... cike da murna yace dad?...eh dad ba zaka ganshi, tafiya yafarayi yana fad'in dad,

Yayinda suka maida kofar suka rufe suna dariya sannan suka koma cikin gidan bangare su suka nufa kasan cewar dama ban garensu daban, bayan sun zauna sai suka fara dariyar mugunta daya yace tab yau akwai kwamatsala wai mahaukaci ne zaya neman me hankali, haka sukai tafira abinsu hankalin su kwance shar bacci yadauke su.

Duk abin nan da'ake Peter yana ciki yana girki amma lokaci lokaci yana lekowa yakalle su duk wahala dasuke bashi yana kallo amma ba damar magana, bayan yagama girki yai wanka bayan yasa kaya sai yayi zaune tare da buga tagumi yana tunanin halinda ubangidan sa yake ciki tare da tmyr kasa meyasa wayan nan mutanen suke bashi wahala haka yaita tunani har bacci ya dauke sa.

Misalin karfe biyar da rabi dad yadawo gida inda ya'iske su Peter tsaye cirko-cirko shida me gadi da masu kula da *Blue,* yayinda Peter sai kuka yake kamar ransa zaya fita bayan anbud'e ma dad mota yafito sai peter yakara gurinsa da sauri yazube kasa yana girzan kuka, gaban dad ne yafad'i cike da fargaba yace peter meke faruwa ne?...cikin tsananin kuka yace yallabai bamuga karamin oga ba cike da tsoro dad yace....

Muje zuwa

✍🏼

*_LUFHAT CE_*

🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍

🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_

🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍

Page2️⃣2️⃣

WRITTEN
By

🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍

OR

🎍 *MEENAT*🎍

Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*

SADAUKARWA GA

*_My lovely blood sisters 👩‍❤‍👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi out last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*

Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN ko AIRTEL na 200 a wannan layin 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi duk zaku iya turowa ta account no kamar haka 0047769671 Abdullahi Amina nagode.

_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

✍🏼

_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_

*Bilal* din nawa ne ba'agani ba?... kai peter ya gyad'a saboda tsabar kukan dayaci karfinsa, yayinda megadi yace eh yallabai wlh mun nemesa kasa da sama cikin gidan nan ba bamu gansaba, cikin tashin hankali dad yace wannan ba gaskiya bane taya zakuce kun nemi yarona acikin gidan nan kun rasa?..

saikace allura...yakareshe fad'i tare da chakumar kwalar rigan daya daga cikin masu kula da *Blue* din, yace fadamun ina yarona yake?...cikin tsoro yace wlh yallabai bamu gansa ba saboda tunda mu kagama buga kwallo dashi sai muka shiga cikin to kuma sai barci yakwashe m....

yakasa karesawa sakamakon marin da dad yashara masa, cikin tsananin masifa me had'e da tashin hankali yace kai! Dan ubanka dama nakawo kune don kuyi barci eye?...nace nakawo kune don kuyi barci... yafad'i tare da sakin shi yakamo kwalar rigan daya shima marin yashara masa, don ubanku sai kun nemo mani d'ana konasa adaure ku haka yabisu yana mari,

cikin tsananin masifa da tashin hankali yayi kan megadi kai, kuma taya akai kabude kofa har yafita alhalin kasan bayada lafiya eye?.. wlh yallabai ban bude kofa ba saidai yau natashi inata fama da gudawa kila lokacin Dana kewaya ne yabud'e yafita, aiba lalai finka bane laifin wayan nan kattan banza ne kuma wlh duk inda yarona yake sai kun nemo mani shi.

Da sauri yaciro wayarsa ya kira ofishin yan sanda yafada ma babban su yaturo masa yaransa suzo sunemo masa yaronsa, ba tare da bata lokaci ba sai gasu cike da mota nan suka tambayi dad ya'akai ba'aganshi ba?...

yace shi bayanan sai wayan nan kattan banza sai megadi nan sukai ma megadin yan tmbyi tare masu kulada shi yan tambayoyi sannan suka karbi koton *Blue* din, yazu fita dad yace sutafi da masu kulada *Blue* su ajiyesu harsai anganshi tukun domin shi beyarda dasuba aikam haka akayi suka tafi dasu don gudanar da aikin su.

**"*****
Abangaren su *Beena* kam yau sun tashi cike da farin ciki kasan cewar abbu yatashi jikinsa da sauki sosai, don haka suka wuni cikin annashuwa duk da dai tawani bangare azuciyar su cike take da kewar ammun su da son sani tana raye ne ko amace?...

Misalin karfe 4:10pm bayan sun idar da sallar la'ar sai abbu yace su shirya suje makarantar islamiya tunda dai yau yaji sauki, haka akayi inda yace subar *Banu* yagaya mata karatun ta idan sungama sai ta tayasa fira sukace to tare da tafiya suka bar,

*Banu* tana fad'in abbuna yau dayawa zaka kalani karalatu na gaskiya murmushi yayi tare cewa to amma fa sai kinyi kema dayawa, tace to zanyi to oya Ina jinki sannan tafara karantawa yana sauraran ta.

****

Abangaren *Blue* kuwa tunda aka nuna masa hanya yaketa tafiya yana magana cikin harshan turanci yake fad'in dad inakake abokina inakake,

sai tafiya yake yana maganganu tare da kalle-kallen hanya da kuma mutane, wayanda suma sai kallon sa suke saidai ganin yanda yake tafiya yana surutu sai akafara tunanin bayada hankali ne, haka yai tafaman tafiya wacce tunda yake be tab'a yin irinta ba arayuwar sa don haka duk yagaji matuka ya galabaita iyaka, ga tsabar yinwa data addabi cikin sa kawai sai yafara kuka,

still yana cigaba da tafiya da kuma kiran sunan dad da abokina wato *Bulama* yake nufi, abindai gwanin tausayi sai kuma can sai kaji yakira aunty bebe da Peter wanda hakan yana nufin "sune mutanen daya sani yakuma saba dasu, ahaka dai yaketa tafiya can yasamu gindin wata bishiya me yawan ganye yazauna tare da jingina jikin bishiyar yana rungume da kwallon gwanin tausayi fuskar sa shab'e-shabe da hawaye, sannun ahankali barcin wahala yadauke sa,

Can kuma yafarka kamar wanda aka cikara da tsinin mashi yatashi ya cigaba da tafiya yana kuka, tare da surutun kiran sunayen mutane da yasani idan yashiga wannan layin yashiga wancan layin har misalin 6:10pm na yamma duk wanda yagansa sai ya tausaya masa, kwallon hannunsa kam tuni yajefar da'ita sbd tsabar wahala ahaka har yashiga anguwan fadaman sarki,

wani layi yabi inda wata me suyan awara take akofar wani gida me dakali biyu, mutane sai siya ake wasu nafadin ladiyo zubamu ta hamsi nikuma ta d'ari nikuma ta talatin hakadai mutane suke tasiya, wasu idan suka siya nan suke zama akan dakalin suci yayinda wasu kuma acikin leda ake zuba masu sutafi da abinsu,
Chapter 13 · 0% Book details