← Book details Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 27

Sashe 12

Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsanani tashin hankali tace subhallahi! Ina ne Nan nake?...ba amsa koda yake amsar kenan acikin daji take wanda tuni ta fahimci hakan, kuka tafashe dashi tare dafadin oh! ni fatima yanzu kiyayyar da yaya muda yakemun hartakai yasa asalwantar da rayuwata, saboda kawai na tambayi hakkina?...

tafiya tafarayi tana kuka sosai saboda tuno halinda iyalinta suke ciki ba tare da ta tsaya daukar jakarta da tarkacen kanta ba wanda ba lallaine tagansu ba saboda duhun gurin, cike da tsoro take tafiya wanda jefa kafafuta kawai take wanda ba takalmi yayinda bakinta yake dauke da duk wata addu'ar neman tsarin da tasani,

Tayi tafiyar da akalla yakai ta awad'aya da rabi kafin ta'isa bakin titi gabad'aya ta galabaita har ba ta'iya ganin gabanta sosai hakan yasa tahau kantiti batare da tasani ba, adai-dai lokacin da wata bakar mota dalleliya tashararo da gudu aikam take tadauke ammu saida tayi sama sannan tadawo kanta yabugi motar tafadi kasa take jini yafara zuba,

Dai-dai lokacin da direban yataka matsiyacin birki da sauri yafito yanufe ta yana fad'in subhallahi!, sannan wani dattijo yafito da sauri wanda akalla zayakai shekara sittin aduniya duk da duhun da garin yayi hakan behana agane farine shi ba,

sanye yakeda farar shadda dinkin manyan kaya ne wato riga da wanda da babbar rida harda nad'in farin rawani akasa fuskar sa manne da farin gilas, dasauri yakarasa gurinsu dai-dai lokacin da direban yadago kan ammu daketa malalar jini tamkar anyanka dabba,

yace subhallahi! mlm yakubu wa muka bige?...cike tsoro yace yallabai wlh wata matace bata ko motsi balle numfashi, innalillahi! yallabai Ina ganinfa ta mutu cike da tashin hankali yace....

_*Wannan page din shine free page na karshe don haka duk wanda yake son cigaban labarin kodaga farko zaya tuntubar wannan layin 08161850024 ko ya turo katin MTN 200 ko yai tresfa ta wannan acc no 0047769671 Abdullahi Amina gt bank ne nagode*_

Muje zuwa

*_Yanzu za'afara labarin ZAUJUN MAJNUN!_*
miji mahaukaci shin ya abin zaya kasance?.....

Tareda

✍🏼
*_LUFHAT CE_*

🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍

🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_

🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍

Page2️⃣1️⃣

WRITTEN
By

🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍

OR

🎍 *MEENAT*🎍

Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*

SADAUKARWA GA

*_My lovely blood sisters 👩‍❤‍👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi out last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*

Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN ko AIRTEL na 200 a wannan layin 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi duk zaku iya tuntuban layin sai abaku account no ba nagode.

_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

✍🏼

_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_

Innalillahi! kai! mlm yakubu kaifa haka kake taya kasan ta mutu?...to yallabai ko motsawa batayi ba gashi jini sai zuba yake, cikin tashin hankali yace to nidai yanzu dauko ta kasata amota mukaita asibiti su dubata,

to yallabai da sauri yad'auke ta yayinda dattijo yabud'e masa kofar baya yasata sannan yarufe, sukaje suka shiga mlm yakubu yaja suka tafi.

"Wani babban asibitin kudi suka kaita da sauri akazo da gadon d'aukar marasa lafiya aka dauketa d'akin taimakon gaggawa aka nufa da'ita,

sosai likitocin suka bawa ammu taimakon gaggawa sunyi nasaran tsayar da jinin saidai bata farfad'oba, amma numfashin ta yana tafiya yanda yadace sannan sun kafito.

Da sauri dattijon nan yatari babban
likitan yana tambayar sa likita ya me jikin?...cikin girmamawa yace ranka yadad'e dasauki amma muje ofis inason magana dakai yace to muje mana,

ayan sun zauna blikitan yace ranka yadad'e Allah yabamu ikon tsayar "mata da jinin don haka inshallah akoda yaushe taza iya farfad'owa...., saidai kanta yad'an bugu kad'an da sauri yace likita akwai matsala ko?..

"eh to yanzu dai bamuda tabbacin hakan harsai "ta farka munga yanayin ta tukun, ajiyar zuciya yayi tare da fad'in to likita nagode ita kuma Allah yabata" lafiya yace amin don Allah inason kasa akula mun da'ita" dakyau nizan tafi gida domin nasar da iyalina halinda ake ciki,

saboda basu saniba kasan cewar mun fito minna ne akan haryamu ta dawowa ne sai wannan baiwar allah ta gitta mana muka bigeta, yace Allah sarki kar kadamu yallabai inshallah za'a kula da "ita yanda yadace,

yauwa nagode sai ka lissafa kudin ka idan nadawo sai na rubuta maka cak to yallabai sai kadawo, sannan yatashi yafita direban sa mlm yakubu yatarbe sa yana tamayar sa yame jiki?...yace da sauki tare fad'a masa abinda likita yace ahaka har suka karasa mgurin mota yabud'e masa sannan shima yashiga yaja suka tafi,

"Anguwarsu dake maitama wani tabkeken gida suka nufa bayan yayi hon me gadi yabud'e masa kofa yashiga masha'allah, gaskiya gidan yahadu matuka kota'ina hasken kwan lantarki ne gefe daya kuma wasu yan' sanda ne tsayayaye kimanin su shida,

bayan direba yabude masa kofa yafito sai yan sandan nan suka gaidashi ta hanyar saramasa hannu yad'aga masu sannan yanufi cikin gida, wani hadadd'en falo yashiga wanda yaji kayan more rayuwar duniya.

Sallamar sace tasa matar shi da yaransa biyu tashi da sauri sukaje suka rungume shi cike da shagwab'a macen tace Abba muna takiranka baka dauka ba duk mundamu, kanta yashafa tare da fad'i yi hakuri *Basman* Abba wani iftila'i yasame mu ahanyar dawowa da sauri matar da namijin sukace me yafaru?...

Nan yafad'a masu duk abinda yafaru wanda shiya hanashi daukan kiransu, cike da tausayi "ammu sukace allah yabata" lafiya yace amin tare da shiga daki yayinda matarsa tabi bayan sa,
to bari muji wanene wannan dattijon.

*Alh salisu sunusi* shine cikakken sunan sa amma sai ana kiransa da alkali *sasu* wato salisu sunusi yakasance babban alkalin, asalinsa bafullacen kano ne aiki yakawo shi abuja inda yake babban alkalin gwamnati,

yanada mata daya me suna haj Lauratu fara me farar aniya kyakkawace tanada kirki sosai yaran biyu kyawawa wayanda sukayo halin uwarsu, namiji da mace namijin shekaran sa ashirin da biyar sunan sa Sunusi amma suna kiransa *Bunayya* yana karatu a university nan abuja yana shekara ta biyu, sai mace ita kuma shekarta goma shabakwai akwai tazara tsakanin ta da *Bunayya* sosai,

Sunan ta fatima sai suna kiranta *Basma* kasan cewar sunan mahaifiyar haj maryam taci wanda suke Kira da ummi *Basma* yanzu take rubuta jarabawa fita sakandiri, gidan Alkali Salis akwai kyakkyawar mu'amala tsakaninsa da iyalinsa sosai wayanda yaimasu tarbiyya mai ban sha'awa,

"Alkali salis mutun ne dayake aiki da gaskiya da rikon amana sam baya daya daga cikin irin alkalan dake karban cin hanci su danne hakkin wani suba wani, shari'a yake ta zallar gaskiya duk wanda bayada gaskiya yakanyi masa hukunci dai-dai da laifinsa kamar yanda addini yace,

hakan wanda yakeda gaskiya yana bashi gaskiyar sa kamar yanda addini yace wannan kenan.

*_Washegari_*
**"*""**""*
Tun misalin karfe 8:00am alkali sahabi wato Abba da iyalan sa suka isa asibitin, bayan sun gaisa likita sannan yakaisu d'akin da aka kwantar da ammu nus biyu ne tsare da'ita har lokacin bata farka ba,

*Basma* naganin halin da ammu take ciki sai tafara kuka kasan cewar ta me tausayi da saurin kuka tamkar *Beena*, basu dad'e dashiga d'akin ba sai ammu ta farka daya bayan daya take kallon su likita yace da nus sudaga ta su jingina ta da filo, ahankali ya matsa kusa da'ita yace sannun yajiki?...kallonsa tayi tare da fad'i sannun yajiki,

"Da sauri yace yanzu inake maki ciwo?...itama tace yanzu inake maki ciwo, kai likita ya girgiza tare fad'in innalillahi!., cike da tashin hankali Abba yace likita ya akayi ne naji tana maimaita abinda kafad'a.....

yace yallabai akwai matsala yace subhanallahi! meya farù likita?..yace yallabai tasamu matsalar mantuwa gabad'aya kwakwalwar ta tamanta komai na rayuwarta abaya, yace innalillahi! likita yanzu menene abinyi?...babu wani abinyi har sai tunanin ta nada yadawo,

yanzu likita kamar zuwa wani lokaci kake ganin tunanin ta zaya dawo?... gaskiya banida tabbacin lokacin da zaya dawo saidai ko idan taga wani abinda yashafin rayuwar ta tabaya, cike da tashin hankali Abba yace innalillihiwa'inna'ilaihirraju'un!, nan dai sukai ta tattaunawa akan laluran data samu ammu.

***"*'*"""***
*Bayan sati biyu* aka sallami ammu daga asibiti taji sauki saidai bata'iya komai ba sai ankoya mata don haka daki guda abba yasa aka ware mata tare da samo me kula da'ita, umma tace komene sunanta?..abbu yace Allah masani *Bunayya* yace to yanzu da wani suna zamu kira ta?...

Da saurin *Basma* tace asamata sunana sai kuringa kiranta umman *Basma* nikuma nakirata da umma na shikenan kaga mamana sunza ma biyu ko?...dariya sukayi dukansu Abba yace haka kikeso *Basman* Abba?.., da ummi da tace eh da kuma yah *Bunayya* yace au aina manta to angama ko sahibata?. yakarasa fad'i tare da kallon Ummi,

murmush ummi tayi tare dafadin tabbas ai uwata duk abinda takeso shi za'ayi, sannan yaka Mata akai sanarwa gidan rediyo akuma dauki hoton ta akai gidan tibi ko Allah yasa agane yan'uwanta ko?...

yace nima tunanin danayi kenan, hakan kuwa akayi duk wani gidan tibi da rediyo ankai saidai kuma shuru babu Wanda yazo yace yasanta,

hakan yadamu Abba da iyalensa sosai saidai babu yanda zasuyi da abinda Allah yatsara don haka suka cigaba da yin addu'a Allah yabata lafiya tare da bayyana inda yan'uwan tasuke, sosai suke kulada ammu wace takoma umman *Basma* tun bata gane sunan har tagane wannan kenan.

****"****
Aban garen *Blue* kam sai ahankali babu sauki saidai agurin allah gashi yanzu masu kula dashi sunsa algusu acikin aikin su, idan kacire Peter gaba d'aya sun daina kulawa dashi yanda sukeyi ada asalima yanzu wahala suke bashi matuka dazaran sunga dad yafita gurin aiki,

Sai su ringa azabtar dashi kasan cewar baya dawowa sai dare don haka kafin sudawo shida *Bulama* duk ya galabaita yafita hayyacin sa, shiyasa yakejin mugun tsoron su wanda hakan yasashi kara hauka cewa duk yarame saboda rashin ishashshan abinci dabasa bashi yanzu,

tunda idan peter yagama abinci zaya bashi sai su hana sai idan sunga dad yakusan dawowa ko *Bulama* sannan su bashi, shikan shi Peter mugun tsoron su yakeji aunty kam *Bebe* duk sati take zuwa ganisa ko satin nanma tazo dazata koma takira peter kicin taciro wani kullin abu tabashi,
Chapter 12 · 0% Book details