← Book details Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 27

Sashe 11

Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sabon me gadi ne yazo yabud'e fuska had'e yace lafiya ke wacece?...saida tagaida shi sannan tace sunana *Beenazeer* nazo daga zariya ne ni d'iyar kanwar me "gidan na ce ba tare da yace komai ba yabud'e mata tashiga,

"Da sallama tashiga falon kirjinta yana bugawa cikin sa'a ta'iske kawu muda zaune shida Safara'u suna ganinta suka kalli juna cike da munafurci tace a ah lale maraba yau *Beenazeer* ce agidan namu?...,

murmushin karfin hali tayi tare da zaunawa kirjita yana cigaba da matsananci bugawa tace eh nice aunty Ina wuni lafiya lau, kawu Ina wuni yace lafiya lau ya mutanan gida?.. tace lafiya lau, yauwa ya'akayi ne?...tace umh! kawu dama munji Ammu shuru ne shine abbu yace" nabiyo ta ko lafiya yace kina nufin Fatima?.tace eh yayinda kirjita yake masifar bukawa yace tun yausheta wuto nan din?..

cikin fargaba tace tun shekaran jiya, kai! aiko batazo ba Safara'u ko kinganta"?...a ah banganta ba ido *Beena* tazaro cike da matsananci tsoro tace.....

Muje zuwa

✍🏼

Alkalamin

✍🏼

*_LUFHAT_*
🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍

🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_

🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍

Page1️⃣9️⃣to2️⃣0️⃣

WRITTEN
By

🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍

OR

🎍 *MEENAT*🎍

Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*

SADAUKARWA GA

*_My lovely blood sisters 👩‍❤‍👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi out last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*

Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN ko AIRTEL na 200 a wannan 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi duk zaku iya tuntuban layin sai abaku account no ba nagode.

_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

*_FREE PAGE_*

✍🏼

_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_

Kawu batazo bafa kuka ce?...eh mana yo karya zamuyi maki?... hannu ta yarfar tare dafa kirji ta furta innalillahi! wlh kawu ammun mu tun shekaran jiya tabaro gida kuma nan tace zatazo, don Allah kawu idan wasa kake kabari wlh kirjina zaya iya tar watsewa dajin wannan wasan,

Cikin tsawa yace ke! nataba wasa dake ne koni abokin wasanki ne dazanyi maki wasa eye?...ance maki batazo ba batazo ba ko idan tazo zamu boye tane eye?...,kai ta girgiza yayinda jikinta yake mugun rawa bugun kirjin ta yatsanan ta wanda bayada misali, cikin rawar murya tace yanzu kawu da gaske kake ammun mu bata zo nan ba?...

Wani lafiyayyen mari yasakar mata akan kyakkyawar fuskar ta ido tarinte, ciki masifa yace ke! dan uwarki da ubanki karya zanyi maki nace karya zan maki eye?...,ke! Dan ubanki tashi kibar mun gida "uwarki kikazo nema ko?..to batazo ba, don haka tashi ko nayi mugun saba maki kinji ko?...

Ahankali ta bud'e idon wani irin duhu tagani amma haka ta mikewa jikinta sai karma yake, tadauki jakarta taku daya ana biyu ta zube kasa sume.

Zumbur Safara'u tamike tare dafadin mun shiga uku Alh kar yarinyar nan tamutu mana agidafa...tsaki yayi mtw! tare da fad'in ko ta mutu babu abinda za'ayi, cike da tsoro tace a ah alh garadai karta mutu mana anan ta kareshe fadi tare da fara girgiza *Beena* tana cewa ke! *Beenazeer!* ke! *Beenazeer!!*

shuru bata motsa ba hakan yasa tace Alh mun shiga uku tamutu fa, tsaki yasake tare da fad'in suma tayi ki dauko ruwa kizuba mata ta tashi tabar mana gida kinaji ko?...to, Da sauri taje ta dauko ruwa afirj in ta yayyafa mata ta dauki lokaci kafin ta farfad'o bakinta dauke da salati,

"Ahankali tamike zaune tare da dafa kai tayi shuru kawu yace ke! da sauri tad'aga kai ta kalle sa yace tashi ki koma inda kikafito domin dai "uwarki batazo nan ba kinji ko?.. kuka ta fashe dashi tare dafadin don Allah kawu kanemo mana "Ammun mu wlh bata gida, cikin tsawa yace ke! Dan ubanki nizan nemo maki ita nasan inda takene?...

cikin rawar murya tace a..a...h! Ina nufin kasa anemo mana ita don Allah, yace bazan saba tunda batazo nan ba idan kuma tazo to bansan gidan ubanda ta tafi ba balle nasa anemo ta, don haka tashi kitafi ga kudin mota kije kifad'ama wannan nakasheshsa "ubanki batazo ba,

yakareshe fad'i tare da ciro kudi acikin aljihun wandon sa yak'irga dubu biyar yamika mata bata karba ba sai kuka take tamkar zata shid'e, cikin tsawa yace dalla gafara karba kitashi kitafi nagaji dajin wannan shegen kukan naki da sauri takarb'a,

domin dai batada zab'in da yawuce takarb'a din tunda dai batada kudin motar komawa gida, ahankali tamike tare da daukar Jakarta jikinta sai rawa yake zuciyar ta tana cigaba da matsananci bugawa aranta kuma tunani take ina ammun su tashiga?....

******
"Ahaka ta tari taxi yakaita tasha tashiga mota sai kuka take gwanin tausayi acikin mota kuwa sai tambayar ta ake lafiya?...

bata iyabada amsa ba domin itadin ba ma'abociya magana bace, sai kuka kawai take wata mata tace ke kodai yammata anata tambayar ki meyasa meki amma kin kyale mutane, cikin tsanani kuka tafad'a masu abinda yasata kuka aikam take suka saki salati matar tace aikam dole kiyi kuka,

domin dakyar idan batafad'a hannun yan garkuwa da mutane ba, wata tace ai idanma yan garkuwa da mutane ne dasauki, suce akai masu kudi su bada ita idan tafad'a hannun yan yankan kai kam saidai wata ba'ita bakam domin kuwa ta halaka eh fa wlh,

aikam take kukan *Beena* yakaru tsoro yasake kamata wani d'an dattijo yace haba don Allah ku kam wani irin abune haka eye?...maimakon kutayata addu'ar Allah yabayyar mata da mahaifiyar ta sai kudinga irin wanyan nan maganganu dazasu sake firgitata saboda Allah fa?...

shuru sukai sai yakalli *Beena* wacce keta kuka yace kiyi shuru y'ata ki daina kuka haka inshallah zakiga mahaifiyar ki, kedai kiyi addu'a Allah yakareta dafad'awa mugun hannun kinji ko?...kai ta gyad'a alamar to, ahaka dai aka cigaba da tafiya sai yamma lis suka iso zariya don anama shirin Kiran sallar magriba, koda aka sauketa saita tari adai-daita zuwa anguwarsu dake fadaman sarki.

******
Zata shiga gida kenan saiga *Bass* da *Bash* sunfito zasu tafi masallaci, ganinta ita kad'ai yasa *Bass* jin fad'uwar gaba don haka da sauri yace Aunty *Beena* Ina "Ammun mu?...
kuka tasaki tare da shigewa cikin gida da sauri,

cikin tsanani tashin hankali yabi bayanta, yana kira d'akin Abbu tashiga dai-dai lokacin da yake kokarin tada kabbaran sallah azaune kamar koda yaushe, shigarta yasa yatsaya yayinda yaji wani irin fad'uwar gaba me tsanani, zubewa tayi agabansa tana cigaba da matsananci kuka,

Dai-dai lokacin da su *Bass* suka shigo cikin tashin hankali suma suka zube gaban Abbun, sai ga *Bana* itada *Banu* sunfito daki dasauri suma suka zube gaban Abbun sai ya kasance sun sashi tsakiya, sai kallon *Beena* suke itakam sai kuka take wanda har yasa *Bana* da *Banu* suma fara kukan, cikin tashin hankali *Bass* yace Aunty *Beena* wai me yafaru ne?...

Nace Ina "Ammun mu kinyi shuru sai kuka kike gashi har su *Banu* sun fara, shuru bata bashi amsa ba, sai kuka take hakan yasa shima *Bass* jin kukan yana shirin kufce masa da sauri yadukar dakai domin shidin ba ma'abocin saurin kuka bane ko don shi namiji ne?...oho.

Shikam Abbu kura mata ido yayi yayinda yakejin kukan ta har cikin ransa domin itadin y'ace mafi soyuwa agurinsa, ido ya lumshe acikin ransa yafurta yah Allah kasaba wani mummunan abune yasamu "Fatima ta ba?...

ahankali yabud'e ido yasake zubasu akan *Beena* wacce tsabar kuka har yasa tafara jinkanta yana sarawa, cike da fargaba yace *Beenazeer* abbu dasauri tad'ago kai fuska sharkaf da hawaye ta kalle shi yace bari kukan nan haka ki fad'amun Ina fatima ta take?..

Cikin kuka tace abbu bansan inda "ammu take ba...da sauri yace ban fahimce kiba?... kawu yace" bataje gurin su ba...cike da tashin hankali yace innalillahi! bataje gurin suba to Ina take?...bansani abbu bansañ kowa'ina acikin abuja balle na nemeta, kuma nace kawu yasa anemo ta yace" bazaya saba, abbu ina ammun mu take?..

wani irin gumi ne yatsatsufo masa agoshi hannu yasa yashare tare da fad'in allahumma'ajirni'fimusibatiwa'akifliminhairinminar! yah ubangiji kabamu ikon cin wannan jarabawa amin, abbu Ina zamuga ammu Ina ammun mu tashiga?..

Cike da tashin hankali yace Allah shine masani inda take kuma shizaya bayyana mana ita, yanzu kutashi kuje kuyi sallah muroki Allah yabayyar mana da ita, sukace to tare da mikewa jikinsu asanyaye *Beena* kam har wani jiri ke d'ibarta gwanin tausayi gabad'a tafisu shiga tashin hankali rashin ammu.

****"****
Abu kamar wasa wai karamar magana tazama babba ba domin kuwa ba ammu ba labarin ta wanda hakan yasake tayar masu *Beena* hankali, sunyi kuka har sun gajin duk sun rame musamman *Beena* da abbu tun suna saran ganin ta har sungaji sun zubawa hukuncin Allah Ido addu'a kam sosai suke yinta.

*_Bayan wata uku_*
*******
Haka rayuwa tamika yau kimanin wata ku kenan da batan ammu abubuwa da dama sunfaru aciki harda rashin lafiyar abbu, wanda tun ranan dayaji labarin rashin inda "ammun take yakefama darashin lafiyar da sai ankwantar sai antayar,

Sosai yakejin jiki garashin lafiyar kafa gata jiki da zuciya wanda idan akacire rashin lafiyar kafa sáuran duk suna da nasaba da rashin "ammu, wanda ba karamin nakasu yasake yiwa rayuwar su *Beena* ba domin yanzu *Beena* da *Bass* sun daina zuwa gurin koyan d'inki da saka har da islamiya ma, saboda sune manya sukeda karfin kula da abbu
Saidai *Bana* da *Bash* ne kawai suke zuwa.

haka dai rayuwa ta mika to sannun ahankali abbu yake samun sauki da taimakon Allah dana baban Abdul, wanda yake kuladasu dai-dai karfinsa domin hatta da abinci yanzu gada gidansa ake basu tunda basu dakomai wata rana kuma sai yayomasu chefane su girka dakansu, don haka suke matukar girmama shi da iyalinsa.

******

"Abangare ammu kuwa saida ta kwana tawuni sannan tafarfad'o misalin karfe 8:00pm na dare bakinta dauke da salati, da kyar ta'iya bud'e idanun ta sakamakon nauyi dasukai mata duhu yamamaye ma ganinta hakan ne yasata sake murza idon ta,

donta tabbatar saidai kuma me?...duhun tasake ganin hakan yasa tajin fad'uwar gaba me tsanani, dasauri tamike zaune tafara kallon inda take shuru tayi na d'an wani lokacin tana tunani tuno abinda yafaru ne yasata mikewa zumbur,
Chapter 11 · 0% Book details