← Book details Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 27

Sashe 8

Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zumbur *Blue* yamike tare da ihun murnan ganin dad yadawo, kai dad ya girgiza tare cewa zauna boy zama yayi shima ya zauna yayinda su *Bulama* sukaci gabada cin abincin suna kuma tattaunawa akan laluran *Blue* din.

Suna cikin haka sai ga Aunty Bebe tundaga harabar gidan take kwala kiran sunan *Blue* da my *Bil* boy kamar yanda take kiransa, dasauri tashiga main falo tana fad'i where is my *Bil* boy?...

doguwa ce da alama tabiyo dad da tsawo, fara ce sosai saidai kamar takara dana zamani domin har wani jaja fatarta keyi balaifi tanada kyau, saidai batakai *Blue* ba domin shikam kyansa guri biyu yadauko da gurin Mom da gurin Dad itakam da alama mamanta tabiyo sab'ani *Blue,*

Shikam daka gansa kaga dad sak! harda tsawon da cikar zati, my *Bil* boy kana Ina tafad'a dai-dai lokacin data karasa shiga karamin falon
Abin mamaki *Blue* naganin ta yamike dasauri har yana zubar da dankalin gabansa, yanufi gurinta da ihun murnan ganin ta harda tsalle,

_Nikam nace toufa dama ance ko mahaukaci yasan nasa"_

Mutuwar tsaye Aunty Bebe tayi tana kallon sa yayinda *Blue* yarike hannun ta yana dariya, cikin rawar murya tace d...a...d haka my *Bil* boy yakoma?...kai ya gyad'a mata sai tasaki kuka tare da rungume shi tana fad'in Oh! my *Bil* boy me yasme ka haka?...

shima sai yasaki kuka harda buga kafa hakan yasa dad yace it's ok bebe, ahankali tayi shuru tana shafa kanshi shima shurun yayi cikin rawar murya tace Dad mutafi asibitin nan dai suka dunguma zuwa asibiti.

***""""***
Su *Beena* kam koda suka fita sun iske Ammu tagama had'a karin kumallo Wanda dumamen tuwon jiya ne sai kunu data dama masu,

Sannan tazuba masu akwano daya komar kodaya yaushe wato *Beena* itada *Bana* da *Banu*, sai *Bass* shi da *Bash* suma akwano daya domin tace masu cin abin tare da Dan uwa yana sa zumuci sosai, bayan tabasu nasu sai tadauki na Abbu taje kaimasa.

Bayan sun gama cin abinci sai *Bana* ta tattara kwanoni zata wanke ita kuma *Banu* takoma gurin Abbu don yasake fad'a mata karatu,

yayinda *Beena* tashiga wanka koda tafito har *Bana* tagama wanke-wanke, don haka sai itama tashiga wanka ko kafin tafito har *Beena* tashirya tana zaman jiranta, don haka da sauri itama tashirya suka fito,

Dai-dai lokacin da *Bass* da *Bash* suma suka fito ashirye, murmushi sukayiwa juna sannan suka shiga dakin Abbu don su sallame su inda suka iske *Banu* tagama karatun hartayi bacci kusada Abbu,

yayinda Ammu take matsama sa kafa nan sukace masu zasu tafi suka amsa masu dato tare dayi masu fatan nasara sannan suka fita, Ammu batabar dakin Abbu ba saida ta tabbatar yayi bacci sannan tamike tadauki *Banu* suka fito dakinta takaita takwantar,

Sannan itama takishin gid'a kad'an sai tafara tunani ahalin dasuke ciki wanda bata tab'a tunanin zasu shigesa ba arayuwa,

gashi yaya "Muda yaki yabata hakkinta haka kawai saboda tsabar mugunta ta yan'uba, ahankali tafurzar da iska me zafi tabakin ta, ranta ad'an bace tafurta inshallah Allah sai yad'orani akanka kabani hakkina,

Ahaka dai tayi ta tunani har sarkin barayin duniya ya dauke ta wato bacci.

*_Asibiti_*
******
Duk wani binciken da yadace ayiwa kwakwalwar *Blue* anyi amma wani abin mamaki babu abinda akagani, wanda zayanu na alamar yayi losing memory sane ko kuma yasamu tabin hankali ne,

Hakan ne yaba likitoci mamaki had'e da tsoro musamman Dad cike da tashin hankali, yace pls Dr Bamalli kusake bincikawa beyi musuba suka sake sakan *Blue* din acikin wani injindin bin ciken kwakwalwar mutu,

injindin sabo ne aka kawo masu kuma saida aka tabbatar da ingancin sa tukun aka kawo masu, amma abin mamaki results din da sauran injinan din suka bayar shima haka ya bayar, cike da tashin hankali dad yace no Dr Bamalli wannan ba gaskiya ba da alama injinan nan sun samu matsala,

idan kuma bahaka ba to kun kafara wasa da aikin ku amma tabbas kwakwalwar yarona tasamu matsala idan bahaka ba babu yanda za'ayi yadinga yin behavior like small kid, don haka kusace bincikawa don nasan maganin da zan d'ora sa akai, cike da bacin rai Dr Bamalli yace.....

Muje zuwa

_Alkalamin_

*_LUFHAT_*
🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍

🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_

🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍

Page1️⃣5️⃣to1️⃣6️⃣

WRITTEN
By

🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍

OR

🎍 *MEENAT*🎍

Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*

SADAUKARWA GA

*_My lovely blood sisters 👩‍❤‍👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi out last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*

Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN ko AIRTEL na 200 a wannan 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi duk zaku iya tuntuban layin sai abaku account no ba nagode.

_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

*_FREE PAGE_*

✍🏼

_*Bismilahirrahamaniraheem!*_

Haba dr L.U kamar ya injina sun samu matasala? kamar yanda kaji nafad'a, humm idan ko haka ne to kaine mutun nafarko dazaya tabbatar da hakan domin kuwa kana daya dagacin wayan da ke aiki da injina,

"au haka zakace?...eh to idan bance maka haka ba to me zance?....tunda agabanka ake komai ko ba haka ba, aibabu abinda bakasani akan aikin ba shine kake wani cewa mun fara wasa akan aikin mu wanda hakan yana nufin harda kai ke nan?..

"tunda aikin kenan guda dasauri yace a ah kudai domin nibana wasa da aikina jiya kwana nayi ina bincike, Wanda ya tabbatar mun dacewa tabbas boy yasamu matsala a akwakwalwar sa amma yanzu sai kununa mun wai kwakwalwar sa lafiya lau take wanna ai manakisa ne kawai za'ayi mun,

"Da sauri dr Bamalli yace a ah bamu muka nuna maka ba na'urori dai suka nuna maka, kuma kagani sannan mu babu wata manakisar da zamu samaka tunda duk abinda yasame ka yasame mu, d'anka ai d'an mu ne koba haka ba?....suka amsa da tabbas haka ne,

to kagani tabbas kwakwalwar *Bilal* kam tasamu matsala saidai bana tunani yashafi asibiti saidai k....da sauri dad ya katseshi dafad'in to idan baishafi asibiti ba me yashafa?... har dr Bamalli zayayi magana da sauri dr lb ya girgiza masa kai alamar ya kyale,

don haka dad yaci gabada cewa nidai nagane kawai bakusan taimaka mani ne dad'in abin banan bane kad'ai asibiti, so zan dauki yarona nakai shi inda kwararru likitoci suke su dubamun shi, dr Bamalli yace ashe kai dinma ba kwararre bane?....

Cike da jin haushi yace kune dai ba kwararru ba tunda kunkasa gano abinda yake damunsa, amma nikam tabbas na kware akan aikina tunda har nagano brain dinsa yasamu matsala, ok tunda kakware aida saika tsaya ka kagano abinda yake damun sa basai ka kawosa gurin wayan da ba kwararru ba,

Ai tun kafin kace na gano, kuma nafad'a maka idai so ne kawai nasake tabbatarwa ko bakaji abinda nafad'a ba ne?...eh naji to aiyanzu ka tabbatar don haka sai kaje kadora shi akan magungunan dasuka dace, yanzu kuwa yafad'i tare da kokarin daga *Blue* dayake zaune yanata faman wasa da filon gadon asibitin, dad kam sai fad'a yake kamar zaya ari baki sudai sauran likitocin sai kallon sa suke har suka fita daga d'akin.

Cike da mamaki dr bamalli yace ah! wai shi "Dr L.U wani irin murd'add'en mutun ne haka?...dr Ib yace humm! aikai dai bari halinsa sai shi yanada mugun ra'ayin rikau, saikace akansa akafara boko mtsw! wani dr yayi tare da cewa indai boko ne aimunga mangwafa kai! kaji mutun fa agaban safa akai komai, koba aikomai agabansa ba aishima dr ne yasan komai akan aikin,

humm! aikana wasa da "dr L.U yadauki boko da matukar mahimmanci arayuwar sa data iyalinsa, wani dr yace to aisai yamatsa kuma kunsan Allah tunda kukaga duk na'uronin nan basu nuna komai dangane da abinda yashafi brain dinsa ba, to tabbas ciwon sa bana asibiti ba ne,

Dr l.b yace inafa na asibiti nifa tun jiya nafahimci haka nigani nake kamar aljannu ne suka shafesa, idan kuma basu bane zato zunubi kilan anyi masa asiri ne tabbas cikin biyu za'asamu daya, idan ba haka ba babu yanda za'ayi yaro natsatse kamilalle cikin lokaci daya yakoma kamar *MAJNUN*,

wlh kaidai ni tausayi ma yake bani, ga Ubansa yaki yadda ya fahimci haka ah! to basai yaje yayi abinda zayayi ba gaskiya kam, Allah dai yasawake yakuma bashi lafiya duk suka amsa da ameen sannan suka fara firfitowa daga d'aki.

Dad kam yana fitowa su *Bulama* suka taresa da sauri Aunty Bebe takama hannun *Blue* tana cewa my *Bil* boy ya jikin?...be amsa mata ba saidai kwab'e fuska dayayi zayai kuka tare kokarin d'ora kansa akafad'ar ta,

yayinda papa da *Bulama* suka had'a baki gurin fad'ar me akace yasame sa?...cikin bacin rai yafad'a masu duk yanda sukai inda ya karashe dacewa kuji fa, maganar banza wai babu abinda yasamu kwakwalwar sa,

Da sauri *Bulama* yace in possible dad babu yanda za'ayi a ce wai babu abinda yashafi brain dinsa yake wannan behavior din kamar wani karamin yaro, aunty bebe tace gaskiya karyane basudai bincike sa dakyau bane....dad yace inafa suka bincika, kunga ku kyalesu" kawai mutafi gida muyi shirin tafiya,

Ke bebe muje ki koma gida ki kulada "mijinki da "yaranki kinji?...cikin sanyi murya tace pls dad mutafi tare, yace no baza aihaka ba Barr naji kace kanada important shari'a gobe ko?... kai papa yagyad'a wanda tunda yayi shuru bace komai ba azuciyar sa yanason yayi magana, akan lamarin nanfa bana asibiti ba ne amma yakasa koba haka bama yasan koya fad'a masa bazaya yarda ba,

Don haka bayada abinfad'a sai abinda dad yace, yayinda dad yaci gaba daya cewa yauwa kai kuma son muje kasama mana tickets guda uku na American Dani dakai da boy tunda already munada visa ko?...,yes dad yauwa idan munje anyi dace to shike nan idan kuma ba ayiba sai muwuce germany ko?..ok dad,

Sannan ya kalli papa tare da cewa koya kagani Barr?...,da sauri yace eh hakan yayi sannan suka shiga mota suka tafi gida,
Abu ga masu gidan rana wato raina inji malam ba haushe yace idan sunyi yawa sai inuwa,
Chapter 8 · 0% Book details