← Book details Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 27

Sashe 2

Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gani nayi 'yar karamar su tasaki hannun dayar takama duka hannuwan babbar tareda daga Kai ta kalle ta sannan ta kwab'e fuska, cike da yarinta tace Aunty *BEENA* yanju shi kenan ankole mu daga school baza mu qala zuwa ta ba kenan?..

shuru tayi tana kallon ta tsawon wani lokacin ba tareda ta bata amsa ba, hakan ne yasa ta turo baki tareda sakin hannuta taje gurin babban namijin ta kama hannun sa duk biyu tace yah *BAS* shikena daga yau mun daina zuwa school?..shima shuru yayi bai bata amsa ba sai kallon ta da yake,

don haka taje gurin dayar macen tace Aunty *BANA* ki fada mu baza mukara zuwa school ba?..itama shuru tayi tana kallon ta, cikin sanyi jiki ta kalli dayan namijin tareda turo baki tace yah *BASH* aikai ma nasan bazakai mun magana ba tunda su Aunty *Beena* basuyi mun ba, ai baruwana daku kuma aina gane saboda bamu biya kudi bane shine aka koremu to ai kafar "Abbun mu tana ciwo baya iya tafiya balle yasamo kudi yabamu, sannan shikuma "kawu Muda yaki ba "Ammun mu kudinta balle tabiya mana shine suka koremu,

ta nagama fadin haka sai ta fashe da kuka me ban tausayi, aikam dasauri su kayi kanta yayinda *Beena* ta tsugunna tayi tsawon dai-dai ita tareda rungume ta ahankali take girgiza mata Kai alamar tayi shuru, shuru tayi sannan tace Aunty *Beena* sbd bamu kai kudi bane akakore muko?..kai ta gyada mata alama "eh, fuska tasake kwab'ewa tace to ai "Abbu bayada lafiya to aunty *Beena* wane zaya bamu kudi mukai school?.. cikin tsananin tausayi Kansu tace....

_Muje zuwa yanzu za'afara_

So
More
Comments more
typing and pls share it
🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍

🎍 *_ZAUJEE-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_

🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍

Page3️⃣to4️⃣

WRITTEN
By

🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍

OR

🎍 *MEENAT*🎍

Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJEE-MAJNUN_*

SADAUKARWA GA

_My lovely blood sisters 👩‍❤‍👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi our last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin ba adadin fa irin so muchhhh lovo_💋💋💋.

*Littafin nan na kudi ne duk me bukata zaya iya turo katin mtn ko airtel na 200 a wannan layin 08161850024 idan kuma tresfa zakuyi duk zaku iya tuntuban layin sai abaku acc no nagode.*

_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

_FREE PAGE_

✍🏼

_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_

Sai kuma tayi shuru na kusan tsawon mintin biyu da'alama magana tanayi mata wuya, sannan ta sauke ajiyar zuciya ahankali cikin zazzakar muryar ta me dad'i tace "ALLAH shine zaya bamu don haka karki damu domin yasan halin da muje ciki kinji ko? kai ta gyada alamar to,

tace yauwa my *Banu* to d'anyi mun dariya mana nagani, aikam dasauri tawashe d'an karamin bakinta me dauke da fararan hakora, tace yauwa kokefa to mutafi gida kinga "Abbu da "Ammu suna can sukad'ai ko?..tace to tareda juyawa ta kalli *Bass* cike da shagwab'a ta mika masa hannu tareda fadin yah *Bass* dauke ni kaji?,

cikin wasa yace nakiya ke da kikace baruwanki damu, so muma baruwan mudake ko my *Bash* yace eh d'iyar kawu "muda kawai yakarasa fadi tareda yimata gwalo, kafa tafara bugawa cikin shagwaba tace Aunty *Beena* kingan shi ko?..

murmushi tayi wanda kusan tare sukayi da yan'uwan sannan, tace kai yah *Bass* itakam d'iyar "Abbu da "Ammu ce bata kawu muda ba ko?.. tace eh kawu Muda yace wai haka? kai ta gyad'a almar eh yace to shikenan yar *Banu* *Banu* ta yakareshe fadi tareda daukanta yadora akafad'arta,

sannan suka cigaba da tafiya abinsu gwanin sha'awa sunayi suna fira me cike da kaunar juna ahaka har suka isa gidan su dake anguwan fadaman sarki alokaci tuni *Banuja* tayi barci, kasan cewar tsakani anguwar su da school din akwai nisa.

Wani gida suka shiga me bakin get wanda kallo daya zakaiwa harabar gidan ka fahimci masu shi suna cikin wani hali, domin kuwa filawoyin dake shuke a harabar gidan duk sun bushe saboda rashin ishenshen abincin su da basa samu,

Duk kansu bakinsu dauke da sallama suka shiga wani babban falo wanda yake dauke da wasu tsofaffun kushin din da duk yadinsu ya yayyage,

Daku na hudu ke acikin falon don haka direct suka nufi daya daga ciki still bakin su dauke da sallama wanda basu shigaba har saida aka amsa masu tareda basu izinin shiga tukun, sannan suka shiga.

Inda suka iske wata kyakkawan mace fara amma ba irin faudin ba tareda wani kyakkawan mutun wankan tarwad'a wanda kallo daya zakai masa kafahimci yanajin jiki matuka kasan cewar yanda yake fitar da numfashi, kwance yake akan wata lotsatsiyar katifa yayinda rabin jikinshi yake rufe da bargo, saidai banda kafafun sa domin kuwa suna saman ciyarta matar tana manmatsa mashi ahankali,

Lokaci daya su ka dago kai tareda tsura masu ido, kallo daya zakai masu ka gane su din ne iyayen su saboda tsananin kama, cike da ladabi suka zube agaban su tareda cewa Abbu sunnu da jiki Ammu sunnu da gida,

da kai Abbu ya amsa sabani Ammu da tace yauwa sannun ku, amma lafiya naga kun dawo ba lokacin tashi ba? cikin sanyi murya *Bana* tace Ammu ankoro mune saboda bamu biya kudin makaranta ba, kuma yan school din mu suna tayi mana dariya wai mu duk time sai ankore mu saboda Abbumu baya biya mana kudin school,

kuma yau har saida *Banu* tayi kuka, ko *Bash* yace eh saida Aunty *Beena* ta lallashe ta tayi shuru sannan yah *Bass* yagoya ta har tayi bacci.

Da sauri Ammu ta kalli Abbu wanda shi din ma ita yake kallo cikin b'acin rai tace kagani ko kagani ko? haka kakeso mu cigaba da rayuwa cikin kunci? yanzu haka abincin da zamuci yana neman yafi karfin mu ga ciwon ka kullun karuwa yake,

Sannan shima karatun so ake ya tsaya masu, gashi kullun nayi magana sai kace nayi hakuri na kyale shi" to kasani wannan karon bazan kyaleshi ba dole naje yaya Muda yabani hakkina kome zaya faru yau saidai yafaru Amma bazan yarda ba, eheee! sannan ta sauke kafafun shi daga saman cinyarta ahankali tamike.

Ahankali yabi bayanta da kallo har ta fice daga dakin sannan yamaida hankali kan yaranshi, wayan da tsabar ladabi tunda "Ammun su tafara magana kansu ke duke har tafita.

Cikin sanyi murya me dauke da murmushi Abbu yace to yan albarka kuje kucire uniform din bakomai Allah zaya rufamana aciri inshallah kunji ko?, ahankali suka ce to tareda mikewa har da *Bass* dake goye da *Banu* suka fita amma banda *Beena*, shuru yaratsa dakin na wani dan lokaci sannan Abbu yace ya akayi ne ta Abbu maman Ammu?...

ahankali tadago kai idanun ta cike da kwalla cikin sanyi murya tace Abbu maganar "Ammu yana nufin zataje abuja gurin kawu Muda kenan ko?... kai ya gyad'a mata alamar "eh ido ta lumshe aikam take hawayen suka zibo cikin muryar kuka tace Abbu meyasa zakabar ta taje?

yace saboda tana bukatar zuwa kin kuma sannan bazan hanata ba tunda alkawari na daukarma "lnna ta, duk abinda Ammun ku tabukata nayi mata muddun be sabawa shari'aba to nayi mata, tace amma Abbu kasan kotaje "kawu Muda bazaya bata hakkin taba tunda tunba yau take zuwa ba amma be bata ba,

yace haka ne tace to kagani hakan yana nufin baya daninyar bata don inda yanada niyya da yabata, tunda yau shekara hudu kenan tana tafama wahala akan abu daya, yace haka ne amma kinsa halin Ammu ku dakafiya tace to nidai tunda be da niyyar bata hakkin ta don Allah Abbu kace ta kyale "shi aigida biyu ne wanda idan ba duniya akwai lahira,

cikin sanyin jiki yace haka ne zan mata magana ki kwantar da hankalin ki kinfan banson kinasa damuwa aranki ko? kaita gyada sannan ta tashi tafita jiki bakwari.

Dakin Ammu tashiga bakinta dauke da sallama, tsaye ta isketa hanun rikeda wayar nokia gefe kuma jakace ga kaya zube akasa, tsugunawa tayi tareda daukan kayan tana ninkewa tanasawa cikin jakar bayan tagama tarufe jakar,

sannan ta dukar da kai cikin sanyi murya tace don Allah Ammu idan kinje "kawu Muda be baki hakkin ki ba kiyi hakuri ki kyale shi yabaki inda bayada shi kinji? ba tareda ta kalle taba tace to sannan tadauki hijab dinta me ruwankasa dake rataye jiki kofa tasa alamar shirin tafiyar take,

Sannan tace to nizan tafi sannan tadauki pos dake ajiye saman gado tareda budewa taciro kudi naira dari biyar ta mikawa *Beena,* tareda cewa gashi kirike ko zaku siya wani abun ai akwai sauran garin dawa da na rogo ko?

kai ta gyada alamar eh tace to don Allah kikula da kanki tareda kannanki wanda nasan kinayi amma kikara, sannan banda yawon banza duk danasan ke bama'a bociyar sa bace, amman ki kula kinji ko?

Cikin sanyi murya tace to, Sannan tace yauwa yauwa yau ma zakije gidan "maman "Abdul din
ne gurin sakar?..tace eh to Allah yabada sa'a amaida hankali, sannan adawo dawuri atafi islamiya, sannan ki matsawa babana yaje gurin aikin sutafi tareda *Bash* idan *''Banu* na ta tashi ki kulamun da'ita sosai kinji?

tace to Allah tsare hanya tace to Amin Allah yayi maku albarka tashi ki kiramun babana yarakani bakin titi na hau mota zuwa tasha, ahankali ta mike tareda cewa to tafita batare da dadewa ba sai gasu tareda *Bass* har yacire uniform yana riga da wando nawani fari yadi, ba tareda yace komai ba yadauki jakar suka fita saida tashiga dakin Abbu sannan tafito yatafi raka ta,

Yayinda *Beena* tashiga dakin su cikin sanyi jiki tacire uniform tarage daga ita sai vest iya guiwa batada kiba saidai tanada shave me kyau, gata da dukiyar fulani dasuka cika mata kirji tanada matukar yalwar kashin kai wanda yakeda yawa da tsamo gashi baki sidik tanada ido me matukar kyau infact dai *Beena* kyakkyawace sosai,

ahankali ta zauna akan dan karamin gadon su me dauke da wata lotsatsiyar katifa ahankali ta lumshe ido, tafara tunanin rayuwar su ta baya.

*_ASALIN SU_*
Chapter 2 · 0% Book details