← Book details Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 27

Sashe 25

Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Don Allah ina nake nan Kuma kusu wanene bansan kuba don Allah karku cutar Dani kamar wayan can "mutanan,

"koda yake naga bakuyi kama da masu cutar da mutam ba don haka ku taimake ni kuboye ni kar "mutanan nan su sake kamani akaro na biyu, su halakani wlh inada ahali "y'ay'ana biyar "mijina bayada lafiya yaya "muda ne daga naje karban hakkina shine yace" sukasheni,

takarashe faɗi tare da fashewa da kuka yayinda *Basmatinta* ta tayata cike da tausayin ta, Abba yai gyaran murya cikin sanyin murya me cike da tausayin ta yace" ki kwantar da hankalin kamar yanda kikace mudin bamasu cutar da mutum bane,

maganar hakkin ki kuma kina inda za'akarbar maki abinki da izinin Allah yanzu dai alhamdullahi! mun godewa Allah dakika dawo cikin hankalin ki, da sauri taɗago kai ta kalleshi cike da mamaki yace" bigeki mukai da mota.....

"Daga Nan dai faɗa mataba koshi wanene sannan yabata labarin komai tundaga lokacin da suka bigetan har losing memory ta datayi har irin Shaƙuwar dasukai da *Basma* har zuwa yanzu wanda yau kimanin wata hudu zuwa biyar kenan,

"daga ƙarashe yace don haka karki damu komai zayayi dai-dai inshallah! abinda nakeso dake yanzu zuwa anjima zaki faɗamun komai game da'ake saboda nasan ta'ina zanfara tunkaran shi "yayan naki kinji ko?...kaita gyaɗa sannan taɗaga Kai ta kalli *Basma* wacce taji kaunarta tashiga ranta lokaci ɗaya.

"Cikin sanyin murya tace *Basmatin* umma meyasa kike kuka umuh?.. hannun Tamika mata tare da faɗin zonaji meyasa kike kuka haka umuh?...da sauri taje tafaɗa jikinta cikin kuka tace umma na Ina sonki karki tafi kibarni kinji?...

cike da sonta tace nima Ina sonki Kuma bazan taba barinki ba, *Bunayya* yace tab! amma dai yarinyar nan bakida hankali badole takoma gurin ahalinta ba koba kiji tace" ya'yanta biyar ba sannan babansu bashi da lafiya ba?..

"Cike da shagwaɓa tace to aitare zamu tafi ko ummana?...tace indai zakije zantafi dake ban zantafi da yah *Bunayya* ba, dariya tayi tare fadin yeeee baza'a dakai ba dariya akayi gaba daya yayinda *Bunayya* yace saina rankwashi kannan naki kuma nima sai naje Nan dai aka kama fira.

*******
"Kwanan ammu biyu acikin asibitin aka sallame ta domin taji sauki bayan sun koma gida sai abba yafara Shirin tunkaran kawu muda inda yasa aka aika mashi da sammaci, sannan abba yace da ammu dole tayi hakuri tacigaba dazama har agama shari'ar idan yaso sai takoma gida

"Lokacin da kawu muda yaga sammaci yasha mamaki matuka koda yabuɗe takardan yaga sunan wacce ke karanshi saida ya kusa zaucewa saboda tsabar tashin hankali,

cike da bacin rai yakira yaran dayasa sukasheta yafara zuba masu masifa Wai meyasa basu kashetaba sukace masa aisun kasheta?... sukace wlh tamutu cike da takaici yakashe waya yana zuba bala'i.

"Ammu da *Basma* kam cikin kwana biyu sun sake Shaƙuwa inda duk tabata labarin yaranta inda tace mata ai *Beenazar* ɗinta zasuyi sa'annin juna cike da murna tace aizata zama ƙawata ko?...tace inshallah haka dai suke zama suna fira abinsu gwanin sha'awa,

Yayinda akashiga kotu akafara gudanar da shari'a gadan gadan kasan cewar Abba yanada kwararre lauya shiyasa abin yazo da sauki, domin ko bugun farko kawu ya amsa laifinshi,

daganan shari'ar tafara tafiya dai-dai yanda akeso wanda kana kallon yanda shari'ar ketafiya zaka fahimci ammu batada hakkinshi, koɗaya asalima shikeda hakkinta Dan haka nema batare da ya wahalar da kanshin ba yakuma wahalar da lauyoyi,

"Da alkali yafaɗi gaskiyar iya adadin ƙadarorin da maƙudan kuɗaɗan da mahaifinsu yakari, Abba yace aika juya dukiyar ko?...yace eh ankuma samu riba ko?..

"yasake cewa eh to dole har dasu yakafadi aikam kawu muda yafaɗi, sannan abba yabashi sati biyu yahaɗo Kan komai ya amsa da to cike da wani irin tsoron Abba Daya kamashi, aidole abba kam akwai kwarjini da haiba ga kwarewa akan aikin shi.

*Bayan sati daya*
*********
"Aban garen *Beena* da *Blue* kuwa suna cikin rayuwar su me daɗi kwatsam saiga tauraruwa me wutsiya ganinki ba alkairi ba tazo masu, wato aunty *Bebe*,

"Ranan wata lahadi da misalin 11:30am nasafe ta'iso
dukkansu suna part din dad kasan cewar gurin firan su kenan koda yaushe, musamman ranan asabar da lahadin harda *Bulama* ake haɗuwa ayita fira,

*Blue* nan maƙale da *Beena* wacce yakeji kamar yagoyata, dad yana kan kushin zaune yayinda sukuma ke zazzaune akan kafe ita da *Blue* da *Bulama* kan *Blue* yana kan cinyarta, wai sai tayi masa kitse hakan ne yasa take tafaman jagula lallausan gashin da yake cukurkuɗe, sallamar tane nayan boko yakatse su wato excuse me...., *Bulama* he ya amsa da yes come in.

Zumbur *Blue* yamike cike da murna yana faɗin my aunty *Bebe* oyoyo rungumesa tayi tare da faɗin oyoyo my *Bil* boy, cike da murna dad yace *Bebe* kece ba waya dariya tayi tare fadin dad surprise nace zanyi maku *Bulama* yace gaskiya aunty kinyi mana zuwan bazata,

"Zama tayi kusa da dad tana gaida shi *Bulama* ya gaida ita sannan *Beena* tamatso kusa da'ita tana gaida ita, saidai me tana shaƙar kamshin turaren aunty *Bebe* taji zuciyar ta kamar zata fito take taji wani irin amai yazomata da gudu tamike tanufi toilet,

"Amai tadinga kwarawa ba ƙauƙautawa zumbur aunty *Bebe* ta yamike tabita kirjinta yana bugawa cike da tashin hankali, take faɗin meyasa meki?..

Bata iya bata amsaba domin Aman yaci karfinta, cike da fargaba tace sannun Kai ta gyaɗa mata *Blue* ma wanda tuni ya'isa toilet din sai sannun yake zubamata, tare da riƙeta yana sorry cikin ki yana ciwo ne shima Kai ta gyaɗa mashi bayan tagama aman sai ta wanke Baki da fuska sannan *Blue* yarikota suka tafito,

"Aunty *Bebe* na biye dasu zuciyar cike da tunanin meke faruwa dad da *Bulama* dake tsaye suka fasa xuba mata sannu, cike da damuwa dad ya kalleta yace sannun *Beenazar* dama bakida lafiya ne?...

kanta duke tace dad lafiya ta kalau kawai dai naji zuciya ta natashi sai Kuma naji kaita yana sarawa, yace ayya sorry yanzu yakikeji?...tace umh Ina ɗanjin kaina yana cigaba da sarawa Kuma har yanzu inajin tashin zuciyar,

cike da tsoro aunty *Bebe* tace umh! kamar yadaya kikace kinaji?...zatayi magana dad yace ko zaki dubata ne da sauri tace eh dad ok *Beenazar* kuje kiyi mata bayani tace to dad,

"Ɗaki suka shige cikin hikima aunty *Bebe* tayi tama *Beena* tambayoyi inda take tagano tana ɗauke da ciki, wani irin gume ne yakaryo mata cike da tashin hankali tafita inda *Beena* me biye da'ita kirjinta yana bugawa.

Cike da tashi hankali tace dad akwai matsala cikin tsoro yace meya faru?...tace dad ciki take dashi fa ajiyar zuciya yay tare da murmushi yace Kai *Bebe* to mine bin matsala aciki?...

dad cikin fa watan shi hudu da sati biyu Kuma kaga yau dayin bukin wata uku kenan cif kaga kenan bacikin *Bil* boy bane, yace tabbas haka domin jiya mukayi lissafi da *Bulama* ko?...

kai *Bulama* ya gyaɗa cike da fargaba cike da bacin rai yakalli *Beena* wacce gabadaya tagama rikicewa dajin wannan batu yace.....

Muje zuwa

*LUFHAT CE*

🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍

🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_

🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍

Page3️⃣3️⃣

WRITTEN
By

🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍

OR

🎍 *MEENAT*🎍

Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*

SADAUKARWA GA

*_My lovely blood sisters 👩‍❤‍👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi our last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*

Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN na 200 a wannan layin 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi zaku iya ta account no kamar haka 0047769671 Abdullahi Amina gt bank nagode.

_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~

https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/

✍🏼

_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_

"Au kina nufin kina dauke da cikin shege kika yarda aka ɗaurawa ɗana ke?...kai ta girgiza cike da tsananin tsoro...., Da sauri aunty *Bebe* tace karya kike dashi aka ɗaura aini tun farko banso auran nan ba Amma dad yakafe saida akayi aiga irinta nan....,

"cikin bacin rai yace ainayi tsammanin yarinyar kirkice kamilalliya ashe bansani ba shashashace marar kamun kai to kisani ni bazan ɗauki wannan shegen cikin wa ɗana ba....,

saboda haka yanzun nan basai anjima ba kitattara naki danake kibar mun gida kije can kinemi uban shegen cikin ki kinji ko?.... aunty *Bebe* tace dadai yafi kam wato da za'a likawa *Bil* boy tunda anga bashida hankali ko?...

"To Allah yakamaki saiki tashi kitafi can da tsiyarki kinji....,wani irin kuka *Beena* tasaki me cike da tsananin firgita da tsoro wannan bakon al'amari dayazo mata rana tsaka, Shikam *Bulama* wani irin gumi ne yake tsatsufo mashi tako'ina saboda tsananin tsoro gaba daya yashiga confused,

"Shikam *Blue* tunda akafara maganar yake rabon idanu yakalli wannan yakalli wannan domin dai baya fahimtar komai, sai dayaga *Beenan* shi tafashe da kuka sannan cikin damuwa yace sorry my *Beena* friend are sick?...

bata saurare shiba kuka kawai take cike da tashin hankali tace dad aunty *Bebe* me kuke faɗane ni kwata-kwata ban fahimce ku ba...., aunty *Bebe* ce ta harare ta tare da cewa ah! dad kaji y'ar raini hankalin yarinyar nan Waima bata fahimci abinda muke faɗaba?...

"Harara ya zubawa *Beena* cike da bacin rai yace rabu da mara kunya aizata gane,. tsaki mtsww! tayi tare cewa bari naganar da'ita kunnen *Beena* takama tare da cewa ciki! cikin!! dake jikin ki bana *Bil* boy bane kije can kinemi uban shegen cikin ki amma ba ɗan uwana ba kinji....?

Cikin tsananin kuka tace a ah aunty *Bebe* idan har ciki ke gareni to wlh na yah *Bilal* domin bantaba tarayyã dawani ɗa namiji ba idan bashib......,da sauri aunty *Beben* tace karya kikeyi taya za'ayi wanda bayada hankali ya'iya tarayyã aure dake?....

"Dad yace abinda nake tunani kenan...yau kaima kafaɗa, cikin rawar murya *Bulama* yace aunty *Bebe* aɗan sake bincike.... da sauri tace wani irin bincike bayan wanda nayi ko kana nufin bansan aikina bane?..da sauri yace a ah ba hakan bane....,
Chapter 25 · 0% Book details