← Book details Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 27

Sashe 6

Zaujun Majnun Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tukun na aka kirashi akace masa yafarka saidai still yanata fisge-fisge, wani abin mamaki ansakeyi masa alluran koya sake komawa bacci Amma ko gyangyad'i bai kamashi ba balle bacci duk yafita hayyacinsa gwanin tausayi,

Hakan yasa suka saka masa ankwa kafa da hannu sannan suka maida daki suka kulle gudun karya fito.

Koda aka bud'ema Dad dakin yashiga mamaki ne yarufe shi nagani yanda aka hada yaronsa dagado aka daure kafa da hannu tamkar hauka sabon kamu, cikin masifa ya kalli nurse din tare da ballamasa harara yace wannan wani irin walakanci ne?...

yaron nawa zaku daure da ankwa saikace mad ko kun bincika kunga ya haukace ne?..
yace Sir wallahi bai bada damar ayi bincike ba saidai ya nayinsa yanuna kamar kwakwalwar sa ta tab'u, cikin tsawa yace keep quiet! jo,

Malam zoka kunce mun yaro kaji ko?.. dasauri yace Ok Sir yaje yafara kokarin kwance masa hannuwa, shikam *Blue* yana gani Dad yasaki wani irin mahaukacin kuka me cike da tsabar shagwabar da ko yaro dan shekara uku albarka, hannun yamikawa Dad tare da sake b'are baki yasaki wani kukan dayasa Dad saurin karasawa gurin shi,

kirjinsa yana wani irin halbawa saboda tsananin tsoro daya ziyarce sa alokaci daya, nagani wannan sabon al'amari dayasamu yaron sa.

Rungume shi yayi akirjinsa dake matsananci bugawa, ahankali yasa hannun sa yanashafa masa lallausan gashin kansa cikin rawar murya me cike da tsoro yace it'.....s O.....k m.....y bo.....y, fadamun inayake maka ciwo?...

beyi shurun ba kamar yanda Dad yabukata balle yabasa amsa tambayar dayayi masa, asalima sake b'are baki yayi yana wani sabon kukan har sheshshaka wanda yasa Dad sake tsorata tare da fad'awa cikin tunani.

Tabbas yasan yaronsa shagwab'abb'e ne saidai kuma aishid'in jarumine Wanda duk wahala abu bayayi masa kuka amma yau meke faruwa ne?...yake irin wannan kuka haka kamar wanda ake yankan naman jikinsa,

Dasauri yaduba hannun *Blue* aikam abuga fari gurin da'akasa masa ankwa duk yayi jajir, ayya no wonder yake wannan kukan kuce dama sokukai ku kashemun shi ji hannunsa fa haba wannan wani irin zalinci ne haka eye?....yace sorry Sir wlh munyi iya kokarin mu don yatsaya amma yakiya shiyasa muka yanke hukuncin dauresa, yace Ok yayi kyau yi shuru my boy kaji?...

Cikin wani irin muryar da Dad be tabasanin shi da'ita ba yace Dad I want to go home now, cike da tsoron Dad ya kallesa tare da tab'a wuyan sa yace boy what's wrong with you voice?....,baki yasake b'arewa tare da buga kafa cikin shagwaba yace Dad I say i want to go home now, dasauri yace ok tashi mutafi, tashi yayi yana me sake kwakume Dad tamkar wanda za'akama.

"Sir zaka tafi dashi ne kuma?...eh kar ku kashemun shi abanza, "Sir yana bukatar good treatment fa, yace zanyi masa ko kamanta Ubansa Dr ne?... No "Sir ok to bani hanya da sauri yamatsa suka fita, drive yana ganin su yabude masu mota suka shiga yaje yaja suka nufi gida.

Suna isa gida direct main falo suka nufa dashigar su *Blue* yasaki Dad tare da buga wani irin tsalle yafada saman kushin, yadauki pillow yafara jefasa sama yana chab'ewa yana dariya me had'e da ihu irin dai idan yaro yasamu abinda yaimasa dad'in, chan kuma sai
yatashi zumbu yasake fad'awa saman wani kushin d'in,

yadauki pillow yajefar kasa
Haka dai yake tafaman yi har da irin tuntun na tsakar falo sai daukan su yake yana jefarwa yana tsalle, tare da ihu da dariya tamkar karamin yaro irin marasa jin magana d'in nan,

Dad kam mutuwar tsaye yayi yana kallon sa yayinda kirjinsa ke cigaba da matsananci bugawa shin meke shirin faruwa ne?....cikin karfin hali yace my boy meye haka kakeyi kamar karamin yaro eye?...

fuska shagwab'e yace Dad I'm play, cikin mamaki me had'e da tsoro Dad yace haba my boy kaifa babban yaro ne amma meyasa kake wasa irin na k'ananan yara umuh?...

kuka yatsaki tare da buga kafa yace Dad where's my Toys ido Dad yazaro cike da tsananin tsoro yace......

Muje zuwa

Daga✍🏼

*LUFHAT*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*® _PEN: WRITER'S ASSOCIATION_*

*~_Only the exquisite_~* *~__and whizkid_ _writers_~* ~*_are_* *_opportune to_* *_be__*~
*~_pen writers_~*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍

🎍 *_ZAUJUN MAJNUN_*🎍
( _Miji mahaukaci_)

🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍

Page1️⃣1️⃣to1️⃣2️⃣

WRITTEN
By
🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍

OR
🎍 *Meenat*🎍

Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*👇🏼
and now
*ZAUJUN MAJNUN*

SADAUKARWA GA

*_My lovely blood sisters👩‍❤️‍👩Hadiza (Aunty) and Nana firdausi our Last born do u know what...? sisters humm l really love love love yours irin babu adadin nan fa irin so muchhh love_*.💋💋💋

Littafin nan na kudi ne duk me bukata zaya iya turo katin mtn k airtel 200 a wannan 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi duk zaku iya tuntuban layin sai abaku acc no ba nagode.

*_FREE PAGE_*

✍🏼

*_Bismillahirrahamanirraheem!!!_*

Me kace?...my boy....cike da shagwab'a yace my toys, dad kam had'e miyau yayi jikake kuttt....yayinda wani irin zufa yakaryo masa, cikin tsananin tashin hankali yace Oh!!!! God wai meke shirin faruwa da yarona ne?...

A ah! to kodai wasa yake mun to kuma aiba watan wasa bane, balle yace" to kodai kwakwalwar sa ta samu matsal ne?...dasauri yace No!!! in possible, sai kuma yatsura wa *Blue* din ido yayinda shikuma sai wasa yake da filo,

tamkar karamin yaron wanda hankalin sa yake kwance, Cikin sanyi murya me cike da fargaba yace my boy....,banason irin wannan wasan so kadaina kaji ko?.. d'ago kai yayi yakalli Dad tare dayin shuru na d'an wani lokaci da alama be gane abinda dad din yake nufiba, da hausa yai maganar (kasan cewar duk maganar da turanci sukeyi)

don haka sai yatab'e baki kamar zayayi kuka sai kuma yaci gabada wasa da pillows din, idan yajefa wannan yacab'e sai yajefa wannan can yacab'e.

Cikin tsanani tsawa Dad yace l say stop it!...cike da tsoro yasaki pillows din tare da makurewa jikin kushin yasaki wani irin kuka, yayinda jikinsa yake kerma sosai wanda yasa dad saurin isa gurin sa zaya rungume sa, cikin kuka me had'e da shagwab'a yace don't touch me...

Aikam cak!!!.,
dad ya tsaya tare da tsura masa ido cike da tashin hankali, yace boy nifa dad dinka shine kake cewa karna taba ka?...baki yaturo cike da shagwab'a yace bakai ne kake yimun ihu ba,

Cikin sanyi jiki yace am sorry bazan kara yimaka ihu bakaji?..to tashi kaje kai wanka sai kazo kayi breakfast kaga tunjiya bakaci komai ba oya tashi kaji my boy?...

kafad'a yamak'e tare da fad'in no! I don't want to eat, yace sorry my boy kaji?...yace no haba my darling boy to sai kayimun wanka sannan zanci abinci,

Ido dad yazaro tare da fad'in boy yau ni zanyi maka wanka kuma?.. yes amsan dayaba sa kenan yana turo baki hawaye nazuba tamar anbud'e fanfo, zama dad yayi akan kushin jabar tare da d'ora hannuwa akai cikin tashin hankali yace Oh! God kodai yarona yasamu matsalar kwakwalwa ne?.. ya Allah yanzu me abinyi?....

Dasauri yatashi tare da cewa to tashi muje kayin wankan yakareshe fad'in yana d'ago shi, suka shiga wani tsararren falo me dauke da kushin kalar royal blue da yellow masu asalin kyau, direct toilet suka shiga Dad yahad'a masa ruwa me d'umi acikin kwanan wanka,

Tunda yananshi ma'abocin san kamshi ne don haka yazuba masa turarukan wanka Cikin ruwan sosai, sannan yace to kacire kayanka sai kayi wankan bari naje nasa peter yahad'a maka breakfast kaji?...

Cike da shagwab'a yace dad wait for me.... yace no boy kayi mana kafad'a yamake tare da fad'in no, ok to inazuwa kafara tub'e kayan yafad'i tare da fita toilet din da sauri, domin gabada hankali sa atashe yake, da wannan bakon lamari daya samu tilon dane.

******
Misalin karfe 6:00am su *Beena* ne zaune a dakin Abbu ko wanne hannun sa rike da alqur'an me girma, yana karantawa cikin nutsuwa kasan cewar sun saba duk bayan sallah asubu sai sunyi karatun alqur'an, don haka kowane su yana fitar da kalma akan k'a'ida,
idan kacire *Banu* datake koyo yanzu,

Duk kansu suna karatawa dai-dai ko dayake suna d'anyi kuskure tunda dama Dan adam ajizine, yayinda *Beena* take gyara masu wanda hakan be hana shima Abbu sauraran su dakyau ba idan yaji sunyi bata ko kuskure saiya gyara masu.

Ido ya lumshe ahankali yana ciyaba da sauraran su, yayinda yakejin sanyi aransa yanama Allah godiya da ya azurta shi da kamilar mace ta haifamasa kyawawan yara nutsatstsu masu hankali da ilimi da biyayya, ahankali yafurta Allah ka rayamun su akan tafarki madaidaiciya katsare mun daga sharrin mutun dana aljan ameen,

Ahankali yabud'e ido tare da kallon wani tsohon agogon
dake manne abango dakin, inda yanuna masa karfe 7:00am saida ya tabbatar kowa yakai karshen aya sannan yayi gyaran murya Wanda yasa sukai shuru suka nustu.

Sannan yafarayi masu nasiha akan ruyuwar duniya yana me tsoratar dasu suji tsoron Allah susani duk abinda suke yana ganinsu, su kuma guji cin amana hassada kyashi da shirka dacin hakkin wani domin suna kai mutun ga halaka hakama *ZINA,* karku kusance ta kuyi hakuri da halinda kuka tsinci kanku Allah yanasa ne daku sannan kukiyaye kanku da kawuna ku,

Hakadai Abbu yayita masu nasiha me matukar kashe jiki kamar yanda yasaba yimasu aduk lokacin dasuka gama karatu, inda daga karshe yace ina me rokon Allah ya shiryar daku shirin addinin islama yatsare ku akan tafarki ma daidaiciya, Allah yaimaku albarka"suka amsa da amin.

Sannan yace to ayi mana addu'a ahankali suka daga hannuwa sama harda Abbu yayinda *Beena* tafara kwarara masu addu'a, me ratsa jikin d'an adam sosai take zubama su addu'a suna amsawa da amin har saida muryar ta yafara rawa alamar zatayi kuka, hakan yasa Abbu karban addu'a y masu.

Bayan sun shafa sai yace to aje idan akwai wani aikin ataya "Ammu sai akarya kumallo akuma yi hakuri da abinda akagani, idan angaba sai atafi gurin koyan dinki da sakan idan anje akauda kai daga abun mutane sukace to tare da mikewa suka fita,

Amma banda *Banu* data nufi gurin Abbu ta zauna cike yarinta tace Abbu ban iya nan ba ta kareshe fad'i tare da turo baki, murmushi yayi tare da shafa kanta yace karki damu *Banujan* Abbu zaki iya inshallah, yanzu kije kikarya kumallo saikizo mukarayi ko?....
Chapter 6 · 0% Book details