← Book details Zarinat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 16

Sashe 9

Zarinat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

K'ara sowa tayi tare da zama kusa da shi cinyar su na gugar ta juna,

Kwantacen sajen sa wanda yasha gyara ta shafo tare da fad'in "Dear naga kamar ka rame kodai idanuwa na ne" Hmmmmmm ba dole na rame ba kina barina da yunwa nine koda yaushe sai dai nasha tea da auren ka " Sorry kar ka damu akan ka Kawai zan koyi girki zansa a turomin video's na girki kala_kala sai abincin da kake so zan girka " ya bud'e baki zaiyi magana k'amshin turaren zarinat ya bugi hancin su gabaki d'aya d'agowa sukayi tare da kallan hanyar d'akin ta

Sanye take da wani material red mai masifar kyau an masa d'inkin da ya k'ara fito dashi sosai, kuma ya mata kyau kunsan dai yarda abu red yakema farar mace kyau hmmmmm ta saka sark'a ta da awarwaro na alfarma, yau kam har powder ta shafa ta mata kyau sosai ita dai ce bata san shafawa, sai lipgloss d'in da ta sha ta gyara girar ta, kamar abunda aka zana, sai k'ara min mayafinta da ta yafa white, takalmintama white shoes, hannun ta dafe da waya a kunne da alama waya takeyi, yarda takeyi ne zai tabbatar maka da mom takewa saboda yarda take zuba shagwa'ba

Husna cikin ta ne ya murd'a ganin zarinat dan bata ta'ba tsammanin takai kyawon haka ba tasan nesa ba kusa ba tafita da komai

Sallama sukayi da mom ta k'ara so wajen tare da duk'asawa ta gaida yah ansar, wanda ya kafeta da ido tun d'azu, amsawa yayi cikin fara'a ta tashi ta zauna

Gyaran murya yayi tare da fad'in "Abinda yasa na tara ku anan bakomai bane face na samar muku driver na nan yazo wanda zai rik'a kai ku duk inda zaku je sai kuma abu na biyu wanda jan kunne ne a gareku ban yarda ba ban lamunce ba d'aya daga cikin ku tahau taxi ba idan ma ta kama dole sai kun hau to tare da k'auk'auran dalili wanda zaisa khau kunji ni dakyau? " Ya fad'a tare da kallan su zarinat ya gyad'a masa kai husna kuwa bata ma san me yake fad'a ba tanacan ta fad'a duniyar tunanin yarda zata k'ara mallake yah ansar ya zamana ba macen da yake so da K'auna kamar ta

Yah ansar ya kira sunanta da k'arfi ta zabura, zarinat ta d'ago ta kalleta suna had'a ido husna ta harari zarinat itama ta mayar mata

Yah ansar yace" Kin ji mena fad'a banyarda da hawan taxi ba " Murmushi ta saki tana k'ara shigewa jikinsa tare da fad'in
"Dear ai kaima kasan bana hawan taxi " Good zaku iya tashi " yana fad'in haka zarinat tayi saurin Mik'e wa dan bazata iya jurar kallan wannan iskancin da taga husna nayi ba
Yah ansar baiso ta tashi ba jin yayi kamar ya bita yayi ta kallanta shi kansa baisan dalilin da yasa yake son kallanta ba

Suma tashi sukayi suka nufi d'akin husna

Zarinat na shiga ta fara aikin abinci ta gashi yau zatayi bak'i yan department d'in su sunce zasu zo, tun da safe ta surfe wake dan alale ce zatayi

K'arfe goma sha biyu, yah ansar zaune yana aiki a system d'in sa dan yau baije aiki ba gaba d'aya bayajin dad'in jikinsa, wayarsa ce ta fara rura alamun kina na shugowa d'auka yayi yaga sunan faruk abokinsa ne ya kara a kunne, daga 'bangaren faruk yace " Gamu bakin door " au haba dan allah " Nidai zoka bud'e muna kasan madam yanzu ba jurar tsayuwar nan takeyi ba" Yana fad'in haka ya kashe kiran, ya juyo ya kalli matar sa tare da fad'in"Sorry gashinan tafe...............................................

Comment and share fisabilillah ♥️

💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋

Mallakar
Zainab dodo✍️

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂

_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 1️⃣2️⃣

Aje aikin da yakeyi yayi yaje ya bud'e musu k'ofa, murmushi d'auke a fuskarsa ya bama faruk hannu suka gaisa tare da k'ara sowa cikin falon suka gaisa da zarah

Yah ansar yace " Ko sanarwa babu sai dai kawai na ganku girshi "Ai daman nace idan zamu zo bazan sanar maka ba sai dai ka ganmu ahhahhh ango! ango! ango kasha k'amshi " Hhhhhhh kai bana san iskanci muje ciki ku fara ganin husna sai muje wajen zarinat"Okay let's go " faruk ya fad'a tare da kama hannun matarsa suka nufi 'bangaren husna yah ansar gaba suna biye dashi a baya

Waje ya basu suka zauna ya wuce uwar d'aki dan kiran husna,

Tana nan kwance tana abunda ta saba ( chart kenan) sanar mata yayi ta fito sunyi bak'i, tace " To bak'i kuma daga ina? Su waye? " Idan kika zo zaki gansu " yana fad'in haka ya fice

Yatsina fuska tayi tare da jan tsaki tace"Mutum na tsaka da jin dad'insa azo a katse masa" ta fad'a tare da Mik'e wa ta nufi hanyar falo

Tana zuwa bako sallama ta samu waje ta zauna tare da d'aura k'afa d'aya saman d'aya tana dannar waya, zarah ta saki baki tana kallanta

Yah ansar yayi gyaran murya tare da fad'in "Husna miye haka kinyi bak'i amman zaki shigo ki zauna ko sallama baza ki musu ba" D'agowa tayi tare da fad'in " Ohhhhhhhhhhh I'm very sorry i forget wallahi kasan abubuwan ba d'aya ba ina wani abu ne a phone shiyasa hankali na ma baya nan sorry fa, ta fad'a tare da kallan su faruk zarah ta cika sosai dan taga wulak'ancin na husna yayi yawa wato ma bata ko lura dasu ba bayan kuma akan su aka kirata ta fito

Yah ansar yace "Abokina ne faruk wanda nake baki labari sai kuma matar sa zarah"

" Ayyah Sannun ku" Yawwa sannu fatan kuna lafiya ya amarci?" Faruk ya fad'a" fine " ta fad'a tare da ci gaba da latsar wayarta

Zarah ta sakarma faruk harara na kula ta da yayi

Yah ansar shima baiji dad'in yarda ta musu ba

Zarah tace" Muje muga d'ayar sai mu wuce dan inaga ba dad'ewa zamuyi ba "Okay ku tashi muje" duk suka Mik'e

"Amarya mu mun wuce" faruk ya fad'a ba tare da ta d'ago kanta ba tace " Okay sai anjuma" Mu jima da yawa" zarah ta fad'a tare da yi gaba ta barsu a baya, suma biyota sukayi

'Bangaren zarinat suka nufa

Bakin su d'auke da sallama suka shiga, wani irin daddad'an k'amshi ne ya ziyar ci hancinsu, suka shiga raba ido musamman zarah da take d'auke da jaririn ciki, ba kowa a falon sai TV dake kunne tana aiki, zarah ta rik'a kallan falon ba k'arya kayan sunyi masifar kyau sun mata kyau ga yarda kuma aka tsara komai zaa kyau

Yah ansar ya nuna musu waje su zauna, ya nufi bedroom d'in ta dan kiran ta har ya kusa kai sai gata ta fito ta sauya kayan d'azu tana sanye da abaya black tasha kyau sosai, mayafin abayar ta d'aura sa saman kafad'arta ta kama gashin kanta da white ribbon 🎀 hannunta rik'e da wayarta, tana tunanin yarda zatayi da alaler da ta dafa tunda su saudat sunce ba zasu samu daman zuwa yau ba sai wani lokaci

Yah ansar ta gani tsaye a gabanta, baki ta bud'e zatayi magana yayi saurin cewa "Kinyi bak'i muje ki gansu abokina ne tare da matar sa"To,ta fad'a tare da d'ora mayafinta a kai suka k'ara so cikin falon sallama tayi duk suka amsa ta zauna tare da fad'in " Sannun ku da zuwa ya hanya" Alhamdulillah,duk suka fad'a, zarah ta sake fuskarta dan da ganin zarinat tasu zata so d'aya ba irin husna ba ce tare da yaba kyawon zarinat a zuciyarta

Mik'e wa tayi ta nufi kitchen taje ta d'auko lemon juice ya d'au sanyi sosai da cup's uku ta d'ora saman filet takawo, ta ajiye tare da zuzzubawa ta Mik'a ma kowa zata Mik'a ma yah ansar sai da tad'an duk'a cikin bangirma ya amsa, yana jin dad'in yarda ta kar'be su

Zarah tasha lemon tare da fad'in "Waiii kin sanyayamin zuciya ta daga 'bacin rai da ta shiga" Yah ansar da faruk duk sun gane mai take nufi

Zarinat tayi murmushi

"Ni nama manta ban gabatar miki dasu ba" yah ansar ya fad'a yana kai cup bakin sa " Wannan abokina ne faruk duk cikin abokai na dashi muka fi shak'uwa wannan kuma matarsa ce Zarah in Sha Allah muna sa ran nan da wata shidda zata haifo muna d'an mu" Lahhhlahhhlahh kace har an kawo ma rahoto " zarah ta fad'a cikin wasa" Tun yaushe kedai allah ya sauke ki lafiya "Hmmmm amin ai kaima kamar gobe ne za'a cemin matarka zarinat nada ciki, zarinat ta kalli zarah tare da sunkuyar da kanta k'asa yah ansar ya kalleta tare da sakin k'ayataccen murmushi
" Waya sani ma ko ta harbu" faruk ya fad'a" Wallahi fa abu a duhu waya sani"zarah ta fad'a

Zarinat ta Mik'e tare da fad'in"ina zuwa" ta nufi kitchen, yah ansar yace" kun gani ko kun korar min mata kunya gareta sosai " Uhmmm kunya ko duk nan muka fito takalmin mu suka tsinke" cewar zarah duk suka sa dariya

Kulolin abinci ta kwauso daga kitchen takai dining ta aje ta koma kitchen ta d'auko filet guda uku, ta bud'e kular da alalen ke ciki ta banye leda uku uku ta zuba a filet, kasan cewar manyan d'auri tayi shiyasa ta zuba ma ko wane filet uku_uku amman banda d'ayan bata zuba na d'aya filet d'in ba tasa spoon ta yayyanka tsakiyar a lalen, ma sha Allah mai kwai ce a ciki tayi, ta zuba sauce d'in da tayi mai kayan ciki a ciki abun sai wanda ya gani gwaunin burgewa sai k'amshi ke tashi

Ta d'auko ta nufi falo, ta ajiye d'aya gaban zarah d'aya kuma gaban faruk ta koma kitchen ta d'auko musu ruwa masu sanyi, ta koma dining dan had'ama yah ansar nashi
Chapter 9 · 0% Book details