Sashe 8
Zarinat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun da aunty larai ta shigo inna ke mata wani kallan uku saura kwata, aunty larai ta lura da ita tsaff da irin kallan da take mata, dan da aunty larai da inna tasu bata jitu ba inna nuna isa da iko da masifa da sakin magana duk yarda tazo mata ba ruwanta, ita kuma aunty larai rashin hak'uri
"Aikin banza a ka ce ga banza anwa kuti bulala" aunty larai ta fad'a tare da wucewa dan tasan idan tace zata tsaya to bazasuyi mai kyau ba gashi kuma ita ta isko ta dan haka koda ita ce da gaskiya za'a ce batada gaskiya don ita ta sameta har gida
"To yarda aka zo haka za'a koma ba'a girka ba bare a yi zaune a bud'e rumbun ciki ayi ta ci ba" Inna ta fad'a sosai yarda aunty larai zata ji, aunty larai har ta fara cire takalmi taji abinda inna ta fad'a ta mayar da takalmin tare da juyowa ta dawo ta tsaya gaban inna tace
"tsohuwa Kallan ni da kyau ki gani, aunty larai ta fad'a tare da juyawa" Kinga alamun yunwa a tare da ni? Ko namiki kama da maicin irin wannan abincin naku "K'aryar banza har ni za'a nunama arziki "Wallahi dole a nuna miki kinsan ko gaba da gabanta in banda k'addara mai zai kawo fatima a gidan nan bare har aji wai anan take aure mtsssssww kai allah dai wadaran naka ya lalace "K'addarar nan da kika kira ita ta kawo ta sannan da naci ta nace masa sai da ya aure ta " Hehehehe sauya magana dai naci wallahi ba wanda baisan yarda d'anki ya nace mata ba tana da wanda zata aura yazo ya lik'e sai da akayi da shi " yanzu dai koma mine ne ke ya dama" Mtsssww, aunty larai taja tsaki tare da juyawa
"Me kike fad'a idan ba tsoro ba ki dawo ki fad'a? " Kanki akeji mahaukacin ya fad'a rijiya "
D'akin ta shiga ta ga Fatima kwance ta kudumdume cikin bargo"Iyyeeeee lallai yarinya baccin kima kike yi "ta fad'a tare da sa hannu ta yaye bargon, idan ta biyu ba bacci take ba sanyin da take jine yasa ta lullu'be aunty larai takai hannu ta ta'ba ta tare da fad'in"Bakyada lafiya ne?" Kai ta gyad'a mata" Subhanallah sannu ina nasir? Yasan bakyada lafiya?" Nan ma kai ta gyad'a mata" wayarta aunty larai ta d'auka ta lalubo number nasir bugu d'aya ya d'auka ta sanar masa gata tazo ta sami Fatima ba lafiya zasuje asibity, yace to shikenan in Sha Allah shima gashi nan tafe ta kashe wayar
Hijab d'in ta ta d'auko mata ta saka mata ta taimaka mata suka fito, inna na d'aki suka fice da motar ta tazo dan haka basu tsaya neman wani taxi ba suka wuce asibityn dake kusa dasu suka je aka amshe ta suka yi gwaje_gwajen da zasuyi suka ga maleria ce da ita suka rubuta maganin da za'a siya, nasir ya iso aunty larai tace ya tsaya wajen ta taje ta siyo magani, an saka mata ruwa ko zataji k'arfin jikin ta
Aunty larai taje ta siyo maganin ta dawo, ruwa na k'arewa aka sallame su, aunty larai tace nasir ya koma Kawai kasuwa dan yanzu jikin nata yayi sauk'i sosai, godiya yayima aunty larai sannan ya wuce suma suka wuce saman hanya ta tsaya ta siya mata hanta gashashshiya, da kayan marmari
Suna shigowa gidan inna na fitowa daga d'aki, da kallo ta bisu tare da tunanin yaushe suka fito to,
Hannun aunty larai inna ta kallah ganin uwar zundur cike da kayan marmari, sai da ta had'iyi yawu, had'a ido sukayi da aunty larai suka sakarma juna harara aunty larai tace "Nan gani nan bari"
Fatima ta gaida inna amman ko kallo bata isheta ba bare ta amsa suka wuce d'aki
Suna zaune saiga wata yarinya inna ta aiko yarinyar mak'otansu tace "Wai hajiya tace ki fito ki d'ora girki"aunty larai tace
"Je kice ni hajjatani larai ita idan haji sau d'aya taje to ni hajjatani larai nace baza tayi ba kinji "yarinyar tace" Eh "
Tazo ta sanarma inna abunda tace, inna ta koma d'aki dan bata iyawa dan ma yau sunyi da sauk'i ita da aunty larai
Aunty larai bata wuceba sai da taga jikin Fatima ya dawo normal sannan ta wuce, tana fita inna ta shigo d'akin tayita zazagama fatima masifa tare da fad'in ta tashi ta d'ora musu girki, ta bud'e ledar kayan marmarin ta d'ibi wanda take so ta fito allah dai bai kai idanunta ga ledar hanta ba da itama sai taci
Fatima ba yarda ta iya haka ta fito ta d'ora girkin...
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
"Wai baki gama girkin bane? " Yah ansar ya tambayi husna" Wallahi bansani ba ko sun gama " Ban gane baki sani ba ko sun gama wai badai kina nufin harda ni abincin yan aikin nan zanci ba "Eh mana"Hmmmmm kema kinsan bazai yuwuba dan Wallahi bazan ci abincin da yan aikin nan zasu girka ba "To yanzu me kake so? " Ki tashi ki girka min nawa " Ai kasan ban iya girki ba" Baki iya girki ba?" Ya fad'a cikin jin mamaki da furucin ta" Eh" kallanta yake yama rasa mezai ce
Tace " To idan bazaka ci ba kaje gida wajen ammi ka ci " Miye amfanin auren nawa da nayi indai har zanje gida cin abinci" Ta'be baki tayi ta koma ta kwanta
Fita yayi daga d'akin ransa a 'bace ya nufi d'akin sa,
Zarya ya rik'a yi cikin d'akin shidai bazai iya cin abincin yan aikin ba kuma baya iya cin abincin siyarwa sannan bazai iya zuwa gida cin abinci ba dan abun akwai kunya gashi yunwa yake ji to yanzu mezanyi? Ya fad'a a fili, toilet ya shiga yayi wanka ya fito d'aure da towel a k'ugunsa yaje gaban mirror kamar mace ya shafa wannan ya shafa wancan ya gama ya saka boxer ya zura jallabiyar sa ya haye gado yayi kwanciyarta sa, cikin sa yaci yana k'uwa dan haka ya tashi zaune tare da zura takalmin sa ya sauko saman gado, ya nufi kitchen d'in 'bangaren sa,
Tsaye yayi yana tunanin mezai dafa shida ba girki ya iya ba Lipton kawai yasan ya iya dafawa, k'arasawa ciki yayi ya dafa tea ya fito dashi...............................................
Comment and share fisabilillah ♥️
💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋
Mallakar
Zainab dodo✍️
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫
Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari
TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 1️⃣1️⃣
Zama yayi saman kujerar d'akin, ya shanye tea d'in gabaki d'aya ya ajiye cup saman table d'in wajen, cikin sa ya shafa wanda yakejin yanzu kam alhamdulillah ya k'oshi ya jima zaune a wajen sannan ya Mik'e ya nufi gado ya hau ya kwanta agogon hannun sa ya cire ya aje a gefen sa, ya lumshe idanunsa da haka bacci yayi gaba dashi
Husna ganin har goma ta gota bai shigoba yasa taji dad'i dan a takure take tana san tayi wayarta sosai, kuma tunda yakai wannan time d'in bai shigoba tasan ba'a nan zai kwana ba, ta tashi ta saka wata arniyar rigar bacci wacce bata 'boye mata komai ba, tana gama saka rigar aka kira ta a waya, number bata nan ce ba number k'asar waje ce, d'auka tayi cikin hanzari ta kara a kunne banji abinda aka ce daga d'aya 'bangaren ba amman naji tace " Sorry gani nan" ta kashe kiran tare da hayewa gado ta kunna data sai gashi an kira ta video call da number nan cikin sauri ta d'aga tana wani yauk'i irin na yan barikin nan
Fira suka d'an ta'ba da mutumen zuwa can yace "Wai yaushe zaki dawo ne?" In Sha Allah nan bada jimawa ba zan zo " Gaskiya kam ya kamata nayi kewarki sosai ina mijin ki ne?" Yana d'akin sa " ta fad'a tare da ta'be baki
" Beb tun da na d'and'ani zumar ki naji ba macen da nakeson na kasance koda yaushe a tare da ita kamar ke " Murmushi ta saki tare da fad'in"Wacce irin zuma kenan? " Dariya yayi irin ta shak'iyan nan kana yace" Zan baki wani labarin da bakisan dashi ba " Wane irin labari ne? Ina jinka" Kin tuna kafin ku wuce kusan kwanan ki biyar a waje na iya kar mu romanc kin hanani na kusan ce ki,
da naji labarin aure zakiyi naji bazan iya hak'ura wani d'ah namiji ya fara sex da ke ba kafin ni shine na nemo k'waya mai k'arfi na zuba miki a lemo kika sha na biya buk'ata ta kwanan ki biyu kina bacci kin tuna lokacin da kika farka kika ce min jikin ki duka ciwo yake miki?"
Shuru tayi tana nazarin kalamansa tare da zancen zuci" Kenan na dad'e da rabuwa da budurci na ba ansar bane ya kar'bi budurcin ba to ya akayi hakan ban gano ba? Hmmmmmm lallai odo sai na nuna masa kuskurensa na kusan ta ta ba tare da sahalewataba duk da hakan dai nagode allah da yasa ansar bai gane komai ba
"Hi beb " Numfasawa tayi tare da kallan wayan ta banka masa harara ta cikin wayan ta kashe kiran, tana kashewa ya sake kira ta kashe da taga zai dameta sai ta kashe wayar gabaki d'aya
Yau kwana hud'u kenan yah ansar kullum cikin shan tea yake da safe da rana da dare saboda bazai iya cin abincin masu aiki ba, ita kuma husna ba iya girki tayi ba gashi yana jin kunyar yaje gida yace ma ammi ta samai abinci dole ya hak'ura ya rik'a shan tea
Misalin k'arfe goma na safe ya shiga 'bangaren ko wacce yace suzo babban falo zasuyi magana, ya dawo falon ya zauna jiran su, husna ta fara fitowa tana tafiya tana juyi sanye da wasu k'ananun kaya riga da wando, yah ansar kallo d'aya yayi mata ya d'auke kai shi baisan miyasa take son saka k'ananun kaya ba gashi ko kyau basa mata idan ta saka su ta koma Kamar wata balbela