← Book details Zarinat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 16

Sashe 14

Zarinat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunyi yi tafiya k'arfe uku suka isa gidan, mai gadi ya Bud'e musu gate suka shigo, d'aya daga cikin ma ai katan gidan yazo ya kar'bi kayan su ya shiga dasu ciki

Afrah na ganin su da gudu tazo ta rungume zarinat tana murnar ganinta, su aunty Maryam na nan zaune a falo ana mata k'unshi harda yaya bilal na wajen zaune suma sunyi farin cikin ganin su sosai

Nan suka zauna aka gaggaisa a ka shiga fira kiran sallah la'asar ne ya tada su maza sukayi masallaci sukuma sukayi d'aki

Bayan sun dawo masallaci zarinat ta kawo ma yah ansar abinci wanda k'anwar aunty maryam ta girka, bai wani ci da yawa ba ya aje tare da Mik'e wa yayi musu sallama ya fito zarinat ta rakasa har mota ya shiga itama yace ta shigo ta kar'bi sak'o ta shiga

Kud'i ya Mik'a mata masu yawa yace ta bama aunty maryam, ya d'auko ledar kayan baby's d'in da ya siyo ya mika mata tare da fad'in "Wannan a bama baby" To sun gode sosai " ya sake bata kud'i yace wannan nata ne koda zata siya wani abu, godiya tayi masa sosai, ya matso face d'in sa dai_dai tata yana k'ok'arin d'aura lips d'in sa akan nata, tunowa tayi da yarda ta gansu d'azu shida husna tayi saurin janye fuskarta tana turo baki,

Kallanta yake" Why?" Kalmar da ta fito masa kenan "Why rinat?" uhm uhm to ai matarka ta maka kafin ka fito " ta fad'a cikin shagwa'ba, yah ansar da mamaki yake kallanta, ita kanta sai da ta furta maganar ne sannan taji nauyin ta, hannu tasa ta bud'e murfin motar ta fito tayi masa allah ya kai lafiya ta wuce, sai da ta shige sannan ya tada motar ya fice

Kayan ta bama aunty maryam da kud'i, tayi gadiya sosai, aunty maryam ta zaunar da zarinat aka sa mata lalle

Ranar suna yaro yaci sunan aminu, sunan Mahaifin aunty maryam wanda aka masa lak'ani da abba.....................................................

Comment and share fisabilillah ♥️
💋💋 ZARINAT ( زرينة )💋 💋

Mallakar
Zainab dodo✍️

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂

_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 1️⃣8️⃣

Kwana biyu da sunah amman bata koma ba duk da yah ansar ya kira ta yace zai zo d'aukar ta tace, yayi zamansa basai yazo ba yaya bilal zai wuce da ita dan shima garin zai je, amman har yanzu shuru ka keji

Yau yah ansar koda ya dawo daga wajen aiki a gajiye gashi yunwar da yake ji allah ya gani ya gaji da shan tea ya kwanta dan haka yana dawowa ya tasa husna a gaba akan dole sai ta girka masa wani abu yaci, tashi tayi ta shiga kitchen shi kuma ya wuce d'akin sa yayi wanka

Tsaye tayi cikin kitchen tana kallan komai gadai kayan abinci nan kala_kala amman bata san yarda ake dafawa ba wata dabara ce ta fad'o mata dan haka ta d'auko wayarta ta kunna data ta shiga wajen Downloading tayi searching na video ake had'a delicious food

Wani video taci karo dashi na fried rice 🍚 shi ta d'auka tayi downloading, ta d'ora tukunya ta zuba ruwa, ruwan na fara zafi ta zuba shinkafa a ciki, ga video taga ansa boiling in ten minutes, ta k'ara wuta sosai cikin 5mint ta saukar da shinkafar ta juye a gwau_gwau( mazubi) ta mayarda tukunyar kan wuta ta zuba mai yayi zafi ta zuba markad'ad'd'un kayan miyan ta

Cikin k'ank'anin lokaci ta kammala ta zubo masa takai cikin falo ta aje tayi zaune tana huci,

Tun da ya shigo d'akin yake jin k'aurin girki ya iso ya zauna " ka dawo? " Eh ya na ganki haka ne?" Dan bakaga wahalar da nayi bane wajen girkin nan duk na gaji" Yawwa sannu ko kefa da haka kike min girki ai ba wanda zaiji kanmu " Nidai gashi nan ka d'auka wallahi na gaji bazan iya kawo ma ba " Ba matsala" ya fad'a tare da Mik'e wa ya d'auko abincin yana bud'e wa k'aurin girkin ya bugi hancin sa " Baby wuta kika saka da yawa ne naji sai k'auri yakeyi" Eh wai saboda nayi saurin gamawa " okay, ya fad'a tare da Mik'e wa ya nufi kitchen yaje ya d'auko filet da spoon yazo ya zuba ya zauna

Sai da ya cika spoon ya tura baki, cikin mugun sauri ya fito dashi, husna dake kallansa tace "Dear lafiya?" Sai da ya d'an d'auki lokaci kafin ya samu daman magana dan ji yayi bakinsa ma ya d'auke " Wannan wane irin girki ne haka,ya fad'a a fusace" Me yayi?" D'auka kici kiji" d'auka tayi itama tana saka wa ta fito dashi ta tayi kitchen da sauri ta wanke bakin ta ta fito

Abincin gashi bai dahuba ga gishiri da magi da yayi yawa kamar me

Kallanta yayi yaja tsaki tare da fad'in " Aikin banza" ya fice daga d'akin

" To mena zuba da yawa haka wanda yasa abincin ya kasa ciyuwa? Husna ta tambayi kanta, masu aiki ta kira suka d'auke abincin

'Bangaren su zarinat, suna zaune a d'aki ita da aunty maryam tana k'ara koya mata wasu dabaru na yarda zata kula da mijinta da yarda zata saye zuciyar sa da kyawawan dabi'u

Wayar tace ta fara rura alamun kira na shigowa, dubawa tayi taga yah ansar ne ta d'aga, aunty maryam ta fita ta bata waje

Sallama tayi masa ya amsa " Ki tabbatar da gobe kin dawo" kalmar da taji ya fad'a kenan
" Yaya dan allah ka barni har zuwa jibi idan yaya bilal zai zo sai mu wuce tare" Umurni nake baki ba neman shawara ba" yaya please please please 🥺" kinji me nace ai" yana fad'in haka ya kashe wayan

Zarinat shuru tayi ta rasa abun yi, harda wayar ta kasa janyewa saman kunne allah ya gani bataso komawa gobe ba, tana zaune a haka har aunty maryam ta dawo ta sameta, aunty maryam ta tambeta lafiya take zaune haka kamar wacce aka aikoma da sak'on mutuwa, sanar mata tayi aunty maryam ta bata hak'uri, tana k'ara lurar da ita wasu abubuwa

Washe gari, yaya bilal ya bayar da mota a kaita

Koda suka iso bataga motarsa ba alamun baya gidan,
Cikin main falo ta shigo bakin ta d'auke da sallama ta shiga husna na zaune a falo tana kallon tv, kallo d'aya tayi mata ta d'auke kai taja kayanta tayi 'bangaren ta, husna tabi bayan ta da harara tare da fad'in " Gayyar tsiya an dawo kenan"

Sarai zarinat tajiyo ta sai dai bata tamka mata ba ta yi tafiyarta

Tana shiga ko hutawa bata tsaya yi ba ta aje kayan ta ta fara gyaran d'aki duk da ba wata k'ura ko datti da yayi ta share tayi mopping ta saka turare d'akin ya d'au k'amshi ga sanyin AC ga k'amshin turare suka had'e sanyayen k'amshi na ratsawa, tana gamawa ta d'ora girki, tuwon semo da miyar egusi ne

Bata wani jima ba ta gama, ta fad'a toilet tayi wanka tare da d'auro alwala sai da ta gabatar da sallah sannan ta shirya cikin wani yadi marar nauyi daguwar riga, rigar tana da d'an Fad'i da k'asa wajen gefen k'afafuwa an masa tsaga kayan basu kama jiki sai dai yadin yana lik'ewa a jiki mutum haka ake siyar da kayan tare da mayafin su, ta gyara face d'in ta ta shafa jambaki pink, yayi mata kyau sosai ta feshe jikin ta da turaruka masu dad'i ta yafa mayafin kayan yarda ta yafa sa ta fito da gashin ta ya k'ara mata kyau sai k'amshi ke tashi a jikin ta

Falo ta fito ta zauna, ta kira faridah ta sanar mata ta dawo suka d'an ta'ba fira

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
"D'an banza fito–fito tana baka kana shanyewa shiyasa kake k'ara lek'ewa ohh ni y'ar nan daman ance inda ranka kasha kallo yaron nan bansan lokacin ka koma haka ba tunda kayi aure idanunka suka bud'e nabar ganema kan ka wai zaka fito ne ko sai na shigo d'akin, inna ta fad'a had'e da rik'e k'ugu
" Kadai san d'akin ba bak'ona ba ne wajen shiga dan ba kunyar shiga d'akin nake ba " ta fad'a tare da k'ok'arin cire takalmin ta tashiga sai nasir ya riga ta fitowa" Waya ce ka fito ne ai da kayi zamanka ka gani zan shigo ne ko kuwa?

" Haba inna dan allah kiyi hak'uri wallahi magani nake bata bata jin dad'i sosai" iyyeeeee magani kake bata sannu wato ga MATAR SO ko tunda hannu ta sara da zaka zauna bata magani kaji min wani sabon salon iskanci " Inna bata jin k'arfin jikin ta taya zata iya bama kanta" To mu lokacin mu ba ai wannan iskancin ba magani ba wanda zai baka zai zaka d'auka kasha abun ka " Inna wannan ai zamanin ku ne aure fa saboda ibada da kuma taimakon juna yasa ake yi" Ahhahh malam nasuru bara na kawo maka shimfid'a ka zauna sai ka fad'a min dakyau yarda zan gane d'an jabbura kai ni zaka fad'a ma aure saboda ibada da taimakon juna tun kafin a haife ka nasan da wannan karatun " Allah ya huci zuciyar ki inna ban Fad'i maganar da niyar 'bata miki rai ba dan allah ki gafarce ni.................................................................

Comment and share fisabilillah ♥️

💋💋 ZARINAT ( زرينة )💋 💋

Mallakar
Zainab dodo✍️

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂

_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 1️⃣9️⃣

In Sha Allah remains one page mu kammala free page's, so mai son ci gaba da karatun wannan littafin sai yayi payment a saka sa a paid group two hundred 200 ne kacal👌sannan da d'in da d'ahwa ba iya littafin kawai zan rik'a muku posting ba in Sha Allah zan koyar daku abubuwa guda 9
Chapter 14 · 0% Book details