← Book details Zarinat Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 16

Sashe 2

Zarinat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Daddy baya nan ne " ta fad'a" Eh suna wajen meeting "Okay allah ya taimaka"Amin kin San dalilin da yasa nace kizo zamuyi magana "Aah mom"To zarinat ina son ki natsu ki bani aron kunnuwanki anan wannan maganar mai muhummanci ce" To mom" Zarinat "Naam"Kin san dai bazamu za'ba miki abunda zai cutar dake ba ko?" Eh " ta fad'a tare da d'aga kai " To daddyn ku ya yanke hukunci zai aura miki d'an uwanki Ansar"da wani irin mahaukacin sauri ta d'ago tare da kallan mom tana tunanin ansar! Ansar! To wane ansar kenan?

Mom kamar tasan tunanin da take yi yasa tace "Ansar d'an kawunku" Wani irin harbawa zuciyar ta tayi da k'arfi nan da nan saiga hawaye sun zobo mata...............................................

💋 💋ZARINAT ( زرينة )💋💋

Mallakar
Zainab dodo✍️

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂

_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 2️⃣

Kuka ta fashe dashi mai sauti, mom ta janyota jikinta tare da bubbuga bayanta alamar lallashi,

"Ya isa haka mana princess" mom ta fad'a tare da d'agota takai hannunta gefen gado ta janyo tissue tasa tana goge mata hawayen fuskarta

" Princess kiyi hak'uri ki d'auki wannan hukunci da mahaifin ki ya zartar akan ki ina san ki kasance mai hak'uri da juriya mai tawakkali a wajen allah idan kika kasan ce a hakan sai kiga al'amurra sun zo miki da sauk'i duk da nasan kina yi ni kaina ina son naga kinyi aure kinje d'akin mijin ki, kinsan wani abu kuwa princess? " Mom ta fad'a tana kallan fuskarta, Kai ta girgiza mata tana sauke ajiyar zuciya

"Kinsan irin wannan auren shi ne ake kira da auren gata saboda bako wace mace bace take samun irin wannan auren ba sai yan gata kamar princess d'ita " Mom ta fad'a tare da shafo face d'in zarinat, murmushi tad'an yi, tare da fad'awa jikin mom ta kwantar da kanta gefen kafad'arta, mom ta rungumota tana bubbuga bayanta tace " Zarinat"Naam" ta fad'a cikin muryar kuka

" Nasan ba'a kyauta miki ba bakya son wannan auren amman ki d'aure kiyima iyayenki biyayya in Sha Allah zakici ribar wannan biyayyar "

Hawaye ne masu zafi suka zubo mata"Princess kin san banasan ganin xubar hawayenki d'aga min hankali suke yi please ki daina wannan kukan ko kinasan na shiga cikin damuwa?" Da sauri ta girgiza kai
"Yawwa to kidaina idan ba haka ba zan iya shiga cikin damuwa, abu d'aya nake so dake princess ina san ki kasan ce surukar kirki mata ta gari " Mom taya zan iya hakan bancin ban shiryama wannan al'amarin ba"Shiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii babyna bana son kina fad'in haka nasan zaki iya in Sha Allah zaki iya " da haka mom tayi ta bata kalamai masu sanyi

( Wacece zarinat)
Su biyu ne a wajen iyayen su sannan manyan mutane ne attajirai masu ji da nera, daga ita sai yayan ta, lokacin da aka haifi yayanta bilal, an d'auki tsawon shekaru kafin mom ta sake samun wani ciki, iyayen su naji dasu sosai suna basu gata da kulawa yarda ya dace kuma sun basu tarbiyar da ta tadace, zarinat
Yarinya ce da tunda ta taso bata ta'ba yin k'awa ba ko saurayi ita kad'ai take rayuwar ta itama abun na damunta sai dai ba yarda zatayi tunda allah bai kawo mata ba , sai da aka kaita boarding school sannan ta samu k'awaye, tunda suka kammala school shikenan duk suka rabu
Saboda babu wacce suke gari d'aya amman suna chatting, har group d'in makaranta suka bud'e, haryanzu duk da tana university amman bata da k'awa,
Tana da timetable tasan lokacin da suke da lecture dan haka tun kafin lokacin zataje ta zauna har ayi a gaba ta wuce,

Wannan kenan

🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Bayan dad ya dawo, ammi taje masa da zancen ansar, yace "ina sam hakan bazai ta'ba yuwuwa ba" Ta sanar ma ansar yarda sukayi, ya shiga cikin damuwa da tashin hankali, can wani tunani yazo masa, dan haka ya shirya ya nufi gidan su zarinat, ya samu daddy ya fad'a masa duk abunda ake ciki nak'in amincer da dad yak'i yi akan auren sa da waccen, daddy ya ce yaje Kawai in Sha Allah daga ya Fito daga gida zaije ya samesa akan maganar kuma zai amince,

Ansar ya tashi da farin ciki dan yasan, shi kad'ai ne wanda idan yacema dad ga abunda za'a yi bazai musaba saboda tsananin k'aunar da yake yima d'an uwansa shiyasa baya iya yin musu dashi

( Ansar da zarinat d'iyan wah da k'ane ne Mahaifin ansar shine babba Mahaifin zarinat shi ke bimasa, suma su uku ne ga iyayen su,

Alhaji abubakar, dad kenan Mahaifin ansar, Alhaji sani, daddy Mahaifin zarinat, sai hajiya rabi, k'anwar su)

Ansar su biyar ne a wajen iyayen su maza hud'u mace d'aya, wacce ita ce ta zamo y'ar autar su, kuma ita ke bima ansar

Daddy na fita kamar yarda yayima ansar alk'awari kuwa sai da ya fara zuwa wajen dad, da yaje ma dad da maganar duk da baya iya masa musu akan magana amman wannan sai da yayi dak'yar daddy ya shawo kansa ya amince

☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
Abincin fa baka ciba" Fatima ta fad'a
" Hmmmmmm ni yanzu bata wannan nake ba zo ki d'an ji " Uhm uhm harfa na zuba kar yayi sanyi"lallai naki wasa ne yarinya" ya Mik'e tare da zuwa ya rufe d'akin ya dawo ya cire kayan jikin sa ya rage daga shi sai gajeren wando, yasa hannu ya d'ago ta, tana sanye da hijab dogo har k'asa hannu yasa ya cire hijabin daga ita sai wata y'ar riga lahelahe marar nauyi ita kad'ai ce a jikin, ya janyota jikin sa tare da had'e bakin su waje d'aya, ya tallabe ta suka fad'a gado, suka shiga farantawa junan su...........................................
💋💋ZARINAT ( زرينة )💋💋

Mallakar
Zainab dodo✍️

Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂

_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 3️⃣

Bubbuga d'akin inna keyi da k'arfi " Nashiga uku na nasuru cikin wannan uban zafin zaku shige d'aki ku rufe wai zaka zo ka bud'e k'ofar nan ko kuwa, kajimin d'an banza tasakaka d'aki tana baka kana shanyewa kana tsotsewa zaku bud'e k'ofar ne ko sai na fita na samo majiya k'arfi sunzo sun 'balle k'ofar "

Nasir da sauri ya Mik'e daga saman fatima ya lalubi jallabiyar sa ya zura, itama ta janyo rigarta ta mayar,

Koda ya bud'e k'ofar har ta juya, ai kuwa da sauri ta juyo tana kallansa"Cikin wannan uban zafin me kukeyi a d'aki salon wata cuta ta kamaku azo ana 'barnatar da kud'i wajen neman magani " Yi hak'uri inna bamu jiki bane bacci muke yi"Iyyeeeee lallai yaro mayar dani k'aramar yarinya tunda bansan aikin da nake yi ba ta saka ka d'aki ta rufe ta bud'e maka kana lasa "

Wata irin kunya ce ta kama nasir kamar ya nitse duk da bayau ta saba da fad'in abun da duk yazo bakin ta ba, harta fatima da take bakin k'ofa la'be kunya kamata tayi

"Ina ita tsohuwar munafukar take? " Fatima jin ta fad'i hakan yasa tayi saurin fitowa kanta a k'asa

" To a wuce ga keso can na shimfid'a aje a zauna kuma kusha iskan duniya ace duk wannan iskan mai dad'i da ke kad'awa ku sunk'e cikin d'aki kamar wasu sabbin aure to a wuce" Fatima gaba nasir biye da ita a baya suka nufi keson

" Wannan! Wannan! anya ba'a baka ka shanye ba wannan bita zaizai haka mtswwww" inna ta fad'a tana nuna nasir

Dukan su zama sukayi saman shimfid'ar, sunyi shuru bamai cewa uffan gwauda ma inna tana d'an magana duk da mafi yawancin maganar tata fad'a ne

Suna zaune hadari ya taso nan da nan ruwa suka sauko, duk sukayi d'aki har inna ta biyo su d'akin, dukan su da mamaki d'auke a fuskarsu suke kallan ta, inna ko ta nemi waje ta zauna

Nasir ya d'auko lema yace "Inna gashi ki kunna sai kiyi d'aki kar ruwa su jik'aki kinga dare nayi kuma ruwan nan kamar zasu d'an jima kafin su d'auke" Mai suwa ka aje dan anan zan kwana yanzu fisabillilah wannan ruwan da akeyi masu k'arfi so kake naje d'aki ni kad'ai gina ta fad'o min ko?" Ta fad'a tana kallan fuskarsa "Yi hak'uri ba nufina ba kenan allah ya huci zuciyar ki "Amin"

Fatima ranta yayi mugun 'baci, kar tayi magana kuma ace bata da kunya

Nasir ya juyo ya kalleta, tayi saurin d'auke kanta tare da hayewa gado tayi kwanciyarta tare da jan bargo ta lullu'be jikinta

🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Ansar kwance saman makeken gadon sa hannunsa dafe da waya a kunnen sa "Please stop crying baby" idan banyi kuka ba beb mezanyi yanzu ace harda wata za'a d'aura maka aure bayan ni"Nafa gaya miki komai nima ba'a san raina za'a yi auren nan ba zuciya ta ke kad'ai ce wacce take so da burin kasancewa a tare da ita " Uhmm har kasa naji wani sanyi acikin rai na love you so much my dear" Love you too baby ni ba wannan ba wai yaushe zaki dawo gashi antura anje anyi magana auren nan fa ba jansa za'a yi ba idan ma anjasa da tsawo bazai wuce 1 month ba amman kina ejib zaman ki kamar ba amarya ba "Hhhhhh kai dear next week in Sha Allah zan dawo da yanzu ma jibi zan dawo amman saboda auren nan dayazo girshi yasa mom tace nazauna a can akwai shirye_shiryen da za'a min gobe ma mom zata zo nan"
Chapter 2 · 0% Book details