Sashe 1
Zarinat Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
💋💋 ZARINAT ( زرينة )💋💋
Mallakar
Zainab dodo✍️
Paid book ne
Maison magana dani zata iya tuntub'ana ta Wannan number 👇👇👇
09046495943
Chart only 👂
Dedicated to my daughter Narnah khadija( Muhibbaty) allah ya albarkaci rayuwarki my daughter much love for you fisabillilah ♥️ 😘 ♥️♥️♥️♥️♥️♥️
_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫
Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari
TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 1️⃣
Gida ne mai kyau gwaurgwadan gidan talaka bawan allah mai rufin asiri, d'aki biyu ne a gidan sai dai ba'a jere suke ba d'aya na dubin wannan 'bangaren d'aya na dubin wannan,
Wani mutum ne ya shigo ahankali yake tafiya kamar mai tsoron kar a kamasa, ahankali har ya isa bak'in k'ofar d'aya d'akin, sai da ya juya bayan sa yaga ba kowa yayi sauri ya shige ciki
Zaune take saman sallaya tana lazumi, ganin sa yasa ta saki murmushi tare da saurin Mik'ewa tsaye tana fad'in " Sannun da zuwa" Hannu ya d'aga mata alamun tayi k'asa_k'asa da muryar ta, kana yace " Ina inna ne? " Tana d'akin ta "Ungo kar'bi wannan bara na d'auko takalmi na kar ta gane na dawo" To" ta fad'a tare da sa hannu ta kar'bi ledar hannun sa,
Cikin sand'a ya sake komawa bak'in k'ofar yasa hannu ya d'auki takalmi sa juyawar da zai yi ya koma yaji muryar inna ta doki kunnuwa sa tana fad'in "Allah ya toni asirin ka fito fito naganka" Sumi sumi ya juyo tare da zube takalmin k'asa ya fito, inna ta k'arso wajen
"Wato dan kar insan ka dawo ne shine ka shigo gida kamar 'barawo to allah ya nunamin kai " Inna ba haka ba ne nayi sallama banga kowa ba shiyasa nayo d'aki" Ohh so kake dai kace k'arya nake maka ko toma dai idan ba haka bane su talakmin da ka dawo d'auka ina zaka kai su? " Shuru yayi tare da sosa kai kana yace" Inna daman naga alamun akwai hadari ne shiyasa nadawo na d'auke takalmin kar ruwa ya jikasu su lalace "
Inna ta saki baki tare da d'aga kanta sama"Kai nasuru kaji tsoron allah ina hadari yake wanga waje ga rana nan tarmasisi kace min wai dan kar ayi ruwa takalmin ka su jik'e to naji ina ledodin da ka shigo da su? " Suna d'aki ya fad'a yana k'abar fuska
"To d'auko su Mik'omin nan nagani " Bai ce komai ba kuma bai motsa ba ganin haka yasa inna cewa" Au bazaka shiga ka d'auko ba ne to ni bara nashiga na d'auko ai ba kunyar shiga d'akin nake ba" ta fad'a tare da bangaje shi ta shiga d'akin ya biyo bayanta
Tana shiga bata tsaya ko ina ba sai gaban matar da ta hango ledodin a hannun ta, tana zuwa ta Mik'a hannu tare da fad'in " Mik'o min" Mik'a mata tayi tasa hannu ta amsa, ta bud'e ledar kayan miya ne aciki ta ajiye ta bud'e d'ayar d'aurin nama ne gassashe guda biyu a ciki babba da k'arami, bud'e k'ara min d'aurin tayi ta jefa tsoka d'aya a baki tana fad'in "Wai sau nawa ina fad'a maka ba'a sabama mata da cin dad'i ne idan ka siyo ka rik'a mik'o min na kamma bata wannan ai yayi mata yawa " ta fad'a tana k'ara jefa d'aya a baki
"To inna allah ya bani idan ban siya mata ba wazai siyo mata ai kuma kinga ba koda yaushe bane nake siyowa ba sai idan na samu kud'i ne nake siyo muku " Uhmm haka ne kuma to ku kar'bi wannan" ta fad'a tana Mik'a masa k'ara min d'aurin data bud'e take ci " Inna wannan ai naki ne bakiga wancan yafi yawa ba wancan mubiyu ne wannan kuma ke kad'ai ce" Nagani Nasuru nace nagani amman wannan zan baku wai kai bakasan gata ne nake muku ba bana son ku saba da cin irin wad'an nan abubuwa kamata yayi nida nake tsohuwa na rik'a cinsu baku ba kar'bi ka gani naje naci nawa " ta d'aura masa a hannu ta fice
Juyowa yayi ya Kalli matar sa yace " Fatima kiyi hak'uri kinji in Sha Allah komai zai wuce karki damu "Murmushi ta saki tare da fad'in"Lahhh wallahi babu komai ai gaskiya inna ta fad'a ita ya dace ace ta rik'a cin wad'an nan ba mu ba "Uhmmmmm " Nasir ya fad'a Dan yasan ta fad'i hakan ne kawai dan kar ya damu
"Kar'bi ki ci ni daman ba ci zanyi ba" Miyasa to? " Naji cikina na d'an murda min idan naci sa ciwon zai iya zama babba 'Subhanallah sannu ka sha magani kuwa?" Eh nasha gama sauran a aljihu" Okay sannu to ko zaka k'ara sha ne sai ka d'an kwanta ka huta " Wa ni rufamin asiri na kwanta yanzu kar kisa inna ta shigo d'akin nan ta kasa ta tsare"Hhhhhhhh " Dariya tayi tare da fad'in" kai Abban humaira"Ai kema kinsani sarai basai na fad'a ba " To yanzu dai bara na d'ebo ma ruwa ka k'ara Shan maganin"To shikenan "
Ta cire hijabin ta wuce dan d'ebo masa ruwan, da kallo yabi bayanta har ta fita ya lumshe idanunsa, allah ya gani yana buk'atar kusantar matar sa shine ma dalilin da yasa ya dawo gida amman yasa ba daman yin haka tsaki yaja a k'asan ransa
Har ta d'ebo ruwan ta kamo hanya sai ga inna ta fito da d'akin ta, ta tsare ta tare da fad'in " Ina zaki je da ruwa kuma cikin d'aki ko wani abu kika ci nashan ruwa? " Aah kai masa ne zanyi yasha magani "Au wai daman bai koma ba to meya tsaya yi haryanzu bai koma ba" Cikin sa ke ciwo " To maza kai masa ruwan yasha ya koma kasuwa"To " ta fad'a tare da wuce wa tayi d'aki
Tana zuwa ta Mik'a masa ruwan ya 'ballo maganin yasha ta kar'bi kofin ta ajiye tare da fad'in"Sannu yanzu ya kake ji? "Da sauk'i sosai "ya fad'a tare da janyota ta fad'o jikin sa, bakin sa yakai satin kunne ta yad'an ciza kad'an tayi y'ar k'ara cikin shagwa'ba tana yarfa hannu tace "Da zafi fa"Dagaske? " Kai ta gyad'a masa"Uhmmm i need you maman humaira ta " Zaro ido tayi waje tare da fad'in"Yanzu?" Kai ya gyad'a mata tare da mairairaice face " Tabb kai ma fa kansan inna baza ta bari ba ka bari har anjima idan ka dawo kaji"Wayyoooo ki tausayamin mana nafa dad'e banyi ba " To ai ba laifi na bane inna ce bata bari da mun shigo d'aki tace mu fito waje " Uhmmmmm, ya fad'a yana shinshinan wuyan ta
Inna ce ta k'aullah masa kira" Nasuru! !Nasuru! Kai wannan nasuru" dak'yar ya iya furta kalmar "Naam inna"Uban me kuke a cikin d'akin har yanzu da baka fito ka wuce ba "Gani nan fitowa"Aah karma ka fito ku dangoma a ciki "
Fatima ta tashi daga saman k'afafunsa, ya Mik'e, ta mik'o masa hular sa ya saka, hannu yakai zai janyota tayi saurin jan baya "Muje dan allah kar mu k'ara wani laifin" ba tare da yace komai ba ya kama hanya ya fito ta biyo bayansa
Yayi ma inna sai ya dawo tace "Allah dawo lafiya,har ya kusa fita ta dakatar dashi tare da fad'in"Yawwa idan zaka dawo kad'an biyomin da abu mai d'an dad'i dad'i wanda zan sama bakin salatin nan nawa "To" ya fad'a tare da fita
"Wannan! wannan ! Anyi bita zaizai awajen nan kai gaka dad'ah duk inda mata ta jaka kana can ohhh inda ranka kasha kallo"Inna ta fad'a tare da juyowa ta kalli wajen da fatima take tsaye
"Ke tsohuwar munafuka tsanyuwar uban mekike yi anan baza ki wuce d'aki ba, juyawa tayi ta shige d'aki
"Shegiya kamar wata mutuniyar kirki idan ka ganta simi simi da ita................
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
Had'aden saurayi ne zaune gaban ammin sa fari ne soll kamar balarabe ga kwantacen sajen sa wanda ya k'ara masa kyau ya had'u tako ina,
Marairaice face yayi kamar zaiyi kuka ya kalli ammi tare da fad'in" Ammi please"
"Ansar auren nan fa ko kanaso ko baka so dole sai anyi shi danma ka sani abbanku sun riga da sun yanke hukunci "Yanzu ammi ba abinda zaki iya yi akan maganar auren nan " Babu dan bani da ikon da zan sa ayi kuma bani da ikon da zan hana ayi " Innalillahi haba dad yazakumin haka wallahi akwai wacce zuciyata ke so kuma mun riga da munyi alk'awarin aure a tsakanin mu " iKon Allah to sai a warware alk'awarin shikenan" Ammi dan allah ki taimakemi kimin wata alfarma dan allah ammi na"Tame kenan? " Yawwa ammi dan allah a had'a da wacce nake so a d'aura muna auren nasan idan ke kika jema dad da maganar zai amince amman wallahi ni idan naje ko tsayawa saurarena ma bazai yi ba dan allah ammi ki taimakamin wallahi muna son junan mu sosai"Ammi ta kallesa tare da nazarin kalamansa
Sannan tace "To shikenan zan gwauda amman kasani idan bai amuntaba"zai ma amince in Sha Allah "Allah ya yarda yasa kuma hakan shi yafi zama alkhairi"Amin ammi na
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
Kyakkyawar budurwa ce fara ce sosai, gata da manyan ido eyelashes d'in ta zagar_zagar ga dogon hancinta bakin ta dan dai_dai la'b'banta pink dasu girar ta cikakka fuskarta ma haka, ga fuskar sumul_sumul gwaunin burgewa
Tana sanye da abaya mai shegen kyau tayi rolling kanta da mayafin abaya, hannun ta sanye da wani tsadadden agogo mai masifar kyau, tayi tsaye bak'in k'ofar wani d'aki ta k'wank'wasa k'ofar
"Shigo" Bakin ta d'auke da sallama ta shiga
"Wowwwwww my princess irin wannan kyaun haka ma sha allah tubarakallah " Murmushi Kawai tayi tare da k'arasawa wajen matar ta zauna kusa da ita, tare da gaidata cikin girmamawa, ta amsa