Sashe 8
Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A dai dai ƙofar gidan ya tsayar da motar, kowa ya fito Ashrof da Imran ya baiwa mukullin gidan ta buɗe suka fara fito da kayan ita da Abid, haka ta kwasa Abid ya ɗauki wasu kowa ya fara shigowa gidan, da mamaki kowa ke kallon ƙatuwar bakkon da ke shaƙe da kaya sai suka fara tunanin ko Imran ne ya siyo kayan jarirai amma ban da Sadiya da ta san cewa sun sayi komai na haihuwa dan dama tun lokacin da aka mata scanning aka sanar da su ƴan biyu ne.
"Allah darki jakata ki yafe mini, wallahi abubuwa sun sha kaina na barki duk kin sha sanyi a wofi, kuma ma dai da laifin wannan ja'irin yaro Imirana yana jin sanda na janyoki amma dan mugun hali ya rufe ƙofar ɗakin ban samu na shiga da ke ba" Inna ta faɗa tana kama makamar da ke jikin jakar. Abid kwa mai zai yi in ba dariya ba wai jaka ake cewa tana shan sanyi.
"Inna wai kina nufin jakarki ce wannan?" Ashrof ta jefawa Inna tambayar da mamaki, Sadiya kwa tuni ta buɗe ɗakin da ta karɓi mukulli wurin Ashrof ta shige ɗaki, Mama da Hajiya ma baya suka mara musu.
"To ta uwaki ce in ba tawa bace, wato ku kun raina mutanen ƙauye gani kuke mu ba za mu iya siyen jakar nan ba, to tawa je na siya tun lokaxin tana jaka shida da rabi(1300) Ba yanzu da farashinta ya faɗi ba.
"Ni fa ina nufin kayan da kika kwaso a cikinta ba wai tsadar jakar ba mai za ki yu da kaya har cikin jakar nan" Tunanin Ashrof kar Inna ta ce sati guda za ta yi sai an yi suna da kuwa sun banu.
"Ikon Allah haka fa Malam ya titsiyeni wai ina zani da kaya haka kamar wanda zan ƙaura, yo Allah na tuba kwana arba'in nan ne? Ga lokacin sanyin nan hatta bargona sai da na ɗakko saboda Imirana mai mugun halin nan" Ta faɗa tana zige zip ɗin aikuwa ta yi ido huɗu da abin sallarta. Wani salati ta rafka.
"Ni Azumi zuwa birni yau bai min rana ba, yo ina daÉ—i an manta da faÉ—ar ubangiji, ashe duk abin nan da ake banyi sallah ba, ba azahar ba la'asar ga magriba ta kawo kai" Ta faÉ—a tana janyo abin sallar daga ciki.
"Wai Inna kwana arba'in ɗin me za ka yi da kaya niƙi -niƙi haka har da su bargo?" Cewar Ashrof tana kallon Inna Abid kuwa har riƙe ciki yake dan tuni ya harbo jirgin Inna "Lallai akwai dirama a gidan nan" Ya faɗa a ransa yana ƙara darawa.
Ashrof dai baki sake take kallon Inna dan ita ta gane manufarta kawai dai so take Innar ta amsa da bakinta dan ta ƙara tabbatarwa.
"Ka ji yarinya da tambayar ƙwaƙwa yo meye baƙo a nan da baki fahimta ba, ZAMAN WANKA na zo in yiwa jikata mana" Inna ta faɗa, hakan hankalinta kwance, hakan ya yi dai dai da shigowar Imran da ya ji maganar Inna tamkar saukar aradu a kunnuwansa, har wani amsa kuwwa maganar ta masa a kunnu, sakin ledar maganin hannunsa ya yi wacce ya biya wani kemis ya siyo...
Next page 😂😂😂
Ba a fara ba zaman wanka🤣🤣🤣
Masu son grp na Æ´ar zaman wanka
09030283375
.......😂😂😂
Mai son shiga grp É—in dan samun cigaban buk É—in ya mn mgn 09030283375 Wtsapp only
🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩â€ðŸ¼
(KWANA ARBA'IN)
NA
MAMAN AFRAH
🅿ï¸5ï¸âƒ£
"Zaman wanka?" Imra ya tambaya a fusace.
"Eh zaman wanka mana ko a kan ka zan zauna da ka wani hayayyaƙo min kamar wani ubana, ko da dai da duka zaka hauni Imirana" Inna da ta miƙe tsaye daga durƙuson da ta yi tana riƙe da sallayarta.
"Haba Inna wai mai yasa kike haka ne, Yaya Imran fa kamar siriki yake a wajenki" Cewar Ashrof kamar ta saki kuka ganin abin da take yiwa Imran É—in a gaban abokinsa gashi mahaifiyarsa a gidan amma Inna duk bata gansu ba.
"Ashrofa, Ashrofa, Ashrofa, kin ji na kiraki sau uku to wallahi ki fita daga sabgata ko ke ce uwata mai daddawa da zaki takura min ko uwaki Rakiya ta yi kaÉ—an ta ce za ta sani abin da ban yi niyya ba"
Wani takaici ne ya sanya Ashrof juyawa da sauri ta shige ɗaki, Imran kuwa juyawa ya yi ya fice daga gidan, Abid da ya juya yana ƙunshe dariyarsa zai marawa Imran baya.
"Kai yaka ɗan nan, yo kai sunan naka ne wahalar faɗa gereshi, ka ce ba Abida ba, to koma dai menene zo ɗauka min jakar nan ka shigar da ita ɗaki, dan babu dalilin da zai sa ta ƙara zama a waje sanyin duniya ya ƙare a kan ta" Ta faɗa tana haɗa mayafinta da abin sallar ta rataye a kan igiya.
"To Inna" Abid da bashi da zaɓi sai bin umarninta dan haka ya ɗauki jakar ya shiga ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. Hajiya ce ta amsa masa, shi ma gani duk sun yi jingum-jingum sai bai ce komai ba ya ajiye jakar ya fita, su duka suka bi jakar da kallo, suna jinjina ƙoƙari irin na Inna dan basa ce wauta ba a shiga uku.
BanÉ—aki ta wuce ta É—auro alwala ta shimfiÉ—a sallayarta a waje ta shiga gabatar da sallolin da ake bin ta, tana sallar amma kunneta a É—aki.
A can cikin ɗaki kuwa Hajiya ce ta katse shirun da cewa "An kawo tukunyar dafa ruwan wanka babba irin wacce ake dafa abincin gidan suna gata can a waje da kuma itace duk suna nan, dama yadda muka tsara da Imran cewa tun da gidana babu nisa da sassafe zan ke zuwa ina ɗora ruwan wanka in wanki jarirai, ita kuma Ashrof take zuwa tana wuni shi ya ce zai ke kwana da su, amma yanzu tunda Inna ta zo ZAMAN WANKA sai a ruguje wannan tsarin" Ta faɗa tana kallon Mama da gabaɗaya damuwarta ta bayyana a fili ƙarara.
"Haba Hajiya ya zaki ce haka bayan ga tsarin da aka yi kin san dai gidan nan ciki da falo ne kawai to shin a ina Inna za ta zauna?" Cewar Ashrof cikin sanyin murya.
"A gidan uwaki zan kwana, na ce a cinyar uwaki zan kwana Asharofa, wato ma saboda rashin ta ido har zama kuke ku yi da ni, Allah na tuba nawa ne kwana arba'in kwanci tashi asarar mai rai kamar yau ne fa za su ƙare, ban da abinku ma yarinyar da ta haifi ƴaƴa biyu ai kamata ya yi a yiwa Hassan arba'in ɗinsa da ban ta Hussainin ma da ban. Amma shi ne kuka zauna kuna ɗaya biyu, to ni nan gani nan bari farar tunfafiya ko sama da ƙasa za su haɗu babu yadda za a yi in fasa ZAMAN WANKAN NAN" Inna da idar da sallarta kenan ta faɗa tana tsaye a bakin ƙofa dama tana sallar amma kunnuwanta a wajen su Hajiya dan ta ji waye mai son ta zauna waye kuma wanda bai goyon bayan zamanta a gidan.
"Allah baki haƙuri Inna wannan fa tsari ne da aka yi tun kafin a san da zuwanki ne aka yanke wannan maganar"
"In ma ba a san da zuwana ba ai yanzu an sani, kuma ita Asharofa da take cewa ciki da falo ne a gidan menene aibu tun da har ciki biyu ne wato ɗakuna biyu, shi Imirana ya ɗauki ɗaya mu ma mu ɗauki ɗaya ni da mai jego da jarirai, ke ko ma ciki ɗaya ne a gidan nan sai dai muke yin kai da ƙafa da Imirana ehe"
Sadiya jin maganganun Inna suka tuna mata da maganar Imran lokacin tana da tsohon ciki.
"Ni fa wallahi ban son wannan al'adar da ake yiwa mace idan ta haihu ta ZAMAN WANKA saboda bana son abin da zai rabani da ke ko na second guda ne da, bare ma ba mu da wadatattun É—akunan da za a zo gidan nan a zauna, ni zan ke muku komai ke da jariri daga magriba zuwa wayewar gari da safe Hajiya tun da kusa muke sai ta zo ta musu wanka ta miki abin da ya dace in ya so Ashrof sai take zuwa tana wuni tana yin girki"
Halima kin ci wake da shinkafar ki" Ta katsewa Sadiya tunani tana ƙarasowa kusa da ita ta zauna wani takaici ne ya tare mata a zuciya.Ganin Sadiya ta ƙyaleta ta ce
"Oh ni Azumi na ji na gani an kashe tsohuwa da ranta, ke ma bakya son zaman nawa ko me? Lallai in da ranka kasha kallo, yanzu ke Halima ZAMAN WANKAN ne bakya so a miki saboda ke mahaukaciya ce ke, kin manta gabaɗaya jikin ki faci ne sai fa da aka ɓarka ki kamar wata takarda aka maida aka ɗinke kamar wata ƙwarya, sai da aka miki ɗinki bakwai. So kike a barki daga ke sai wannan kurman yaro a gida cikin dare ya haike miki ya ƙara ɓarka ki, gabaɗaya ki tashi a aiki, dan da ganinsa fitinanne ne ido fici-fici yawa na ƴan cena (China) To wallahi kika sake aka barku ya nemi ya shiga rijiyar jikin ki kika bashi dama wallahi sai dai ke ba wata dan wallahi ko likitoci basa iya ɗinke ki ba tun da wurin ɗanye ne sharaf kuma wani cikin ne zai shiga nan da wata shekarar in dawo suna haɗe da ZAMAN WANKA amma in ina nan aradu ko hannunki bai isa ya kama ba bare ya shiga jiriyar ma, amma dai bari in yi shiru ciki ba dan tuwo kaɗai aka yi shi ba" Ta faɗa tana tashi ta nufi kan frige ɗin falon ta shiga bubbuɗe ledojin da Imran ya kai asibiti.
"Kai kurma ma ya san dai dai wallahi ashe siyayya ya iyo mana ta pan zaman jinya ɗan arziƙi, kun ga fa ta faɗa tana nuno musu hanta ce da kayan marmari (Fruit)" Da soyayyiyar doya, da ƙwai cikin ƙwai sai kuma maltina guda biyu masu sanyi"
"Ku ɗaɗɗauka " Ta faɗa lokacin da ta ɗauki hanta ta sanya a baki, shi ne ta miƙa musu takarda.Gabaɗaya babu wanda ya karɓa.