Sashe 11
Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Daman ma sumar da ke ta yi a kai ki asibiti mu ga ta yadda za ki yi ZAMAN WANKAN" Ya faÉ—a a zuciyarsa a fili kuma ya ce.
"Eh za a gyara ne"
"Ai gwara a gyara amma ni yanzu ai ina ga sai ka samo min madarar ruwa gwangwani uku na sha"
"To" Kawai ya ce ita ma kuma sai ta ja bakinta ta yi shiru.
"Hajiya ta ce sai gobe za ta yi wanka sbd kumburin jikinta in ji likitoci" Ya faÉ—a a hankali kamar mai raÉ—a.
"Eh sai gobe har yaran ma ai sai goben tun da an goge musu jiki da zautun kuma saboda mura kuma yanzu ai dare ya yi" Mama ta bashi amsa.
"Allah kaimu" Cewar Imran kuma dama ya yi hakan ne dan Inna ta ji kar ta je ta tarki yiwa yaran wanka.
"Halima ki sa yaron nan a nono mana tun da ya tashi ko babu ruwan nonon in yana tsotsa zai zo" Inna ta faÉ—a tana kallon Sadiyar.
"To" Ta ce Mama ta miƙa mata Hussainin ta sanya shi a nono.
"N a dama za ki fara bashi, kuma koyaushe za ki bashi kike fara yin bismillah kafin ki bashi, sannan kike lura wajen bashi nonon dan kar ya danne masa hanci in yana sha, kuma sai kin tiƙe nonon a hannunki in zaki basu kin san nauyi yake musu idan aka bar musu ba a riƙe ba" Cewar Mama tana ɗan nuna mata yadda za ta yi.
"To Mama"
"Wayyo Allah na wallahi ciwo"
"Haka za ki daure"Cewar Mama.
"Ke ma Rakiya da wani abu yo wane haka za ta daure, bada nono ai ya zama wajibi ciwo ko dole ne, Allah na tuba kika haihu ma, ai fitowar É—a shi ne babban abu" Cewar Inna.
Babu wanda ya tanka, Sadiya kwa sai rurruntse ido take jin zafin da nonon ke mata da yaron ya kama kan.
"Ashrof ba Inna Hassan É—in mu tafi kin ga har an yi ishsha'i" Cewar Mama.
Gaban Inna ne ya bada wani diririmdim, jin wai an ce a bata Hassan.
"Ni har ga Allah tun da aka ce yaron yana da fatar miciji a bayansa nake jin tsoronsa gashi ni ce MAI ZAMAN WANKA dole dai ni zan wankeshi, wayyo Allah na shigenge" Inna ta faÉ—a a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.
"Yo ku bari mana a ɗan jima muna hirarmu ai kwa rage dare, ko kuma in Halima ta gama shayar da Husainin sai in karɓeshi ki bata Hassan ɗin shi ma ta bashi nonon.
"Haba Inna tun jiya da dare fa muka baro gida muka zo nan kwanan zaune muka yi, tana naƙuda da sassafe muka tafi asibiti dama mun je asibitin a daren suka ce da saura mu koma gida kuma yanzu har an yi ishsh'i bamu tafi ba tun da dai Allah ya sauketa lafiya yaran ma suna cikin ƙoshin lafiya kuma gaki ai sai mu je gida sai kuma gobe in muna raye" Cewar Mama cikin sanyin murya dan ta harbo jirgin Inna kawai dai Hassan ne bata son karɓa.
"Ni Azumi na ɗakko ruwan dafa kaina" Ta ce a ranta a fili kuma ta yi dariyar yaƙe ta ce.
"Kayya Rakiya, ai ban sani ba, to, to, babu komai ai, da yanzun da anjiman duk É—aya ne Allah bamu alheri"
"A gaba ma wallahi sai kin gwammace ko Kano baki zo ba bare gidan Imran" Cewar Imran a ransa.Ya tashi ya fita.
"Amin Inna" Cewar Mama.
"Inna ga mijinki Hassan" Ashrof ta faɗa tana dariyar ƙeta a ranta, a fili kuma tana danne dariyar yadda ta ga Inna na wulwulga idanu.
"Ba dai wannan rabi da rabin ba, rabi mutum rabi maciji, mijina Malam yana can a ƙauye" Ta ce a ranta a fili kuma ta ce.
"To ai ni Husainin ne mijin Hassan É—in na sake shi"
"A'a Inna ai aure da ke babu saki, ke da shi mutuƙaraba" Ashrof ta faɗa tana ɗorawa Inna Hassan a cinya, Inna ji ta yi kamar Ashrof ta ɗora mata miciji a cinya haka dai ta daure ta riƙe yaron gabanta na duka uku-uku.Sallama suka musu suka tafi, Inna dai ko sallamar tasu bata karɓa ba.
"Halima kar fa a shiga haƙƙin yaron nan ki karɓeshi shi ma ko bashi nonon" Inna da ta sanya hannu ta ɗan jijjiga yaron ya buɗe ido dama da niyya ta yi hakan.
"Inna shi ma fa wannan É—in ba sha yake ba, kawai dai ciwo nake ji"
"Yo ai dai shi ma ko fatar ce ya tsotsa dan kar Allah ya kama ki kin nuna musu banbanci" Ta faɗa tana ta Allah -Allah Sadiya ta karɓi Hassan, Haka ta zarewa Hussaini nono, aikuwa ya tsallara ihu, a hakan Inna ta miƙa mata Hassan ɗin take lallashin Hussainin.
Bayan sun yi bacci yaran Sadiya ta sanya kowanne a gadonsa ta kwantar tare da sanya bargo ta lulluɓesu. Zuwa can Imran ya dawo gidan dan dama yana waje a zaune takaici ya hanashi shigowa gidan, dan shi bai saba zuwa yawo ba. Da dai ya gaji da shaƙar sanyin sai ya kulle gidan ya shigo, lokacin Inna jakarta na gabanta ta fito da bargwanta tana maida kayan. Yana shigowa bayan ya yi sallama Sadiya ta amsa sai ya wuce bedroom Sadiya ta tashi ta bi bayansa.
"Ba ni da raƙumi da akala ba" Cewar Inna lokacin da Sadiya ta bi bayan Imran.
Tambayarsa ta yi abin da zai ci, dakyar dai ta lallaɓashi ya amince zai sha fura, Inna da ke falo ta ce.
"Wa ankarahu ake ankara dai, ana yi dai ana zaman ƙuda da buzuzu, wato zaman doya da manja" Ta faɗa cikin ɗaga murya. Suna jin ta babu wanda ya yi magana, har Sadiya ta fito ta ɗauki furar a falo, da yake a cikin kwanon sha take haar luday akwai a cikin hannun frige ɗin haka ta ɗauka ta koma cikin bedroom ɗin Inna dai sai taɓe baki take.
"Bari dai in cire atamfar nan ta akwatin ƙarfe kar in kwanta da ita alharamun giya a gidan liman" Ta faɗa tana ɗakko wata doguwar riga marar nauyi a jakarta ta sanya ta linke atamfar ta sanya a jakat ta rufe ta ajiyeta gefe. Bayan ta koma ta kwanta jin tsit babu motsin su ta tashi cikin sanɗa ta je baki ƙofar bedroom ɗin ta tsaya ba tare da sun sani ba, ta kama labule a hankali ta ɗan leƙa. Imran ta gani zaune a bakin gado sai Sadiya da ke zaune kan bed side drower tana bashi fura a baki. Da sauri Inna ta saki labulen ta dawo ta zauna daɓas dan ita hankalinta bai kwanta ba da kasancewarsu su kaɗai a cikin ɗaki.
"Ni Azumi ba da ni ba wai gyaɗa a kabari, ya za a yi ina gidan nan ni da na zo ZAMAN WANKA in bari a yi aika-aika ai yadda na gan su ɗin nan kusa da juna a zaune shi a bakin gado ana jimawa sai dai in ji sun rufo ƙofa" Ta faɗa a zuciyarta, sai kuma ta ce.
"Halima, Halim, Halima" Har sau uku amma bata fito ba kuma bata amsa ba Sadiya kwa ta tashi za ta fito sai Imran ya riƙe hannunta ya marairaice mata, hakan ya sa bata fito ba shi kuma da gangan ya yi hakan dan kawai ya ga abin da Innar za ta yi.
"Sa'adiyya, Sadiyya, Imirana, wai bakwa ji na ne" Ta faÉ—a tana tashi tsaye daga zaunen da take.
" Ko dai basa cikin hayyacinsu ma dai, kar fa kudirarren yaron nan ya je ya ɓarkewa yarinyar nan ɗinkin da aka mata, ita ban da ma shashanci jiki duk faci amma za ta biye wa namiji" Ta faɗa tana tafa hannuwa, jin shirun ya yi yawa sai ta nufi ƙofar ta kusa zuwa jikin labulen sai ga Sadiyar ta fito da sauri ta koma ta zauna a kan kujerar kusa da hanyar bedroom ɗin ta wayance dan da a kan kujerar wajen bakin ƙofar falo take a zaune.
"Inna gani" Sadiya ta faÉ—a tana haÉ—e rai.
"Dama na ji shiru ne nake kiranki"
"Haba Inna shirun me kuma me zan miki to"
"Babu komai É—iyar nan taimakon ki zan yi dan kar ki hau dokin zuciya yaron nan ya kai ki ya baro ki"
"Haba Inna wai wacs magana kike haka ne, kar fa ki manta mata da miji muke fa"
"Yo dan an ce mata da miji kuke sai me to, ai yanzu kin haramta a gareshi"
"In ji wa"
"To halasta masa kan ki wallahi kika sake ya janyo ruwa a rijiyar nan Allah sai kin É—auka a injin markaÉ—e aka saka ki"
Takaici ne ya sanya Sadiya ta juya ta koma ta bar Inna tana sababi ita kaÉ—ai.
Masu son grp zaman wanka 09030283375
Masu tambayar Beelal ina baku haƙuri sai ranar monday in sha Allah za a posting.
🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩â€ðŸ¼
(KWANA ARBA'IN)
NA
MAMAN AFRAH
🅿ï¸7ï¸âƒ£
Inna na nan zaune abin duniya ya ishe ta, jin sun yi ɗif basu da alamar fitowa, wajen gadajen yaran ta nufa sai da ta ƙare musu kallo ta gane Husainin dan bata so ta taɓa Hassan, hannu ta sanya ta ɗan jijjigashi aikuwa ya ɗan motsa ya yi ɗan kuka kaɗan.
"Ka yafe min ɗan nan ba da niyya zan yi ba ban son na ɗauki alhakinka, jihadi zan yi in ƙwato waccen shakatafin gyatumar taka, da babanka ke neman wuce gona da iri" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ce
"Halima zo É—an nan ya motsa"
Sadiya da dama ta ji ɗan kukan da Hussainin ya yi, hakan ya sanya ta ɗakko kwanon furar da Imran ya sha dan ta fito da shi, tana zuwa idanunta suka sauka a kan Inna da ke ƙoƙarin ƙara taɓa Hussainin da zuwa lokacin tuni bacci ya ƙara surarsa ya yi awon gaba da shi.
"Dama na yi zaton hakan, haba Inna yanzu meye amfanin tashin yaron nan"
"Ya koma bacci abinsa fa Halima, tashin sa ya yi amfani mana, tun da gaki kin fito dama kuma burina kenan"