← Book details Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 19

Sashe 13

Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah da hikima yake, shi yasa ya sanya mata ke zubar da jini bayan sun haihu (Jinin haihuwa) Amma ba dan haka ba Allah kaɗai ya san yawan matan da matansu za su ke maida musu mahaifa nan da nan (Su yi tarayya da su) Musamman in aka samu kudurarru masu jaraba, tuni za su haƙƙewa mai jegon saboda basu san wahalar naƙuda ba, shikenan mata su ringa haihuwar kwenika" Ta faɗa tana gyaran ɗaurin ɗankwalinta ta taso ta fito. A hankali ta leƙa falon dan tabbatar da Imran ɗin yana bacci, ganin filon da ya jera sai ta ɗauka shi ne ke bacci da yake ma fitilar falon ma a kashe take bata kunna ba dan bata so ma ya tashi.

Haka ta nufi bayin gadan-gadan har tana haɗawa da sauri jin fitsarin ya matseta. Imran da ke cikin bayin jin takun Inna yasa ya ƙara jingina a jikin bangon da ke kallon ƙofar bayin ya baza hannu ya sanya hular sai ya sunkuyar da kai. Inna jin fitsarin na nema zubo mata ganin fitilar a kashe sai bata kunna ba kawai ta shige bayin. Sai da ta je tsakiyar bayin kawai sai ganin abu ta yi fari ƙal,kallon abun ta yi da kyau ta ga mutum ne a take ta ji ƙafafunta sun fara karkarwa, hannu ta miƙa ta dafe jikin bango tana cewa.

"Innahu min sulaimana wa innahu bismillahir rahmanir rahim, ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba" Ta faɗa har lokacin tana karkarwa, so take ta gudu amma ƙafafunta sun ƙi bata dama, ji take kamar a wurin aka dasa ta.

Imran ganin tarkonsa ya kama tsuntsu ya ce a ransa.

"Mu zuba ni da ke mu gani, ba dai kin ce ke ZAMAN WANKA za ki yi ba ai ga wurin nan"

A hankali ya fara takowa yana nufota, dama ƙafarsa ko takalmi babu, Inna ganin aljani ya doso ta a nata tunanin kenan, sai haƙoranta suka fara haɗuwa da juna kafkafkaf, gaba ɗaya ta tsure ji take aljanin nan yana dafa ta mutuwa za ta yi, ji ta yi kawai fitsarin nan ya ƙwace mata, yana bin ƙafafunta, aljanin na matsowa a hankali ita kuma faɗuwar gabanta na tsananta. Imran kwa duk nufotan da yake bai ɗago kan sa ba, jib Inna ta zame ta zauna ƙafafunta sun kasa ɗaukanta, ganin dai da gaske aljanin na miƙo hannu hakan yasa ta fara rarrafe domin ƙwatar kan ta, tana rarrafawa yana ƙara matsota har suka fito daga bayin, dan Imran rage tsawo ya yi sai ta ga ɗan guduldili ne aljanin, tana rarrafe tana salati dan so take ta yi ihu amma ta kasa gabaɗaya bata da karazana.

Ta fito daga bayin yana biye da ita tana rarrafawa duk ta zubar da takalmanta, suna fitowa ta juya tana rarrafe dan rarrfenma dakyar take yi sai Imran ya yi saurin juyawa cikin sanɗa ya koma cikin bayin, Inna sai da ta kusa shiga falon da rarrafe ta waiga aikuwa sai ta ga babu aljanin hakan ya sa ta ɗauka ɓacewa ya yi.

Hakan ya sanya ta cigaba da rarrafen duk da tana jin kamar aljanin zai rafkota ya maidata bayin. A haka ta shigo falon, kallon katifar Imran ta yi ganinsa lulluɓe yasa ta cigaba da rarrafe dan ba za ta tsaya a falo ba tashinsa sosai take jin tsoro, haka ta wuce cikin ɗakin tana jin rigarta jigif da lemar fitsarin da ta saki.

```Imran```

Tun da ta waiwaya ta ga baya nan, sai ya laɓe daga bayin ya cire kayana ya bar singlet da gajeran wandonsa, sai da ya dai dai ci Inna ta kai bedroom cikin sanɗa ya dawo falo ya ɗauke filillikan ya mayar da su mazauninsu ya sanya kayan da ya cire a ƙasan filo ya koma ya kwanta ya rufa.

```INNA```

Gadon ta kama hannunta nankarkarwa so take ta hau amma ta kasa hawa ga bakinta ya kasa magana, hannu ta kai ta kamo ƙafar Sadiya ta kama babban yatsan Sadiya take ja, dan bakinta ba zai iya kiran sunan Sadiyar ba.

Sadiya da gabaɗaya ta yi nisa da bacci bata san Inna na jan yatsanta ba. Imran ya tabbatar yanzu Inna taa cikin halin ƙaƙanika yi dan haka ya miƙa ƙafarsa ya bugi jikin kujera, ai Inna na jin ƙaran sai ta ɗauka aljanin ne ya biyo ta, ganin Sadiya ko motsi bata yi kamar gawa hakan ya sanya Inna ta lallaɓa ta shige ƙasan gado...

Masu son shiga grp zaman wanka 09030283375

🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼

(KWANA ARBA'IN)

NA

MAMAN AFRAH

🅿️8️⃣

Inna sai numfarfashi take, nishinta na fita ta kwanta lifet da ribda ciki, kawai jiran tsammani take, dan duk tunaninta aljanin ne ya shigo kawai neman inda take yake yi.

"Allah ka gani ZAMAN WANKA na zo, hanyar zumunci ne, idan kuma ba aljani bane mala'ikan mutuwa ne Allah ka yafe min kura-kuraina, ka haÉ—a mu a aljanna da Malam, ka sa ni kaÉ—ai ce matarsa a can ban da Tasalla" Cewar Inna a zuciyarta.

Gabaɗaya ta sanya hannunta ta riƙe ƙafar gadon, duka hannayenta a jikin katakon suke, dan gudun kar aljanin ya ɓanɓarota daga ƙasan gadon. Har aka fara kiran assalatu Inna tana ƙasan gado Sadiya kwa bata falka ba, saboda kwana da ta yi ta waye tana gwagwarmayar naƙuda hakan ya sanya ta gaji bare haka nan ma nauyin bacci gareta.

```IMRAN```

Tun da ya buga ƙafarsa a jikin kujera ya ƙara razana Inna, jin ɗif a ɗakin babu motsinta hakan ya sanya ya gane ta mugun tsorata dan haka bai ma san lokacin da bacci ya ɗaukesa ba. Sai dai lokacin sallah ya yi alerm ɗin wayarsa ya fara masa sallama, tashi ya yi ya kunna fitalar falon ya fara kiran Sadiya sau boyu kawai ya kirata dama ba dan ya tasheta ya yi kiran ba dan Inna ta jiyo muryarsa ya san tana nan har lokacin a tsorace dan haka ɗakin ya nufo ya zo ɗaukan kayansa dan ya yi shirin tafoya masallaci. Daga setin da Inna take a ƙasan gado daga nan drower kayansa take, haka ya buɗe ya sanya kayan da ya yi amfani da su wajen tsorata Inna ya ɗora musu wasu kayan ya ɓoye su yadda ba za a gani ba ya ɗakko wami yadi riga da wando, ya juyo ya fito daga ɗakin sai dai ya yi matuƙar mamaki da Inna ta ji shigowarsa amma bata fito ba, kuma ya tabbatar idonta biyu, dan babu yadda za a yi bacci ya ɗauketa dan bata cikin kwanciyar hankalin da bacci zai ɗauketa.Sosai abin ma ɗaure masa kai da ya ga bata kan gadon, yana tunanin inda za ta ɓuya a ɗakin sai da ya je zai buɗe drower ne ya hangi rigarta a ƙasan gadon aikuwa kamar dai ya yi ta ƙyaƙyata dariya.

"Ashe ma abin naki tsoro ne ba dai ke MAI ZAMAN WANKAN da za ta addabi mutane ba ma ji ma gani wai an rufe tsohuwa da ranta" Ya faÉ—a a zuciyarsa ya fito falo ya sanya yadin da ya É—akko ya fita domin yin alwala ya tadi masallaci.

```INNA```

Tun da Inna ta hangi hasken fitilar falo gabanta ya shiga faÉ—uwa dan duk tunaninta aljanin ne.

"Ya Allah ka makantar da aljanin nan kar ya ganni, idan kuma shi ba aljani bane mala'ikan mutuwa ne ka sa in cika da imani, ka haÉ—a ni a aljanna da Malam Allah ka sa ni kaÉ—ai ce matarsa a can ban da Tasalla" Ta faÉ—a hawaye na gangarowa daga idanunta.

Har sai da ta ji Imran ɗin yana ƙwalawa Sadiya kira hakan ya tabbatar mata ba aljanin bane Imran ne ya tashi. Ta san jin Sadiya bata amsa ane ya taho ɗakin. Amma sai ta ƙyaleshi har ya gama uzurinsa ya fice.

"Babu abin da zai sa na faɗa maka akwai aljani a bayi, sai ka je kaima kun yi ido huɗu da shi ka gan shi ra'ayal aini, sannan in ga ƙarshen kurmanci dan na san yau in ka rinƙa ƙwanzama uban ihu sai duk maƙota sun ji ka sai ka gwammace kiɗa da karatu, dan yaro bai san wuta ba sai ya taka, yau za mu ga ƙaryar rainin wayo" Inna ta faɗa a ranta tana hasashen yadda Imran ɗin zai yi idan ya ga aljanin.

Shiru -shiru bata ji ihun Imran ba, abin ya bata mamaki dan ita mugunta ce ta sa ba za ta faɗa ba ma bare ya fs zuwa bayin, tana a haka sai ƙaran buɗe ƙofar gida ta ji ya fita masallaci, sosai ta girgiza da hakan.

"To ko dai aljanun gidan ne basa yiwa masu gidan komai si baƙi, ko dai tun da ya ɓace lokacin da na waiwaya bai ƙara fitowa ba shi sa Imran ɗin bai ganshi ba?" Ta rinƙa saƙa-da warwara zuciyarta.

Har sai da gari ya ɗan fara haske sannan ta ji ƙaran ƙofar gida alamar Imran ya dawo daga masallaci, kamar jiran dawowarsa yaran ke yi, uka tashi suka fara kuka a tare. Hakan ma ya yi dai dai da shigowarsa ɗakin ya fara tashin Sadiya daga bacci, haka ta tashi tana ɗan yatsina fuska tare sa murza idanu irin na wanda ya tashi daga bacci.Haka ta ɗauki Hassan ta yi bismillah ta sanya shi a nono, shi kuma Imran ya ɗauki Husainin yana jijjigashi a kafaɗarsa. Sai bayan yaran sun ɗan yi shiru ta lura Inna bata kan gadon.

"Inna har ta tashi sallah kenan" Ta tambaya tana kallon Imran.

"Sa'adiyya, Sa'adiyya" Inna da ke ƙasan gado ta shiga kiran sunan Sadiya.

"Ikon Allah daga ina nake jiyo muryar Innar ne?" Ta faÉ—a tana É—an waiwaye -waiwayen É—akin dan ta ni muryar a É—akin ne.

"Halima kin ganni nan" Cewar Inn jin bayanta ya tokare da jikin katako ta ma kasa ko da yinƙurin fitowa daga ƙasan gadon dan ta san dai yanzu aljanin ko yana nan dai, ba zai zo a tun ba ga masu gidan a nan kuma gari ya waye shi kuma zuwan dare ya yi jiya.

"Ina kike Inna?"

"Ko a cikin drower take" Cewar Imran a fili a ransa kuwa sai dariyar ƙeta yake yiwa Inna.

Hannu Inna ta ɗauke daga riƙon da ta yiwa katakon, ta sanya a jikin filankin gadon ta shiga bugawa da hannunta.
Chapter 13 · 0% Book details