Sashe 7
Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Sannunku kun ji, sannunku da ƙoƙari yau kowa ta san yadda ta zo duniya da irin rigiji gabjin da uwarta ta yi lokacin haihuwarta, da wanɗanda yau ne suka yi ta fari da kuma wanɗanda sakewa suka yi, sai a wasa haƙora kuma domin cin sadakin gado "Ragon suna" Cewar Inna da ta buɗe muryar tana ta faɗa wa matan da ke wurin su kwa mai za su yi in ba dariya ba. Hajiya kwa gadon Sadiya ta wuce, ta bar Inna tana ta yawan yi, kallon nurse ɗin nan Inna ta yi ta ɗazu ganin tana darawa kan maganar da Innar ta yi Inna ta mere baki ta ce
"To fa harda su kaza a cin danƙo?' Bata jira cewar nurse ɗin ba ta wuce gadon Sadiyar tun kafin ta ƙarasa ta fara rafka uban salati
tana cewa.
"Wayyo Allah sannu Halimatus Sa'adiyya, sannu kin ji"
Wani uban bugawa kirji Sadiya ya yi da ta ga Inna.
"Na shigesu mai Inna ta zo yi kuma daga haihuwar ba dai ta zo bane har suna, in kwa haka ne to tabbas akwai matsala dan ta san kafin ranar sunan nan sai ta ginshi kowa" Ta faÉ—a a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.
"Yawwa Inna" Ta faÉ—a a hankali kamar bata so.
"Ikon Allah ya wuce mamaki sai kallo, yanzu ke ma Halima halin mijin naki kika koya? Magana kamar mutum baya so ni na kasa ganewa gayu ne hakan ko kuwa rainin hankali ne, ace Allah ya tsaga maka baki dan kake magana amma kake tauyewa baki haƙƙinsa" Cewar Inna lokacin da ta ƙaraso ta samu gefen gadon ta zauna da yake Halimar ma a zaune take ta jingina da filo.
Shiru Sadiyar ta yi bata ce komai ba.
"To ni in baki so zuwana ba in tashi baki alekum in koma inda na fito, dama dan ke zan yi, dan ɗana kuma marigayi, ai dai yau kin ɗanɗana haihuwar kin ji kin banbance tsakanin aya da tsakuwa kin kuma ƙara sanin muhimmancin ƴaƴa a wajen iyayensu da na iyaye a wajen ƴaƴan ma baki ɗaya.
" Ni ban ce ba Inna"
"A'a to in ma bakya so ai ba faÉ—a za ki yi ba, dama abu É—aya ya kawoni amma kuma yanzu ya zama biyu, zuwa na yi in miki barka in miki jaje duk a tare"
"Jaje kuma Inna?"
"Yo jaje mana, barkar Hussaini zan miki, sai kuma in miki jajen Hassa...
Ai Inna bata ƙarasa ba sai Sadiya ta fashe da wani kuka mai cin rai, dan ita zaton ta Hassan ɗin mutuwa ya yi.
"Haba Inna ya zaki sakata kuka?" Hajiya Amina da take haɗawa Sadiya shayi dan ta sha ta ji ƙarfin jikinta ta faɗa cikin fusata dan abin na Inna ya fara wuce gona da iri.
"Yo ba dole ba in mata jaje ba wannan yaro da fatar bayansa take ta miciji ai abin a jajanta ne, ko ba haka ba bayin Allah?" Ta faɗa tana kallon mutanen ɗakin da wasu hankakinsu ke kan su babu wanda ya ce wani abu wanda ta basu dariya dai sun ɗan dara a ɓoye wanda kuma ta basu haushi sun ji haushi.
Dafe kai Sadiya ta yi tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya jin ba mutuwa ya yi ba dan ita sosai take jin son Hassan É—in har ya fi na Hussainin saboda baiwar da ke tare da shi.
"Shi yasa aka hanaki shigowa amma kika shigo dama na san in banda surutu babu abin da za ki zo ki yi" Nurse ɗin nan da ta taso daga kujerarta da aka tanada domin su ta faɗa lokacin da ta ƙaraso wajen gadon domin yiwa Sadiya allura.
Hajiya kwa jin abin da Inna ta ce sai ta ce
" Allah kyauta"
Tana ga shan shayin, aka mata allurar, Inna dai bata ƙara yin magana ba har Sadiyar ta tashi suka je wurin nurse ɗin ta rubuta musu sallama tare da magungunan da za a siya. Da yake basu da kaya a ɗakin sai kawai kayan shayin Hajiya ta ɗakko suka taho Inna na yiwa ƴan ɗakin sallama tana ɗaɗɗaga hannu masu dariya suna yi ita kwa ko a jikinta dan ita iya gaskiyarta take komai ba dan wani abu ba.
Tafiyar da Sadiyar ke yi ce Inna da ke bin su a baya ta lura da hakan ya sa ta ce.
"Halima wannan tafiyar tantatan da kike yi fa sai kace wata wacce aka yiwa shayi?"
"Haba Inna yo wanda ya haihu har a haɗashi da ɗan shayi, ai haihuwa tafi gaban wasa, bare ita da ta haifi tagwaye kuma ɗinki uku aka mata a waje daga ciki kuwa huɗu aka mata dan bayan an ƙarata ta sake ƙaruwa da kan ta shi ya sa take tafiya...
"Halima ɗinki bakwai kenan aka miki sai ka ce wata ƙwarya? Yo ki ce min Sa'adiyya babu bayani yanzu Imirana zai daina wannan rawar kan da rawar ƙafar, tun da duk an miki faci a mafitar ɗa, shi kwa namiji dama wannan wurin yake wa da an ce babu to ke kuwa mace kin kaɗe a wurinsa har ganyenki dan wata zai nema ya aura"
"Faci fa Inna sai kace wata tayar keke?" Hajiya Amina da ta dakata da tafiya ta faÉ—a tana kallon Inna.
"Yo meye marabar dambe da faÉ—a Amina? Da bakinki fa kika ce É—inki har bakwai to aikuwa bagaruwa ma bata yi wannan aikin ba"
Kunya ce da haushi duk suka kama Sadiya abin da Inna ke mata a gaban sirikarta idanunta har ƙwalla suka kawo.
Har suka fito babu wanda ya ƙara magana Inna kwa sai taɓe baki take yi abinta.
Suna fitowa suka samu an sanya komai a motar abokin Imran da Imran É—in ya kira domin ya maida su gida, Inna tana hango Imran a zuciyarta ta ce
"Wannan ai shi ne sauna kira mana shasha sha in ka ga sakarai ku taho tare, wato dai har yanzu bai tafi neman sadakin gado ba (Raguna) Kar dai a ce ba zai yiwa yaran nan yanka ba amma kwa in haka ne da Imirana ya cuceni ya jayo min abin faɗa a ƙauyenmu, dan yo mai zan ce idan na gama zaman wanka zan koma ƙauye ne babu naman suna son ayi dani cewar ba a yiwa jikata yanka ba, ni da nufi na in a ban kashina in sanya a cikin mai (Kakide) Dan kar ya lalace amma ni ban ga yaron nan yana da niyya ba" Ta faɗa a zuciyarta lokacin da suka ƙaraso wajen motar.
Mama riƙe da Husaini, a baya, da Sadiya, sai Hajiya riƙe da Hassan wanda ta karɓa yanzu a hannun Ashrof, suka shiga gaba ita da Ashrof ɗin, Imran kwa dama a machine ɗinsa zai tafi.
"Inna can zaki shiga fa" Hajiya ta faÉ—a ganin Inna tana wani kalle-kalle
."Haba Amina ai ban ce miki ban sani ba, ko kina nufin a ɗan sahu zan koma ai wallahi ko babu wuri sai dai ɗaya daga cikinku ta haƙura ni in shiga" Ta faɗa tana shiga bayan Imran ya rufe musu ƙofar yana jin haushin Inna. Abid kuwa abokin Imran sai dariya yake abinsa dan sosai yadda Inna ke magana ya bashi dariya ya daɗe yana jin labarinta wajen Imran idan ta zo gidansa wai baya son matar takura masa take sai kuma ɗazu da yake bashi labarin zuwanta a waya, sai yau dai Allah ya sa ya ga Inna da idonsa.
Tun da suka hau kan titi take ta kalle -kalle abinta babu wanda ya ce wani abu, zuwa can ta ce
"Oh yau ai na ga ta kaina da na biyo Imirana, ko kallon titi ban samu na yi ba, yo ni da lokacin ma ina zaman garin nan ko unguwa zani in ba wani nisan azo a gani gareta ba bana hawa abin hawa da ƙafata nake yawo, yo in a ƙafa ne sai ka gama kallon gidaje masu kyau da abubuwa a hanya amma in a abin hawa ne sai dai ka ke ganin wulgawarsu wul-wul" Ta faɗa tana taɓe baki babu wanda ya tanka ta sai Abid da ke tuƙi yana darawa abinsa.
" Ka ji yaro ya sunanka?" Ta tambaya tana É—an É—aga murya yadda zai ji ta.
"Abid" Ya faɗa yana ƙunshe dariyarsa yana kuma jiran mai zai biyo baya dan ya tabbata sai ta masa ƙwasƙwarima a sunan kamar yadda Imran ya ce ta jagwalgwala masa suna wai Imirana.
"Ikon Allah wai na kwance ya faÉ—i, Abid kuma ka dai ce Abida wato sunan mata ma kai aka saka maka"
Sosai Abid yake dariya.
"Ka yi dariya man É—an nan a rasa sunan da za a saka maka sai sunan mata"
Har lokacin dariya yake. A haka suka gangara hanyar da za ta sada su da gidan Sadiya, a cikin tafiya aka zo gidan da Imran ya shiga wajen abokinsa, aikuwa idanun Inna suka sauka a kan abokin Imran da ke tsaye yana latsa waya lokacin sanye yake da riga da wanda na yadi.
"Abida ka ga wancan wanda ya É—ago maka hannu?"
"Na ganshi Inna kin san shi ne?"
"Yo ina fa na san shi ɗazu ne dai abokin ka kurma Imirana ya shiga gidan karɓar zaitun ni duk tunanina asibitin ne, ka san shi ba bayani zai yiwa mutane ba, aikuwa na bi bayansa, na shiga ɗakin, ka ga wannan kana ganinsa dai yanzu cikin shigar kamala ko to wallahi in ka ganshi a cikin gidan wasarere yake zama jiki babu kintsi"
"Ƙazami ne kenan Inna"
"Ashsha wane irin ƙazanta haka dai yake zama jiki babu kintsi ni na san abin da na gani ɗazu" Ta faɗa tana jan bakinta ta yi shiru ganin bai harbo jirginta ba ita kuma ba ta so ta yi ɓaranɓarama shi sa ta yi shiru.