← Book details Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 19

Sashe 2

Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lah babu komai wallahi, ai mu ma maza wani lokacin da namu laifin sai mu hana mace zuwa abin da bai dace mu hana ba, kin ga wannan ai bai dace ko kusa na hanaki ba, wallahi na aminci Allah kiyaye hanya" Ya faɗa yana sanya hannu a aljihu ya fiddo dubu biyu ya miƙa mata.

Hannu biyu ta sanya ta karɓa tana ta rafka godiya

"Yaushe zan dawo kuma?"

"Kamar ya yaushe za ki dawo ba zaman wanka za ki mata ba ai zan ce kwana arba'in ne ake zaman wanka ko an canja shi daga haka ne?"

"A'a ba a canja ba sai dai da yake haihuwar fari ce ana iya ƙarawa ma a yi arba'in biyu wani sa'in ma in mijin mai sakin fuska ne bai nuna alamar gajiyawa ba har arba'in uku ana yi" Ta ce tana ƴar dariya.

"Inyeee to abin ya zama hauka kuma ba zaman wanka ba, ke yanzu sai ki yi sama da watanni uku a gidan mutane yo ai har yaron ya fara zama ma, amma ana yiwa uwarsa zaman wankan haihuwarsa ai da kunya ma gote-gote da ke ki zauna a gidan yara har arba'in uku"

"Ni fa ba wai cewa na yi zan yi arba'in uku ba kawai dai ina faɗa maka ne abin da ake yi, amma ni kwana hamsin zan yi, sannan jar miya da naman kaza sun ratsa ni" Ta faɗa tana lashe leɓenta dan har yawunta ya tsinke.

"Ko da na ji, Allah kiyaye"

"Amin, amin Malam" Ta ce tana kallon Tasalla da ta cika ta yi fam kaɗan ya rage ta yi bindiga dan baƙinciki.

"To Tasallele, mu zamu tafi birni sai Allah ya ƙaddara saduwarmu, kike sana'ar man ƙuli na da nake yi dan kar kasuwar ta yi ƙasa ganin ana zuwa nema babu sai mutane su ɗauka na daina yi ne kwata-kwata amma in kina yi da na dawo sai in ɗora daga inda kika tsaya, kuma kowa ya tambaye ni ki ce masa na tafi Kano ta dabo tunbin giwa jikata ta haihuwa zan mata ZAMAN WANKA" Ta faɗa tana dariya, Malam dai kaibya girgiza a ransa yana tunanin ranar da matan nasa za su girma gashi dai sun tsufa amma in suka yi wani abin kamar yaran mata.

Haushi ne ya ƙara cika Tasalla wato bayan sana'arta ta waina, hallaw take sana'ar mai da ƙarago ita tana can tana cin shinkafa da miya da nama, har wata ƙwallar takaici ce ta kawo a idonta. Ganin Malam ya kalleta ta daddage ta danne ta ce mata

"Sauka lfy"

"Sana'ar man ƙulin fa?" Ta tambaya da sheƙiyanci.

"Ba zan yi ba" Ta bata amsa a takaice.

"Kin huta" Ta faɗa tana dariya dan ta lura Tasallar ta shaƙa sosai.

"Amma kin san dai yanzu motar kasuwa ta tafi, sai dai ki hau machine ki je Garki ki hau motar Kanon a can ko?" Malam ya katse musu maganar dan ya lura abin na neman zama fitina gwara a rabu lafiya.

"Eh dama yanzu mota ai ta tafi dan rana ta yi sosai dan azzahar ma ta kusa hantsi ya dubu luday"

"Yawwa a gaishe su"

"Za su ji" Ta faÉ—a tana tashi daga zaunen da take ta buÉ—e labulen ta fito daga turakar Malam É—in.

Ɗakinta ta koma ta ɗakko lalle ta sanya a bakkon (Ghana mostgo) Ta ɗaga dakyar ta fito da ita daga ɗakin ta ajiye a ƙofar ɗakin ta ɗakko kwaɗo ta kulle ɗakinta ta sanya mukullan a cikin pos ɗinta. Ƙofar gida ta fita ta sanya Lawwali almajirin Malam ya samo mata mai machine, aka ɗakko jakar za a fice da ita dai dai nan Malam ya fito daga ɗakinsa ya ga Lawwali ɗauke da jakar.

"Azumi lafiyarki kuwa?" Ya tambaya da mamaki.

"Me ka gani Malam" Ta faÉ—a cikin nuna rashin fahimtar inda tambayarsa ta dosa.

"Wannan jakar ce za ki yi tafiyar da ita, kin shaƙeta da kaya kamar wanda za ki ƙaura can"

"Ba fa kaya bane kaÉ—ai Malam har da bargona a ciki ka san lokacin sanyin nan kar inje ina bani-bani a gidan yara gwara na tafi da abuna" Ta faÉ—a tana murmusawa.

"To ai shikenan" Ya faɗa, suka fito tare ta hau machine almajiran Malam na ta ɗaga mata hannu, ta tsakiyar ƙauyen suka bi duk inda suka wuce ana ɗaga mata hannu alamar Allah kiyaye dan an ganta da jaka a gaban machine kuma duk yawanci an san tana da ƴan uwa a birni da yake ma ƙaramin ƙauye ne, tun da a can ne ma ta fara aurenta na fara har ta haifi ɗanta ɗaya tilo kafin ta auri Malam ɗin, da har yau basu taɓa haihuwa da shi ba. Duk inda suka gifta sai hannu ita ma take ɗagawa alamar ta tafi har sai da suka hau hanyar da za ta sada su da garin Garki L.G sanna ta sauke wata ajiyar zuciya mai ƙarfi ranta fari ƙal tana jin wani nishaɗi dan babu abin da ya fi faranta mata sama da yadda Tasalla ta shaƙa, da kuma yadda jama'a ke ta ɗaga mata hannu lallai zuwa birni da daɗi.Gabanta ne ya bada wani rass tuno da halin mijin Halimar sam bashi da sakin fuska ga rashin ta ido, tunaninta ma yadda zaman zai kasance...

To fa dandandan dan dan dan dan, ku biyo ni dan jin wannan labari mai cike da barkwanci, shin ya zaman zai kasance tsakanin masu gida da kuma ƳAR ZAMAN WANKA

🥰😘😍

Mai son cigaban labarin ya mn mgn 09030283375 wtsapp only

👩‍🍼ƳAR ZAMAN WANKA🤱

(KWANA ARBA'IN)

NA

MAMAN AFRAH

🅿️2️⃣

Tun da ɗan acaɓan ya kaita tasha, ta biya shi kuɗinsa har gaban mota ya ajiye mata jakarta tana ta zabga masa godiya kamar wanda ya kawo ta kyauta. Mota na cika suka kama hanyar Kano, Inna Azumi ta samu wata tsohuwa mai shegen surutu irinta aikuwa suka rinƙa zuba kamar daman sun san juna, tafiya ta yi tafiya Inna Azumi ta fara gyangyaɗi a haka suka ƙaraso Tashar ƴan kaba ɗan sahu ta samu unguwa uku zai kai ta, suna cikin tafiya ta tuna cewa bata sanar da Mamar Halima ba dan dama ƙarya ta yiwa Malam a kan cewa ta ce ta taho, kawai dai Inna Azumi ta kira su gaisa sai take ce mata suna asibiti Sadiya na naƙuda shi ne fa ta shiryo ta taho ba tare da ta sanar da ita ba.

Ganin wayar babu caji ta mutu ta taɓe baki a zuciyarta ta ce

"Yo ya za a yi da ni, ni da gidan ɗana duk da dai ya mutu amma ai babu mai korata daga gidan jikokina, dole na je na tabbatar kar na fara zuwa gidan Halima(Sadiya) Na tarar an bar ta a gidansu saboda wankan jego, ko da kuwa ma hakan ta kasance dole na mayar da yarinyar ɗakinta na mata zaman wanka dan ba kasafai wasu mazan ke son matansu su je gidan iyayensu wankan jego ba" Tana cikin saƙar zucin ta lura sun kusa layin da za a ajiyeta, dan haka ta shiga nunawa ɗan sahun inda zai bi har dai suka ƙaraso ƙofar gidan, idanu ta ƙwalalo lokacin da ta yi tozali da danƙareran kwaɗo a ƙofar gidan ɗan sahu bai ankara ba ya ji ta ce

"Na shigenge ni Azumi"

"Lafiya dai Baaba" Ya faÉ—a yana kallonta da mamaki, ganin ta dage sai zabga salati take kamar an ce wani ya mutu.

"Yo ba dole ba na yi salallami É—an nan ka ga gidan da na zo a rufe"

"Haba Baaba ya za a yi da ki taho baki sanar da mutanen gidan ba, gudun haka ne ya sa ake faÉ—a, gashi na ga da alama ma kamar ba a gari kike ba dan na ga lokacin da kika sauka daga mota"

"Wallahi kuwa É—an nan ba a gari nake ba daga wani garin nake, amma na san inda zan same su, mu je tarauni"

"To Baaba" Haka ya juya kan napep ɗin suna tafiya tana ta faman surutu har suka kawo ƙofar gidan da ta nuno masa zai ajiyeta tun kan su ƙaraso.

"La'ilaha illallahu muhammadur rasulullahi S.A.W, yau dai na ga ta kaina wannan wane irin abu ne kamar an haɗa baki" Ta ƙarasa faɗa tana tafa hannuwa.

Ɗaga ido ɗan sahun ya yi aikuwa ya sauke a kan ƙofar gidan ashe nan ɗin ma a kulle.

"Gakiya Baaba kin taka fawul a ce ko ina babu kowa kamar basa son zuwanki" Ya faÉ—a yana tuntsurewa da dariya.

"Kai É—an nan ka kiyayeni ni nan da kake gani can gidan É—ana ne nan kuma gidan jikata kuma na san inda suke suna asibiti jikartawa za ta haihu zatona duk sun dawo shi ya sa"

"To ki musu waya mana" Bani sa caji kai bari dai ka ga" Ta faɗa tana fitowa daga napep ɗin ta lissafa kuɗinsa ta biyashi kamar yadda ya faɗa, ya fito mata da jakar kayanta kamar yadda ta buƙata.

"Baaba ziyara kika zo ko ƙaurowa kika yi?" Ya faɗa cike da sheƙiyanci lokacin da ya ɗaga bakkon ya ji wani uban nauyi.

"Ka ji ni da ja'irin yaro to ina ruwanka" Ta faɗa tana juyawa ta shige gidan da ke maƙotaka da gidan Sadiyar, shi kuma ya ja ya tafi yana ta dariya dan hatta yadda take magana dariya yake bashi, ga wani uban gwaggwaronta kamar bututun zuba kalanzir.

Tana shiga suka gaisa da matar ta sanar da ita gidan Sadiya ta zo a rufe, nan matar ta ce suna asibiti tun da sassafe. Matar ta ce ta zauna kafin su dawo dan ta gane kakar Sadiya ce ta taɓa zuwa gidan sun haɗu lokacin ita Inna Azumin ta zo, cewa ta yi bari ta samu ko almajiri ne ya ɗakko mata jakarta.
Chapter 2 · 0% Book details