← Book details Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 19

Sashe 5

Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah sarki ƴar nan,ko da na ji shi dama tunani ai baiwa ne, kin ga ke kin fi hango jirgina wallahi dama yunwa nake ji tamkar an mini sata a cikina, ayi maganar nisan ma, gashi na je gidan Rakiya a rufe daga nan na tafi gidan Halima can ma a rufe, haka dai na haɗu da taƙadarin yaron nan Imirana, ya ringa gudu da mai adaidata sahun da ya ɗakkoni na binsa yadda kika san a filin tsere haka ya ringa gudu, ko yanzu daga bakin babbar ƙofa (Get) Zuwa nan daƙer na ƙaraso a ƙafafuna, in da kara ai akuyar gidan sirika ma iya ce, ko ni ba uwar Halima bace ai Kakarta ce in banda dalili mai sa a leƙe gindin sirika mai zai kawoni gidan Imirana" Ta kwashe yadda aka yi ta faɗa tana kallon Hajiya Amina.

"Da me ya kai ki bin Imran yaron da ni ma addu'a nake binshi da ita a kan Allah shiryeshi wannan halin nasa tun yana yaro, kin yi sa'a ma da har ya yarda kika biyo shi asibitin bai tafi ya barki a ƙofar gidan ba, ko ya ɓace muku da ke har napep ɗin ku yi ta bulayi a titi ƙarshe mai napep ɗin a ajiyeki a inda kuɗinki suka ƙare"Cewar Hajiya a zuciyarta a fili kuma sai ta ce." Ta faɗa tana bin su duka da kallo irin ko ba haka ba.

"Inna duk nan fa babu bare ko ma abinci kika ce a zubo miki ai baki yi laifi ba duba da irin nisan tafiyar da kika yi daga garinku zuwa nan" Hajiya Amina ta faÉ—a tana kallon Inna Azumi.

"Allah sarki ƴar nan,ko da na ji shi dama tunani ai baiwa ne, kin ga ke kin fi hango jirgina wallahi dama yunwa nake ji tamkar an mini sata a cikina, ayi maganar nisan ma, gashi na je gidan Rakiya a rufe daga nan na tafi gidan Halima can ma a rufe, haka dai na haɗu da taƙadarin yaron nan Imirana, ya ringa gudu da mai adaidata sahun da ya ɗakkoni na binsa yadda kika san a filin tsere haka ya ringa gudu, ko yanzu daga bakin babbar ƙofa (Get) Zuwa nan daƙer na ƙaraso a ƙafafuna, in da kara ai akuyar gidan sirika ma iya ce, ko ni ba uwar Halima bace ai Kakarta ce in banda dalili mai sa a leƙe gindin sirika mai zai kawoni gidan Imirana" Ta kwashe yadda aka yi ta faɗa tana kallon Hajiya Amina.

" Humm Inna kenan, a nunawa na rigingine farin wata, ai ni sai dai na bada labarin Imran, dan ma ni yana raga min kasantuwata mahaifyarsa, kema da gangan ne ai, duk wanda ya sayi rariya ai ya san za ta zubda ruwa, me ya kai ki bin Imran yaron da, ni ma addu'a nake binshi da ita a kan Allah shiryeshi wannan halin nasa tun yana yaro, kin yi sa'a ma da har ya yarda kika biyo shi asibitin bai tafi ya barki a ƙofar gidan ba, ko ya ɓace muku daga ke har napep ɗin ku yi ta bulayi a titi ƙarshe mai napep ɗin a ajiyeki a inda kuɗinki suka ƙare"Cewar Hajiya a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.

"Sannu Inna gaskiya kin yi ƙoƙari, wallahi kai kuma Imran ka kiyayeni a kan me za kake gudu baka ganin tsohuwa ce?" Hajiya Amina ta faɗa tana kallon Imran da ke wani haɗe rai yana kauda kai gefe irin bai yi laifin ba ma.

"Hajiya baki san yadda tsohuwar nan ta takura min bane, ta kasa fahimtar ni ko ganinta ban son yi" Cewar Imran a zuciyarsa a fili kuma sai ya ce.

"Sorry Hajiya" Ya faɗa yana sosa ƙeya.

"Au Allah, wato sorre, a soron gidanku na kwana, kai kenan taƙidarancin naka har uwarka bai baka bari ba to Allah wadaran naka ya lalace wallahi" Cewar Inna tana jijjiga kai irin na ga abinda ya fi ƙarfina.

Mama kanta ta kawar gefe tana jin wata irin kunya ganin gabaÉ—aya Inna tana kwance musu zani a kasuwa.

"Ina za a kai wannan abin kunyar? Ta faÉ—a a ranta.

"Haba Inna ki yi shiru dan Allah" Ashrof ta faɗa jin ɓaran-ɓaramar Inna ta yi yawa.

"Ashrof miƙo mata abincin" Mama ta faɗa dan ta kawo ƙarshen maganar.

Idanun Inna a kan kwanukan abincin wani mai jan murfi da ratsin yellow shi ya fi tafiya da hankalinta dan tana tunanin wataƙila a samu abinci mai daɗi a ciki, cikin ikon Allah kwa sai Ashrof ta miƙo mata shi, hannunta har karkarwa yake wajen karɓar tana washe baki.

"Yawwa Asharofa kamar kin san shi nake hari shi ne a raina" Cewar Inna a zuciyarta lokacin da ta kama kwanan da hannu biyu ta buÉ—e.

Fuskar Inna ce ta sauya har suka lura da hakan, ba komai ya sanya fuskar Inna sauyawa ba sai arba da ta yi da wake da shinkafa.

"Ni da na sanya ran wankin ciki, in samu jar miya idan hali har da naman kaza amma in ga wake da shinkafa da mai da yaji, to Allah suturibuƙui inji kishiyar mai doro" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta yi saurin gyara fuskar ganin kowa ya lura da ɓata ran da ta yi ta sanya hannu ta kai kyawawan lomomin guda biyu, hakan ya yi dai dai da buɗewar da Ashrof ta yiwa ɗaya daga cikin flask ɗin aikuwa Inna ta yi ido biyu da shinkafa da miya ga wani uban namomi a saman.

Tufff Inna ta tofa da duka lomar abincin da ta take bakinta taf da shi ta ce.

"Amma Asharofa baki da imani wallahi, akwai wannan abincin mai rai da lafiya amma kika bani wannan ci ka mutun?" Ta kai ƙarshen maganar tana ture flask ɗin gaban nata.

GabaÉ—aya suka saki baki suna bin Inna da kallon mamaki.

"Inna abincin Aunty Sadiya ne fa da za ta ci idan ta falka"

"Ka ji ni da yarinya mai shegen iyayin tsiya yo Allah na tuba meye marabar dambe da faÉ—a? Abinda ya yi ni ai shi ya yi yarinyar nan, in kuma kin manta ne in tuna miki" Ta faÉ—a tana janyo kwanan gabanta.

"Ikon Allah na zaune ya faÉ—i, lallai in da rai da rabo" Cewar Inna lokacin da ta luntuma hannu cikin abincin ta cika hannu ta kai bakinta ko bismillah babu.

Mama dai kan ta na ƙasa dan ta rasa bakin magana, dama abincin Sadiya ne Hajiya Amina ta girka mata takanas ta koma gida ta iyo girki dan ta samu ta ci idan ta falka.

"Ya rabb, matar nan ta addabemu" Cewar Imran a zuciyarsa yana dafe goshinsa da hannu.

Loma É—aya biyu, a ta uku sai kawa Inna ta saki kuka, kukan da ya sanya duk waÉ—anda ke kusa da su suka waigo suna kallonta, dan wasu ma zatonsu ko mutuwa aka yi.

"Inna lafiya?" Mama ta tambaya da mamaki.

"Haba Rakiya ba dole in yi kuka ba, yanzu a ce kuna cikin irin daular nan amma ko ki ce in zo in yi ko da shekara ne a marmarce ni ma in yi wankin ciki amma kika barni ina fama da karta kafura (Miyar kuka) Da tuwon masara wanda in Tasalla ta tuƙa da yake bata iya ba kana ci yana maka dariya" Ta faɗa tana ɗaukan cinyar kaza ta yagi tsokar har wani lumshe ido take.

"Na shiga aljanna na maƙale" Cewar Ashrof da bata san ma maganar ta fito ba.

"Yo waye zai shiga aljanna ya fito É—iyar nan kowa ya shiga ai ya ga wajen zama" Ta faÉ—a tana suÉ—ar hannunta da take jin daÉ—in miyar har tsakar kan ta.

GabaÉ—aya mutanen wurin dariya suka saka, wani saurayi da ke tsaye yana kallon Inna daga can gefensu a ransa cewa yake.

"Tsohuwar nan da za ta yarda in ɗauketa vedeo in sanya a status na san duk wda ya gani sai ya ci dariya kamar me sannan na san kowa ya gani sai ya yi replay har na rasa saƙon wanda zan duba, wallahi za ta yi kyau da comedy sosai ma" Ya faɗa a ransa yana kallon Inna daga can inda yake yana ta dariya.

Imran kwa ganin hankulan mutane duk ya dawo kan su hakan ya sanya a fusace ya bar wurin.

Sai da ta cinye abincin tas duk da yawansa ta suÉ—e kwanan ta maida murfin ta rufe, ta É—auki pure water biyu ta kora ta ce

"Kai garin daɗi ba kusa ba, Allah sarki Malam da ƴar Tasallar sa suna can ana fama da dambu ni kwa nan na samu abinci na ci na yi nak" Ta faɗa tana miƙa hannunta can gefen tabarmar ta tilla wani pure water ɗin ta wanke hannunta.

"Jama'a ina wuninku" Ta faÉ—a tana kallon Hajiya Amina da Mama.

Dariya Hajiya Amina ta yi dan wallahi sosai Inna ta bata dariya wato sai da ta ƙoshi ne ma za a gaisa, ita mamakinta ɗaya ma da Inna bata tambayi mai haihuwar ba bare ma abinda aka samu ba, sai ta abinci ma take.

"Lafiya ƙalaw Inna, kin zo lafiya" Ta faɗa har lokacin tana ƴar dariya dan wallahi ta kasa riƙe dariyar.

"Lafiya ƙalaw, wallahi" Ta faɗa tana maida kallonta kan Mama ta ce.

"Kin ji Rakiya yaushe kika koyi mugun hali ne, ace ke baki gaisheni ba ni na gaisheki amma kuma kin kasa amsawa sai ɓata rai kike kamar na miki mugun abu, yo in shinkafar da na ci da nama ne ai rabona ne ya tsaga, ita kuma wake da shinkafar shi ne rabon Halima haka Allah ya tsara tun fil azal ni Hajiya Amina ta girkawa abincin tun da rabona ya rantse sai na ci kin san rabon kwaɗo ba ya hawa sama"

"Ina wuni Inna" Mama ta faÉ—a kamar ta yi kuka dan wallahi yau dai Inna ta gama zubar musu da kima da mutuncin a idon siriki da uwar sirikin ma baki É—aya.

"Yawwa ko ke fa, lafiya ƙalaw ya abin da aka samu, mai ta haifa Halimar?"

"Ƴan biyu ne duka maza?"

Salati Inna ta É—auka tamkar an yi wani abu, sai da ta gama salallamewa ta ce.
Chapter 5 · 0% Book details