Sashe 18
Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da asuba bayan sun idar da sallah sun yi azkar sai Ashrof ta shiga gyara gidan da yake yanzu bata zuwa makaranta sai islamiya da yake ta kammala secondry school kuma bata cigaba ba da karatu da yake ƙa'idar babansu ce tun kan ya rasu cewar babu wacce za ta cigaba da karatun sai dai in ta yi aure ta cigaba a ɗakin mijinta. Ko Sadiya ma tana kamamala secondry school aka mata aure. Bayan ta kammala komai suka karya ta yi wanka ta shirya sai Mama ta ce ta bari sai kamar ƙarfe tara sai ta tafi dan kar ta yi musu sakko.
```Hajiya```
Tana idar da sallah ita ma ta shiga hada hadar gyara gidanta da yake wuni biyu kennan bata zauna ba dan haka gidan yana buƙatar gyara sosai dan haka ta shiga gyarawa a ranta tana ta tunanin yadda Imran da Inna suka kwana ko ya aka ƙarshe.
```INNA```
Rawar sanyi ta fara tamkar wacce masassara ta yiwa mugun kamu, ta shiga wani irin tashin hankali da ya sanya ta kasa gane ina mafitarsa take, so take ta je ta buga ƙofar tare da roƙon Imran ya fiddota dan ta san matsawar ta ƙara wasu lokuta tare da Hassan a ɗakin to tabbas babu abin da zai hana ta suma in ma bata yi gawa ba. A tsaye take amma kuma ƙafafunta sai rawa suke kallon Hassan take da ke kwance kan shawul gaba ɗaya ya gama sawaya daga mutum zuwa miciji kan sa ne kaɗai na mutum amma dai yana a inda aka ajiye shi ko yunƙurin motsawa bai yi ba.
Ganin yadda Hassan ya mata shamaki da zuwa wurin ƙofa hakan ya sanya ta yanke shawarar neman ɗaukin Imran duk da ta san da gayya ya rufe ta amma ya zame mata farilla tusa a masallaci ta nemi ya buɗe ta.
"Imirana, Imirana, dan Allah ka taimaka ka buɗe ni kai ma da ɗan nan ya zame maka dole ka gudu daga ɗakin bare ni ɗorin ɗosano kakar uwarsa" Ta faɗa tana magiya amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa ko motsin Imran ɗin ma bata ji. Amma hakan bai sa ta saduda da neman ɗaukin daga gareshi ba dan haka sai ta ƙara ware murya ta ce.
"Imirana indai mutuwa kake so in yi billahillazi ba sai ka rufe ni da Hassan a É—akin nan ba lokaci na ma yana tafe zan mutu ba sai ka haÉ—ani da wannan abun ba"
"Inna in kin ga na buɗeki to tabbas sai kin wanki yaron nan, ya zaki yi ki wanki ɗan uwansa amma shi kiƙi masa wanka, sannan bayan haka ma har ki ce wai shi ɗan ruwa ne bayan kin san baiwa ce Allah ya masa, ba ke ce jiya kika ce kar ake raba kan su ba, tun da har Allah ya halicce su a ciki ɗaya? Amma shi ne ke kika fara nuna musu banbanci, baki san ba a yiwa tagwaye haka ba ransu ɓaci yake"
"Haba Imirana ya za ka faɗi haka da bakin ka, son dai ka sanya Hassan ɗin ya min wani abu, ni ban nuna musu banbanci ba, kuma da kake batun ba a nuna musu banbanci ni dai na san ba a ɓata musu rai in ransu ya ɓaci suna ɓatawa mutane abinci ko ayi ta dafa abinci yaƙi dahuwa amma tun da uwata mai daddawa ta haifeni ban taɓa jin inda aka yiwa ɗan mutum baiwar komawa miciji ba"
"Wai wa ya ce miki miciji ne bayansa ne fa kawai fatar ta miciji"
"Ƙur'ani miciji ne, dan baka ga yadda ya koma ba yanzu wallahi kan sa ne kawai na mutum" Inna ta faɗa idanunta a kan Hassan tana sakin kuka dan sai ta ga girman macijin ya yi yawa.
"Ki wankesa sai na buÉ—eki"
"Wallahi ba zan wankeshi ba, ta ina zan fara wanka wannan abu himili guda wallahi da in wankesa gwara ya kasheni in san mutuwar shahada na yi, ai da uwaka Amina ce ba za ka rufeta a É—aki É—aya da maciji ba"
"To zage ni Inna sai in buÉ—e miki"
"Ni shegiya in ji É—an daudu ba zan fara ba ma ina so ka buÉ—e ni ta ina zan fara zaginka ai ko banza ba zan ce maka ba"
"Gashi kwa kin faÉ—a kn ce banza"
"Sa'adiyya, Sa'adiyya, dan Allah ki fito daga bayin nan, ima dalili kamar wacce za ta koma budurwa in kin yi zaman ruwan zafin, bayan har Æ´aÆ´a biyu sun keto ta gabanki ba yadda za a yi ki koma kamar da, in kuma wanka kike in ba fatar za ki canja ba dan Allah ki zo ki ga halin da Innarki Azumimi take ciki duk na fita hayyaci na...
"Sadiya fa bata jinki kawai ki min abu É—aya in buÉ—e ki ya katse mata magiyar da take yiwa Sadiya.
"Me kake so, ko goyaka ka ce in yi Imirana zan goya ka in dai ka fito dani"
"Kin ji matsalar ai, so nake ki kirani da suna na, na asali wato ki ce IMRAN inda kin faÉ—a to zan buÉ—eki"
"I,Imir, Imirana" Ta faÉ—a dakyar dan ta kasa faÉ—ar yadda yake so.
"IMRAN kawai nake so ki ce"
"Haba wnnnn rashin imani har ina tayaya bakin tsohuwa zai iya faɗar wannan abu ban da ɗaukan alhaki wallahi Imirana duk ranar da na fito za ka san ka min wannan wulaƙanci" Ta faɗa tana rushewa da kuka.
"Sai ki bari sai kin fito ɗin, ke ba matar malam bace ki yi addu,a kawai ki kuɓuta"
"To ai mutum ba ya ƙin ta mutane" Cewar Inna.Jin abin da Imran ya ce sai ta tarki yin addu'ar amma ruɗani ya sa ta manta komai, tunani ta shiga yi can sai kawai ta ji wani karatu ya faɗo mata a baki.
"Alif, am baki, waw, zal, ba, alif, baƙi, lallam, hakuri" Ta faɗa da ɗaɗɗaya kamar yadda ta ji almajiran Malam na biyawa da allo. Imran yana kwance rigingine tsabar dariya yana tunani wai dama matar nan akwai maganinta aka bari ta addabi mutane, dariya yake tun ƙarfi can ya ce.
"Am, baki,"
Sai Inna ta karɓa da cewa 'Waw zal"
Ƙaran dariyar Imran kawai Inna ke ji, hakan ya sanya ta fara neman yadda za ta samu mafita dan ta ga bashi da niyyar taimakonta. Idanunta ta mayar inda Hassan ke kwance aikuwa ta yi arba da gabaɗaya ya koma maciji har kan, idanunta ta zaro ta ce.
"Hassan kai ne ka koma haka,duk da hausawa sun ce kaƙi naka duniya ta so shi, ka so shi duniya ta ƙi shi, to yau dai ga ranar, ni dai na ƙika dama ba wani haɗi garemu ba,Allah tsari gatari da saran shuka, uban gyatumarka kawai na haifa, ni ma ban da shishshigi shiga dangin miji da ganamasgo me ya kaini zuwa ZAMAN WANKA, ya Allah ka raba bawa da wahala gwauro a teburin mai shayi" Tana faɗar haka ya fara ja baya har sai da ta ji ta tokare da jikin drower waigen mafaka ta fara amma bata gani ba, idanunta ne suka sauka a ƙasan gado inda ta kwana jiya kawai sai fashewa da kuka ta yi ta ce.
"Ni Azumi na ga takaina, tun da na zo birnin nan nake yin angamo da abubuwa, na yi angamo da mazaƙutar (Al'aura) abokin Imirana, na yi gamo da aljani cikin dare lokacin da ake cewa mahutar bawa amma haka na kwana a tsakanin katakwaye, sauron duniyar nan ya gama cinye min ƙauri, ga riga a jiƙe duk sanyin nan amma rigar tana naniƙe dani da lema da komai haka na jure na kwanta, yanzu hallaw daga garin Allah ya waye a rufe ni da miciji a ɗaki" Ta faɗa tana jin haushin kan ta da bata fito daga ɗakin ba lokacin da Imran ya karɓi Hassan.
Da sauri ta nufi akwatunan Sadiya da aka musu É—aya kan É—aya, guda huÉ—u ne, hakan ya sa ta hau kan su amma tana iya hango jelar Hassan na kaÉ—awa tana motsi, da sauri ta diro daga kan akwatuna ta taka gado, ta buÉ—e drower step É—in wardrobe É—in ta kalla ta ce.
"In ka ji mutum na cewa ba zan iya ba to bai kama shi bane, ƙafafunta ta ɗora a kan step ɗin cikin drower ta ƙanƙanme a haka ta yi matakala da step ɗin sai gata ta haye saman drower can saman ta hau kan ta na gab da silin.
"Taimakona ɗaya da Allah ya yi lokacin sanyi ne da ace zafi ake fanka a kunne ai da an yi gudun gara an tadda zago, da fil fanka za ta ɗauke min kai" Ta faɗa tana kallon ƙasa inda Hassan yake har lokacin yana nan a micijinsa.
Sai da ta ji ta zaune dandam, ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ce.
"Allah raba bawa da wahala, na san dai komin nisan dare gari zai waye, amma ban da dai matar mutum kabarinsa babu yadda za a yi Halima ta auri wannan yaron marar imani" Ta faÉ—a tana rafka uban tagumi.
Ƙaran buɗe ƙofar bayi ne ya sanya Imran daina dariyar da yake ya tashi zaune sa sauri ya koma kan kujera ya zauna ya ɗauki Husaini ya riƙe dan ba ya so ko Sadiya ta san gashin ƙumar da zai ke yiwa Inna a gidan dan ya san ko ba komai kakarta ce kuma ba za ta ji daɗi ba.
Da sallama Sadiya ta shigo falon, amsa mata Imran ya yi mamaki ta yi da ta ganshi ɗam a zaune fuskarsa fes da alamar yana cikin nishaɗi, mamaki take yi daga jiya zuwa yau Imran ya sauya ya zama mai yawan fara'a kumai magana ba ta masa wahala yanzu, danganta hakan ta yi da ƙaruwar da aka samu.
"Ina Innar?" Tambaya tana kallonsa.
"Tana ciki Hassan take yiwa wanka"
"Ikon Allah shi ne har da rufo ƙofa" Ta faɗa tana sanya hannunta ta tura ƙofar, ashe kafin ta shigo falon Imran ya buɗe mukullin da ya sanya, dan haka ƙofar kawai ta tura ta shiga. Inna da ke saman drower tana jin duk abin da suke cewa, a ranta ta ce