← Book details Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 19

Sashe 6

Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma wallahi kin cuceni Rakiya, yanzu a ce jikartawa ta haifi tagwaye duka maza amma tun zuwana wajen nan kika kasa faÉ—a min har sai da na ci na gwatse?" Ta faÉ—a tana sakin wata gyatsa.

"Ki yi haƙuri Inna dama jira nake na faɗa miki to kuma na ga kina ta ƙoƙarin ki ci abinci"

"A'a babu niyya ango ya kwana da wando, yo bana ci abinci ba, lafiya ce ta kawo haka, yanzu da za ki bi É—akunan marassa lafiyar asibitin nan, za ki tarar ana ta fama da su a kan su ci abinci, to duk dan basu da lafiya mu kuma da muke da lafiya ai sai mu ci ba sai an faÉ—a mana ba"

"Allah bar mana Inna" Cewar Ashrof tana dariya dan ta m daina jin haushin abin da Innar ke yi kuma dama inda sabo sun saba da halinta kuma mai hali ai baya canjawa.

"Amin ƴar nan, in da gaske kike, dan na san wani so yake ma ka mutu y bar ganinka saboda ba ya son ganinka amma babu yadda zai yi da kai sai kallo" Ta faɗa tana kallon inda Imran yake amma sai ta ga wayam ba ya nan, baki ta taɓe ta kalli Mama ta ce.

"Wai ina mazajen nawa ne, ko sai na roƙa za a bani in gan su, kuma ita Halima da ake ta faman cewa bata falka ba, ragwanta ta yi a haihuwar har ta suma ake jiran falkowarta?"

"A'a allurar bacci suka mata, saboda tana buƙatar hutu" Cewar Mama tana miƙa mata yaron hannunta.

"Kai duniya inda ranka ka sha kallo, wato yaron ma yana hannunki amma baki bani ba, ni kuma ban lura ba ko dan an ce hankali ke gani ba ido" Ta faɗa tana karɓa yaron ta buɗe shi tana ta yaba kyansa.Babu wanda ya ce wani abu, sai da ta gama ganinsa ta ce

"Wai ina É—ayan ko ba za a bani su lokaci É—aya ba dan kuna tsoron in gudu da su?" Ta faÉ—a tana kallonsu.

"Wannan tsohuwa da ɗaukan ƙafa take" Cewar Hajiya a ranta a fili kuma sai ta ce

."Kin ga ɗayan Inna, wannan Husaini ne, shi ne ƙaramin wannan kuma shi ne Hassan ɗin, an haifeshi da wata baiwa ne" Ta faɗa tana ɗorawa Inna a cinyarta daga gefe sai ya zamana gefe ɗaya Hassan ɗaya gefen Husaini.

"Allah sarki bawan Allah, ashe da baiwa aka haifeshi, yo banda abinki ai an fi son Æ´an baiwa" Ta faÉ—a tana buÉ—e fuskarsa tana ta sakin murmushin farinciki.

Ashrof kwa dariya take dannewa dan ta san yanzun nan Inna za ta tsorata in ta ji baiwar da ke tare da yaron.

"Ai gabaÉ—aya fatar bayan Hassan É—in ce kamar jikin miciji, kin san wasu Æ´an biyun ma ana haifar É—aya mutum É—aya miciji saboda baiwa ce id...

"Jikin miciji fa kika ce Amina?" Inna Azumi ta faÉ—a tana zaro idanu jikinta gabaÉ—aga ya É—auki karkarwa dan tsoro...

Next page.😂😂😂

Yanzu fa aka fara wasan 🤣🤣🤣

Masu son grp É—in Æ´ar zaman wanka

09030283375

🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼

(KWANA ARBA'IN)

NA

MAMAN AFRAH

🅿️4️⃣

"Kai jama'a shi kuma irin tasa baiwar kenan?" Inna ta faÉ—a gabaÉ—aya jikinta ya É—auki karkarwa, musamman da ta ji Hajiya Amina ta ce wai wasu maciji ake haifa É—ayan kuma mutum.

"Wallahi sai ma kin buÉ—e kin gani da idaonki kin san an ce gani ya kori ji"
Cewar Hajiya Amina.

Daidai nan Imran ya dawo riƙe da ledoji a hannunsa amma Inna ba wai ta ledojin take ba duk kwaɗayinta da son abin duniya sai ta ji duk bata cikin nutsuwarta.

"Ni Azumi barni in mutu maza su kai ni ba mata ba, ai in kin ganni a lahira kaini aka yi" Ta faɗa tana ɗaukan Husainin ta miƙawa Mama ta ɗauki Hassan ɗin hannunta na karkarwa har yaron ya so kuɓucewa ya faɗi.

"Haba Inna ya za kike garaje a kan jaririn da aka haifa yanzu" Imran ya faɗa a fusace dan yanayin da Innar ta miƙo yaron tamkar wacce ta riƙo kashi.

"Jakar uban nan kayya, ɗan malafar uba ka ce fa, ashe dai kana magana rainin hankali ne yasa kake maƙe murya kamar ka haɗiyi rariyar tankaɗe, to dukana za kayi fa da hayayyaƙo min, yo wa ma ya sani ko haka bayanka yake irin na miciji abu a duhu, wa ma ya sani ko kai yaron ya gado na san ko haka naka bayan yake wannan yarinya Halima ba faɗa za ta yi ba, dan mu kaf danginmu babu masu fatar macizai"

"Me kika ce" Imran ya tambaya yana kafeta da idanunsa da suka masa jajir dan da ace matar nan bata da haÉ—i da matarsa wallahi sai ya shuka mata tsiya tunda ita bata san annabi ya faku ba.

"Yo ni kwa mai na ce, abin da wancan ya ce shi na ce kirarin mai tsoro" Cewar Inna tana kawar da kai gefe.

Hajiya kwa ta kasa furta komai dan yadda Innar ta jangwaɓar da yaron tamkar ɗan mutuntumi ba ɗan mutum ba.

"Ina ƴan uwan Sadiya Abdussamad wacce ta haifi ƴan biyu ɗazu?" Wata nurse da ke tsaye ta faɗa tana daga tsaye kan barandar ɗakin haihuwar sai wani yatsina take tana taɓe baki.

"Gamu nan" Cewar Ashrof tana miƙewa tsaye.

"Haba Asharofa bakya barin in bata amsa dai dai da ita, to in banda raini ta kallemu duk mun haifi uwarta ma mun yi jika da ita ta wani mere baki, ina Æ´an uwan Sa'adiyya" Inna ta faÉ—a tana gwada maganar matashiyar.

Wani kallo nurse É—in ta watsawa Inna, ta ce

"Ta falka ana buƙatar mutum ɗaya ya zo, dan sallamarta ma za a yi dan babu matsala" Ta faɗa tana gyara hijabinta da yake iya kafaɗarta.

"Bismillahi ku bari ni in je tun da ni kaɗaice banganta ba, ku duk a nan na sameku" Inna ta faɗa tana miƙewa ta gyara ɗaurin zaninta tare da ɗankwali, ta daidaita mayafinta.

"Haba tsohuwa ya ana neman masu ɗan gwaɓi -gwaɓi za ki taso bayan ke ma da za a taimaka miki kina buƙatar taimakon, ta ya za ki taimakawa wani?" Ta faɗa tana kama tsantsa.

"Ke ki kiyayeni da ganinki ko auren fari baki da shi amma sai a ɗaukeku aiki saboda kun yi karatun masu jajayen kunne, ku ke karɓar haihuwa kafin ku je gidan miji kun gama haddace komai, kun san ta yaya ake haihuwa har kun ɗinkesu tamkar wata ƙwarya, to ni nan har gozomanci na yi a ƙauyenmu" Ta faɗa tana hawa kan barandar da za ta sadata da
É—akin haihuwar.

"Inna dan Allah ki bari ko Mama ko Hajiya su je mana ke fa ko É—akin baki sani ba" Ashrof ta faÉ—a tana marairaicewa.

"Ke rufe min baki matambayi ai baya ɓata, zan tambaya kuma ma Allah na tuba ko daga bacci na tashi ai bazan kasa shaida Halima ba, duddubawa zan yi har in ganta, ke ɗin da gulma ajali in ba a yi ba a mutu" Ta faɗa tana wani gatsinen gefen hanci.

"Ki bari Mama ta je" Cewar Imran lokacin da ya ajiye ledojin hannunsa ya nufo wajen Innar dan ya ɗan bata baki, dan shi a kan matarsa zai iya yin komai ko da ba ya so. Mama kuwa ranta in ya yi dubu ya ɓaci ji take dama bata sanar da Inna Sadiya na naƙuda ba da yanzu duk haka bata faru ba ta rasa bakin magana tana da kara, bare kuma ƴar fari ce Sadiya a wajenta, kuma Inna sirika ce a wajenta ko da kuwa ɗanta baya raye uwa ce a wurinta.

Bare kuma Hajiya ita mai za ta ce tun da ba daga ɓangarenta Inna take ba.

"Lallai Imirana to wallahi in kuma ganin bakinka a ƙunshe kamar wani balangu a takarda, tun da har kana magana, kai da kake da aiki jajawur a gabanka, wato an haifa maka ƴaƴa biyu ai yanzu kamata ya yi ace kana kasuwa siyo sadakin gado (Raguna) Sai ka tsaya kana shiga shari ba shanu" Ta faɗa tana yin gaba ta barshi tsaye baki sake, tana shigewa ɗakin nurse ɗin ta ce "Mutum ɗaya ta taho dan wannan babu abin da za ta yi in ba surutu ba"

"To mun gode ki yi haƙuri kin san tsofaffin nan sai a hankali" Hajiya da ta baiwa Ashrof Hassan ta faɗa tana tahowa dan zuwa wajen Sadiya ganin Mama tana yiwa Inna kara ba za ta bita ba.

Ashe Inna tsayawa ta yi bata tafi ba, dan haka nurse É—in na shiga É—akin ta ganta a tsaye a hanyar shiba É—akin dan akwai É—an tazarar zuwa inda masu haihuwad suke.

"Ƴar nan an buga an barmu" Inna ta faɗa tana ƴar dariya.

."Nonsense" Cewar matashiyar tana jan tsaki ta juya abinta.

"Uwaki ce nosi wallahi ba dai ni ba, ƴar kare kawai da kai tun na haihuwa, ai duk da ban san abin da kika faɗa ba yanayin yadda kika yi maganar da kuma yadda kika yi tsaki na san ba abin arziƙi bane, to aniyarki ta biki"

Ganin Hajiya ta taho ya sa ta yi shiru, haka ta bi bayan Hajiyar suka tafi har suka je É—akin.

Suna shiga ɗakin gadaje ne sun kai talatin da yake ɗakin hutu ne inda ake ajiye masu haihuwa bayan sun haihu shi asalin cikin ɗakin da ake haihuwar yana daga ciki amma ana iya jiyo ihun masu haihuwar da ke naƙuda saboda kusa ne ƙofa ce ta raba.

"Ke rufewa mutane baki, lokacin da kika je kika karɓo cikin wa ya raka ki wajen mijin, to yanzu ma haka zaki sha wahalarki ke kaɗai" Cewar Inna cikin ɗaga murya, jin wata mai naƙuda ta daddage tana ihu tana cewa a kawo mata agaji.

Kowa bin ta yake da kallo kawai wasu na dariya.
Chapter 6 · 0% Book details