← Book details Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 19

Sashe 12

Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ido kawai Sadiya ta bi Inna ta fice daga É—akin domin kai kwanon kicin.Tana dawo wa falon ta samu Inna ta rafka uban tagumi, ji ta yi wani tausayin Innar ya kamata hakan yasa ta ce.

"Inna ko bacci kike ji ne a ɗakko miki katifa, akwai ƙaramar katifa sai a sanya miki a nan ɗin ko?" Ta faɗa tana kafe Inna Azumi da ido ganin ta yi saurin ɗauke hannunta daga tagumin.

ta saki baki ya layar mai tafiya tana kallon Sadiya.

"Ko da wani abun ne Inna?"

"Yo Allah na tuba ba dole ki ga na saki baki ba Halima, yanzu ni har lokacin bacci gareni a gidan nan ni da na zo ZAMAN WANKA?"

"Kwanan zaune za kike yi?"

"Yo ba gwara kwanan zaune ba ka san a zaune kake, ai bakam zan ke yi saboda tsaro ba wai dan tsoro ba, yo idan na kwanta na saki jiki ina bacci ai sai dai kuma a saka ki a kogin bagaruwa"

"Wai Inna bakya jin kunya Imran ya ji abubuwan da kike faɗa? Wai shin ma kin manta mace tana yin jinin biƙi idan ta haihu kurum ki ɗorawa kan ki, ki hana mutane sakat da zancen abu ɗaya?"

"Kunyar me zan ji? Na ce kunyar me zan ji Sa'adiyya, ai kunyar marar kunya tsoro ne, kuma ma da kike maganar jinin biƙi shi shaiɗan ina ruwansa da wani jinin biƙi lokacin da zai ɗau hankalinku ma kina ina, sai dai bayan komai ya lafa ku yi istigfari, kuma wallahi ni nan Azumi ƙafata ƙafarki, babu yadda za a yi in kwanta a falo sai dai mu kwanta da ke da yaran a cikin ɗakin, shi Imirana ki saka masa ƙaramar katifa a falo ya kwanta"

"Haba Inna mai gidan ne za a sakawa katifa a falo?"

"Eh mana, wato kina nufin in barku a ciki ni a nan ban san me za ku yi ba gwara dai idona idonki Sa'adiyya hankalina zai fi kwanciya kuma in san ZAMAN WANKA na zo"

Imran da ke ciki wani baƙinciki da takaici ne ya lulluɓeshi, ga kan sa da ke matuƙar masa ciwo sanadin wannan hayaniyar da Inna ke ta faman yi bakin ta ko gajiya ba ya yi.

Tuno wa da maganar mahaifiyarsa ya sanya ya miƙe zaune daga kwancen da yake a kan gadon , ya tashi dafe da kan sa yana ciccije leɓe, yana raya wa a ransa sai ya rama abin da tsohuwar nan ta masa. Sadiya ya ƙwalawa kira, da sauri ta shige ɗakin.

"Oh ni yarinyar nan ta rako mata, ji yadda take sauri kamar za ta tashi sama, ko dan tsoronsa ma take kamar wani mala'ikan mutuwa"

"Ɗakko yaran ki maido su nan, ki kai min katifar falo, ku kwanta a nan ɗin" Ya faɗa fuskarsa cike da damuwa. Shiru Sadiyar ta yi tana ɗan jin babu daɗi amma dai ta san hakan shi ne mafita a wurinsu dan tsohuwar nan sai ta sa a maimaita yaƙin badar dan kaɗan daga aikinta ta tada tarzoma.

Cikin sanyin jiki ta amsa masa, haka ta ɗakko yaran Inna tana kallonta ta shiga da su, tana kai su ɗakin duk ya ɗaukesu ya ƙara ganinsu yana jin wani farinciki na maye gurbin baƙincikin, da yake ciki ya so ace, yau su kaɗai za su kwana a gidansu da ya nuna musu kulawa su da mahaifiyarsu fiye da kima, to amma Inna ta warware komai addu'a ta riga fata.

Katifar ta ɗauka ta kawo falon ta shinfiɗa zanin gado, ta ɗora filo tsaf. Inna dai tana kallonta bata ce mata komai ba, ta koma ta ɗakko bargo ta ajiye masa, ganin Sadiya ta ce masa za ta shiga banɗaki ya kwantar da yaran yana jin ƙaran rufe ƙofar banɗakin da Sadiya ta yi aikuwa ya tashi cikin hanzari ya cire kayan jikinsa, sai da ya tuɓe tsaf daga shi sai singlet da gajeran wando gadan -gadan ya nufo falon Inna da ta hangame baki tana hamma bata ankara ba sai ganin mutum ta yi ya fito, ai bata san lokacin da ta katse hammar da take ba ta fara jero salati tana, sanya hannu a fuska tana cewa.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil, ni Azumi na ga abin da ya fi ƙarfin gani, Allah ka rabamu da mugun ji da mugun gani, haba Imirana ka manta cewa ba ku kaɗai bane a gidanku akwai ƴar ZAMAN WANKA?" Inna ta faɗa har lokacin idanunta a rufe da hannunta, a duniya ta tsani ta ga namiji haka a tuɓe.

Ko kallon inda take bai yi ba ya nufi kan katifarsa ya kwanta ya ja bargo ya rufa. Cikin. Sauri Inna ta tashi ta shige bedroom É—in tana neman faÉ—uwa a ranta tana cewa.

"Oh yaron nan bashi da kunya ko kaɗan, ko dan dama hausawa sun ce abokin damo guza, ashe dai shi ma halinsu ɗaya da abokinsa da na iske a wannan gida ya yi wasarere, gabaɗaya halittar jikinsa na leƙowa waje"

Tana nan zaune sai ga Sadiya ta shigo ɗakin, dan ita Sadiya da farko ma ta ɗauka Innar ce ta kwanta a falon da yake Imran har kan sa ya rufa da bargon sai da t shigo ne ya buɗe ya mata magana cewar ta miƙo masa wayarsa a kan mudubi.

"Halima ashe dai mijinki bashi da kunya?"

"Me kuma ya yi Inna kin ce ya koma falo ya koma to me kuma kike so ya miki?.

"Ana ga yaƙi kina ga ƙura yo ai na ga yana so ya min kora da hali, in ba kora da hali ba ya za a yi ya san ba ku kaɗai bane a gidan, kawai ina zaune sai ganin mutum na yi sangamgam ya shigo falon babu neman izini gandaƙai-gandaƙai ko suturar kirki babu, da da sanyin nan ma amma ya zauna da kayan banza"

Sai lokacin Sadiya ta gane abin da Innar take nufi, ba tare da ta tanka ta ba ta É—auki wayar Imran tanjuya za ta fita Inna ta ce.

"Ki taho min da bargona a kan kujera, ki haÉ—o min da wannan sauran maltinar guda É—aya ta É—azu"

Tafiya Sadiya ta yi ba tare da ta ce komai ba, tana fita daga É—akin Inna ta rafka uban tagumi, idanunta a kan gadon Hassan.

"Ni Azumi da zan yi kwana Hamsin amma tun ban kwana ɗaya ba na fara fuskantar abubuwa, ga yaro mai bayan miciji ga ubansa yana yawo da jiki babu maraba fa tsirara, haka kawai lokacin fatarar nan fa ake rashin kuɗi ya je ya sa in gamo da ganin al'aurarsa, ni Azumi in shiga uku in ma ban makance ba" Ta faɗa a zuciyarta dai dai nan Sadiya ta dawo ɗauke da bargon da maltinar, ta miƙa mata dama ta buɗe mata kwalbar maltinar. Haka ta kafa kai ta shanye tas ta miƙa kwalbar kan mudubi ta ajiye, lokacin Sadiya tana shan magungunanta.

"Ni da nake ta shan maltina kayan ruwa, ko ya zanyi da fitsari, dama ya lafiyar kura bare ta yi hauka, ni mai yawan fita fitsari cikin dare, bare na cika cikina da kayan ruwa, wannan kurman mutumi falo" Ta faÉ—a tana kallon Sadiya.

"Shi da yake gefe É—aya a kwance kuma ina ke ina shi"

"A'a Halima nake ƙetara mutum ina fita wa ya san fita nawa zan yi"

Sadiya dai bata kulata ba ta yi shirin kwanciya ta hau gadon ta kwanta.

"Inna ki kwanta mana, na ga dai gani gaki gani kuma menene zai hanaki kwanciya?"

"Hankalina a kwance yake, kawai dai ina jin kunyar gadon ne, yo na kwanta a gadon yara"

"Sai ki kwanta mana, ai babu komai ke da jikokin ki"

Wannan kalaman da Sadiya ta mata yasa ta ji ƙwarin gwaiwa ta kwanta ta rufa da bargonta, ita ma Sadiya gadon yaran ta tashi ta maido gefen gadonta kusa da ita dan ma haɗe yake da net ɗinsa sauro ba zai cije yaran ba.

~DARE~

Wajen ƙarfe biyu na dare Imran ya tashi zaune, dan dama ya ji tashin Sadiya wajen ɗaya saura yaran sun motsa, ya basu ruwansu yana dai ji har ta kwantar da su, bai sani ba ko sun sha nono ko kuma nonon bai zo ba, sa'a ma aka yi yaran ba wasu masu rigima bane. Ɗakin tsit baka jin komai sai ƙaran minsharin Inna tun da ta kwanta bata motsa ba, haka ya tashi cikin sanɗa ya leƙa bedroom ɗin sai da ta tabbatar bacci suke sannan cikin sanɗa ya shiga ɗakin drower ɗinsa ya buɗe ya ɗakko farar jallabiyarsa, tare da wata farar rigar sanyi mai haɗe da hula, haka ya lallaɓa ya rufe drower ya fita ba tare da sanin su ba, dan Inna kamar wata gawa haka kawai sai sakin munshari take.

A ransa ya ce

"Kina wannan munsharin koma me mutum zai yi da matarsa sai ya yi baki sani ba, ya faɗa yana jan tsaki tare da yin ƙwafar ganin Inna ta maye gurbin makwancinsa. Jallabiyar ya sanya sannan ya ɗora rigar sanyi a ka sai ya bar zip ɗin a buɗe, haka ya fita ya je bayin nasu ya cire ƙwan fitilar ya dawo ya kwanta.Zuwa can ya ji motsin Inna ta tashi tana cewa.

"Dama na san dole na tashi fitsarin nan duk ya cika min mara"

Da hanzari ya ɗakko filillikan kujera, ya jera a kan katifarsa ya dai daita su kamar mutum ya rufe da bargo, yana gamawa ya lallaɓa ba takalmi
ya tafi banÉ—akin.

_INNA_

Haka ta tashi ta kunna fitilar É—akin, ta kalli Sadiya da ke baccinta cikin kwanciyar hankali ta ce a fili.
Chapter 12 · 0% Book details