← Book details Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 19

Sashe 15

Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ta fito ta ga Imran yana kan katifar ya sanya filo ya jingina da jikin kujera yana latsa waya. Ko kallonsa bata sake yi ba ta fita , wajen da aka tanada tukunya da ita ce ta nufa ga wani ƙaton murhu wanda zai ɗauke tukunyar.Kallon tukunyar kaɗai ya sanya Inna zaro idanu tana tunanin ta yadda za ta ɗor tukunyar haka ta sassaka itacen a murhun ta hura wutar tana ta ɗari-ɗari da tsakar gidan sai take ganin kamar aljanin nan zai fito, har dai ta kammala ta shiga kokawa da ƙatuwar tukunyar dakyar ta ɗorata a kan murhun sannan fa ta je take ɗakko ruwa tana zubawa a ciki sai da ta cika sannan ta rufe ta dawo ɗaki.

"Ina kwana Imirana"Inna ta gaishe da shi jin bai gaishe da ita ba.

"Lafiya ƙalaw" Ya faɗa idanunsa na kan wayarsa.

"Idonka da kunya nangaisheka ka amsa Imirana, dan rashin kunya in zo gidankanZAMAN WANKA in kwana amma a ce ni zan gaisheka?"
Shi dai bai ƙara cewa wani abu ba.Haka ta rinƙa komawa tana iza wutar har ruwan ya yi zafi, ta kwalfa ta kai bayin tana ta addu'a ba dan Sadiya ba za ta iya kai ruwan ba da a ƙofar bayin za ta ajiye. Haka ta yiwa Sadiya wankan nan da ruwa mai zafin tsiya sii tururi yake amma haka ta laflafta mana da tawul, sai da ta gama sannan ta haɗa mata ruwan da za ta shiga ciki wanda aka zuba dettol a ciki, dakyar Sadiyar ta yarda ta zauna.

"Yo wannan har wankan jego ne Halima wanka da tsumman tawul, mu lokacin mu da runhu ake yin wankan ruwan kan tafasa har sai ya yi ja, sannan a sanya ka tsugunna a kan garwashi"

"Garwashi fa Inna"

"Eh mana a sanya turaren gabgab a ciki har sai ya ƙone za ka tashi, amma ke yanzu da wannan jikin duk faci wa zai sanyaki tsugunna ɗinkin naki ya farke bayan ruwan da za a shiga ma cewa suka yi marar zafi sosai"

Haka dai ta fito ta bar Sadiya a zaune a cikin ruwan ta zo ta haɗa wanda za ta wanki Hussaini dan bata ma san yadda za ta wanki Hassan ba dan bata so ma ta ga bayansa bare har ta masa wanka, dan duk maganar nan da ake fa bata yi ido biyu da bayan Hasan ɗin ba.Husssimin ta wanka ta gasa wa cibiya ta shirya shi tsaf, haka dai ta zubar da ruwan ta ƙara haɗo wani na Hassan ɗin danbata so ma dai amma haka za ta daure saboda ita ta ce ta ji ta gani za ta yi ZAMAN WANKA. Bayan ta ajiye ruwan dama Hussainin Imran ta baiwa da yake a bedoom ɗin take musu wankan.Har lokacin Sadiya bata fito daga bayi ba.Inna hannu na karkarwa ta ɗakko Hassan da ke ta bacci haka ta shiga rabashi da kayansa zuciyarta na lugude, shi kwa ya shiga yantsara kuka jin an tashe shi daga baccinsa.Sai da ta tuɓe shi tana ɗauke idanunta sannan ta kalli yaron wani irin zabura ta yi ganin yadda bayansa yake.

"Lahaula wala ƙuwwata illah billahi aliyal azim" Ta faɗa hankali tashe.

"Imirana! Imirana!Imirana!!" Ta shiga zabga masa kira hannunta riƙe da yaron jikinta sai rawa yake...

Masu son grp na zaman wanka 09030283375.🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼

(KWANA ARBA'IN)

NA

MAMAN AFRAH

🅿️9️⃣

```TASALLAH```

Tun da Inna Azumi ta fito daga turakar Malam ranta ya kai ƙololuwa wajen ɓaci, hankalinta ya tashi, ji take tamkar ta je ta dokewa Inna Azumi ƙafa ta karyata katsak ta ga da ƙafar da za ta tafi birnin, ta san dai duk nacin son tafiyarta ba ta tafi da ƙafa a karye ba.Ta so ta nemi alfarmar Inna Azumi a kan ta tafi da ita ko ta ga yadda birni yake amma kuma girman kai rawanin tsiya ba zai barta ta aiwatar da hakan ba, ko ma an yi hakan to kuwa ta san ba za ta tsallake zunɗen mutanen gari ba, a kan cewa ta tafi dangin kishiya shishshigi da neman ɗuwawun zama, bayan nan ta san duk sanda suka dawo ta jawa kanta gori har da gore-gore daga Inna Azumi wanda babu ranar ƙarewarsa .

Takaicin kishiyar tata take ta ƙoƙarin dannewa, wai har da cewa ta riƙa mata sana'ar ƙuli-ƙuli, wannan abu ya mugun tsaya mata a rai. Wato saboda ita basu da kowa a birni hasali ma bata san hanyar da ake bi aje birnin ba, shi ne Malam zai bata izinin tafiya ZAMAN WANKA har kwanaki hamsin saboda yana tsoronta.

"Tasalla ki cigaba da bani labarin mana ke d kike bani labari amma kin yi shiru kamar ruwa ya cinyeki" Cewar Malam ganin tun fitar Azumi Tasalla ta sunkuyar da kai ƙasa ita ba mai zaman makoki ba ita ba mai lazimi ba, gata nan dai kamar an dasa ta.

Dakyar ta danne wani wahaye da yake ƙoƙarin fin ƙarfinta, ta yi dariyar yaƙe ta ce.

"Ai a nan labarin ya ƙare" Ta faɗa kan nata dai a sunkuye dan tana ɗagowa hawaye ne zasu malalo mata.

"Ikon Allah ke fa kika ce mahaukacin ya biyosu suna ta shirgar gudu a titi ana ƙafa mai na ci ban baki ba, ai labarin daga ji ba a kai ƙatshensa ba amma kuma ki ce ya ƙare" Malam ya tambaya mamaki fal fuskarsa.

"Na ce maka a nan labarin ya ƙare" Ta faɗa ƙwalla na cika idanunta daf take da gangarowa amma ta hanasu fitowa dan kissa da kisisina, dan kar Malam ya ce dan Inna Azumi za ta je birni take yin kuka dan tun da ta share hawayen farko a ɓoye bata bari wasu sun biyo bayansu ba.
"To ai shikenan, bari na fita na ga tafiyar Azumi kar ta ɗauki ƙafa cewar ko tafiyarta ban gani ba, haka ya ɗora babbar rigarsa a kan kayan jikinsa ya fito ya barta, dai dai an ɗakkowa Inna Azumi kayanta.

Tasalla kwa na ganin fitar Malam sai ta fashe da kuka tana jin ina ma ita ke Æ´an uwa a birni ta zo tafiya Malam zai rakata ya ga tafiyarta a bi da ita ta tsakiyar gari tana washe baki.

Amma ina gabaɗaya danginta a ƙauye suke, Malam tana jin lokacin da Malam ke cewa Inna Azumi jakar nan kamar wanda za ta ƙaura hakan ya sanya ta tashi ta leƙo ta tagar ɗakin Malam ɗin aikuwa ta yi ido biyu da jakar Inna Azumi da ke shaƙe da kaya almajiri na riƙe da ita.

"Wayyo ni dama ban haɗa kishi da wacce take da dangi a birni ba da na huta da baƙincikin tafiyar Azumi" Ta faɗa a ranta tana sharar hawaye. Tun da Malam ya fita bai dawo ba har ta gaji da zaman ɗakin masa ta fito ta koma ɗakinta, dan lokacin da ta fito ma da ta yi tozali da ɗakin Inna Azumi rufe da kwaɗo sai da ta ji kamar ta yi ta zabga ihu da kururuwa mutane su kawo mata ɗauki, dan halin da ta tsinci kanta a ciki.

Tana shiga ɗakin ta zauna a ƙasa ta shiga rasga kuka kamar wata ƙaramar yarinya kowacce aka ce ubanta ya mutu, sai da ta yi mai isarta ta nemi wuri ta kwanta tana ta saƙar jaki, ta saƙa ta kwance, addu'a take ta yi a zuciyarta Allah ya sa Inna Azumi su faɗi a machine ta ji ciwon da zai hanata tafiya birni ZAMAN WANKA. Jin shiru-shiru bata dawo ba kuma ba a kawo mata wani labari ba ta san cewar Inna Azumi ta tsallake.Haka ta tashi tana ta ƙuncin rai ta ɗora tukunyar danbun rana tana jin a ranta cewar yanzu kenan ita za ta ke ta ɗorawa da sauke wa tun da Azumi birni ta ɗauka.

A haka ta kammala danbun ta raba ta baiwa kowa nasa, Malam kuwa saƙon tafiyarsa wani ƙauye kusa da su ɗaurin aure ya aiko mata, hakan ya sanya ta zuba danbun nata ta shiga ɗaki, zaune take a ɗakin nata ta sanya danbun a gaba amma saboda tsabar kishi da baƙinciki ta kasa cin ko da loma ɗaya ne.

"Ni da cin danbu yana shaƙe min wuya ina korawa da baƙin ruwa ita kuma tana can za ta ke cin shinkafa da miyar ɗanyen kaya ta kora da lemon kwalba ta yi kuɓulɓul da ita" Ta faɗa tana jin wani takaici. Haushi ne ya sa ta sanya ƙafa ta hankaɗe kwanon danbun ba tare da ta ci ko da loma ɗaya ba.

Bayan ta kammala tuwo dab da magariba, lokacin Malam yana waje wurin almajirai ana karatun yamma. Ɗaki ta koma har lokacin ranta ba daɗi a kan tafiyar Inma Azumi birni dan wunin yunwa ma ta yi saboda baƙinciki. Tana ɗakin ta tsinkayi sallaɓar Tsahare aminiyar Inna Azumi, duk a tunanin Tasalla Inna Azumi sun faɗi a machine ne Tsahare ta samu labari ta taho dubiya.

"Wataƙila tana asibitin bayan gari" Ta faɗa tana tashi har da taka rawarta ita ala dole Inna Azumi bata samu tafiya birni ba, sai da ta gama taka rawarta ta ɗaga murya ta amsa sallamar Tsaharen, ta fito baki a washe tana ta fara'a kamar ranar salla.

Mamaki ne ya kama Tsahare ita dai ta san duk ranar da ta zo gidan nan konda Tasalla tana tsakar gida Inna Azumi na É—aki to kuwa Tasalla ba za ta amsa sallamarta ba sai dai Inna Azumi ta amsa mata, amma sai gashi yau wai ita ce har da washe mata baki. Gaisawa suka yi cikin mutunci Tasalla tana jira ta ji ta ce mata ya mai jikin amma sai ta ji ta ce.

"Ikon Allah ashe dai da gaske ne?"

"Hatsarin wai?"

"Subhanallahi! Su waye kuma suka yi hatsari?"

"A'a ba hatsari aka yi ba, kawai dai na faɗa ne" Cewar Tasalla cikin wayancewa ganin babu alamar Inma Azumi ta yi hatsari dan ga mamaki nan ƙarara a fuskar aminiyarta.

"To da mai kike tambaya da gaske ne?" Tasalla ta faɗa tana tana wani haɗe rai tamkar ba ita ce ke washe haƙora ba yanzu, jin haƙarta bata cimma ruwa ba.
Chapter 15 · 0% Book details