← Book details Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 19

Sashe 17

Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kan ta kai ƙarshen maganar Imran ya sanya hannu ya karɓe ɗansa cikin zafin nama da jin haushin Inna yana raya wani abin da zai mata dan bashi ta ɗauka cewa ɗansa ɗan ruwa da ta yi.

"Wash Allah, ai gwada da ka karɓeshi, ai dama kowa da kiwon da ya karɓeshi wai maƙocin mai akuya ya sayi kura, wato ga Inna ƙaramar danga mai daɗin tsallaka, kamar ni a ce a sanya min linzami a baki yo da bakina wa zai hanani magana, aikin banza harara a duhu" Ta faɗa lokacin da ta sauke wata ajiyar zuciya ta tashi ta zauna a bakin gadon tana sakin maganganu. Wani kallo Imran ya watsa mata yana ji kamar ya shaƙeta.

"Aikin banza harara a duhu, ni ban san harara ba sai ido ya faɗo" Ta faɗa tana tana gyatsinan gefen hanci.Imran da ke ƙoƙarin fita daga ɗakin sai kawai ganin kan Hassan ya yi yana wani kamar lanƙwasa kawai sai ya koma kamar yadda kan maciji yake lokacin da ya fasa kai, sai ganin fatar cikin yaron ma ta fara komawa irin fatar bayan, Inna bata lura da abin da ya gani ba dan haka cikin sauri ya kalli ƙasa inda shawul ɗin Hassan da Inna ta ajiye ya ɗorashi a hankali, cikin hanzari ya fita daga ɗakin tare da rufe ƙofar ɗakin ya sanya mukulli.

Inna da ta lura da fitarsa bata san ya ajiye Hassan ɗin ba sai ƙaran rufe ƙofar kawai ta ji, Ta zabura za ta tashi sai ji ta yi Imran ya ce

"Inna kalli Hassan ki gani gashi nan na ajiye miki shi"

Idanu Inna ta zaro ganin fatar cikin yaron ta rikiɗe zuwa irin fatar bayansa, wani uban ƙara ta ƙwalla, dan yaron a setin hanyar da za ta sada ta da ƙofa yake gashi ma ta ji Imran ya rufe ƙofar tare da sanya mukulli...

Masu son grp na zaman wanka

MMN AFRAH 09030283375

🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼

(KWANA ARBA'IN)

NA

MAMAN AFRAH

🅿️1️⃣0️⃣

Last 🆓 page

Wannan littafin kuÉ—i ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

```MALAM```

Sai da aka yi sallar isha'i sannan ya shigo gidan dan tuwansa ma ƙofar gidan aka kai masa inda suke cin abinci shi da abokansa. Cikin gidan ya nufo bayan almajirai sun shigo masa da tabarma da butarsa cikin gidan dan dama yanzu basu da wasu yara a gidan sai almajirai. Duk an aurar da matan suna gidajensu haka ma mazan babu wani ƙaramin yaro yanzu. Sallama ya rinƙa kwalawa daga tsakar gidan Tasalla da ke cikin ɗakinta ta amsa masa dan yanzu dakyar ta daure ta ci tuwo kaɗan shi ma dan tana jin yunwa na neman kwantar da ita shi ne ta daure ta ci, amma ko tuwon ta ɗauka za ta sa a baki sai ta ji wani ƙululun takaici a zuciyarta dan tana tunanin Inna Azumi na can birni tana asuwaki da kaza.

Malam kuwa turakarsa ya sanya kai bayan ya ƙwalawa Tasalla kira kyawawa guda uku, haka ta tashi ta nufi ɗakin nasa tana kitsa yadda za ta yi kisisinar da zai barta zuwa birni dan ko sau ɗaya ne dai a rayuwarta ya kamata ta je birni ko da kuwa kwa Inna Azumi za ta tsireta idan ta je. Da sallama t shiga ɗakin ya amsa mata tana shiga ya ce.

"Wai ni Tasalla me yake damunki ne, ya za a yi ki bar É—akin nan babu garwashi kin san dai ja fi so a kawu wuta É—aki kafin in shigo gida É—akin ya É—au É—imi" Ya faÉ—a yana kallonta.

Shiru Tasalla ta yi dan ita gabaÉ—aya ma yau ta manta da zancen kaiwa wutar É—akin na Malam.

"Wallahi Malam sha'afa na yi ka san yau da gobe sai Allah"

"To sai ki je ki ɗakko yanzu idan baki kashe wutar ba in kuma kin kashe sai ki hura ko dai ki tafi maƙota ki samo" Ya faɗa yana ajiye hiraminsa da ya cire.

" A'a ban kashe ba ma dai cire itacen ne kawai amma akwai garwashi bari in ɗakko maka" Ta faɗa tana ɗaukan ƙaton kaskon wutar Malam ɗin.

Sai da ta ciko shi da garwashi sannan ta dawo ɗakin ta maida ƙofar ta rufe dan dama al'adar Malam ce daga isha'i ta yi yake shigowa gida ya rufe sai kuma gobe in Allah ya sa ana raye. Sai da ya yi shirin kwanciya ya kwanta amma Tasalla tana gaban kaskon nan tana kara hannayenta a jiki tana jin ɗumin wutar.

"Wai kam Tasalla yau duk wani iri nake ganinki ko baki so Azumi ta tafi ba?"

"kai, kai kai, Malam bar faɗa dan Allah, ni da ƴar uwata Azumi abokiyar zamana mai zai sanya na ƙi son tafiyarta"

"Yau É—in kuma Azumi ce Æ´ar uwarki Tasalla ko dai kin yi makuwa ne?".

"Ras nake wallahi, dama ai an ce zo mu zauna zo mu saɓa, amma ai ina ƙaunar Azumi"

Zaune Malam ya tashi da sauri yana ƙarewa Tasalla kallo dan bai taɓa jin hakan ba daga bakinta ko a mafarki.

"Allah sarki ashe akwai ranar da Allah zai nuna min irin hakan nan É—aya tana yabon Æ´ar uwarta ku da bakwa jituwa ko da wasa tun daga girmanku har tsufanku amma kuna faÉ—a sai gashi yau komai zai zama tarihi"

"Yoa ai ka san duk irin makaman yaƙin da mutum ya ɗauka idan ya ajiye nasa kaima ajiyewa kake, wai ɗazu baka ga shigowar Tsahare gidan nan ba?"

"Ni kwa na ga shigowarta dan har gaisawa mun yi"

"Wayyo ashe sai haƙata ba za ta cimma ruwa ba ashe sun gaisa ta faɗa masa me ke tafe da ita" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce.

"Ashe ma ta faɗa maka saƙon"

"Wane saƙo ai gaisawa kawai muka yi da yake da mutane sai kawai ta shigo ciki"

Wata ɓoyayyar ajiyae zuciya ta sauke jin bata faɗa masa ba dan hakan zai bata dama ta sheƙa ƙaryarta son ranta.

"Saƙon meye?"

"Malam kenan" Ta faÉ—a tana É—an sunkuyar da kai alamar tana jin nauyinsa da kunyarsa..

"Dan Allah ki faɗa min Tasallata daga ke ba ƙari"

"Yo na nawa kuma an ce da gwauro ya iyali, Azumin kuma fa da ka ƙaromin ko ka ɗauka na manta to ai in maye ya manta uwar ɗa ba zai yu ta manta ba"

"Ni ba na son tone-tone kawai ki faɗa min ko da na ƙaro Azumi ma ai kece babba kuma matsayinki da ban yake a wurina"

Wani irin washe baki Tasalla ta yi daÉ—i fal ranta masoyinta a yabe ta tare da jaddada yadda take a wurinsa.

"Dama Azumi ce ta baiwa ɗan machine ɗin saƙo ya je gidan Tsahare ya faɗa mata ta je birni sunan jikarta Sadiya, kuma ta zo har gida ta faɗa min mu tafi tare a sha shagali" Ta faɗa tana kallonsa.

Wani irin kallon mamaki yake mata wanda har ya so ya bata tsoro.

"Haba Malam kamar an faÉ—a maka wani mugun abu"

"Yo ba gwara mugun abu ba da wannan kk ma in ce meye marabar dambe da faɗa, Azumin da za ta tafi ya kuka kwashe da ke a ɗakin nan nawa, me yasa bata gayyaceki ba da bakinta sai bayan ta tafi za ta bada saƙo?"

"Malam kenan kai baka san sauyi ya kan zuwa wa mutuɓ lokaci guda ba, ina ga bayan tafiyarta ta ga dacewar hakan"

"Ko jikina kunne ne ai ba zan yarda ba cewa Azumi za ta gayyaceki sunan jikarta ba"

"To ai gashi nan yanzu ka gani ta aiko har gida ka san dai ba zan zauna in shirga ƙarya ba dan kawai ina so in je birni" Ta faɗa tana sanya hannu ta share hawayen kissar da ta ƙwaƙwulo.

Hakan ya sanya jimkinsa yin sanyi, ya ce.

"Ban ƙi taki ba Tasalla kawai dai abin ne da mamaki wai kiɗa a gidan makoki, amma tun da har ta faɗa babu dalilin da zai sanya na hanaki zuwa ai hakan kamar kawo gyara ne a zamantakewar ku Allah nuna mana"

Wani daɗi ne ya baibaye Tasalla har tana rasa inda za ta sa ranta dan daɗi, cikin murna ta yi kan Malam ta ƙamƙameshi tana ta dariya.

"Wayyo kin cukuikuye min wuyan riga Tasalla duk kin shaƙe min wuya, yashe rabon duniya da ayyaraye"

"Wallahi Malam duk daÉ—i ne ya cika min ciki"

"DaÉ—in daidaituwarki da sobar zamanki?"

"DaÉ—in zuwa birni dai" Ta faÉ—a a ranta a fili kuma ta ce.

"Wallahi kuwa Malam zama lafiya ai ya fi zama É—an sarki"
"Allah ƙara haɗa kawunanku"

"Amin Malam"

Haka suka kwanta Tasalla ko baccin kirki bata yi ba tana ta tsara yadda komai zai kasance Allah-Allah take gari ya waye ta je ta san ƙaryar da za ta yiwa Tsahare dan ta tafi da ita ranar sunan.

Da gari ya waye Tasalla bayan ta gama komai ta tafi gidan Tsahare ta same ta tana tuyar ƙosan siyarwa nan suka gaisa ta faɗa mata abin da ke tafe da ita kan cewa Malam ya tilasta mata zuwa sunan Sadiya dan a samu maslaha tsakaninsu, duk da Tsahare ta yi mamakin amma sai ta ce mata babu koɓai Allah ya nuna mana ranar, tun da dai ta san da kuɗinta za ta yi kuɗin mota kuma sauran diramar ta sha kallo tsakaninta da Azumi dan ta san ba za a kwashe ƙalaw ba muddin Azumi ta ga Tasalla a gidan sunan da ba ta gayyaceta ba dan lo lokacin bikin Sadiyar cewa ta yi babu inda Tasalla za ta je bare kuma suna.Haka ta baro gidan Tsahare ranta fari ƙal.

Wannna kenan.

```MAMA```
Chapter 17 · 0% Book details