← Book details Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 19

Sashe 16

Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni fa mai machine ne ya je gidana ya xe min wai Azumi ta ce ya faɗa min ta tafi birni ZAMAN WANKA babu ma ranar dawowarta, wai tafiyar ce ta zo mata a bazata, shi yasa bata je min sallama ba, wai in shirya in je ranar suna, to shi ne fa na ce bari in je gidan in tabbatar to kuma ina shigowa kwaɗon ƙofarta ya tabbatar min da gaskiyar al'amarin" Cewar Tsahare tana washe baki.

Wani haushi ne ya turnuƙe Tasalla kawai sai cewa ta yi.

"Wai sun isa Garkin lafiya kenan?"

"Lafiya ƙalaw dan mai machine ɗin da ya kaita ma ya ce sai da motarsu ta Kano ta tashi ya kamo hanyar dawo wa"

"To ai shikenan, kuma za ki je sunan?" Tasalla ta tambaya tana kafe Tsahare da ido.

"Zuwa kamar da ƙasa ma kuwa, kin san ko bikin jikar tata Sadiya wacce ta haihun yanzu mun je bikin kwanana uku, bare kuma samun ƙaruwa ai mu dole ne ma birni ta ɗauka" Ta faɗa tana washe baki dan ta turawa Tasalla haushi, tun da ba wani zama lafiya suke ba da Inna Azumi dan haka ko lokacin bikin ma bata gayyaci Tasallar ba.

Taɓe baki Tasalla ta yi ta juya ta shige ɗaki abinta, ita kuma Tsahare ta fita daga gidan tana jin daɗi cewar gaske ne Inna Azumi ta tafi birni ashe wannan karon ma akwai wankin ciki da na baki.

Tasalla na shiga ɗaki ta rinƙa gewaye -gewaye ta rasa abin da yake mata daɗi, dan haka ta ci alwashin da Tsahare za su je sunan nan sai dai ta fanjama fanjam ta san abin da za ta faɗawa Malam ya barta su je birnin.

```MAMA```

Tun a napep ɗin suke ta jajanta halin da zaman Inna zai kasance a gidan Sadiya yadda Imran yake da faɗin rai ga girman kai rawanin tsiya, bugu da ƙari ma baya ƙaunar mutane su raɓeshi, ga Inna kuma da ɓaranɓarama, kwata -kwata bata yin abin da ya dace sai ta saki baki ya layar mai tafiya ta rinƙa zuba kamar lalataccen famfo babu ruwanta da mijin Sadiyar bare kuma mahaifiyarsa, tabbas dai akwai gwarama dan Imran ba ƙyalewa zai ba ita ma kwa Innar bata tsoron ta mutu bare ta yi rai kawai komai ta fanjama fanjam.

"Amma Mama bakya gani tsofa ne ke sanya Inna waÉ—annan abubuwan?" Ashrof ta tambaya tana kallon Mama.

" Haba Ashrof ko ma da tsufa ai da sha'anin Inna wani abin ai dole take kauda kai, ki ga fa daga cewa Sadiya tana naƙuda shikenan ta haɗo kaya shimili guda ta taho ZAMAN WANKA, ba tare da ta sanar da kowa ba"

"Kuma haka ne, amma gaskiya ya kamata ta canja halinta Mama ko dan take ja mana girman mu a wajen Hajiya da kuma Imran É—in ma dan irin wannan ai sai ya ta ja mana raini"

"Yo na nawa kuma an ce da kuturu a gama lafiya, ai sai dai kar a ƙara kuma in da sabo ai su ma zuwa yanzu sun san wacece Inna"

"To Allah kyauta"

"Amin"
A haka dai har suka isa gida suna fitowa daga napep É—in Mama ta buÉ—e musu gidan suka shiga. Bayan sun É—an huta suka rama sallolin da ake binsu, sai Ashrof ta fita ta siyo musu awara suka ci suka kwanta suna Æ´ar hira.

"Wai Mama baki lura da yadda idon Inna suka firfito ba lokacin da zan miƙa mata hassan, bakinta sai mutsi yake kamar mai zikirin safiya da maraice" Ashrof ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya.

" Yo tsoronsa fa take, dan ta ji an ce fatar bayansa irin ta miciji, ban da Inna menene na tsoro ita da za ta yi ZAMAN WANKA, wankansu fa da shirya su har ma da goyo da raino duk ita fa za take yi" Mama ta faÉ—a tana Æ´ar dariya hasasho yadda za ta kaya tsakanin Innar da Hassan da ma ubansa Imran.

"Allah Mama ni fa tausayi take bani, yanzu wanann ƙatuwar tukunyar ta yaya za take ɗorawa a murhu da ruwa ai ba za ta iya ba ma, idan kwa ta tarka wallahi wataran sai dai ta tumbulu cikin ruwa dan hantsilawa ciki za ta yi" Ashrof ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya.

"Baki da dama Ashrof wato dan kin ga Inna bata nan ko, shi sa kike faÉ—ar hakan amma da tana nan si ta baki amsa dai dai da ke"

"Mama har hango Inn fa na yi ta faɗa ruwan tana iyo kamar kwaɗo tana neman ɗauki, Yaya Imran yaƙi fiddota, tana cewa Imirana ka ji tsoron Allah ka fiddoni, idan na mutu nauyi ya rataya a wuyanka, shi kuma ya ce mata in kin mutu dama kwananki ne ya ƙare" Ta ƙarasa faɗa tana dariya har da riƙe ciki hango yadda za a yi diramar kawai take.

"Ke ki kiyayeni, in ke kakarki ce ai ni uwa ce a wurina" Mama ta faÉ—a tana dariyar ita ma, dan ta san tabbas da ace hakan za ta faru Imran ba zai fito da Innar ba musamman in aka ce Sadiya bata kusa ko da zai fito da Innar daga tukunyar to sai ta sha wahala ita ma kuma idan ta fito sai ta rama ta wata hanyar dan bashi ya ci daga haka suka kwanta abinsu.

```HAJIYA```

Tun da ta sauka a napep ɗin ta shiga gidan nata jiki sanyi ƙalaw dan kwata -kwata haɗin Inna da Imran bai yi ba musamman da ya kasance za ta shiga haƙƙinsa na rabashi da kwana wuri ɗaya da masoyiyarsa dan ta san Inna ko giyar wake ta sha ba za ta bari su kwana ɗaki ɗaya ba ma bare kuma wuri ɗaya sai dai ta san Imran dai dai yake d Inna duk ta yadda ta ɓullo masa sai ya zame duk da dai ta gargaɗeshi a kan zaman Innar a gidan.

```INNA```

"Imirana kar ka jinkirta wajen amsa kirana dan Allah ina cikin halin ƙaƙanika yi" Cewar Inna har lokacin hannunta da gabaɗaya jikinta ma tsuma suke suna karkarwa kamar an jona jikinta a wutar nepa ko transpomer.

Imran kuwa yana jinta banza kawai ya mata dan ya san zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi, tabbas ya riga da ya san cewa arba kawai ta yi da bayan Hassan. Jin kiran nata ya cika masa kunne tare da karaɗe gabaɗaya gidan hakan ya sanya ya kwantar da Husaini a kan kujerar ya tashi a hankali ya leƙa ta jikin labule ba tare da ta sani ba.

Hangota ya yi a zaune magashiyan ga uban baho É—auke da ruwa, sannan ga Hassan É—in a hannunta sai jijjiga hannunta ke yi.

"To fa ga zara ga wata" Ya faɗa yana komawa ya zauna a kujera yana dariya ƙasa -ƙasa yadda ba za ta jiyo ba.

"Imirana wallahi ina cikin matsala dumu-dumu, ka zo kar yaron nan ya koma maciji gabaki ɗaya, in shaga uku, dan idan na ganni da riƙe da miciji muraran babu shamaki suman da zan yi sai ya fi cikin carbi idan ba dakyar ba ma na ƙarasa ƙiyama a haka" Inna ta faɗa tana sakin kuka.

Jin shiru dai babu alamar motsin Imran gashi ta san ko ta kira Sadiya ba jinta za ta yi ba dan tana can a bayi, kuma bayin a rufe, sannan ma ita kawai so take a taimaketa a rabata sa yaron a karɓeshi daga hannunta dan ta ma kasa jajiyeshi.

"Imirana wallahi mutsu-mutsun da yake a hannu na yana motsi ji nake kamar maciji na riƙe, yo ina daɗi ace ina riƙe da ajalina, yo maciji ai mutuwa ne, wannan ai mutuwa kusa ne" Ta faɗa tana ɗaga muryarta dan Imran ya kawo mata ɗauki.

"Wannan tsohuwa da zan san inda MALAM Abubakar bilhaƙƙi mai magununan nan da ake tallarsa a tv wallahi da na ce masa ya zo ga wacce za take masa talla ba sai ya sha wahala ba dan tsaf za ta ke karaɗe gidan talabijin da wannan shegen surutun nata marar kan gado marar kai da ƙafa.Ya faɗa yana tasowa daga kan kujerar ua nufi ɗakin.

"Yawwa É—an albarka ai gwara da ka tausaya min ka zo"

"To wai meye kika dameni da kira kamar wata makauniya" Ya faÉ—a yana kallonta.

"Haba Imirana da rashin kira karen bebe ya ɓata"
"To gani ai"

"Riƙa nan riƙa Imirana" Ta faɗa tana ɗago Hassan ɗin.

"Kamar ya na riƙa Inna, ni zan masa wankan ne?"

"Haba Imirana shin kusan haka jikin yaron nan yake amma aka bari na tuɓeshi tsirara na yi mugun gani"

"To menene a ciki"

"A'a sa komai a ciki mana, kasan kowa da kiwon da ya karɓesa wai maƙocin mai akuya ya sayi kura"

"Ki masa wankan mana"

"To inda riƙeshi in dubo Halima a bayi"

"Haba Inna in mafaÉ—in magana wawa ne ai majiyinta ba wawa bane" Ya faÉ—a a zuciyarsa a fili kuma ya ce.

"Bari na dubo miki ita da a kan dubo Sadiyar ne kike ta wahalar da kan ki har da kuka Inna"

"Ka karɓesan dai ni na dubo ta, ka san mutum baya ƙin ta mutane wai an ce ɓarawo ya gudu"

"Inna magana fa zarar bunu ce, ke kika ce mun san jikin yaron nan haka yake kika tuɓeshi yanzu kuma kin canja maganar kenan"

"Bari dai in fito maka a mutum Imirana, karɓi yaron nan dan ba zan iya tashi in ɗorashi a gadonsa ba saboda yadda jikina ke tsuma ga arangamar da na yi jiya da dare duk jikina ciwo yake, ka karɓeshi kar in je in luntumashi a ruwa, dan ni ban ma yarda ɗan mutuma bane wannan"

"ÆŠan nawa ne ba É—an mutum ba, to wallahi kika saka shi a ciki sai mun yi shari'a"

"Yo in ba ɗan aljan...Shiru ta yi da faɗar aljannun tunowa da ta yi da yadda suka kwashe da aljani da dare har ta ƙarasa kwananta a ƙasan gado hakan ya sa ta saki akalar maganar ta kama wata.

"Da za ka yarda ku kai shi bakin ruwa a gani indai ya gangara ya shige ruwa to dama É—an ruwa ne, in ba haka ba tayaya zai yi rabi mutum rabi miciji"
Chapter 16 · 0% Book details