← Book details Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 19

Sashe 4

Yar Zaman Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ƙauyancin uban wa? Na ce ƙauyancin uban wa, to tun kafin a haifi uwar mai sabulu farfela take da farinta" Ta faɗa tana jin kamar ta saki fitsari dan gabaɗaya an dagula mata lissafi ga yunwa ga wani fitsari da ya cika mata mara ga wannan jijjigar da napep ɗin ke yi sai ta ji a ranta ta fara ɗan da na sani kaɗan ba da yawa ba na tahowa ZAMAN WANKA, da tana gidanta da yanzu ta ci ta ƙoshi tana bacci ko kuma tana kama ƴan kuɗaɗenta daga masu zuwa siyan mai da ƙuli amma wani ɓangaren na zuciyarta sai ya bata ƙwarin gwiwa.

"Kar ki karaya bayan wuya sai daɗi, daga yau ne fa wahala ta ƙare za ki fara cin kayan daɗi" Wani murmushi ne ya suɓuce mata har sai da ta ɗan rausaya kai.

"Ka daina zabga wutar nan haka gudun ya yi yawa"

"Bakya ganin yadda wanda muke bi yake gudu kamar zai tashi sama.

"Rabu da Imirana mugun hali ne da shi ka yi tafiyarka a hankali ka ji"

"In ya ɓace mana ke zaki kaimu wajen da za ku je?"

Shiru ta yi bata ƙara magana ba, wata kwana Imran ya shiga dai dai wani gida ya faka machine ɗin ya sauka ya faka machine ɗin ko kallon su Inna bai yi ba ya tura gidan ya shiga.

"To ki fito mana tun da mun zo ashe ma babu wani nisa sosai"

"Nan ne asibitin?"

"Asibiti kum?"

"Eh mana asibiti za mu je"

"Haba Hajiya nan ya miki kama da asibiti nan ai gida ne"

"Gida kuma, wai ni me ya sa Imirana ya raina mutane ne haka, ya za a yi ya shige wani gida ya bar ni ko bayani ba zai mini ba" Ta faɗa tana saurin sakkowa daga napep ɗin ta ce mai napep ɗin ya jira ta, a fusace ta tura ƙofar ita ma ta shige tana shiga ta ga wani ɗaki da ke a farkon shiga gidan, bata yi wata- wata ba ta bankaɗa labulen kawai sai ganinta suka yi bakam ta shigo kamar an jefo ta.

Wani kallo da Imran ya jefawa Inna Azumi shi ya sanya ta wayance ta ce

"Ikon Allah ashe ba mu zo asibitin ba, wallahi duk zatona ɗakim haihuwar ne nan" Ta faɗa tana saurin juyawa ta fito da sauri dan shi da wani da alama abokinsa ne ya miƙo wa Imran ɗin zamzam a robar zamzam. Abokin kuwa yadda Inna ta yi ya matuƙar bashi dariya, Imran kwa tsaki ya yi ya fito ya hau machine ɗin.

Inna kuwa mai napep ganin ta fito da sauri sai abin ya bashi mamaki har ya so bashi dariya.

"Kin masa magana?" Ya tambayeta lokacin da ta fito ta shiga napep É—in.

Inna da gabaɗaya take a ruɗe ba wai kallon da Imran bane ya sa ta gigice ba, abokin nasa ne babu kaya a jikinsa daga shi sai ƙaramin wando wanda ake kira inpant, to har ga Allah bai san ya yi wawan zama ba ashe Inna ta hango abu ya leƙo ta ƙafar wandon wannan ne abin da ya ruɗa ta dan ita yaushe rabonta da ta yi ido huɗu da bananar ma ta manta, dan su yanzu an tsufa, ganin bananar abokin Imran ne ya ruɗa ta, hakan ne ya ruɗa ta ta dawo da sauri har tana neman yin tuntuɓe. Dan da alama ɓa abokin nasa gwauro ne dan ɗakin nasa a bakin ƙofar gidan ne daga ciki kuma tana jiyo hayaniyr mutane daga cikin gidan.

" Ashe ruwa zai kama" Ta faÉ—a dan ta waske amma a ranta sai salati take ko idanu ta rufe sai ta ga abu kawai. Da haka dai har suka iso asibitin bayan sun sha uban gosulo. A wurin da aka tanada dan ajiye napep a nan ya sauke Inna haka ya yanka mata uban kuÉ—i ta bashi, dan Imran ko tsayawa bai yi ba bare ta sa rai zai biya kuÉ—in napep É—in.

Tana bawa mai napep ɗin kuɗi ta fara sauri-sauri gudu-gudu dan ta tarar da Imran dan machine ana iya zuwa da shi har ƙofar ɗakin da mutum zai je da ke asibitin na gwabnati ne, ashe da ɗan tazara zuwa ɗakin haihuwar dan haka kafin Inna ta kawo ta gama jigata dan ma tana iya hango Imran ɗin da yake wurin babu kwana bare ya ɓace mata.

"Oh ni da bani da kuɗi yau da na tagayyara, wannan yaro ko kaɗan bai san mutunci ba, uwarsa kwa ba haka take ba lallai albasa bata yi halin ruwa ba, na ɗauka shi zai biya min kuɗin tun da shi ya tsare ɗan sahun amma sai ni na biya, ko ma ya tsaya idan ma ba zai biya ba, sai ya ce Inna ki biya kuɗin amma shiru maƙatau babu niyya wai ango ya kwana da wando" Take ta zancen zuci har ta ƙaraso wurin ɗakin haihuwar.

🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼

(KWANA ARBA'IN)

NA

MAMAN AFRAH

🅿️3️⃣

Ƙarƙashin bishiyar da aka tanada dan zaman masu zaman jinya can ta nufa inda ta hango Imran ya yi, dakyar take iya ɗaga ƙafarta dan lokacin har an yi sallar la'asar amma Inna ba azahar ba la'asar dan wajen sha biyu ta baro ƙauyensu. Da jan ƙafa ta ƙaraso wajen da suke zaune a tabarma, dan tun daga nesa ta hango Hajiya Amina mahifiyar Imran, Ashrof ƙanwar Sadiya, sai kuma Ruƙayya mahaifiyar Sadiya, sai Imran da ke gefen mahifiyarsa da alama magana yake mata

"Wash Allah nah" Cewar Inna kamar an shaƙe mata wuya tana neman kan tabarmar ta zauna daɓas. Da mamaki suke kallonta su duka, Inna Azumi kwa saboda wahala ta ma manta da cewar ba a san da zuwanta ba.

"Inna!" Ashrof da Mama Ruƙayya suka faɗa da mamaki.

"Rakiya dan Allah ku taimaka min da ruwa wallahi maƙoshina duk ya bushe ƙamas ko yawu na haɗiye sai na ji wucewarsa wani garrrr yana cin birki saboda bushewar maƙoshin a maimakon na ji wucewarsa midik"

"Humm ai bari ba shegiya bace da ubanta" Cewar Imran a zuciyarsa dan yadda idanun Innar suka koma sun wani ƙanƙance kaɗai ya isa ya sanya ka dariya duk ta fita hayyacinta, ga gwaggwaron gaban goshin ya koma gefe har ɓangaren hagun ɗin ɗankwalin ya zamo ya ɗan rufe gefen idonta amma duk bata kawo a ka ba.

"Inna wai kin ganki kwa kamar wata maroƙiyar" Ashrof ta faɗa tana tuntsurewa da dariya.

Inna ji ta yi ba za ta iya magana ba, amma da sai ta ji amsa dai dai da tambayarta, amma ina! Babu hali. Hatta Mama Ruƙayya da Hajiya Amina dariyar suka ƙunshe ganin Innar a birkice sai wani faman nishi take kamar ta yi tseren gudu.

"Gashi Inna" Mama ta faɗa tana miƙa mata pure water guda ɗaya da ta ɗakko a cikin leda.

"Haba Rakiya kamar wata almajira, za ki bani ruwa ƙwalli ɗaya" Ta faɗa a fusace dan ita ba ma ruwan ɗaya bane ya ɓata mata rai, so ta yi Mamar ta ce mata ga abinci dan ta tabbatar yanzu idan ta sha ruwan nan cikinta ƙullewa zai yi.

Mama kwa faranti ta ɗauka ta ɗora ruwan har huɗu ta miƙa Innar, har lokacin tana mamakin zuwan na Inna Kano da ma yadda aka yi ta gane asibitin da suke.

Ruwan ta kalla guda huÉ—u ga cikon na biyar É—in a hannunta,ta ce.

"Kai Allah na tuba wannan ruwa kamar wata saniya ina zan kai shi ma son in sha ya ƙulle min ƴaƴan hanji, mu wallahi zamanin da ba haka muke yiwa baƙo ba sai mun fara gabatarwa baƙo sanwa (Abinci) Kafin mu kai ga bashi ruwa, amma yanzu zamani ya banbanta halayya wani wurin ma sai ka je baƙunta ka tafi amma ko ruwan ma ba zaka samu ba to amma ke kin yi ƙoƙari ma da kika bada ruwa har biyar da babu gwara ba daɗi amma da ace ko kaɗan kuna haɗawa baƙi da abinci duk ƙanƙantarsa ai da hanau ƙwara mannau" Ta faɗa tana sauke idanunta a kan wasu food flaks har guda uku da ke ajiye a gefe.

"Wai Inna dai ko yunwa kike ji?" Ashrof ta tambaya tana kallon Inna da sheƙiyanci ganin duk idanunta ya faɗa bakin nan a bushe kamar mai azumin nafila.

"Yo Allah na tuba yunwa sai ta karni za a san ina jinta, cikin nan nawa kaɓar an yi shara ko motsin ɗiyan hanjina bana iya jiyowa duk sun yi likimo ko kuwa suma suka yi" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce.

"Asharofa kar fa ki min fassara ato, ni ba wai ina roƙon a bani abinci bani kawai dai ina koyawa uwarki abinda ya dace ta yi ne, idan ta yi baƙi amma ba wai kaina nake yiwa tanadi ba"

"Wannan tsohuwa da shegen ɓatawa mutane suna take, wai asharofa sai ka ce wata tinkiya, ni ta ce min Imirana kamar wani gatari, sannan ko Sadiya ma Sa'adiyya ko kaɗan bata iya seta bakinta kamar wacce aka gutsirewa gefan harshe" Imran ya faɗa a ransa yana aika mata da harara a ɓoye.

Kunya ce ta rufe Mamar Sadiyar jin furucin da Innar ta yi, ga sirikinta ga Babar sirikin amma ko kaÉ—an Innar bata san kunya ba.

" To da yaushe ma ta zo, ko gaisawa fa ba a yi ba amma har ta ɗora min laifin rowa, ni ban taɓa ganin tsohuwa mai rangwangwan irinta ba" Mama ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce.

"Inna wallahi ina shirin baki abinci ne ka wai dai wani lokacin an fi fara gabatar da ruwa kafin abincin ne"

"A'a Rakiya a lokacin zafi ba amma a lokacin sanyin nan ai an fi jin yunwa a kan ƙishirwa, amma ba wai ina nufin ina cewa yunwa nake ji a bani abinci ba, kawai da ku ɗauka hira ne muke kowa yake faɗar abinda ya dace a yiwa baƙo idan ya kai ziyara " Ta faɗa tana bin su duka da kallo irin ko ba haka ba.

"Inna duk nan fa babu bare ko ma abinci kika ce a zubo miki ai baki yi laifi ba duba da irin nisan tafiyar da kika yi daga garinku zuwa nan" Hajiya Amina ta faÉ—a tana kallon Inna Azumi.
Chapter 4 · 0% Book details