← Book details Yar Lesbian Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 78

Sashe 6

Yar Lesbian Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Page.....7
Feenah ce Sanye cikin wani material milk colour yana dauke da Ratsin Brown Ajikinshi, dinkin Riga da Siket ne yazauna tsam Ajikinta Mayafi ta daura Akai Brown colour Haka takalmi da jakarta duk Brown ne, Wani Dan Siririn Agogo ne manne A hand dinta Sai wani zobe makale da yatsanta, Kai daka ganta Kasan Akwai Hutu Atare da ita Dan fatar jikinta luwai take, bawani make-up tayima face dinta ba Amma hakan be hana kyawunta fitowaba. Mumy ce ta turo kofar tace my daughter baki gama Shiryawa bane Haruna tun tune yake jiranki A waje fa, nagama mumy kinsan nace miki Tare Zamu tafi da Leemah bata karaso bane sai yanzu, yakamata Kifitoh haka nan, "Alright" Mumy nafito. Toh daughter fadan da namiki dazun Allah yasa yashigeki Sannan kinji Abinda da dadynki ya fada miki, Allah ya bada Sa'a kikula da kanki kinji, Zuwa tayi tace thanks mumy ta yayinda kuka yakeson kwace mata, Haba feenat banace banason Yawan kukan Nan ba idan bakya Son tafiyar ne Saiki fasa, da Sauri tasaki mumy tafara Share Hawayenta,mumy Ina Twins? Suna wajen Baba Ladi jekiyi musu Sallama, Zuwa tayi tasamesu Baba Ladi namusu wasa Suna dariya, Kissing dinsu tayi A kumatu daya bayan daya taima baba ladi Sallama, kukan mubeen taji Alama Yanaso yabita tajuya ta daukeshi mubeena itama tamika Hannu, Ina Zan iya daukanku duka Baba Ladi Dan Allah daukota muje bakin gate. Suna karasawa Mumy ta Amshi mubeen daker ya yarda Feenat ta shiga mota. Suna fita ta hango motar su Leemah Haruna tsaya. Yana tsayawa Leemah tafito tashiga, Leemah tayi fes Don itama badaga baya ba wajen kyau. daret hanyar Abuja driver ya dauka.
Karyar kika Zuba ma Mamy tayarda Zamu tafi tare ko? feenat tafada tana kare mata kallo, dariya Leemah tayi tace yau Kai tsaye nafada mata tadanyi fada daga bisani kuma tayarda........ Ai gara mumy bata So maybe wani Abun ya Sameki ne but Shifa daddy Kai tsaye yake nuna bayason wani da Namiji yakulani, Kinsan Wlh Leemah Ran nan da daddy yake waya da Inna Nafisa ta yola inaji tana cemai yakamata Aimun Aure tunda Shima da ya Auri matarshi bata kai yawan Shekaruna ba, Wai Sai ce mata yayi Yana tsoron mazan yanzu ko Anyi Alkawari Za'a cigaba da karatu Sai Anshiga Su hana, cemai tayi A hada ni Aure da babban yaron Uncle dina Nazir, Amma firrrr daddy ya kauce maganar da take mai, kuma Leemah Wlh kabeer yarone mai hankali da Addine Kuma dama addini Shine babban Abu mai taka Rawar gani wajen Niman Auren miji nagari, ke bama Haka ba babban Sojane wanda Kasar Najeria take Alfahari dashi, kuma Wlh Ga Kyau idan kika ganshi Kama da dadyna yayi Sak. Gaskiya feenah daddy yayi Nisa burinshi kawai yaga Ance yau ga yarshi tazama wani Abu toh baya lura da kedin macece? daya sani gaba daya burin nashi kan yaya Nazir dinku ya daura da yafi. Idan baki manta wani hadisi da muka taba yi muna Aji Shida A islamiyya ba, "Sahihul bukari ne" "Alkam ya Ruwaito hadisin" CEWA! "Watarana sayyidina Usman yasamu Abddullah bin Mas'ud (Abu Abdrrahman) Sai yace mishi ya Abu Abdurrahman Shin na Aura maka budurwa domin ta tuna maka da yarintarka" Awata Ruwayar kuma " Shin Na Aura Maka budurwa domin ta tunatar dakai Samartakarka" kinsan me wannan Hadisi yake nufi, wannan hadisin yana Gaya mana cewa Aure Shine kwanciyar Hankali kuma Aure Shi ke Samar da natsuwa. Ke Wlh duk Matar dakiga ko mijin dakikaga Suna korafe korafe Kan Cewa basu Samun natsuwa game da iyalansu Toh ki tabbata Soyayar da Suka Kullah Kamin Suyi Aure ba Soyayyar Gaskiya bace, idanma Ansamu wanda Suka kulla Soyayar Gaskiya din Toh tabbas Basu San Yaya Ake Sarrafa taba, Soyayya ba'Ita ke Haifar da natsuwa gidan Aure ba Sarrafa Soyayyar Shine Ke Haifar da natsuwa. Misali Atambayeki me kika fi So Arayuwanki Saikice Waina, Sai Akawo miki Waina har kashi biyu, dole wacce kikaci Kikaji tafi dadi ita Zaki yaba, Sanan Kuma idan kika gama Zakiso Kiji wacece ta Sarrafa wannan wainar. Toh Haka Abun yake idan Ma'aurata Suka iya Sarrafa Soyayya Zaman takewar Aurensu Zata daure Sosai. Kuma duk mace Ko Namiji da baya Samar ma dayanshi natsuwa Shine Zakiga Aure yana tabarbarewa. Bafa natsuwa ta kwanciyar Auratayya kadai ba natsuwa Zamn auren Gaba daya nake nufi. Manzon Allah S A W yace. Idan kuka Samu NamijI mai Addini da kakkyawar dabi'a Toh ku'aurar mishi da yar'uku ANNABIN ALLAH FA Akace, wanda duk wanda yabishi yashiga Aljannah, Haka kuma duk wanda ya kaucemai Wlh Saiya Koka. feenat kinga Addi da dabi'a mai Kyau Sone manyan Abu da Suke da Muhimanci game da Aure, Allah S.W.T yana cewa da Za'a kawo mahaifiyarka San'nan Akawo mazon Allah S A W Ace kazaba Allah yace Zaka Zaba Annabi ne. Yakamata ki fahimtar da daddy yagane Aure Shine darajar diya mace, ke kojiya Saida muka kara magana da Abba yace indai inada muradin Aure tare da tsayayen Saurayi namishi magana, feenat Kinsan mazan yanzu dole Sai Kana bincike Akansu Sosai. Kingani Anbani Zabi ballatana Ke dana fuskanci Sha'Awa gareki mai karfi, ina lura dake Sometimes Idan Muna Kallo ko Wani fira yanda kikeyi, Amma mucigaba da Addu'a Allah ze kawo mana Mafita. Feenat da tunda Leemah take magana ta mayar da Hanklinta duka Kanta tace besty kedin ta dabance wlh Shiyasa banida Abokin Shawara wanda ya huce ke, Allah yabarmu tare. Haruna dake driven duk yanajinsu yaran sun burgeshi kuma yadau Alkawarin idan yadawo Saiya ma Alhji magana gameda ya Aurar da feenah. AHAKA Suka karasa Abuja Cikin Makekeyar makaranta da Akayita domin mata Zallah. Sunyi komai cikin Lokacin Kankani hostile Suka nufa Ana ganinsu Aka duba sunansu kowacce Aka bata key din dakinta domin dama Anmusu komai kamin Su karaso, key daya Suka amsa Suka dire a wani makeken daki da gado ne kato a tsakiyarshi Sai wardrobe dake gefe, dauke Dakin yake da toilet dakin dai daidai irin yanda Su feenah kesonshi. Wanka duka Sukayi Sannan Sukay Searching Unguwar domin nemo wajen Abinci dadai wasu Abubuwan.
After 2 months
Su feenah Ankara Wayewa Suna kokari Wajen karatunsu domin yanzu gabaki daya makarantar Nan Ansan da Zaman NAFISA .U. IBRAHIM (feenah) da HALIMA .A. MUHD ( leemah) kowani Malami yana Alfahiri da Su da irin kokarinsu, Sun Samu wani malami wanda Suka ware lokaci yake koyardasu bangaren Islamiyya. Wanka kuwa babu wanda Ze nunamusu bare Uwa uba Kyau da tsafta, Komai Nasu Abun birgewane, gashi basa kula kowace Mace komunji dakanta, Lokaci Zuwa lokaci Kowacce Ana Zuwa mata daga gidansu. Shakuwa mai karfi takara Shiga tsakanin kawayen Nan biyu, matsalar dasuke Samu dayace yawan Sha'awa da feenat takeyi. Akwai wani Zuwa da Su daddy Sukayi Feenat tacire kunya Ta sanar dasu Mumy Amata Aure Amma Sukace Zancen Banza tafara karatu tayaya Zata yanke, data fahimtar da mumy Abinda ke damunta Cewa tayi Tarinka Azumi da Karatun qur'an Sannan duk lokacin da taji Tarinka Shan lepton da lemon tsami. Ahaka Rayuwa taci gabanmusu, Idan Leemah tace Zata gayama Mamy domin taje ta Samu mumy sai Feenat tace bataso Kunyar Mamy takeji haka Leemah ta hakura ta Rabu da Ita. Kowacce Tana Waya da brother dinta dake Kasar waje, duk Sanda Feenat ke waya da yaya Nazir saita bashi labarin Leemah, Shimakam yaya Nazir yaji Son ganin yarinyar, itakuwa Leemat da tafara ba Yayanta labari bayama Saurarenta Yake kashe wayar. Yauma kamar kullum Sunje wani Restaurant dake cikin garin Abuja Sunacin Abinci, Wasu yanmata Suka hango Su biyu Suna nufosu Suna karasowa dayar tayimusu Sallama. Amsawa Sukayi yayin Yayin Leemah tayi musu izini Su Zauna. Zama Sukayi dayar tafara magana Ni Sunana KAUSAR HAFIZ Wannan kuma ta nuna wata dake bata Rai Kamar bataso Zuwa wajen nasuba Sunanta KHADIJA AMINU. Leemah tace "Nice" yayin da itama ta gabatar musu dakanta da feenah. Kausar ce wow Ai na lura kuna Son junanku da Alama kundade tare domin tare nafara ganinku a Skul, Room dinmu Shibe No. 12 na yaba da Hankalinku Naga Ana kuyardaku Islam Shine Nida kawta mukeson Muyi joning dinku, da Sauri Khady tace kikeso kiyi dai Murmushi kausar tayi tace O.k. nakeson Nayi, feenah tace badamuwa mun Amince Amma Tunda ke kadai kikeso pls ke kadai muke bukata. Da Sauri Khady taja tsaki tabar wajen. ba Damuwa Ngd da karbata da kukayi Zanso nazo nakara muku gdy wajenku. Pls idan Zakizo kada kikawomana waccen Banzar dan Zan'iya marinta Leemah ta fada tana kara tamke face, Sannan Room dinmu 14 no ne, Sai kinzo dahaka Leemah taja hannun Feenah Sukabar wajen.
Chapter 6 · 0% Book details