← Book details Yar Lesbian Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 78

Sashe 39

Yar Lesbian Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Su feenah karatu Ake tukuru ba Sanya gaba dayansu yanzu sunmaida hankali kan karatunsu Kasancewar wata daya kadai y Rage musu su kammala.fatansu Ayanzu be wuce Su Samu Sufita da Good Result ba. Babu Abunda ya Ragu Cikin Soyayyar Leemah da Nazeer sai ma Abinda ya karu.Zuwa yanzu iyayen Nazir da iyayen Leemah Sun San Cewa Akwai maganar Aure Atsakanin yaran nasu biyu.Farin Cikin dasuka nuna baya misaltuwa dan har Walima Mamy tayi Acewarta Abinda ta Dade tanason ya kasance ya kasance. Rayuwar Kausar da Yusuf ma gwanin Sha'awa Suke yinta.baya wuce 4day's bezo ganin Kausar dinshi ba. Duk sanda yazo kuwa yana Samu ya rage Zafi Abu dayane Kausar har yanzu taki yarda Shine Yusuf ya kusanceta, Kunya takeji bangare guda tsoron Abunda Za biyo baya take.Leemah tasha mata fada kan tayarda da mijinta babu wata matsala Amma ina taki. Khadija babu yanda bataiba dan ganin ta dawo Cikin su Amma fir Sunki yarda da Hakan, feenah ce taja mata kunne kan kada takara takowa zuwa room dinsu,ba karamin takaici Ranar khady tayi ba dama haushin feenah takeji,dan haka tasha Alwashin Saita mata Fiye da Abinda tayi mata Ayanzu. Hankalinsu Ayanzu ya Rabu biyu Ga Exams din dasuke Shirin yi gakuma bangare guda malamin dake koyar dasu islamic yasasu Sunemo Topic Akan matsalar Matan Aure Ayanzu! Yace Hakane Ze gane cewar karatunshi ya Zauna ko Aa.Zasu gudanar da walima Ranar dazasu fita dan haka Ranar Zasu gabatar da program din. ZUWA yanzu Atsakaninsu Suke tattauna yanda zasu gabatar da Abun domin sunason faranta Ran malaminsu Aranar walimar. Mr yazeed har Yanzu be Samu wacce tayi daidai da Ra'ayinshi ba dan haka yanzu ya bar Zaben Allah agareshi. Matsalar daya yanda Abba ya takurashi yasamo matar Aure yabashi lokaci kankani,yace idan besamu ba Akwai wata yar Abokinshi ita Zaiba yazeed din. Haka Rayuwa tacigaba Kowa da tashi damuwar Arai. Yau tunda Inno ta farka take jiran Abba yasakko Kasa. Abba na sakkowa ta tareshi Amadi katashi lafiya ko? Lafiya qalau inno yanaganki da kaya haka? Yawwa Amadi yola Nakeson Zuwa Ayau din nan! Yola kuma inno me Zaki Achan? Yau naga ikon Allah tsareni Zakai da tambaya,danfa Kada kanemeni ne yasa nafada maka dayanzu na tafi ma ni. Mamy dake Sakkowa tace Ayi hakuri mamah munason musan wajen wa Zaki! Wajen Aminiyata zani Nafisatu kakar Nazir. Ayya inno Zumunci Zaki hakan yayi dadai Ai. Aikuwa fatima nadade banga Nafisatu ba gara Muma murinka Zumunci da Sauran lokacin daya rage mana. Allah yakaro muku tsawoncin Kwana da lafiya mai Amfani Abba ya fada.Atare inno da mamy Suka Amsa da Amin! Inno yazeed ne Zai kaiki ko? Da Sauri tace Aa nikam bana gayyar Sode, Yusufa ne Zai kaini jiya na sanar dashi,idan danta tsaka ne nikam na yafe,hakanan yaje yasakani a Rami. Inno tunda dai Zuwa jibi Zamuje kibari muje tare kada adaura ma yusuf Nauyi. Aaa nikam bazani daku ba Amadi dan ina tsohuwa Kawai Saina Shiga Cikin Maza.tafiyar ku daban tawa daban.Kuma yusufa yaron kirki shine yace Zai kaini bawani Nauyi kawai nadanje Mu gaisa Kwana biyu ne nadawo. Toh inno ba damuwa Allah ya tsare Hanya bari nafita nayo miki tsaraba yar kadan. Allah yamaka Albarka Amadina Saukin kan Nan naka A Nono kasha, Shikuwa Yazeed Chan yabiyo dangin uwarshi dan ba fatima yabiyo ba itama Akwai Saukin kai. dariya Mamy tayi ta tashi tabar wajen yayin da Abba yafita yimata Siyayya. Atare Abba da Yusuf Suka shigo bai wani zaunaba yace inno tafito.fita tayi Su mamy namata rakiya har saida motarsu tafita tukun Suka koma Ciki.

Page...41/42
Chapter 39 · 0% Book details